Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 28

Sponsored Links

Sallama tai agaban dakin mijin Anty Lami suka bata izinin shiga dakin ta shiga kanta akasa tace “ina wuni Abba” murmushi yayi yace “Hamida kenan tawaje na, zauna kinji abinki” yanuna mata kan kujera, tabe baki Anty Lami tayi tace “wlh bakai zabi me kyau ba indai Hamida ce ta wajen ka Alhaji, wanan miskilan yarinyar kayan haushi kenan, yarinyar nan saita sama ciwon zuciya” “baruwan ki tsakanin uba da ya sai Allah, ya kike kinji y’ata” dan murmushi tayi Anty ta harareta tace “ja’irar banza kawai” sunnar dakai tayi da sauri tace “lpy lau Abba” gyadakai yayi yace “masha Allah, ashe abinda yafaru kenan Allah ya kyauta ya kiyaye gaba amma ke mesa bakima iyayenki explaining ba, tsaya ma menene asalin abinda yafaru ya akayi kika hadu dashi yaron mara lafiyan?” ahankali kanta akasa tace “da ina dawowa daga makaranta yaboyoni, nina tsayama naji tausayinshi ne sabida naga shine yataba taimakana a Lagos dana fada ruwa” da sauri Anty Lami tace “au shine daman?” girgiza kai tayi tace “bashi bane yan biyu ne amma kaman ninsu daya nadauka shine, shi kaman baida hankali ne nace yatafi yaki tafiya yadunga bina yana kuka harnakai gida akofar gida yace min zaisha ruwa na shiga gida na daukomai ina dauka najuyo kawai naganshi abayana ashe yabiyoni ciki, shine na kulle kofa dankar Kaka taganshi tasa Abba koya Faruk yadaken” hararanta Anty Lami tayi tace “kaji wawancin natako Alhaji inda ace tafadi ko Kaka saita bashi wajen kwana inyaso washe gari a nemi gidansu amma tai shiru, waye zaiga kato daga dakin yarshi baiyi tunanin wani abuba incedai bai miki komiba ko?” gyadamata kai yayi ahankali, Anty Lami zata cigaba da mata masifa yadaga mata hannu yace “ya isa haka” , ya kalli Hamidan yace “tun dazu dasafe da mahaifiyar ki takira tafada na shirya naje gidan naku amma lokacin mahaifinki yatafi gidan kaji haka nabishi wajen nan yafara koromin laifuffukan ki, Hamida kema baki kyautawa fisabilillahi ace baki attending lectures, saida aka tura zainab taje department dinki nan yan ajinku sukace rabon dasu ganki harsun manta, Hamida karatun nanfa kanki kikemawa, ina ruwanki da mutane mezasu miki iye?” da sauri Anty Lami tace “su dena kashe kudinsu wlh akanta nafada ma mamanta ai, aure yarinyar nan take bukata bawani abuba, duk wani abinda zai fitar da Hamida waje batason shi itad…” shiru tayi sabida mugun kallon da Alhaji ya mata saanan ya kalli Hamida da kanta ke kasa yace “tashi kije ki kwanta in Allah ya yarda gobe da safe zamu maidake inyaso sai atattauna mu lallaba Kaka tahakura, tashi kije ki kwanta Allah bamu alkahiri” tashi tayi ahankali tace “nagode Abba” tajuya tafita yabita da kallo yana girgiza kai sanan ya kalli Anty Lami data rakata da hararan takaici, yace “ku dena abinda kukeyi yarinyar nan ba itatai kanta ba, Kune iyayenta dole ku nuna mata so ayanda take, sanan kununa mata taso kanta ayanda take, kune zaku bata confidence amma wanan abun dakuke mata saisa kuma batason rabanku zakiga saidai ta gwammace ta zauna ita kadai kokuma ki ganta da Ihsan, kokuma ta nemi wani irinta wanda halin su yaso yazama daya, addu’a zaku mata wata rana sai labari” ahankali Anty Lami tace “hakane nagode Alhaji” murmushi yamata yace “bakomi Hamida y’ata ce kaman su Ra’is da Ra’yyan” murmushi tayi nan suka cigaba da hira.

