Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 35

Sponsored Links

No Edited
Zamu fara page biyu kullum, biyu a arewabooks ɗaya a WhatsApp group🤓……. MIJIN MALAMA it’s a paid book Subscribe before you read….. Via WhatsApp for more information 08119237616Zame hannunsa ya yi yana ɗan kame fuskarsa a hankali kamar bai son magana ya ce “Remove the vail” Ta yi saurin ɗago kanta zata kallesa amma ta kasa ya yi mata wani irin bala’in kwarjini, ta kasa cewa komai ta kasa aikata abin da ta yi niyya. Ajlaal ya tsuke tamau yau sai ya ga abinda ya turewa buzu naɗi. Bakinta na rawa ta ce “Baa…ba…baaaa!” Ta kasa furta abinda tayi niyya kaifin idanunsa sosai ya tasirin a kanta a hannun ta ce “Am sorry i can’t do that” Ta faɗa tana ƙoƙarin barin bakin bedroom ɗin nasa, wanda ta turje taƙi yarda ta shiga domin ta san sirrinsa ne. “Fita” Ya nuna mata hanyar fita tun kafin ta nufi hanyar ai kamar zata kifa duk da girman jan ajinta haka tayi waje, zata gilma ta gabansa ya sanya hannunsa mai taushi ya fizgota ta dawo gabansa, kai tsaye kuma fuskarta ya nufa da hannunsa He tried to lift the mask off her face. Duk jikin Majeederh rawa yake nan da nan ta ruɗe ta marairaice ita bata taɓa ganin rashin kunya haka ba, daman larabawa ba wani ta ido gare su, gashi ba zata iya yi masa rashin kunya ba, ta rirriƙe shi ta ce “Please don’t”
“Ohh!” Ya furta yana riƙe hannunta gam, sai ka rantse ba Mai martaba bane, ganin da gaske yake ya sa ta ce “Please Mai martaba” Nan ma ya yi mata banza aikowa ta daddage ta sakar masa cizo a hannu da sauri ya saketa yana faɗin “Auchhhii” Ta re da ɗan lumshe idanu sai kuma ya buɗe, suna haɗa idanu ya zaro mata manyan idanunsa ta kwasa da gudu ta nufi ƙofa ya yi saurin shafa kansa tare da nufar bedroom ɗinsa. Tun kafin ya ƙarasa ya ji muryar Ƙhulud na faɗin “Ya na ganki tsaye?” Ita dai Majeederh ba ta yi magana ba, Ƙhulud ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce “To wannan hakin kamar kin yi tsere na zaki fa?” Sai a lokacin Majeederh ta ɗan sauke numfashi tana kame kanta ta ce “Zan ta fi”
“Baki isa ba, sai mun yi lunch tare, Mai martaba bai faɗa miki ba?” Ganin Majeederh ta ƙi cewa komai ya sa Ƙhulud kallonta frm head to toe,She wants to understand Majeederh’s situation but she can’t understand anything. Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce “Ba dai miskilancin naki kika gwadawa mijina ba?” Majeederh ta harareta ta ce “The train at six o’clock in the evening will drop me off, I don’t want to miss the train” Ƙhulud ta ce “Ki rasa mana, sai a ƙara neman wani” Kafin Majeederh ta ce komai Ƙhulud’s ta shige haɗaɗɗan Bedroom ɗin Mai martaba Ajlaal Sultaan, komai na bedroom ɗin white colour ne, the furniture, bedsheet, Curtain, everything da ake zubawa a bedroom ba ɗakin Ajlaal fari ne, ga wani irin ƙamshi mai sanyi dake tashi. Ƙhulud tayi tsaye tana kallonsa ya fito daga toilet yana tsane ruwa akansa ta ce “Ba dai wanka kayi ba?” Shi dai bai ce komai ba, har ya nemi saman kujerar dake kusa da tafkekekn royal bed ɗinsa ya lumshe idanunsa tare da riƙe kansa da hannu bibbiyu, Fulani Ƙhulud ta ƙarasa kusa da shi tare da zama a hankali ta leƙa fuskarshi suka haɗa idanunsa taga idanunsa jajur “Takawa lafiya kake?” Ya yi shiru sai kallonta da yake tasan kuma ba magana zai yi ba ta ƙara da cewa “Kun gaisa da Malama Majeederh?” Sai a lokacin ya ɗauke yana miƙewa tsaye tare da nufar wajan mirror ta ce “Ran Takawa ya daɗe ina ta magana?” A hankali cikin kasala ya ce “Wa fa?” Ta ce “Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, baka ganta ba?” Yana nufa wajan clothes ɗinsa ya ce “Gaskiya, bamu ga kowa ba nan ta zo?” Ta ce “Wai da gaske naga har tsakiyar parlour fa ta shigo, daman Majeederh ɓoyewa ta yi haka last time kuka mini fa ku baku san zumunci?” Shi dai bai ce komai ba ta ce “Ina nan saka kaya kawai ka fito” jin haka yasa ya fasa ɗaukar Jallabiyar da zai saka ya dawo kusa da ita ya zauna yana ɗan turɓune fuska ya ce “Haka zamu zauna” Ta gwalo ido ta ce “Ba kaya?” Ya jinjina mata kai kafin tayi magana ya sunkuceta sai zuwa other bedroom ɗin nasa dana zare idanu ta ce “Ajlaal cikina ya tsofa please ka rufa mini asiri” Ya direta yana binta da wani irin kallo kallo ɗaya tayi masa tasan ba zai ji roƙan ba ya ce “Me?”
