Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 23

Sponsored Links

23 & 24

_This novel is for sale karki karanta in baki biyaba_

_in kinason this novel, xaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

Related Articles

_you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_

 

 

Ware manyan fararen eyes dinshi yayi yana wani irin cute smile yace “Mami” daidai lokacin sauran mutanen duk suka iso sukai turus ganinshi tsaye yana kallon Mami dasu dasuka karaso wajen, dan duhun data gani dan sunyi blocking ray din rana dayake shigowa ta kofan yasa ahankali tadan leko da kanta daga bayanshi, mutanen data gani yasa da sauri ta komar da kanta bayanshi ta labe.

Sake zaro ido Aadil yayi sosai ya kalli Aabid dayay shiru yana kallonshi kaman yanda kowa na dakin ke kallonshi yanda yay mugun butu butu, wandon jikinshi kaman an kwaba kasa akai, kafarnan da babu ko takalmi ajiki tai busu busu, shimin jikinshi ma tai datti idanunshi sunyi suntum sunyi wani iri alamun yaci kuka, fashewa dawani irin Kuka Mami tayi ta shigo dakin da sauri tayo kanshi tace “Aadil, my baby” budema Mami hannu yayi yana wani irin jumping yana murna kaman dan yaro. “oyoyo Mami, oyoyo Mami, oyoyo Mami na” tana karasowa gabanshi yawani irin fadajikinta ya kankameta yana tsalle da kafa hakan ya bayyanar da Hamida dake labe abayanshi ta sunnar dakai kasa tama rasa ma me zatayi har wani soshe soshe take, kallon ta Mami da duka kowa na dakin suke yi barin ma Aabid dayaji gabaki daya numfashin shi ya tsaya chak, Cikin wata irin murya yace “Amatullah” da sauri ta dago kanta ta kalli direction din da aka kira sunanta daidai lokacin Aadil yasaki Mami shima yajuyo cike da murna yace “Mami look at Hamida, my wife” kallon Aabid Hamida tayi saikuma ta kalli Aadil dayay magana yanzun nan wani irin faduwa gabanta yayi bana wasa ba dan bambamcin da ayanzu tagani ajikinsu shine daya tsaf tsaf yake yaci shadda gizna kanshi sanye da hula tangaran, shaddar jikinshi har wani irin kyalli yake yana walkiya sai dayan kuma wanda yake daka daka yana sanye da singlet da dogon wando amma kamaninsu daya tsaf, kasa kallon sauran manyan mazan dakin tayi da tsohon dake sanye da glsass yana rike dayar Sanda tasake sunnar dakai tahade hannayenta dake wani irin bari tana murzawa da sauri da sauri tana numfashi sama sama. Sakin Mami Aadil yayi yaje dawani irin gudu yafada jikin Aabid batare daya lura da yanayin dayake ciki ba yaja hanunshi yace “come, come and talk to My Hamida Bid” yaja hanunshi yakawo shi gaban Hamida da kanta ke kasa har lokacin tana murza hannuwanta yace “Bid see my Hamida” yasaki Bid yajuya da sauri ya kalli Mami daketa binshi da kallo kaman zata hadiyeshi da so yace “Mami see Hamida my wife” da gudu yay wurin Baffa yafada jikinshi wani irin murmushi tsohon yayi ya shafa kanshi yace “Hassan” da sauri ya dago kanshi yana turamai baki a shagwabe yace “Am Aadil grandfather not Hassan” sake bubbude manyan idanunshi yayi yakama hanun Baffan yace “zokaga My Hamida Baffa” da sauri yakawo grandfather wajen, sanan yakoma yana wani irin tsalle yana kallon Abie da idanunshi sukai jajir yanamai wani irin murmushi kaman ya cinyeshi da so yace “Abie come and see my Hamidaaa” yaja hanun Abie yakaishi wurin kafin yakoma ya kwaso duka Uncles dinshi yakaisu gaban Hamida sanan ya tsaya shima kusa da Aabid yana kallon Hamidan da duk suka tsaya suna kallonta babu wanda yay magana cikinsu yana murmushi yace “Bid u see my Hamida, she’s my Hamida” wani irin murza hanunwanta Hamida take jikinta nawani rawa, murmushi Mami tayi tace “baiwar Allah a ina kikaga Aadil?” ahankali tadago kanta ta kallesu, wani irin jiri tafara gani yanda duk suke kallonta bakinta har rawa yake tana nishi sama sama tace “i…ina…na…w…wun…” batakarasa gaisuwan ba tai wani irin baya a sume dan kwalin ta data lulluba dashi tai daurin ta wuya ya xame yay kasa arude Aabid ya mika hannu zai tarota yace “Amatullah! ” arude Aadil yamika hanunshi zai tarota shima yace “my Hamida” da sauri Aabid yatarota Aadil ya tsugunna ya dafa kafadar Aabid yana kallonta yasaki kuka yana kallon fuskarta yace “wat happen to her Bid?” dagokai Aabid yayi yace “mutafi da ita gida Mami” da sauri Abie yace “munsan tane da zamu kwasheta mutafi da ita gida?” makemai kafada Aadil yayi yana goge kwallan dayake hakan yasa Baffa yace “muje akira likita yadubata koba komi ga Aadil nan yasaba da ita, daga gani ita ta taimake shi, kumuje, yaka Aadil” zuwa wurinshi Aadil yayi yana waigen Hamida da Aabid yadaga, Baffa yarike mai hannu duk suka dunguma suka fita daga wajen, saida suka salami su inspecta sanan suka shiga mota sai gida.