Koda takoma daki dadduma tahau tai salla sanan tai shafa’i da wuturi tajawo AL Qur’ani ta karanta danyau bata karantaba sai wuraren sha daya sanan ta rufe ta ijiye ta kwanta akan dadduman tai shiru tana kallon yatsunta tanajin wani irin sosai, ahankali tafara kirga yatsun kaman yanda Aadil yakeyi kafin takai hanun saman kan idanunta tafashe da kuka sosai da ita kanta batasan kona menene ba but deep down jitake tanaso ta ganshi koda sau dayane, tasan hala yanzu yatashi yana nemanta yana kuka, sosai tafashe kukan tawani irin lankwashe har bacci ya kwashe ta ahaka.

 

Related Articles

Bubbugamai kafada da akeyi yasa yabude idanunshi ahankali kanshi namai wani irin masifaffen ciwo ya kalli waiterncikin muryan maye da bacci yace “wat?” ahankali yace “sorry Sir natadaka, we’ve closed this is 1 nadare, you have to go zamu rufe” wani irin dogon tsaki yaja yana bude idanunshi da kyar dake neman rufewa yace “nawane bill dina” “56,000 naira Sir, 3 bottle of rum kasha” da kyar ya sauka dagakan kujeran dayake kai zaune yatura hanunshi a aljihu yaciro wallet dinshi yazaro ATM card dinshi ya jefamai a fuska yakara kife kanshi saka katin a pos yayi ya mikomai yace “your pin sir” saka pin dinshi yayi kanshi na juyawa mutumin ya cire kudin shi sanna ya mikamai atm card din da slip ya karbi ATM card din yafara tafiya yana layi da kyar yakai parking space ya zube a wurin yana amai saida yayi yagama sanan yatashi yana tangadi yatashi ya xaga wajen mazaunin driver yabude ya shiga ya kunna motar.

 

Yaja yana bubbuge ido da kyar da kyar yakai gida yay horn aka budemai gate ya shiga yay parking yakai kusan minti biyar zaune sanan yafito ya rufe motar yay wurin tap din dake wajen yabude ya wanke fuskarshi sanan ya kuskure bakinshi yarufe tap din yazaro handkerchief daga aljihun shi yana goge fuskarshi tass sanan yawuce cikin gida yana tafiya ahankali yabude palonsu ya shiga, hayaniya yaji sosai. “kuka yaketamin kan ina Hamida, daga nafadi mai gaskiya nace tatafi gida shine yafara convulsing” taku yaji daidai lokacin Abie da Suleman dake sanye da jallabiya sun fito rike da Aadil dake wani irin convulsing sosai kumfa nafita daga bakinshi idanunshi suna kakkafewa kaman wanda ke shirin mutuwa, Abie nafadin. “innalillahi wa innailaihi raji’un, innalillahi wa innailaihi raji’un, Hassan, Hassan” Mami na kuka sosai, duk wani mayen dayake ciki wartsakewa yayi ya kalli Mami data fito da gudu tana kokarin saka hijabin data riko a hannu harta na neman fadi kasa, arude Abie yace “Sulemanu tsaya kaga kar yaron nan yafadi daga hanunmu ya karye, tsaya mu kwantar da shi nan akan kujera tukunna he’s running serious temperature jikinshi kaman wuta” kwantar dashi sukai akan kujera amma tsabagen yanda jikinshi kewani irin jijjiga uncomfortably yana bankarewa yasa yayo kasa da sauri suka tareshi suka kwantar dashi akasa, Suleman yaciremai riga suka taru sunamai fifita arude, fashewa sosai Mami tayi takama fuskarshi tana jijigashi tace “Aadil, Aadil haka zakamin? Eh, haba Aadil dan Allah kamin adalci, Aadil, Aadil dina tashi, dan girman Allah katashi har gidan damuka kai yarinyar zan kaika kaji Aadil din Mami, Aadil” Mami takirashi a mugun raunane tana wani irin kuka, jiyayi kafafunshi sun kasa daukanshi wani irin fadi zaune yayi yadafa hanun kujera yana kallon Aadil dake convulsing jikinshi duk shatin belt din dukan dayamai dazu.
_🌹IN BANI 🌹_

 

 

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button