Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 24

Sponsored Links

Saida yay bacci sanan Mami tarufa mai bargo takashe wutan dakin nasu tarage karfin Ac tafito, dakin da Hamida take tawuce ahankali tabude kofan har lokacin Aabid na zaune agefen gadon yazuba mata ido, budewan kofan dayaji yasa yadago kai, murmushi Mami ta sakinmai takaraso ta zauna kusada shi, ahankali yadaura kanshi kan kafadarta ya sauke ajiyar zuciya, shafa kanshi Mami tayi tace “menene Son?” dan murmushin yake ya kakalo mata yace “babu komi Mami na” dagashi tai daga kafadarta ta kalli fuskarshi jin yanda yay maganan danta tabbatar da abinda ke damun shi, lumshe ido yayi da sauri dan yasan tsaf Mami zata gano da damuwa a idanunshi, ahankali kira sunanshi. “Aabid” bude idanunshi yayi ya kalleta, nunamai Hamida tayi da ido tace “you called her Amatullah dazu kasanta ne daman?” shiru yayi yana kallon fuskar Mami kaman bazaice komiba saikuma yace “eh nasanta a Lagos nataba ganinta tafada ruwa nacirota nakaita asibiti daganan bankara ganinta ba saiyau” murmushi Mami tayi tace “Allah sarki, hala saisa itama ta taimaki Aadil maybe tazaci kaine” murmushi tasakeyi tasake jan kumatun shi tace “tashi muje kaci abinci idan ta farka sai a gaggaisa da kyau amata godiya saimu maidata gidansu ko” gyadama Mami kai yayi yatashi suka fita daga dakin, dining ta kaishi tazubamai abincin kadan ya iyaci sanan yakoma ya zauna a falon yana kallon CNN amma gabaki daya hankalinshi nakan dakin da Hamida keciki.

 

Kiran sallan azahar dayaji yasa yatashi yafita masallaci hakanan yakejinshi wani iri yarasa mesa kalman da Aadil yafada saimai yawo yake a kunne. “Hamida my wife” runtse ido yayi da karfi da kyar ya lallaba ya shiga masallaci yaje yay salla sanan yadawo ya bude kofar dakin datake har lokacin bacci take, maida kofar yayi yarufe yakoma kan kujera ya zauna har akai la’asar yasake dawowa ya lekata har lokacin bacci take yakoma kan dogon kujera yasake zama yana chanza tasha zuwa tashan kwallo.

