Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 4

Sponsored Links

4…..

Kiran salla asuba yatada ita daga bacci mai dadin datakeyi, ahankali tabude idanunta tana karanto addu’an tashi daga bacci ahankali Ihsan tagani sanye da kayan bacci zaune achan edge of bed tana mata danne danne a wayanta, tadage tanayi kuwan harda murmushi da sauri ta tashi zaune cikin cool siririyan muryanta takira ta. “Ihsan!” a mugun firgice Ihsan ta kalleta da sauri ta ijiye wayan tana sauka daga kan gadon tai hanyar kofa tsorace tace “am sorry Anty Hamida, please don’t beat me, am looking for a friend for you kiyakuri please Anty Hamida na, wlh bazan karaba kinji sorry” tai maganan tana komawa baya tana kokarin kama handle din kofa, yanda taga ta daburce yasa da sauri tadau wayan dan taga metayi da wayanta akan Facebook messenger taga Ihsan na chatting dawani account mai suna Aadil Muhammad Thani, da sauri ta zaro ido ta daura hannunta ta dafe kirji, tsabagen mamaki ma takasa bude chat din ta kalleta tace “innalillahi Ihsan you are chatting with a man on my phone” ta sake dafe kirjinta, da sauri ta ijiye wayan kan gadon ta sauko tace “saina fadama Anty Lami wat u are doing” da sauri harda gudu Ihsan tadawo ta rike hanunta tafashe da kuka sosai tace “dan Allah kiyakuri, dan girman Allah kiyakuri Anty Hamida, I just wanted to find a friend for you naga baki da friends a facebook dinki, jiya da mukazo duknai adding nasu, and I only tell him my name and your name, I told him we are looking for a friend, and shikadai ne nakeson sunanshi saisa ma namai magana kuma is yaki accepting friend request dinne shine namai magana, and baima kulani ba, bece komiba, am sorry kinji Anty Hamida” tsayawa tayi tana kallon Ihsan din mamaki ma take ta yanda tasan kan chatting she’s just 10 fa, she’s sure a wurin Anty Zainab taga tanayi harta koya, fizge hanunta tayi dan kawai ta kara tsorata tace “nidai baruwana, as small as u are har kin iya begging maza suyi accepting friend request dinki, no kinma iya adding dinsu on top of that begging dinsu suyi accepting naki dakuma wayana, my phone ko sabida kin rainani, Allah kaimu gida saina fadama Baba” tana fadin haka tawuce tabude bayi ta shiga ta rufe, fashewa dawani irin shegen kukan tashin hankali Ihsan tayi tadaura hannu akai, a rayuwata tana mugun tsoron Baba, rasa mezatayi yasa tadau wayan da sauri tana kokarin typing dama baimayi replying ba amma yanda hanunta ke rawa sosai yasa tama kasa typing tai pressing voice recorder cikin kuka sosai tafara VN tace “please Uncle kagani I don’t know you, please don’t accept the friend request again, dama I was looking for a friend my Anty Hamida she’s always alone batason mutane, everyday our grandmother use to insult her and she cries, and I hate to see her crying, please kayakuri don’t accept d request am just 10yrs old ina basic 1 ne, kaga Anty Hamida tace saita hadani da Baba ina using phone dinta in the night ina magana da maza, please am sorry ai banyi magana dakai bako? Kaima shaidane, and u are d only one danama magana ma because your name is so cute, Maybe ma empty account ne bakama chatting, okay bye bye I will not do it again” tura voice note din tayi tana kuka sosai harda majina abunka da auta kuma shagwababbiya sanan tai deleting conversation din gaba daya ta zauna a wurin tana kuka sosai ta ijiye wayan, bude kofan Hamida tayi tafito daga bayin da sauri ta tashi tafada jikinta tasaki wani kukan tace “please am sorry Anty Hamida i will not do it again” sosai tabata tausayi hakan yasa ta share mata hawayen tace “to dena kukan, waya koya miki chatting?” cikin kuka tace “no body inadai ganin yanda Anty zainab ke chatting ne intanayi saisa nima nayi naga bakida friends a facebook saiyan gidanmu, I want you to be chatting kaman Anty zainab ne saisa, am sorry kinji bazan karaba wlh I’ve even told him not to accept kuma nai deleting komi” murmushi tayi tace “don’t try that again, jikiyo alwala kafinan na idar nabaki hijabi na kiyi sallan kema” gyadamata kai tayi tana matse kwalla tawuce ta shiga bayin, nafila tafarayi kafin tai sallan asubahi ta cire hijabin tabama Ihsan din tana matsawa gefe tana azkar, Ihsan ta karba tasaka takabbarta sallan itama.

