In Bani 34
Da asuban fari Kaka ta tashi tana mitsike ido tana salatin annabi ta wuce bandaki tayo abunda zatayi tafito daure da alwala tadau charbin ta tasaka hijabi tahau kan sallaya ta kabbarta salla, saida gari yay haske sanan ta sallame ta ijiye hijabin kan kujera tafito tabude kofar sasan ta tafita tai dayan sasan indata tarar da Hamida da Zainab suna sharan compound din, Hamida ce tafara gaisheta tana murmushi tana sunnar dakai. “ina kwana Kaka” ballamata harara Kaka tayi tace “rike gaisuwar ki munafika” dariya Zainab tayi itama tace “ina kwana Kaka” kallon Zainab din Kaka tayi yanda takema Hamida dariya tana washe baki tace “ke dalla chan rufe mana wanan bakin mai kama da rubabben shadda” wani irin ware manyan idanunta Hamida tayi kaman ba itaba tawani irin fashe da dariya tana kallon Zainab din tana yatsine hanci tace “hmmm saisa naji wari” wani irin gudu Zainab din tayi tabita, da gudu Hamida ta saki tsintsiyar akasa tana ihu tana dariya tana kwalama Mama kira Kaka tace “Allah ya wurgo ubanku gidan yaga abinda kukemai kulllum agida inya tafi masallaci” tasakai ta shige falon tana Kwalama Mama kira, fitowa Mama tayi daga dakinta rike da charbi tace “ina kwana Umma” daure fuska Kaka tayi ita a dole fushi take tace “lau, ba gaisuwar ki nazo najiba nazone nafada miki ki kira Lami tazo ita da mijinta, sanan kuyi hadadden girki, baki zanyi da sassafen nan, girki mai rai da lafiya fa” ahankali tace “to Umma” juyawa tayi zata fita saikuma tajuyo tace “ina Ihsan banganta ba?” “tana daki ne, tari take da mura shine nace kartai sharan” “maganin shan ruwan sanyi, babu randa bana wakar subar shan ruwan sanyi amma saisu nuna nai kadan, anjima tazo ta amshi zuma da tafarnuwa awajena tasha zatasami sauki, tarin zai lafa” ahankali Mama tace “to Umma angode” yaye labulen tayi tafice daidai Baba na bude gate yana shigowa sanye da farin jallabiya da hula akanshi da sauri su Hamida suka gaidashi amsasu yayi da sauri ganin Kaka yasa yataho dadan saurin shi yasamu ya lallabata, shan mur Kaka tayi ta dauke kai kaman bata ganshi ba tai hanyar Sasan ta, da sauri ya cin mata yasha gabanta cikeda damuwa kaman zai mata kuka yace “haba Umma inata gaidake kinki amsani wai har yanzu baki huce ba eh?” hararanshi tayi tace “gafara kabani sasana zan shiga ko” matsawa yayi hakan yasa tabude kofa ta shiga yabi bayanta da sauri ta shiga falo ta zauna akan kujera da sauri ya zauna kusa da ita ya daura kanshi akan kafarta ko kadan ya tsani yaga Kaka na bata rai dudda yasan ba’a mata komai kawai itake kirkiro rigima da kanta amma baya taba barinta ta dinga fushi for long, ta riga ta tsufa d fact dat she’s very strong bai zama guarantee na cewa wani ciwon bazai kamata ba saisa yake lallabata dan yawan fushi zai iya jawo mata hawan jini ko ciwon zuciya, ahankali yace “kiyakuri Umma na bazan kara ja dakome zaki ceba, kowani hukunci zaki yanke kinyi daidai bazan kara cewa wani abuba Umma kinji” sosai zuciyarta yay sanyi amma saita daure tace “kai alkawari bazaka kara ja da hukunci naba?” da sauri ya daga kanshi jintamai magana yace “eh Umma kome kikafada daga yanzu hakan take kuma haka za’a bita bazan kara cewa wani abuba” kallonshi tayi saikuma ta kece da kuka taja bakin zaninta ta daura akan fuskanta tana share hawaye, arude yace “dan girman Allah Umma kidena kuka, wlh, wlh, wlh Umma kinji na rantse miki bazan kara, bazan kara ja da maganan kiba ke zaki dinga yanke hukuncin komi daga yanxu” cikin kuka sosai tace “baka sona ka tsaneni Sama’ila gani kake takurama nakeyi dankaga kai kadan karagemin aduniya baban Faruku mai sona maijin maganata ya rasu, wayyo Allah