“Nothing” Nan da nan Mai martaba Ajlaal Sultaan ya sanya Ƙhulud yin baccin dole ya shirya cikin wata golden ɗin Alkyabba mai masifar kyau da ɗaukan idanu yana fidda ƙamshin LONG BOARD. Wayarsa daya daɗe bai ɗauka ba ya ɗauka tare da kiran wani Digits, a nutse cikin izza da gadara ya ce “Follow her” Yana faɗin hakan ya kashe kiran ya juya ya tsorawa fuskar matarsa Ƙhulud da kallo sai kuma ya ɗan shafa kai ya ce “Harnarn”…….. Majeederh ce tsaye tana kallon kanta a madubi ganin irin sauyin da tayi, tana mamakin yadda take zama tamkar wahainiya, yau ƙirjinta ya cika sosai gobe kuma taga ya koma yadda yake, duk da irin ciwon idanun dake damunta wanda ta same shi sanadin nacin karatu a Egypt, bai hana nuna asalin zubi da tsarin halittar ƙwayar Idanunta, duk inda ake neman cikakkiyar mace wayayyiya, mai hankali nutsuwa sanin ya kamata, educated one za a sanyata a ciki, duk inda ake neman mai ma tsarin diri na ɗaukan hankalin ɗa namiji nan take dole ka sanya Majeederh, takai ta cika bata buƙatar a rayuwar yanzu wanda ya shige ta ganta a ɗakin mijinta, when? Sai kawai ta ɗan yi murmushin takaici a fili ta ce “Bani da rabo ba” Ta sauke liƙab ɗin tare da jan trolley ɗinta zuwa waje, ta shiga mota suka nufi airport, tana zuwa ta samu an fara shiga saura few minutes ya rage jirgin ya tashi, ta shiga ta zauna a mazauninta tana mai sauke numfashi bata jin daɗin komai, dauriya kawai take da nuna jarumtarta a fili. Tunda ta shigo Jirgin idanunsa yake kanta, bai ɗauka zai sake ganinta sbd tun a hall ɗin musabaƙar ya nemeta ya rasa, muryarta kawai tabar masa wacce take masa amsa kuwwa a cikin kunne! Duk wani juyi da harabar daƙiƙo zuwa sakanni, da juyewarsu zuwa mintuna har kawo su zama awa guda basa taɓa tafiya ba tare da amon muryarta ba da bugun zuciyarsa, jin muryar a cikin lokaci ɗaya ta wargatsa masa lissafin shekarun da ya yi na bayyana ta mantar da shi ainahin abinda ya kawo shi Saudiyya. Ganin kamar zata buɗe idanu ya sanya ya ɗauke kai yana mai da dubansa ga Hammad dake masa magana ƙasa ƙasa amma baya ji, tunaninsa ya yi ƙaura daga masarrafar dake sarrafa nutsuwarsa ta ƙwaƙwalwa… Hammad ya ce “Meke damunka wai?” Ya haɗe fuska ya ce “Da aka yi me?” Hammad ya yi shiru sai kuma ya ce “Tun jiya da muka bar hall ɗin nan naga sauyi a tare da kai, babu shiru kasa muka shirya dawowa Naija wai meke faruwa?”
