Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 17

Sponsored Links

17…
Hararan shi Yusuf yayi daya dawo yace “shine ko abani labari, who is she?” dan yatsine fuska yayi yace “a girl I met yesterday” da sauri Yusuf yace “and??” tsayawa da tafiya Khaleel yayi ya kalleshi yace “and wat, nace jiya muka hadu I just helped her out ne da wani guy ya kwace jakarta shikenan” murmushi Yusuf yay suka cigaba da tafiya chan yace “she is nice” ahankali yace “yea ga shegen surutu ba” dariya Yusuf yayi batare daya kara cewa komiba sukaje suka biya kudin kayan sanan suka wuce school dinsu Faiza.
Tsabagen farin cikin daya mamaye zuciyar ta batamasan me aketayi a class ba dan murmushi kawai take tana kara kallon special number Khaleel datai saving da my superman.

Haka tai wasting 4 hours lecture dinan tunanin Khaleel barinma yanda yawani zo ya mika ATM card yabiya kudin nanne yafi tsumata.
Koda daddare Islam bacci tayi ta barta ido biyu sabida jira take Khaleel ya kirata ganin har 11 bai kirata ba yasa ta dialing number shi har tagama ringing bai dauka ba, sake kira tayi nanma bai daukaba wani iri taji sosai ahankali ta ijiye wayar taja bargo ta kwanta ta rufe ido da kyar bacci ya dauketa.

“Goggo jikan ki yay kawa fa” ajiye maficin datake fifita musu wani dan kasko data daura ruwan shayi akai anan tsakiyar falon ta tayi tace “kai da gaske Yusufa” kallon Khaleel dayay kaman bejishi ba yayi yace “gashi nan ki tambaye shi, wlh Goggo yarinyar badai hankali ba, ai in sha Allah watarana zan kawo miki ita ki ganta” sosai Goggo taji dadi, batace komiba ta sauke shayin daketa uban kamshi ta zuzzuba musu a cup, dauka yayi yay sipping kadan sanan ya ijiye saida yadanyi sanyi sanan ya dauka ya shanye ya goge baki ya tashi ya Kalli Yusuf yace “zanje Gym” kafin Goggo takirashi yafita daga dakin da sauri dan bayason surutun su, part dinsu ya wuce ya shirya cikin kayan gym, wata gym singlet ne dake kama jiki mai ruwan toka tadan budemai kirji sosai yasaka, sai dogon wandon shimin, yasa sport shoe na Nike, yadau wani dan madaidaicin towel ya daura akafada yadau car key da wayar shi, da sport bottle dake cike da warm water na glucose and lime yafita.

Related Articles

“ke Farida, Farida, wai bataji nane” tana zaune a dining itada Islam suna hira taji Anty Hindu na kwala mata kiran nan kaman ana yaki, da sauri ta tashi tana amsawa, sama tayi tai sallama tabude dakin Anty Hindu dake zaune da Dad suna magana, kudi Anty Hindu ta mika mata tace “ki kira bala ya kaiki inda nake siyo fruit a kasuwa yasan wajen kisiyo, babu fruits agidannan yau” karban kudin tayi tajuya tafita daga dakin, dayake tariga tai wanka tunda sassafe yasa Hijab dinta kawai ta dauko da wayarta ta sakko, dining tazo tasami Islam na taya Mum yanka kubewa ta kalli Mum tace “Mumy Anty Hindu ta aikeni kasuwa plz Islam tarakani” Mum ta kalli Islam tace “zaki?” gyada kai tayi “tashi kutafi to, amma kuyi sauri” da gudu Islam tai sama Hijab ta dauko milk daya kai mata gwuiwa tadaura akan atampa dayake jikinta tabita suka fita waje bala ya dauke su suka tafi. Suna zaune a motar takara dailing number Khaleel saida wayar ta kusa katsewa ya dauka, ajiyar zuciya ta sauke mai kara har saida Islam ta kalleta, dawani irin calm voice tace “good morning Mk” ahankali yace “ya kk” murmushi tayi daya bayyana fararen hakoran ta tace “Alhamdulillah” “gud” yafada tareda yin shiru itama shiru tayi, hayaniyar dataji ata bangaren shi ne yasa tace “ina kake haka da ake hayaniya sosai?” wlh kawai dan bayason wulakanci ne saisa amma dis girl is really disturbing him, kaman bazaiyi magana ba chan dai yace “gym” da sauri tace “wani gym?” shiru yayi hakan yasa ta kalli wayar ganin yana kan line har yanzu yasa ta mayar kunne tace “hello are you there” batare daya amsa ba yace “infinity gym, bye gat to go now” Ya katse wayar. Bala ta kalla tace “dan Allah Bala dan kaini infinity gym” da sauri Islam ta kalleta tace “ba kasuwa aka aikemu ba” yarfe hannu sama tayi tace “dalla forget kasuwa, I wanna see my superman face tukun” tabe baki Islam tayi ta juya ta cigaba da kallon hanya, agaban wani babban building da aka rubuta infinity gym ajiki bala yay parking. Hannu Islam ta daura akan kirjinta sabida yanda taji yana bugawa.
[6/13, 8:48 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button