na, kaduba fa da baki daya nacemai yasaki shegiyar matar nan nashi Maman Faruku ya saketa amma kaiko kullum nunamin kake ban isa dakaiba, banjin dadinka ko kadan, agaban matarka, yayanka, kai agaban duk duniya ma kake nunawa niba komi bace agareka ba, nasan inda ace kasan guban dazaka sakamin a abinci naci namutu da tuni kasamin naci na mutu danka gaji da wahalata da matsalata so kake ka huta” “innalillahi wa innailaihi raji’un Umma, Umma dan yarasullullahi kiyakuri wlh bazan taba iya kashe uwata ba uwardata haifeni ba” tadan hujin yatsun data daura akan fuskarta take kallonshi yanda taga yay kaman zaiyi kuka dukya tsure yasa tai wani irin murmushi jin dadi aranta dan tasan ko yaji abinda ta aikata anjima bazaice kalaba sabida fargaban karta sake irin abin nan, share hawayen tayi tass tass tai tagumi tai shiru tana kallon sama kaman wacce akama rasuwa, ahankali yace “Umma, Ummana dan Allah ki kalleni” kallonshi tayi sai shar saiga hawaye, rudewa yayi gwanin ban tausayi yatashi tsaye daga kan kujeran yasa hannu a aljihu yaciro yan bandir din dari biyar biyar da wani makocinshi yanzun nan bayan sallan asuba yabiyashi kudin kaji guda dari daya saya, yadaura mata kudin acinya yace “gashi Umma sukenan gareni yau, nabaki kome zakiyi dasu kiyi amma dan Allah kiyakuri kinji” washe baki tayi kaman ba itace tagama kukan ba tadaga kudin tana kallo tace “kai Sama’ila wayan nan sababbin kudaden fa nawane?” “dubu dari da hamsin ne” murmushi tayi sosai tace “a’a baza ai hakaba, bandai dubu hamsin din saman kaika rike darin ko, Allah ampana” tai maganan tana kwance robalin ta kirgo dubu hamsin ta cire ta tura a lalita sanan ta mikamai sauran tana murmushi tace “Allah shi maka albarka, Allah karo kasuwa agidan kaji, Allah ya tsaremin kai yakaremin kai daga shairin mahassada kaji Sama’ila Sama’iloli yaci kafan bunsuru yahana Kaka bacci” murmushi yayi sosai aranshi yace Umma da son kudi yarasa uban me zatai da kudi haka hatta lipton shiyake kawomata ko tsinke bata siyafa amma sai masifar son kudi, “kanajina” da sauri ya kalleta tace “yau bazaka fita gidan kaji da wuri ba zamuyi manya manyan baki ne” da sauri yace “su waye Umma?” dariya tayi tana ballan goro tace “in sukazo zaka gansu, ka kira Mijin Lami yazo dakuma limamin unguwa, sanan kayoma Haleematu cefane nace ta girka haddden abinci wanda zamu tarbi bakin dashi, ka siyo lemukan kwali kaji” ahankali yana kallonta yace “to Umma shikenan” murmushi tayi sosai tana washe baki tace “yauwa dan albarka na, tashi katafi tun jiya banga Faruku ba baizo yasha furan shiba shegen goran” dariya yadanyi yace “kina kewan abokin fadan nakine kenan anjiman nan nasan zaizo wurinki” dariya Kaka tayi tace “wanan shegen goran ne zanyi wani kewan shi Allah kyauta, nidai yi sauri kaje kayi abubuwan dana saka” to yace yafice yanama kiran Abban Ra’is sukace suna hanya dan Mama takira, anty Lami na zuwa itada Mama da yaran su Hamida da Zainab suka fara girkin bakin Kakan, sukuma su Abba suna falo suna hira, wuraren tara da rabi suka gama komi Kaka dataci gayu cikin wani lashin hadari lace best lace dinta kenan tunna aurenta ne, bata saka lace dinan sai occasionally, tashigo kitchen din sai albarka take samusu, bakaramin Mamaki sukayi ba ganin kaka da kayan dan sunsan sai akwai babban abu take sawa, Zainab data gimtse dariyan ta tace “Kaka wlh hadari lace dinan baya miki kyau” dudda ta mata abaya Hamida ta sunnar dakai tana murmushi, Kaka tace “dan ubanki lashin nan ya girmi ubanki, tunna akwatina shegiya yar baka rubabbiyan yarinya kawai” turo baki Zainab tayi tawuce ciki Hamida tabi bayanta sum sum Kaka tabita da kallo.
