Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 46

Sponsored Links

Kamshin turaren dataji yacika mata hanci ne yatada ita daga baccin datake, ahankali take bude ido harta gama budesu Khaleel tazani zaune kusa da ita yaci uban shadda dark brown har kyalli take, ya gyara gashin kanshi da sajen shi sunata shining ya zauna yana kallon fuskar ta, tashi zaune tayi tadan dauke kai ahankali tace “ina kwana” murmushi yamata tareda kamo hanunta ya mikar da ita tsaye jitayi ya rungumeta hakan yasa ta tsorata batare daya saketa ba yace “morning Baby ya darenki” yay maganan tareda sakinta, kauda kai tayi, murmushi yasakeyi mata da sauri tabar wajen wajen akwatin daya bata jiya taje budewa tayi ta ciro wata atampa vilisco dataga an dinka yanama cikin leda da duk wani abu dazata bukata sanan tadan juyo kaman mara gaskiya ta kallai hada ido sukayi hakan yasa ta dauke kai ta tashi ta shiga bayi da sauri ta rufo kofar harda saka key dan bata yarda dashiba wanan kallo kaman wanda yaci maita.
Saida tagama wankan sanan ta shirya ta shafa mai tasaka kayan da aka mata dinkin riga da sket, ba karamin haushi rigan yabata ba dan V neck akama dinkin saidai kayan sun mugun amsanta, black da pink ne kalar atampar hakan yakara fito da hasken fatar ta, rashin comb yasa ta tattare gashin nata tai pakin dinshi ahaka sanan ta daura dan kwalin dan simple daurin tayi, gaban mirror bayin taje ta tsaya tana kallon kanta wani haushi ne yazomata ganin yanda gaban rigan yasa kana hango saman kirjinta dan rigan yakamata chas ajiki, tsaki tayi ta tuge daurin dan kwalin kanta ta warware sanan tadan yafa aka yarufe mata har wuya sanan tafito, ganin baya dakin yasa ta bude box din ta maida kayan data cire ta feshe jikinta da turaren data gani sanan tarufe akwatin tana kokarin daga akwatin taji yay sallama ya shigo, ciki ciki ta amsa batare data kallai ba ta daga akwatin ta juyo fadawa jikinshi tayi dan kwata kwata batasan yana bayanta ba, kokarin fita daga jikinshi tayi da sauri, yadaura hannayen shi a waist dinta yana kallon idonta mayar da kanta kasa tayi takai hanunta ta daura akan nashi tana kokarin cirewa daga waist dinta, kama hanunnata yay yarike hakan yasa ta fizge hanun da karfi ta tureshi ta juya zata tafi, fizgota yay ya zauna akan gado ya daurata akan cinyar shi kokarin mikewa take amma yariketa gam, dayan hanunshi yasa ya yaye lullubin datayi da dan kwalin ya ijiye agefe yana kallonta kawad dakai tayi gefe ta daure fuska, ahankali taji yakai hannu yana shafa wuyanta wani irin yarr taji tanaji ga heart dinta na racing, ture hanunshi tayi hakan yasa ya rike hanunta gam sanan ya mayar da danyan hanun nashi yana shafa wuyan nata wani iri taji tanaji hakan yasa tafara jujjuyar da kanta kaman wata kadangare, da kyar ta iya ta fizge hanunta ta tashi dagudu zatabar dakin ajikin kofa ya ritsata hakan yasa ya daura hannayen shi biyu a jikin kofar yasata a tsakiya yana mata wani irin kallo, hannu tasa tafara kakkare kirjinta tai crossing hannayen ta daurasu akafada ta yanda bazaiga komiba idanunta suka cicciko da hawaye, cire hanunshi daya yay daga jikin kofar ya daura akan hanunta yarike yacire hannun daga kafadan yana kallon fuskarta, ahankali ta shiga reramai kuka tana mutsitsike ido, hannu shi yasa ta bayanta jikinsu ya hadu tadan komar da kanta baya still tana mutsitsike idanun dake fitar da kwalla, hanun nata yakamo yacire daga ido yadan hura mata iska a ido sanan yace “meke damunki” kokarin cire hanunshi take daga bayanta ya girgizamata kai tareda hada forehead dinshi da nata, hancin shi ya goga akan nata yadan kalli kwayar idonta sanan yace “talk” kokarin kawad dakai take yaki bata daman yin hakan, da kyar tace “kama Farida alkawarin aure, jiya ta shirya she was so happy she invited all her friends shine ka aureni bayan I already told u bazan aureka ba, ashe wayau kamana, Allah kadai yasan wani hali Farida ke ciki yanzu, why did you do dis?” takarashe maganan tareda da fashemai da kuka, tunda take maganan yake kallonta baki ya bude zaiyi magana sukaji muryan wasu mata na buga kofa ta waje, handky yaciro daga aljihu ya share mata hawayen sanan ya kamo hanunta ya zaunar da ita akan gado yace “am coming”. Falo yafita yabude kofa su Ihsan yagani da wasu manyan mata guda uku, Ihsan tai murmushi tace “Umma tace nakawo su, za’a mata lalle ne da gyaran kai, kuma wai kaje” cike da rashin jin dadi ya kalli matan yace “ku shigo” komawa yay ciki yasame ta azaune hanunta ya kama ta tada ita tsaye yace “wurinki akazo, zomuje” make kafada tayi hakan yasa yay folding hanunshi a kirji yana mata wani irin kallo da sauri tajuya zata fita daga dakin yakamo hanunta.
[6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button