Related Articles

Bude kofan da akayi yasa yadago kai Aadil ne ke saukowa yana sanye da plain white t-shirt dakuma wani black 3quater sai uban kamshi yake yay wani irin kyau da inka kallai saika kara, hanunshi rike da manya manyan chocolate guda biyu acikin ledan su, Aabid daya gani azaune yasa ya washe baki yataho da sauri yana tsalle tsalle, shiru Aabid yayi yana kallonshi shi kanshi baisan meka damun shi ba hakanan yaji yanajin haushin shi bana wasaba yakasa manta kalman Hamida my wife dayafada aranshi, inda dane all this tsalle tsallen dayake yi idan yaganshi yanajin dadi amma yau sosai yakejin haushin shi, fadowa jikinshi da Aadil din yayi yasa yadan fuzar da iska yatureshi kadan, dago kai Aadil yayi yaleka fuskarshi yana murmushi, dan murmushin yake Aabid ya sakan mishi ya lumshe ido batare dayacemai komiba, hakan yasa da sauri Aadil ya kalli chocolate din hanunshi dudda ya daukoma kanshi ne da Hamida amma saiya mikamai daya da sauri yace “Bid” dan bude ido Aabid yayi ya kalleshi ya kalli chocolate din dayake mikamai, girgizamai kai yayi yatureshi murya chan kasan makoshi yace “stand up from my body” kin tashi yayi yay shiru yana kara leka fuskanshi kaman maiso gano abinda ke damun shi wani irin tsawa Aabid ya dakamai tareda tureshi da karfi daga jikinshi yace “nace katashi daga kan jikina ko” yay maganan yana tureshi dawani irin fushi yafadi akasa, atsorace Aadil ya kallai dan idan da abinda ya tsana a duniya yakuma kejin tsoro bai wuce tsawa ba, tsaki Aabid yayi cikin fushi yatashi yana kakkabe shaddar jikinshi da Aadil ya yatsine yawuce yafita daga dakin, binshi da kallo Aadil yayi idanunshi nataruwa da kwalla sosai, ahankali ya lankwashe kafa anan kasan falon ya shiga kuka yana share ido yana kallon kofan, kukan shi da Abie yaji yasa ya shigo dakin da sauri dan shigowan shi kenan gidan, karasowa yayi inda yake zaune akasa arude dan kowa nagidan nan ya tsani yaga abu nadamun Aadil yace “menene? Why are you crying” kasa bama Abie amsa yayi sabida yanda Aabid yaturashi kemai ciwo baitaba mai hakaba, da sauri Abie yaciro handkerchief daga aljihun shi ya sharemai bakinshi da fuskarshi yace “wai menene? Why are you crying haka?” kasa magana yayi sai kukan dayake yi sosai, sallama Baffa yayi ya shigo shashin da sauri daidai lokacin itama Mami tafito dan dama wanka take, da sauri Baffa yakaraso yana dogara sanda ya kalli Abie yace “me kuka mishi wai? Yaufa yadawo harkun fara sakashi kuka, dan Allah kome yakeso kudinga mai gobe za’a faramai maganin, daga sokoto mai maganinshi dana kira zaizo” ya zauna akan kujeran dake saitin Aadil din dake kuka sosai yake yadafa kanshi yace “menene? Waya tabamin Hassan iyye?” makemai kafada Aadil yayi cikin kuka yana turomai baki yace “my name is Aadil right Mami” dariya dukansu sukayi harda Baffan yace “dan tselen uwa gadai ubanka nan katambaye shi da aka haifeka Hassan aka yanka rago aka sakama, yanzu dai dena kuka kaji, zomuje mu baga basket ball” yay maganan yana zazzago glass din idanunshi cike da tsokana, Mami murmushi tayi ta tashi ta wuce kitchen dan kawomai fruits din data yankamai ta sakamai a fridge. Makema Baffan kafada yayi yana turo baki yana goge hawaye da bayan hanunshi dayake rike da chocolate da sauri Abie ya karbi chocolate din yace “kawo nan karka tsole idanunka dasu” turoma Abie baki yayi sanan ya kalli Baffan dake kallonshi yana murmushi ya makemai kafada yace “you don’t know how to play basket ball bazan buga dakai ba, i will only play with Bid ko Abie” ya kalli Abie dayay shiru yana kallon d’an nashi feeling wani irin guilt, murmushi Abie yayi ya mikamai chocolate din yace “hakane, nabude ma chocolate din?” gyadamai kai yayi ahankali hakan yasa Abie yabude mai daya ya mikamai, karba yayi yakai bakinshi ya gutsura yanaci kallonshi Abie yayi kafin yatashi ya shafa kanshi yawuce yafita dan yanda yakeji yasa bazaima iya shiga gidan ba yawuce ya shiga motarshi yafita daga gidan, binshi Baffa yay da kallo ganin damuwa akan fuskarshi amma bai kawo komiba dan yasan damuwan bazai wuce ta Aadil bace, taba keyan Aadil yayi hakan yasa Aadil yajuyo ya kalleshi, gefenshi Baffa ya nunamai hakan yasa ya murgudamai baki sanan yatashi ahankali ya zauna a kusa dashi, hannu Baffa yamika mai yace “bazaka sammin ba” wanda yakeci ya mikamai hakan yasa Baffa ya makemai kafada kaman yanda yakema mutane yace “ni kabani wanchan sabon shi nakeso” makemai kafada Aadil yayi sosai yace “this one is for Hamida my wife” zaro ido Baffa yayi cikeda wasa yace “wife kuma Hassan” gyadamai kai yayi da sauri yana washe baki yace “yes i will marry her, she will be my wifeee, just like Abie and Mami” yakarashe maganan awani irin sangarce yana murmushi yana fari da ido sosai, shiru Baffa yayi yana kallonshi yama kasa magana tashi Aadil yayi daga kan kujeran yasa chocolate din a bakinshi ya ballomai yakamo hanunshi yasaka mai aciki yace “bye bye Oldman, lemme go and see My Hamida, Mami” ya kwalama Mami kira kaman zaiyi kuka yace “my fruits” fitowa Mami tayi daga kitchen tamikamai bowl dake cike da sliced fruits dasukai sanyi sosai da fork ya karba da gudu yana tsalle tsalle yay hanyar dakin Hamida Baffa yabishi da kallo har lokacin maganan da Aadil din yayi na ringing akanshi saikuma yay murmushi yaciro wayarshi daga aljihu yatashi yana dogara sandarshi yafice daga dakin yaje rumfan da akamai musamman ta zama ya zauna yay dailing wata number.

