Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 19

Sponsored Links

Harsuka kai wajen kofa security ya bude musu sosai yaji kirjin shi yabuga hakan yasa ya tsaya tareda shafa wuyanshi, waigowa tayi ta kallai tace “why did you stop bazaka zo ku gaisa da Islam ba?” murmushi yamata ya girgiza kai yace “nah, next time ma gaisa bye” bye tamai yajuya yatafi, ahankali tajuya tafita cike da farin ciki ta bude mota ta shiga Bala yaja sukabar wajen.

Cikin gida suka shiga Bala kuma yabiyo su da fruits, da Miemie taci karo a falo tanata wasa da toys din Sameer da gudu Islam ta dauketa ta shillarata sama tana mata wasa, Farida Kuma ta wuce sama dan kaima Anty Hindu sakkon ta. Daukar Miemie tayi ta wuce kitchen Mum da Maman Miemie ne suna yanka nama gaidasu tayi tareda cire hijab ta ijiye akan kofa ta kalli Mum tace “mum ni zanyi” tashi Mum tayi tace “sarkin son aiki bari to na wanke hannu saina tafi da Miemie” hannu ta wanke a tap sanan tadau Miemie suka fita, naman tarike ma Maman Miemie suka dinga yankawa har suka gama, ta tayata suka gama hadadden girki tare, fried rice sukayi da pepper meat sai fruit juice dasuka hada suka jera a dining sanan Islam ta wuce sama dayin wanka.

Wuraren 9 Farida ta tashi afirgice ta kalli agogo a rude tace “na shiga uku Islam shine baki tashe niba dan kinga yau bakuda lectures ko” bude ido Islam tayi cikin bacci tace “sorry nima bacci ne ya kwasheni bayan nagama azkar” daka mata duka Farida tayi abaya ta shige bayi da gudu, ihu Islam tayi tareda buga kafa ta rike bayanta tace “wlh kinci bashi saina rama” leko dakai Farida tayi ta kalleta tamata gwalo tace “kindai san baki da karfi ko I will break ur borns, ragagagga” pillow Islam ta dauka ta jefa mata hakan yasa ta fashe da dariya ta koma cikin bayin da sauri ta rufe kofa Islam ta daga murya tace “Allah sama kiyi latti muguwa kawai” dan bayanta har yanzu zafi yake mata Farida badai zafin hannu ba. (name ur friend dake da zafin hannu, hahah nidai Humi ne wlh😂). Agurguje tai wanka tafito ta tsaya agaban mirror tana shiryawa tana hango fuskar Islam yanda take turo baki, ajiye hodan hanunta tayi tawani zo ta rungume Islam tace “haba tawas sorry to daga wasa, wayyo nasan da zafi ko muga bayan” kokarin tabamata baya take hakan ya mugun bata dariya, dariya dukan su biyu sukahauyi, Islam ne tafara dakatawa tace “wai bazakisa kayaba sai kinyi latti” da gudu ta tashi taje gaban wardrobe ta dauko simple material tasa tadau gyale ta tsaya gaban madubi tana rolling tace “yau Fahad zaizo ko?” gyada kai tayi tace “eh yama dawo jiya wai, yace muhadu a quiks cafe bayan sallan la’asar” pin ta dauka ta kama gyalen sanan ta rataya bag tace “kici gayu sosai fa idan zaki, haka akema maza su haukace akanka, idan superman dina ya ganni har kasa magana yake sabida kyan dayake ga inamai wlh” tai wani fari da ido, kama baki Islam tayi tace “you with this ur superman Faree, wlh kinyi nisa” tace “Islam saima kin ganshi wlh black Arab ko inhar kinsansu he is just like one of them, anyways ki lallaba Fahad fa, idan kuma yaki yarda call me zanzo na same ku awurin na sasan taku u know am good at dat natafi kimin addu’a dan wlh tunanin superman yahanani yin karatu bansan komiba Allah” tabude kofa tafita, girgiza kai Islam tayi tace “Allah shiryeki, gud luck anyway”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button