Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 44

Sponsored Links

Ahankali ya tsugunna agabanta yadaura hannayen shi akan gwuiwarta ta turemai hannu cike da masifa, murmushi yamata yace “stop crying to kinji” make kafada tayi ta cigaba da kukan ta, murmushi yamata yace “okay” tashi tsaye yayi ya cire babbar rigar shi ya zauna agabanta ya lankwashe kafa yay tagumi yana kallon yanda take kukan, hararan shi tayi sanan ta janyo hular hijabin ta tacigaba da kukan, dan dariya yayi ya sanya hannayen shi biyu ya maida hijabin baya hakan ya bayyana fuskar ta, turo baki tayi ta daga hannu kaman yanda yaro yake idan zai daki mutum tana kuka, murmushi yayi ya sanya hannayen shi ya rike kunenshi tareda langabar dakai ahankali yace “am sorry plzzzzzzz” kawad da kanta tayi tacigaba da gunjin kukan ta, ahankali yadawo ta inda fuskarta yake murya chan kasa yace “please stop crying ya isa haka, zomuje kiyi wanka let’s have dinner” yay maganan yana rikemata hannu, fizge hanunta tayi tace “bazan yiba” murmushi yasake yi ganin masifa takeji yau, matsowa yasake yi kusa da ita yakai bakinshi saitin kunnenta ahankali yace “oh are u shy? Okay bari ni naje nafara yi” kin kallonshi tayi saima goge goge hawayen datake yi, ahankali ya mike tsaye yawuce ya shiga wani yar corridor dazai sadashi da bedroom din, tashi tayi tsaye da kyar jin yanda cikinta ke ciwo waige waige ta dinga yi kozata ga wani abu dazata iya rubutu dashi, akan dining table ta hango wani leda dataga an rubuta thanks for coming ajiki, dama ya taho dashi ne danyabama mai gadi, budewa tayi taga memo da byro da goran bottle water da duk anrubuta sunanta da nashi ajiki, memo ta dauka da byro dan tsaki tayi dan wlh Allah yagani bayanda zatayi yine bude marfin byro tayi sanan ta rubuta “please I, I, please I need pad” sosai taji wani irin kunya nakamata ajiye byro tayi akan dining din sanan ta dawo cikin falon, ajiye memo tayi kusa da wayarshi tabar page din datai rubutun abude yanda dazaran yazo zai gani, ta koma kan kujeran ta kwanta tana tunanin gida da Farida.
Alamun tafiyar shi dataji yasa ta lumshe ido da sauri yana sanye da farin jallabiya sai kamshi yake, shigowa falon yay yana kallon fuskarta ganin memo kusa da wayarshi yasa yakarasa wajen dan yasan babu komi akan kujeran daya shiga ciki, daukan memo yayi ya duba, dago kai yay ya kalleta yana murmushi, daukan key din motar shi yayi dake kan center table da wallet dinshi yasa a aljihun ahankali yazo gaban kujeran datake ya tsugunna ba karamin bugawa kirjinta yayi ba jin ya daura hanunshi akan nata data daura akan cikinta yana shafa fatar hanun nata, dayar hanunshi kuma a saman kan hijabin ta ahankali yace “am coming bari naje nasiyo miki” dan dukowa yayi yamata peck a kumatu ya mike tsaye yana kallon yanda jikinta ke rawa murmushi yayi yafita daga dakin.
Abunku da GRA gabaki daya shagunan duksun kulle tsaki yayi yadau wayarshi sako yaturama Ihsan kanwarshi sanan yay kwana yadawo, agaban gidansu yay parking dayake tsakanin gidan da inda akakai Islam baifi gida uku bane tsakani, yana zaune a car Ihsan ta bude gate tafito sanye da Hijab hanunta rike da Leda tana kallon fuskar Khaleel tana murmushi, daure fuska yayi ya mikamata hannu tasaka mai tana dan dariya ciki ciki tace “ka gaisheta Ya Khaleel” harara ya zuba mata yace “nidan aiken kine” eh din tace taruga da gudu tashiga cikin gida murmushi yay ya kunna mota yabar wajen yay horn agaban gidansu mai gadi ya budemai yay parking motar yafito, bude kofa yay dayar sallama tana kwance inda yabarta idanunta a lumshe takowa yay inda ya barta ya ijiye ledan a gefe ahankali yakai hanunshi waist dinta hakan yasa ta firgita ta bude ido da sauri tareda ture hanunshi, murmushi yamata yasaketa sanan yadau ledan yabata ahankali ta karba tareda kawad dakai, hanunta ya kama yace “to tashi kije ciki kiyi wankan” uhn tace tareda turemai hannu folding hannayen yay a kirji ya tsaya yana kallonta ganin gabaki daya duk a tsorace take yasa yay hanyar kitchen yace “am going to the kitchen, jekiyi wankan ki” saida taga ya shiga kitchen din sanan ta wuce hanyar dataga yabi dazu, daki dayane tak a corridor hakan yasa ta bude dakin ta shiga babban gadone royal yaci hadadden zanin gado, sai wardrobe din bango sai yar center carpet a tsakiyar dakin kofar bathroom din tagani yabari abude ta wuce ta shiga tarufe. Takai kusan 10min atsaye tana tunane tunane wai yanzu shikenan haka dama ake aure, shikenan ta auri wanda Farida ke mugun so bayan tai rantsuwa bazata taba auren shiba yanzu ya hukuncin rantsuwarta?.