Kujera taja ta zauna a tsakar gidan, Allah Allah take suzo so kawai take dazaran taji sallama ta shigo dasu, wani almajiri karami ne yabude gate ya shigo da sauri ta tashi tace “kai baki suka aiko ka?” da sauri yace “a’a Hajiya sadakan biyar ko goma nasai omon wanki” wani irin dogon tsaki taja takoma ta zauna sanan ta chusa hannu a lalita tace “zo ungo” tamikamai naira hamsin karba yayi yanata mata addu’a sanan yajuya yafita daga gidan, ba’a wani jimaba wani yaro ya shigo shiru tayi tabuga tagumi batason tasa ranta awanan karan. “Salama Alaykum wai ance ana sallama da masu gidan” da sauri Kaka ta mike tana murmushi sosai ta kwalama Abba kira. “Sama’ila, Sama’ila kufito ku shigomin dasu” fitowa Abba da Abban Ra’is sukayi da sauri Kaka ta nuna musu gate tace “kuna bata musu lokaci tun dazufa sukazo, shashina zaku kawosu” tawuce shashinta sukuma su Abba sukai gate wondering who could bakin Kaka be, bakaramin mamaki sukayiba dasukaga mutanen jiyaba amma duk suka boye mamakin nasu suka gaisa sosai cikin mutunci sanan sukai musu iso. Baffa ne da yaranshi maza uku su sulaiman sai kuma limam dawani amininshi duk sunci manyan fararen kaya suja shigo, ta window Zainab da Hamida da Ihsan suke lekawa sukace su waye wayan nan ita Hamida bama ta ganesu ba wlh hakan yasa suka dinga lekensu har suka shige sasan Kaka.
Zama akayi dayake falon Kaka da girma fes ya daukesu harda wani enough space dazai dau kusan mutane goma ma, gaisuwa akai ta mutunci suka gaishe da Kaka sosai ana raha ana dariya kaman ansan juna nan Anty Lami da Zainab suka gabatar da aban sha da kulolin abinci, ba laifi sunci abincin sosai suka sha lemu sanan aka tattara komi Baffa yabude taro da addu’a ya kalli su Abba yana wani irin murmushi mai nuna tsantsan farin ciki yace “bazan taba mantawa da karamcin ku da alkahirin ku aduniyan nanba, kun taimake ku kun share mana hawaye, ba kowani musulmi zai iya abinda kukayi ba saimai karfin imani da taqwa, kuma inamai tabbatar muku bazamu taba wulakantar muku da yarku ba da izinin Allah, xamu riketa amana sanan ina mai shaida muku da in sha Allah Hassan dinma yakusa samin lafiya yanzu haka zamu faramai na gargajiya ne dazaran yasami lafiya an sallameshi daga asibiti kuma munasa ran za’a dace in sha Allahu, yanda kuka taimake mu kuka sharemana hawaye ubangiji Allah ubangiji ya share muku hawaye kuma ranan gobe kiyama, shi aure dakuke gani yana tattare da dunbin rahma da ni’ima damu bazamu taba sanin mai Allah ke nufi da auren nan nasuba sai nan gaba domin kuwa komi dakaka yafaru aduniyan nan kaddara ce kuma da dalilin faruwanta, fatan mu shine ubangiji Allah ya basu zaman lapiya Allah yakuna albarkaci abinda muke kokarin hadawa ayanzu” atare duk akace Ameen dudda dai Abba bai gama gane kan zancen ba he’s a lil bit confuse, gyara zama Kaka tayi tana murmushi tace “yauwa to Alhamdulillah komi daka gani kaddara ne, mun hadu ta alkhairi insha Allahu mun daura kenan yanzu sai afara gabatar da kayayyakin dana fada muku jiyako, kudin kun gani kunaso, kudin gaisuwan iyaye, kayan