Tura kofan yayi ya shiga dakin yana rike da chocolate din gam da bowl din fruits din, hada ido yayi da Hamida da bude idanunta kenan, da sauri yatura kofan yarufe yazo wajen gadon yana tsalle ya ijiye fruits din agefe, wani irin farin ciki yakeji idan yaga fuskarta bana wasaba, ahankali ta dafe kanta ta tashi ta zauna da kyar tana kallon karin ruwan dake hanunta wanda kadan kadan yake shiga jikinta, wani irin tsalle yayi yafado kan gadon yana leka fuskarta yanda ta runtse ido, dawani irin murya chan kasa yace “My Hamida” ahankali tabude idanunta ta daura akanshi tai shiru tana kallonshi yanda yay wani irin kyau sai kamshi yakeyi farin t-shirt din jikinshi yakamashi daidaishi, murmushi yamata yamika mata sabon chocolate din hanunshi da sauri yace “take” sake lumshe ido tayi tana kara tuna irinshi biyu tagani fa dazu, ganin tai shiru taki karba ta shareshi kuma taki bude ido yasa yafada jikinta kaman zaiyi kuka yace “Hamida my wife wat is it? Are you sick?” da sauri ta bude idanunta ta shiga tureshi da hanunta daya mai lafiya cikin yar siririyan muryanta tace “kadagani” daidai lokacin aka bude kofa aka shigo, da sauri ta dago kanta tana tureshi sukai ido biyu da Aabid da shima ya chanza kaya zuwa black 3quater da white long-sleeve t-shirt dan hakanan yaji yanadan jin sanyi sanyi kaman zaiyi zazzabi wani irin kallo ya watsa musu yana tsaye a wurin yay folding hand dinshi akirji hakan yasa gabanta yawani irin fadi da hannu tasake tureshi tace “ka dagani Aadil” make mata kafada yayi ahankali yana turo baki yace “u are angry with me Hamida my wife” da sauri bakinta har rawa yake tace “a’a am not nika dagani” da sauri yadago kanshi ya kalli fuskarta yana wani irin murmushi yana kallonta yace “yay am happy my wife, take my chocolate” yay maganan yana ciro chocolate din dake bakinshi yakai saitin bakinta yana ware manyan eyes dinshi dawani irin excitement yace “d chocolate is very sweet Hamida my wife” yakai bakinta, kin bude bakin tayi ta kawad da hanunshi, kaman zaiyi kuka ya make mata kafada. “oh’oh” yasake kaiwa bakinta da sauri, kin karba tayi hakan yasa yasaki kuka yafada jikinta zai kankameta, wani irin fizgoshi akayi a zuciye da sauri ya juyo da kanshi hada ido yayi da Aabid da idanunshi sukai ja, kafin ma yace wani abu Aabid yawani irin fizgoshi kaman zai karyashi ita kanta Hamidan saida ta tsorota yawani irin jashi yafitar dashi daga dakin yabugo mata kofa yay dakinsu dashi, bude kofar dakinsu yay azuciye yawani irin turashi da duka karfinshi saura kadan ya buge kanshi a gado yadafa bangon yana haki, da sauri yadago kai ya kalli Aabid din daya mayar da kofa ya rufe yanamai wani irin mugun kallo, yayo kanshi a zuciye yana tattare hanun riganshi sama hakan yasa Aadil yakoma jikin bango a tsorace idanunshi yataru da hawaye sosai yana kallon Aabid din da mugun mamaki dudda baida Ishashen hankali hakanan saiyake ganin Aabid kaman bashiba yau, dan koda wasa ko amafarki Aabid baitaba koda dauremai fuska ba balle ya hankadashi haka cikeda tsana.

