Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 5

Sponsored Links

Banjin daga Khaleel har Eesha wani daga cikin su yay wani bacci mai kyauba, Eesha su Ihsan da Khadija ne suka tasata agaba wai takosa, shiko Khaleel abangaren shi Yusuf da friends dinshi ne suka tasashi gaba wai yakosa yaki bacci dariya yay yaki musu magana.
Misalin 9:30 nasafe na ranan bikin mutane sun cika gidan makil, Aisha ce zaune akan gadon dakin ta tasa wata atampa English wax da aka mata stone work yay kyau sosai, wayarta ta dauka tai dailing number Khadija ringing daya ta dauka, tace “Eesha am coming back yanzu na siyo agogon, gama ninan nafito daga Dunes Abuja taxi nake nema nahau” murmushi Eesha tayi daya mugun kara mata kyau tace “nagode Tawas, kiyi sauri please inaso nabashi yasa kafin lokacin daurin auren ne” katse wayar tai tana murmushi tun jiya bai kirata ba tasan hala fushi yakeyi, murmushi tayi tadau wayar Flashing tama su Ihsan dan sun tafi gidan su dauko kayan makeup din Faiza sunki dawowa.
Wuraren goma da rabi Khadija ta dawo da sauri Eesha ta karbi ledan da akwatin agogon ke ciki, ciro agogon tayi ta bude daga box din wow tace, agogo ne mai kyau Rolex wanda tasaimai da kudin ta 75,000 naira, gashin golden color rufewa tayi ta dau wayarta dailing number Khaleel tayi saida takusa katsewa sanan ya amsa. Murmushi tayi kafin yay magana tace “am sorry Yaya Khaleel” Ahankali ya lumshe ido danji yayi wani sanyi ya ratsa zuciyar shi, dawani irin murya tace “kana ina kana gida ne?” dan murmushi yayi sanan yace “a’a muna bakin layi shagon dinki Ibrahim tela, kayan dazamu sa gabaki daya fashion designer damuka bama dinki yamana wandunan sunyi tsawo sosai shine muka kawoma Ibrahim yarage mana, Mesa kike nemana Kuna bukatan wani abune, nazo?” girgiza kai tayi tace “a’a kabarshi bari nina zo, I want to give you something, something special” da sauri yace “kina amarya kifito akalle min ke lallai to naki, bari am coming” dan dariya tayi sanan tace “ni to ai kofar gidanmu da mutane banaso su ganmu tare ne saisa, Kuma su daddy ne da friends dinshi, saisa nakeson nazo am coming” katse wayar tayi tadau dogon hijabin ta har katsa tasa, Khadija dake shiryawa tacema “Ina zuwa, insu Ihsan sunzo afara miki makeup din, bari nakaima Khaleel wristwatch din” tafita daga dakin a tsakar gida taci karo dasu Mama da yayyin ta, kallonta daga sama har kasa Mama tayi tace “ina zaki haka” Kaman zatai kuka tace “Mama abu zanbama Khaleel a waje plzz” Mama zatai magana Yarta dasuke Kira da inna asabe tace “tafi kinji Eesha” ta kalli Mama tace “kibarta mana daga yauma gidan mijinta zata koma tabarmiki gida, tunda yana kiranta aisaitaje” da sauri tafice tana dariya dan tasan Mama da hanata zatayi, hango su Baba tayi a barander waje hakan yasa taja gaban hijabin ta dan karsu ganeta tazo ta wuce tafita sadaf sadaf daga gate din, da sauri take tafiya hartakai bakin titi, yana tsaye a shagon ya hangota zata tsallako kasan cewa kofar glass ne a shagon, murmushi yayi yacema Yusuf “am coming my queen wanna see me” hararan shi Yusuf yayi shikuma yajuya yafita daga shagon, tana hango shi ta sakin mai murmushi, murmushi yamata sanan ya mata alamu da hannu ta tsaya bari shi ya tsallako, murmushi tasake yi ta make kafada sanan ta kalli titi ganin babu wani abun hawa yasa ta shiga titi ta tsallake first lane, hakan yasa shi ya tsaya yafasa tsallakowa yana mata tattausan murmushi. Kaman ance ya waiga nan yaga wani trailer daya dauko yashi yataho dawani irin mugun gudu tsaki yayi yace “Wayan nan reckless drivers dinan ko” alamu yakara yima Eesha da hannu ta tsaya, gyadamai kai tayi Dan trailer kawai take jira yawuce ta tsallake titin nabiyu, kara taji hakan yasa ta kalli trailer da sauri tayan gaban ne yafashe hakan yasa motar fara kwana, ganin motar yayo dakalin tsakiyar titin datake tsaye zai fadi akai yasa tai ihu “subhanallah Wayyo Allah” tai baya da sauri ta fada titin bayan ta, kararrarraaa naji wani irin kara dayasa gabana bugawa.
[6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button