Abuturab ya ɗago kansa baki ɗaya ya zubawa Hammad ya ce “Stop Interrupt!” Hammad ya ce “Oh tambayar ya kake shi ne ƙatsalandan?” Abuturab ya haɗe fuska ya ce “Ban so”
“To Ubana, wallahi sai na tambaya ai kasan ba ishasshiyar lafiya gareka ba, yanzu idan ka mace mini a nan ai na shiga uku wajan Maysoon” Annurin fuskar Abuturab ya ɗauke nan da nan, ya kasa cewa komai a hankali kuma ya juya ya ƙara kallon direction ɗin da take zaune, yana mmkin yadda tunda ta zauna ba tayi motsin kirki ba. Ana haka jirgin ya fara juyawa a ƙasan kwalta kafin a hankali ya shila sama cikin sararin samaniya…. Mai martaba Ajlaal Sultaan ya sauke numfashi yana jin zufa na karyo masa all over himself, ya ƙara fitar da wani irin ɓoyayyan nunfashi a nutse ya ɗaga kai ya dubi yadda jirgin ke nutsuwa cikin gajimare can ƙasan maƙoshi ya ce “Nigeria” faɗin kalamar Nigeria sai ya ji nan da nan ransa ya ɓaci kansa a shiga sarawa da sauri ya ce “Palace please”
Misalin 10:7 jirkinsu ya sauka a airport ɗin Malam Aminu Kano, a hankali suka dinga fitowa, can ta ta fara tako steps ɗin jirgin hannunta ɗauke da trolley, idanunta rufe tana shaƙar iskar dake kaɗawa, idanunta kuma ta buɗe sosai a harabar wajan bayan ta fito daga can wajan da akai iyaka da jirgi mmki ya ishe ta babu wanda ya zo da sunan tafiya da ita, Ya Allah wacce irin rayuwa take ciki me ya sa kowa ya juya mata baya a dangi sbd kawai ba tayi aure ba? Ta duba haɗaɗɗan agogon hannunta taga dare ya yi ta nufi tafiya daga bayanta ta ji an ce “Hawwa’u” Ta yi cak ba tare data juya ya ƙara so cikin nutsuwarsa ya tsaya gabanta yana zuba mata Idanu ya ce “Ba sai saukarki kenan ba?” Ta ɗan kallesa tana kame kanta fuska haɗe duk da ba ganinta yake ba ta ce “In sha Allah” Aliyu ya shafa kai ya ce “Oh wlcm, na yi dropping Papa ne zai je Brazil” Ta jinjina kanta ya ce
“Can i help you? By dropping off?” Ta ɗan yi shiru sai kuma taja trolley nata zuwa gaba ya yi saurin shan gabanta ya ce “Please Malama Majeederh, it’s my responsibility to do that” A ɗan taƙaice ta ce “No thank you” Ya marairaice ya ce “Don Allah, ki yi mini alfarmar nan” Bata da wani option daya shige shiga motar ta shi…. Tunda ya fara driving ta rufe Idanunta ta samu kanta da faɗuwar gaba sun jima suna tafiya ta ji ya tsaya bai daɗe ba ya dawo hannunsa riƙe da leader alamar takeaway.
“Sorry, Yunwa nake ji sosai kamar n ci babu tun safe da na ci abinci a wani restaurant” Sai a lokacin ta masa ƴar duguwar magana ta hanyar faɗin “Restaurant? Da aurenka? Akwai adalci ga Latifa anya?” Aliyu ya dai kalleta sai kawai ya girgiza ya ce “Bata jin daɗi, shi ne nayi takeaway” Ta ce “Allah ya sauwaƙa” Parking Aliyu ya yi a ƙofar gidansa bayan ya kashe motar ya fito yana zube hannu a aljihu wani irin baiwar kyau Ubangiji ya zubawa Aliyu, domin ko Ajlaal sai dai ya nuna mana hasken fata da suma mai yawa da kuma launin idanu, gashi da wani irin haƙuri da kawaici amma idan ransa ya ɓaci kamar Mahaukaci haka yake yana da ƙulafuci da saka abu a rai. Ya ce “Kamar an rufe gidan ko?” Ta yi masa shiru yana mmkin yadda Majeederh ke feeling kanta da yawa, tsayin shekaru bai taɓa ganin munafukar fuskar da ake rufewa ba. Jin shiru ta ɗago kai suka haɗa idanu ta kame fuska tana jan jakarta zuwa hanyar gate domin tuni gatekeeper ya buɗe tana jinsa yana magana amma ta yi shiru a gareta haramci ne babba da ɗaukar ƙaton zunubi ga yin magana da namiji baligi sai ya zama dole. Tana shiga cikin gidan taga Abbu tsaye a Balcony ta zube har ƙasa ta gaishesa ya amsa a wannan karan ta yi mamaki da ya ce mata “Congratulations” Ta nufi cikin gidan tana shiga Aaliyah ta rungumeta tana ihun murnar ganinta, Majeederh ta cire liƙab ɗinta bayan ta tsuguna ta ce “Barka da dare Mami” “Yawwa” Ta ce tana binta da ido, Raihana ta ce “Allah mai iko! Ana ta shiga rigar Muslunci ana ci da addini” Aaliyah ta kalleta ta ce “Idan fitsari banza ne kaza ma ta yi mana” Raihana ta watsa mata harara tana cewa.