 

Wani irin tsayawa Aabid yayi agabanshi yay folding hanunshi akirji yana wani irin kallonshi, ahankali Aadil ya saukar da kanshi dake rawa sosai kasa hakanan yaji yana wani irin shakkan Aabid din for the first time in his life, ahankali kanshi na rawa sosai ya matsa ta gefenshi batare dayace komiba yazo zai wuce shi da sauri, wani irin fizgo hanunshi Aabid yayi azuciye yadawo dashi inda yake har saida yabuge bayanshi da bango cikin tsawa yace “where do you think you are going?” sosai idanunshi suka cicciko da hawaye kaman maison kara tantance anya Aabid ne wanan yadan dago kai ya kalleshi ganin shine dai yanamai wani irin mugun kallo yasa ya saukar da kanshi dake rawa sosai kasa cike da tsoro dawata irin murya chan kasa yace “i want to go to Hamida My wife’s place” wani irin fizgoshi Aabid yayi yarikemai wuyan riga yace “karka kara cemata your wife” makemai kafada yayi ahankali atsorace hawaye na gangarowa daga idanunshi yace “i don’t want to stay here, i want to go to Hamida my wife’s place” cikin wani irin bakin zuciya Aabid ya sakeshi yadaura hanunshi kan belt din jikinshi yana kwancewa yana zarowa yana kallonshi yace “karka kara cemata your wife” makemai kafada Aadil yayi hawaye na fita daga idanunshi sosai yace “she’s my wife i will marry her just like Abie and Mam…” wani irin zaulamai belt din Aabid yayi da duka karfinshi cikin fushi sosai yace “karka sake cemata your wife” makemai kafada Aadil yayi yafashe da kuka sosai yana sosa kirjinshi da cinyarshi da belt din yasama sabida azaba da zafi dayaji yace “Hamida is my wife” zaulamai belt din yayi da shegen zafi hakan yasa yay ihu cikin kuka sosai yana sosa wajen yace “stop beating me Bid” shima Aabid cikin ihu yace “kaima stop calling her your wife and karka kara rungumeta, she’s my Jewel” Make mai kafada Aadil yayi cikin kuka sosai yace “Hamida is my wife” wani irin mari Aabid ya daukeshi dashi da saida yaga wuta da jiri cikin wani irin layi idanunshi najuyawa sosai yace “she’s my wife” bugashi da bango Aabid yayi ya shiga dukanshi sosai yace “kai mahaukaci ne, Aadil kai mahaukaci ne bazaka taba aure ba danba abinda kasani kanajina, u are mentally unstable, kai pagal ne stay away from my Jewel kanajina mahaukaci” makemai kafada Aadil yayi yana fitar da numfashin da kyar yana kuka sosai yace “she’s my wife” belt din daya yar yakara dauka ya shiga dukanshi sosai kaman uba da d’a yace “kai mahaukaci ne Aadil bakada lafiya bazaka taba auren ta ba, bakada any use a dis life, stop touching and hugging my Jewel, stop calling my Jewel your wife inba hakaba sainai ma shegen duka” make mai kafada yayi wanan karan yakasa magana tsabagen kirban shi da Aabid keyi, hakan yasa Aabid yajawo belt ya shiga dukanshi sosai Aadil na ihu yana kuka sosai yana rirrikemai riga yanaso ya rungumeshi. “stop beating me Bid, stop beating me please” bude kofan akayi Mami ta shigo ganin yanda Aabid ke dukan Aadil da belt yasa tazo wajen da mugun gudu. “Aabid, subhanallahi, innalillahi wa innailaihi raji’un, Aabid zaka kashe dan uwanka ne” tarike mai kafada tana kokarin rike belt din hanunshi tureta yayi ta hanyar fizge kafadarshi yacigaba da dukanshi Aadil dake ihu daidai lokacin Abie da Baffa sun shigo sabida hayaniya da salatin Mami dasukaji, wani irin fizgoshi Abie yayi yace “Aabid kana hauka ne?” fizge kanshi yayi daga hannun Abie yacillar da belt din yafara dukanshi da hannu Abie najanshi amma dukanshi yake yana neman gagaran Abie tsabagen karfi, wani irin tsawa Baffa yadakamai ganin numfashi na neman gagaran Aadil din, da gudu Mami ta daga Aadil din ta rungume tace “ka dakemu tare kaji Aabid” hannu Aabid yadaga zaikara kaima Aadil din duka dudda Abie na rikeshi Baffa ya daga sandarshi ya rafkamai akafa.

 

_Slm Fanmily_
_Daga yanzu typing system dina will change, zan dinga skipping a day but duk ranan posting zan dinga yin 2pages in sha Allah_.

_Thank you_
_🌹IN BANI 🌹_

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button