Tana cikin lazimi Anty Lami tabude kofa ta shigo, hada ido sukayi hakan yasa tai dan murmushi akunyace tace “ina kwana Anty Lami” hararanta tayi tace “dole kiyi murmushi tunda kin gudo nan kin kwana baki kwana cikin jama’a ba, itakuma wanan data biyoki duk kuka kwana anan kun kyauta ai, tunda kun tashi in kugama kufito mukarasa jeren komi” maida kofan tayi tarufe tafice.
Ihsan na idar da sallan suka fita daga dakin, aiki suka farayi suna gyara gidan dan karfe hudu ne boat cruise party su, babban boat abokanan ango sukai hiring na Nire prest company, Zainab da kawayen Ayush din sai maganan party suke dan a arewa basu tabajin anyiba, sai wuraren one suka gama da sauri ta gudu dakinsu Ihsan ma tabiyota salla sukayi Ihsan ta debo musu abinci suka ci dan bataso takara fita dan gidan yacika da baki matan abokanayen shi ga makeup artist din da aka dauko dazata musu makeup suna gamaci tahau gado Ihsan tabi bayanta sai bacci.

Related Articles

Wuraren uku na rana Anty Lami ta shigo dakin taci gayu cikin wani hadadden lace baki daja dayay mata kyau sosai, baki tabude tana kallonsu yanda suke bacci abinsu kafin ta karaso wajen gadon ta daka musu duka a firgice dukansu suka tashi bayi ta nuna musu cikin fushi tace “tashi kije kiyo wanka right dis minute kisa ashobin ki ki fito amiki makeup, ke Ihsan tafi bathroom din dayan dakin kiyi wanka” da sauri Ihsan ta sauka daga gadon ta wuce dan bataso tai missing party nan for anything bata taba ganin party da akeyi a jirgin ruwaba ba kuma akan ruwa ba, kallon Hamida tayi dake sosa ido tace “wuce kema” ahankali kaman zatai kuka tace “Anty Lami ni bazani ba zan zauna gida tareda ke” cikin tsananin fushi Anty Lami ta nunata da yatsa tace “koki tashi kije kiyo wanka yanzun nan kiyi la’asar kije amiki makeup ki shirya kutafi ko wlh na saba miki Hamida, yanzu nafara yarda da maganan mamanki iskancin ki is too much stand up and get out of my sight my friend” da sauri ta tashi sabida tsawan data daka mata, bayi ta shiga tayo wankan tadauro alwala Anty Lami tagani a zaune ga trolley ta ta shigo mata dashi ahankali ta tsugunna tadau hijabin ta tasaka tai la’asar tana idarwa Anty Lami ta nuna mata sea blue ashobi ta wanda shine theme din party anmata wani hadadden gown, daukan rigan tayi tasaka Anty Lami ta tasata agaba takaita falo inda mata kenan dayawa anata makeup sunnar dakai tayi Anty Lami tasa aka fara mata, raurau tai da ido zatai kuka da kyar ta iya hadiye hawayen har aka gama mata makeup din, duka matan falon kafeta da ido sukayi sabida wani irin shegen kyau da tayi kaman ita tai kanta, hadadden takalmi Anty Lami tabata navy blue tasaka tabata glasses dinta tasa bakaramin kyau tayiba yanda ake kallonta yasa jikinta yafara rawa, horn da aka fara musu ana cewa su fito dan abokan ango tun uku da rabi suka taho yasa ta mike da sauri zata tafi daki hanunta Anty Lami tarike tana hararanta tace “wuce dan ubanki saikinje wlh, Zainab” ta kwalama Zainab dake kokarin sa hill dinta taci gayu sosai kaman itane amaryan kira, da sauri takarasa sa takalmin taje inda Anty Lami take tace “gani Anty Lami” murmushi Anty Lami tamata sabida kyan datayi tace “samomin gyale ta yafa dan bazata saka hijabin nanba yau” fashewa da kuka tayi jin ance bazata sa hijabi ba, bakaramin kular da Anty Lami abin yayiba tace “wai ke lamarin nan naki baza’a kaiki asibiti ba kuwa?” tabe baki Zainab tayi tace “Anty Lami wlh haka take ni dama kinbarta ta zauna a gidan inba hakaba wlh kuka zataje tana mana tana sunnar dakai tana neman inda zata labe saikace barauniyar datai sata a kasuwa, yar kauye kawai” hararanta Anty Lami tayi tace “kekuma dena cemata yar kauye wuce ki samo gyalen danace” ta kalli Hamida dake share hawayen cikin muryan lallashi tace “haba Hamida na, mai kama da mamanta, kinga kyan da kikayi kuwa? Bama wanan ba bakiso kije kiga jirgin ruwa yau, kintaba ganin jirgin ruwane ai saidai a tv a film irinsu tatanic, amma yauko zaki shiga cikin jirgin ruwa akan ruwa za’ayi party jirgi na tafiya, dena kuka kinji kije abinki inkin dawo kibani labarin abinda yafaru, kinga karma kibata kwalliyan ki” tai maganan tana share mata hawayen datakeyi daidai lokacin Zainab tafito dawani hadadden navy blue gyale ta warware ta yafa mata a one side aiko tai masifar kyau, murmushi Anty Lami tayi tace “iyye Allah nagode ma wanan kyau irin na yarana haka muje na rakaku wajen” rike hanunta tayi suka fita har wajen tasasu a mota Hamida kaman zatai ihu sabida tashin hankali gabanta har faduwa yake tsabagen tsorata sai sunnar dakai take tana kare fuskarta da gyalen jikin nata, daga musu hannu Anty Lami tayi tana dariya dan abin Hamidan ma looks funny dan yanzu yaga maganan zainab datace tana abu kaman barauniyar datai sata akasuwa.
Tashi motar tayi itakuma ta koma cikin gida tana girgiza kai tace “Hamida, Hamida hmmm Allah dai ya kyauta”.