“Ji saƙarya, ana maganar kan giwa wake jiyo ƙamshin zomo? Mai da wuƙar ni ba tsararki ba ce” Aaliyyah ta riƙe haɓa ta ce “Hooo ƙaasa, to aini walkice daidai da ƙugun ko wanne lalatacce, kuma Majeederh kuturwa uwa ce zama da ita dole murucin kan dutse bai fito ba sai daya shirya” Raihana taja tsaki ta ce “To ai ga sararin subuhana ɗin nan, sai a zuba muga idan za a kwashe daidai, ba girin girin ba ta yi mai” Majeederh dai ikon Allah kawai take kallo domin ita bata ma iya karin magana da habaici ba shi yasa ta rasa fahimtar me suke cewa, Mami na zaune watching all of them. Aaliyyah ta saki dariya ta ce “Ai gurbin idon ba idanun bane, ni masallacin kurawa ce bawa kare limanci daidai yake da datse iskar dake shaƙa, kiyi a hankali domin na kawo kai nasan fari na san baƙi kada ki ja nayi miki wankin babban bargo, domin naga fahimtar ki daidai yake da fahimtar yaron goye, bana son kuma ya kasance duk kun far bakinki kiyi haihuwar guzuma” Raihana ta ce “Me kike nufi da haihuwar Guzuma? An faɗa an ƙara faɗa idan Majeederh tayi zuciya gobe muji loud speaker Liman na sanar da ɗaurin aurenta, waye bai san cewa Majeederh ba auren ne a gabanta ba? Office ɗin data buɗe na mene? Gari gari da take zuwa da sunan kaiwa marayu taimako bayan ƙarya ne na mene? Ke yarinya wahainiyarki ta kiyayi ramata, ta dauwama ba tayi aure ba har Mahadi ya bayyana” Aaliyyah idanunta a cicciko da hawaye ta ce “Bar gaigaye za kici tumu ne, ƙaddara zane gwara ita tata ƙaddarar ya fito sarari mun gani, kuma komai ya yi farko zai yi ƙarshe” Ruma ce ta fito daga ɗaki ta ce “Kaza uwar tune tune mene ya faru kuma?” Kafin Aaliyah tayi magana Abbu ya shigo gabaɗaya suka nutsu ya dinga binsu da kallo kafin ya ce “Kun kyauta, ko wacce ta fice mini daga cikin gida” Raihana ta ce “Abbu ka yi haƙuri baya nan fa, gidan shiru tsoro nake ji” A fusace ya ce “Ya kashe ki, kuzo ku fi ce mini” Jiki na rawa suka ɗauki mayafi da handbags ɗin su ya ce “Shashai, ku dinga faɗa kamar ba jini ɗaya ba zan yi maganin ko wannenku kada ɗan banzan yada dake dawo mini gida” Ya juya kan Aaliyyah ya ce “Dage, basu girmeki ba?” Ta ce “Kayi haƙuri Abbu Anti Jeederh sukewa gorin aure hadda sharri” Ya kalleta ya ce “To kashin awakai, ita Majeederh Ubangiji bai bata baki bane? Sai ke rasai? Ba ita ta sake musu ba da tana cin ubansu tun farko za ayi haka?” Mami ta dinga kallon Abbu sai bata ce komai ba, ya dawo kanta ya ce “Asabe kin kyauta,na kuma gode” Ya kalli Majeederh ya ce “Da safe ki same ni”….. Washegari da safe bayan Majeederh ta shirya cikin wata tsadaddiyyar Abaya Marron irin turkies Abaya ɗin nan ta samu Abbu a parlourn shi yana zaune ya yi shiru bayan sun gaisa ta ce “Abbu gani” Ya ce “Hawwa’u, Hawwa’u, Hawwa’u” Ya yi pointing nata ya ce “Sau nawa na kira sunanki?” Ta ce “Uku Abbu” Ya jinjina kai ya ce “To wallahi Allah na gaji da ganinki a gidan nan” Da wani irin Shock take kallon Mahaifinta tashin hankali ya bayyana akan fuskarta tsoro da wasa fargabar Abinda zai biyo baya ya wanzu a zuciyarta Abbu ya ce “Shekararki 31 a duniya kina gantali,duk sha’aninki suna gidan mijinsu harda yara uku wasu huɗu amma ke kina yawon neman abin duniya? Yaran da aka tsuguna aka haifa akan idanunki duk suna ɗakin mazajan su banda ke, kina jerawa da Majaufiarki kamar sa’arki? Ka kaf Family ke ɗaya ya rage idan kika ɗauke Aaliyyah da Sona? Wallahi wallahi idan ina ganinki a gidan nan zuciyata zafi take daurewa kawai nake idan kuma na ci-gaba da ganinki tabbas zuciyata bugawa za ta yi sbd baƙin cikin ki……

Littafina na kuɗi ne, biya ki karanta cikin kwanciyar hankali da salama da fitar da hakƙina…….

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button