Jiki asanyaye tacire hijabi da doguwar rigar ta ijiye a gefe sanan tafara wanka, sai bayan tagama wankan tarasa yanda zatayi gashi ko kaya daya bata dashi kuma doguwar rigan yadan yi staining balle tamaida, hijabin ta dauka tasaka sanan tadan bude kofa kadan ta leka dakin hada ido sukayi daidai yana ijiye tray din abinci akan drawer dan murmushi yay ya dauke kai ganin she’s so uncomfortable, batare daya kalleta ba yace “am coming” ajiye tray din yayi yakoma gaban wardrobe ya bude wani dan madaidai cin akwati ya dauko ya kawomata nan gaban bayi ya ijiye batare daya kalleta ba ganin ya zauna abakin gado ya juya mata baya yana daddana waya yasa ta tsugunna ta bude akwatin wani doguwan rigan bacci ta dauko mai dan mutunci da undies sanan tadan dago kai ta kallai ganin baya kallonta yasa ta koma bayi da gudu ta shirya tass, rashin sabulu wanki yahanata wanke doguwar rigan, folding tayi tafito daga bayin sanye da hijabi ta tsugunna tasa rigan acikin akwatin sanan ta rufe ta daga akwatin tsaye, ahankali take tafiya tazo zata wuceshi ta fita da sauri dan wani irin tsoro taji tanaji yanda daga ita sai shi agidan nan, hanunta ya riko ya janyota ya daurata akan kafarshi da sauri ta mike tsaye jikinta har rawa yake, tashi shima yay tsaye yasa hannu ya yaye hijabin ta yacire ya wurga kan gadon da sauri tasa hannu tana kakkare gaban rigan kanta akasa duk jikinta na rawa, ahankali taji yakamo hanun yasaka hanunshi cikin nata ya zaunar da ita abakin gadon ya dauko tray din abincin ya zauna kusa da ita dan har jikin su na gogan juna, lafiyayyen fried rice ne da kaji sai cold exotic drink da bottle water ga magani data gani agefe, baice mata komiba ya debo rice din a spoon yakai bakinta girgiza kai tayi jikinta har baribari yakeyi tace “zan zanci dakaina” hannunta ta mika zata karbi spoon din ganin yanda hanunta ke rawa yasa ya ijiye spoon din ahankali ya daura hanun nashi akan nata yakai dayan hanun kumatunta yakira sunanta ahankali “Islaam, Hey relax is me” bata kalleshi ba, spoon din yasake dauka yadebo rice din yakai bakinta very calm yace “please” Ahankali ta bude bakinta kadan yasa mata taci da kyar ta iya tai 5 spoon sanan tace “am okay” bayason yatakura ta hakan yasa yadau maganin dake tray ya ballo kwara biyu yabata yana murmushi yace “for d stomach” Ya nuna cikin ta kawad dakai tayi ta karba yadau ruwa ya bata tasha tana yatsine fuska, tashi tayi tai hanyar kofa zata fita batare daya kalleta ba yace “kizo ki kwanta anan idan nagama cin abinci nixan kwana a falon” dan kallon fuskarshi tayi ganin baya kallonta kokarin debo rice yake hakan yasa ta dawo ciki ahankali tahau gadon nesa dashi sosai ta kwanta tareda jan bargo ta rufe jikinta duka kanta kawai tabari awaje.
Yaci iya cinshi shima yaji ya koshi yatashi tsaye rike da plate din kallonta yayi yanda ta takure waje daya ta juyamai baya murmushi yayi ya bude kofa yafita kitchen ya wuce ya ijiye tray din yafito falo yay locking kofa sanan ya kashe TV ya kashe wuta sanan yay hanyar bedroom din, bude kofa yay ya shigo hakan yasa takara kudundunewa, kashe wutar dakin yay sanan yawuce bayi yay kusan 10min sanan ya bude kofa yafito duk tana jinshi, agaban wardrobe ya tsaya ya cire jallabiyar jikinshi yamaida a hanger sanan ya ijiye, zagayowa yay ta inda take kwance ta bakibakin gadon ya tsugunna batare dayace komiba, azabure ta tashi zaune tana kokkomawa baya tana sheshekan kuka, hayowa yay kan gadon ya zauna agabanta tareda kunna hasken wayarshi ya haskata, kare fuskar tayi da hannu tana kara matasawa baya tana kuka ahankali, kafafun ta yakama yaza yana murmushi hakan yasa tai zuit ta kwanto flat, hayowa kanta yay batare daya hade jikinsu ba kulle idanunta tayi gam tana kuka sosai, ahankali yace “shiiiii” gum tayi ko tari bata karaba, hanunshi yakai tabayan wuyarta yadan dagota kadan yasa hanun ya zare ribbon din data kama gashin ta dashi ya yar akan gadon hakan yasa gashin ya barbazu akan filo ya tsaya yana kallon yanda ta kamkame idonta kirjinta na bugawa fat fat, wayarshi ya dauka ya kashe flash light din sanan ya kwanta a gefenta, hanunshi yakai yadaura akan cikinta hakan yasa takara zabura zata mike ya riketa tareda janyota tafado kan jikinshi.
[6/23, 1:42 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button