 

Wani hadadden daki Aabid ya shimfidar da ita kan makeken gadon dake dakin yana kallon fuskarta, tsugunnawa Aadil yayi gefen gadon yana kallonta shima idanunshi yay jajir, ahankali Aabid yajuyo da kanshi yana kallon yanda Aadil ke kallonta yana leka fuskarta, runtse idanunshi yayi da karfi yanajin ciwo aranshi sosai, daidai lokacin Mami ta shigo dakin karasawa tayi gaban gadon ta zauna ata saitin kafafun Hamidan tana kallon fuskarta tace “ga Dr nan zuwa ya dubata Baba yakira shi, Aabid stay with her karta tashi bakowa” ta kalli Aadil dake wani irin kallonta tamikamai hannu tana murmushi tace “come Aadil, muje kai wanka and change this cloth, kaima Dr zai dubaka inyazo duba friend dinka” make mata kafada yayi yana hararanta a shagwabe yace “she’s my wife” shiru Mami tayi tana kallonshi saikuma tai murmushi tace “naji, muje kayi wankan to kafin kafito nahada maka abinci” tashi yayi ahankali kanshi narawa yana kallon Hamidan tashi itama Mami tayi taja bargo ta lullubeta dashi tarike hanun Aadil suka fice suka rufo kofan, wani irin runtse ido Aabid yayi yafuzar da iska kafin yadaura hanunshi kan zuciyarshi yana dukan zuciyarshi yay hakan kusan na 2min sanan yadawo daidai, zama yayi agefen gadon yay shiru yana wani irin kallon fuskarta, dawani irin murya mai rauni sosai yace “tayaya kika hadu da brother na Jewel? I’m the one for you Amatullah” yay shiru yana kallon fuskarta, knocking da akayi yasa yatashi yay wurin kofan bude kofan yayi Dr ne da Baffa suka shigo dakin, Baffa yace “yauwa gatachan likita adubata” karasawa Dr yayi bakin gado yaduba ta sanan yaciro drip daga katon jakan hanunshi yamata fixing yay allura aciki wurin 15 minutes yabata akanta sanan yajuyo ya kalli Baffa yace “fever ne kawai, i guess tsoron kune yasta ta suma, yanzu dai komi lpy dazaran drip dinan ya kare aciremata and yanzu dai bacci take zuwa anjima chan haka zata farka” murmushi Baffa yayi yace “masha Allah itace taga jikana ta taimaka mai, muje kadubamin jika” wucewa sukayi suka fita daga dakin Aabid yadawo ya zauna.

Duba Aadil Dr yayi yarubuta magungunan daza asayomai sanan yamai allura da kyar ya yarda akamai, yaci abinci nan wani baccin gajiya da wahala yay gaba dashi shima.

 

 

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button