Gabaki daya she’s not comfortable, gashi sai tafiya suke kaman bazasu kaiba chan lekki sukaje sukai parking a parking lot na Nire prest Boat activities, suka fiffito kafin su karasa waterfront din dukansu suna kallon katoton baban Boat din da akai decorating da flowers seablue, ga mutane maza damata suna kida na tashi, karasawa sukayi suka shiga kirjinta wani irin bugawa yake kaman zai tsage da sauri tarike hanun Zainab hakan yasa zainab ta kalleta daidai lokacin dayake duk angama shiga jirgin yafara gudu a ruwan, da sauri ta rike Zainab gam bakinta har rawa yake tace “An..Anty Zainab wlh am scared, please banaso wanan katon jirgin I don’t like water” hararanta Zainab tasake yi dan sosai take jin haushin halin Hamida tace “aisai kiyi tsalle kifada ruwan, look back kiga yanda mukai nisa da wurin da muka bari yanzun nan, jirgi tafiya yake, idan kuma you can swim back there bismilla” girgiza mata kai tayi hawaye zai zubo mata tace “to please hide me kinji, am shy and am feeling somehow, mutane sunyi yawa” tsaki Zainab tayi kafin tajata by fire by force sukai sama jirgin asalin party floor din, ihu Zainab tayi ganin wurin yanda yahadu taciro wayarta zatai selfie tace “Omg this is paradise” Ihsan ma ihu tayi tana tsalle karasawa inda akai arranging kujeru sukayi kida natashi yan mata suka fara rawa, janta Zainab tayi tace “dalla chan zomuyi rawa yar kauye kawai karki kofsani” fizge hanunta tayi da karfi dan sosai kanta yafara juyawa yanda taga mutane dayawa awurin ga karan kida dake tashi ga duman music dahar kwanyanta takeji suna wani irin cika mata kunne kunenta yay wani dumm, duk inda ta juya saita hada ido dawani ko wata ana kallonta, cikin tsananin tashin hankali ta iya bude baki bama tagani da kyau tace “Anty Zainab” sosai idanunta suka fara juyawa hakan yasa ta daura hannayenta kan fuskarta tarufe fuskan kozata dena hada ido da mutane yan rawa na bugeta suna ihu, tai nan tai chan da sauri tace “Ihsan, Anty Ayush, somebody please help me, jiri nake gani” daidai lokacin kuma aka rage kidan wai amarya da ango zasu shigo, ahankali ta janye hanunta daga kan fuskarta ta bude idanunta dake juyawa, gani tayi mutane na komawa kan kujeran wajen suna zama, da sauri kanta na juyawa sosai tafita daga wurin tai baya tana tafiya kaman wacce bata da lafiya, da sauri Ihsan ta tana Zainab dake selfie tace “Anty Zainab kalli Anty Hamida ina zata?” batare data kalleta ba tana selfie ta tace “shareta Ihsan kema kinsan zataje neman inda zata boyene me tsoron mutane, nidai banda lokacin damuwa da lamarin ta am going to have fun and take pictures na nunama yan dept dinmu evidence munyi biki a boat akuma kan ruwa” tai dariya tanajan Ihsan tana hoton da ita.

Da kyar take tafiya tasa hannayenta tasake rufe fuskarta da sauri tafita daga wurin kanta na juyawa tai chan gaban jirgin wurin ba mutane tana kulle ido dan ko kadan bataso ta kalli ruwan dasuke kai da yanda ruwan ke gudu, ihu dataji na jama’a dakuma wani irin duma da sautin music da aka kara kaman zai fasa mata kunne yasa taji duka kanta na juyawa tana ganin jiri sama da dazu kanta na juyawa sosai da sauri ta zare hannayenta daga kan fuskarta ta kalli sama idanunta na kankancewa, sosai saman ke juyamata hakan yasa tafara juye juye itama tana mikar da hannu trying to hold on to something da kyar cikin layi tace “Ma…ma” bayanta ne taji yabugu da karfen jirgi gakida dake tashi ga kanta dake juyawa, wani irin mika tayi kanta yay bayan karfen idanunta suka juya tana kallon ruwan da yanda jirgin ke gudu sosai wani irin iska na walwal da gyalenta dake lilo shima, kara mika tayi hakan yasa glasses din idanunta suka fita daga fuskarta suka fada ruwan yanda take bangara idanunta na kafewa sosai ya rinjayi karfinta kafafunta suka daga tai cikin ruwan itama takai tsundum!.
_🌹IN BANI 🌹_

 

 

_M. Shakur_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button