sarana dakuma kudin sadaki” wani irin kallonta Abba yayi zuciyarshi na neman bugawa, dauke kai tayi kaman bata ganshiba Abban Ra’is kuma yadanyi tapping cinyar Abban ahankali alamun karyay wani abu dazaisa suji kunya hakan yasa yay relaxing wearing a smile, murmushi Baffa yayi yace “to Hajiya” ya kalli su Suleman da Muhammad yace “Bismillah” tashi sukayi suka fita daga dakin basu jimaba suka fara shigowa da kaya niki niki tareda wasu yara yan anguwan akwati set biyu suka kawo guda shida shida na Louis Vuitton, sai manya manyan tabarma guda biyar, dasu goro jaka goma, su dabino sai wasu kwalayen hadaddun sweet da chocolate katon goma, sai su kwalin biscuit saikuma kudi yan dubu wrappers na dubu daidai da bama tasan na nawa bane sai harba ido take shiko Abba da Abban Ra’is shiru sukayi suna kallon ikon Allah, aminin Baffa ne yasake bude taron akaro nabiyu da addu’a yace “ga kayan nagani ina so dinan, gakuma kayan sa ranan, munaso ayanke mana sadaki sanan asaka ranan ko to Bismillah Alhaji” yay maganan yana kallon Abba da miyan bakinshi gabaki daya ya kafe ya bushe, hadiye miyau yayi ahankali ya kalli Kaka data zuba mai idanu irin kallon nan na kace bazaka karamin jayayyaba, dan gyara zama Abba yayi Anatse yana kallon kayan yace “wanan kaya haka Alhaji kaman muna sayar da yarinya agaskiya sunyi yawa, banda haka wanan akwatin ai babu bukatar su awajen sa rana ko? Kawai abarmata su amatasayin akwati kar akawo wan…” “kaga yaron nan nawa bai iya komiba haryau” Kaka tafada tana dariya ganin Abba na neman mata bukulu tace “ko yayyin Hamida gabaki dayansu nina aurar dasu saisa baisan kan abubuwan al’adun mu na hausawa ba, yanzu dai maganan sadaki muke ko?” tai maganan tana hararan Abba ta kasan ido ahankali ya saukar dakai, tace “yauwa sadaki” tace “yauwa sadaki kubada dubu dari, kudin kun gani kuna so dubu dari, sanan kudin gaisuwan iyaye dubu dari” innalillahi wa innailaihi raji’un Abba kawai yake fadi aranshi wace irin uwa gareshi dakeda shegen son kudi haka sabida taga masu kudi ne takeson siyar da yarshi haka dan anasu Ayush duk batai abinnan ba, patting cinyarshi Abban Ra’is yayi hakan yasa yasake murmushi, abokin Baffa yace “to Masha Allah” ya dauko wrap na yan dubu daidai guda uku duba dari uku kenan yamikama Abba cikeda ladabi, asanyaye Abba yamika hannu ya karba yana murmushi Kaka ta saki buda. “ayiriririi” Abba ya kalleta ganin yanda take murna yasa ya kalli Baffa yace “nabaku ubangiji Allah ya kaimu ranan yaja mana rai” Ameen duk akace Kaka tace “sati hudu, nan da sati hudu biki, asabar din dazata fado ana sati hudu ne biki da izinin Allah” takara sakin musu guda dayasa su Baffa dariya sosai nan aka kachame ana hira Abba yadan saki jiki yana basu amsa wuraren karfe daya suka tattara suka tafi bayan sunma Kaka kyautan ragowan kudin wai tarabama jikoki aiko Kaka harda rawa tarakasu har gate saida taga tafiyar su sanan suka shigo gida ta daure fuska rass dan karma Abba yakawo mata wata maganar ta kwalama Mama da Anty Lami kira tace “kuzo mu bude akwati muga abin ciki”.