Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 26

Sponsored Links

26….

Agaban wani babban club Aabid yay parking yabude mota yafito kanshi harwani irin zafi yakemai kaman zai tarwatse tsabagen bacin ran dayake ciki ya juya ya shiga ciki, gaban counter yaje ya zauna ya kalli waiter dake aiki a wurin yana kokarin serving wasu samari dake kallonshi yace “meza akawo ma Sir?” dan bude ido yayi kadan ya kalleshi kafin ahankali yace “rum” da sauri guy din yadauko wani kwalba yabude yazuba awani dan karamin kofi zai mikomai, hararanshi Aabid yayi da jajayen idanunshi kaman wuta yace “give me the whole bottle” mikamai bottle din yayi ya fizge da sauri ya kafa abaki ya kurba yana yatsine fuska yacigaba dasha saida yay kusan rabin goran sanan ya janye daga bakinshi yana zaro manya manyan idanunshi kanshi kaman zai fashe tsabagen chajin daya dauka, da kyar yay relaxing bayanshi ajikin kujeran ya lumshe ido yakafa goran rum din abaki yana tunane tunane.

_Asalin su_

Related Articles

Alhaji Muhammadu Gambo Sawaba (Baffa) shararren business man ne mai kirki bana wasaba, ga taimakon mutane, talaka, marayu da mabukata, babu inda zaka shiga afadin garin kano ka ambaci sunanshi daba’a sanshi ba, matanshi biyu a duniya Rukayya da Maimuna, Rukayya itace ta haifi yaranshi maza guda uku, sai Maimuna wacce itace ta haifi Mami da Big Mum, yarane dasuka taso cikin gata da kulawa kome sukeso shi mahaifinsu ke musu kansu ahade. Kullum akwai direban dake kaisu school yaje yadauko su, lokacin islamiyya ma yakaisu yadauko su.

Kafin mahaifiyarshi ta rasu, akwai lokaci ta tattaro yinata yinata ta dawo birni gidanshi da zama tareda wani marayan yaron makwabcinta a kauye mai suna Abdullahi (Abie), Abdallahi yarone mai natsuwa da hankali wanda akalla zai girmi babban dan Baffa Suleman da shekara daya ko biyu. Tunda tadawo gidan da zama da Abdullahi ta damkama Baffa shi tacemai tanaso yarikeshi amatsayin danshi, gashinan amana, iyayen shi sun rasu, karya bambamtashi dasu Sulemanu, tabashi shine sabida koda tafadi ta mutu tasan yana hanunshi da zama, Baffa baimata musu ko jayayya ba ya karbi yaron dan yaron badai natsuwaba, nan Suleman da Abdullahi suka shaku suka zama abokan juna suna zuwa makaranta tare both boko da islamiyya dudda sun fishi aji.

Bayan wasu yan shekaru sun gama makaranta alokacin Baffa kuma yanso yay retire saiya daura Suleman baban daddanshi shugaban kampanin shi duka ukun, yasa sauran yaranshi maza biyu da Abdullahi duk a kampanin yabasu office suna aiki ana biyan su duk karshen wata makudan kudi, abin bakaramin ciwo yama Abdullahi ba yaso ace shine zai Baffa yabama shugaban kampanin dan yafi Suleman kai a business, banda haka yanada mugun sha’awan yaganshi yazama shugaban kampani, hakanan ya tattara ya watsar da zancen amma abin na nan ranshi ras duk idan yatuna har kuka yakeyi a boye yace wato sabida shi ba danshi bane saisa baibashi shugaban kampanin shiba ko bakomi shima zaiyi kudi wataran, ana haka wani irin soyayya ya kullu tsakanin Abdullahi da Mami bana wasaba, Allah ya dauramai wani irin soyayyan Mami bana wasaba.

Akwai ranan da Baffa yay order wasu hadaddun motoci toyota camry alokacin ana yayyin su yabama duka yaran nashi daidai as end of the year prayer gift amma banda Abdullahi yacemai shi tashi bata isoba, kuma harga Allah bata iso bane dan Baffa yaso yay surprising dinshi ne yatabaji yana hira da Suleman yacema Suleman shi yanason babban mota arayuwan shi jeep na burgeshi hakan yasa Baffa yaso yay surprising nashi kodan jarumtar shi a kampani yabashi shi jeep amma sai tashi bata isoba dan ba’a gama yima motar custom duty ba harsai next week, nan fa bayan komi yadan lafa Abdallahi yasaci hanya yafita daga gidan yatafi kampanin su yadinga kuka yanajin bakin ciki sosai yana zagin rashin kudi da zama a karkashin wasu, dafashi yaji anyi da sauri yadago kanshi wani inyamurin gateman dinsu ne yagani yana sanye da hadadden suit baki, murmushi yamai yace “kasoma gane basu sonka ko Sir? Kawai amfani suke da talent dinka suna making money a kampanin nan” da sauri ya kalleshi yace “ya akayi ka sani?” murmushi yayi ya kalli ko ina na wurin kafin yaciro wata yar Kati daga aljihun wandonshi ya mikamai yace “inhar kanaso yau yau dinan rayuwarka ta chanza from this poor man dakekeci a gindin wasu kana musu boyi boyi kaima kai kudin bala’i, kudin da sunema zasu rokeka, inhar kanason money and fame, kanason dukiya, kanaso kafada aji kahana ahanu, kanaso kadawo yaro mai gari a hannu to ka kira number nan da kagani ajikin katin nan, Ozo zai biyama bukataun ka, zakai kudin ban mamaki, kudin dasu kansu saisun koma suna rokon ka kudi.

_Manage this guys, nai typing duka ya goge, da kyar na iya nai wanan yanzun nan, gobe kuna bina bashin daya in sha Allah_.
_🌹IN BANI 🌹_

 

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button