Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 77

Sponsored Links

Ta karaso inda suke tsaye tace “laaa nan kayo Sadiq daga shigana wanka fa” murmushi Islam tayi ta mika mata yaron, karban shi tayi tace “nagode, nanne gidanku bansan kowa a anguwan ba, jiya jiyan nan mukazo daga Abuja biki gidan baban shi, gidan yacika ne saisa mukazo nan gidanmu, Ya sunan ki?” gyada mata kai Islam tayi ta nunama ta gidansu tace “ga gidan mu nan” matar tace “ba shakka” juyawa Islam tayi ahankali tace “bye” komawa kan bencin tayi ta zauna hakan yasa Matar tabita da kallo kasa tafiya tayi saikuma tadawo inda Islam take, hakan yasa tadaga kai ta kalleta murmushi Matar tamata tace “Sunana Husna Maman Sadiq mekike yi ke kadai awaje?” jitayi kaman ta fama mata ciwo hakan yasa kwalla yataru a idonta, kawad dakai tayi da sauri tace “bakowa ne agidan mu saisa” “ayya to zomuje gidana muyi hira nima ai sai anjima bayan sallan la’asar baban shi zaizo ya daukeni muje dinner, zomuje” maida Sadiq tayi hanun haggun ta, tasa hannun dama takamo hannun Islam kaman tasanta, tashi Islam tayi ta bita badan tasoba suka shiga gidan gidane dan daidau mai kyau dashi ko ina sai kamshi yakeyi zaunar da ita kan kujera tayi sanan tacire hijabi ta ijiye nan kan kujera ta wuce kitchen ta kawo mata drink mai sanyi da snacks ta ijiye mata a gabanta sanan ta zauna kusa da ita ganin tanata kallon Sadiq dake wasa da kayan wasanshi anan tsakiyar falon tace “baki fadamin sunan kiba kawas” juyoda kai tayi ta kalleta ahankali tace “Islam” baki tarike tace “waiwaiwai Islam no wonder kike da shagwaba ai duk masu sunanku haka suke inada kanwa ma haka sunanta Islam” murmushi kawai tayi tace “ni bana shagwaba” “shine dan amfita an bakki ke kadai kike ta kuka ga idanun kinan sunyi jajir” da sauri Islam ta kalleta, dan murmushi tayi tace “bahaka bane kawai” shiru tayi tasa bayan hannu ta goge idanunta, ita kadai tasan yanda takeji bakaramin zafi kirjinta yake mataba, da hijabin ta lullube fuska jin wani irin kuka yazo mata sosai take kukan mara sauti tana wani irin sauke ajiyar zuciya, hanun Husna taji akan hijabin ta janye daga fuskarta hakan yasa tadago rinannun idanun ta kalleta da sauri ta tashi zatabar dakin Husna ta rikota “ina zaki?” Ahankali tace “gida zani” girgiza kai Husna tayi tace “zoki zauna babu inda zaki saikin fadamin meke damunki, zonan mai sunan kanwata” zaunar da ita Husna tai akan kujera sanan taja center table ta zauna agabanta tareda mikamata ruwa ta karba tasha kadan ta ijiye, dafata Husna tayi tace “mecece matsalar Islam? Wanan kuka haka bana lafiya bane? Bansan kiba amma wlh daga ganinki jinai kaman naga yar kanwata, kifadi mini matsalar kona taimaka miki da shawarwari dakuma addu’a” hartagama maganan bata dena kallon Husna ba girgiza kai tayi tace “bakomi kawai kawai” takasa magana “zurfin ciki na halaka mutane fa, yana sakaka cikin matsaloli dabaka taba zatan zaka shigaba, idan bazaki fadimini ba bazan takura kiba dan nasan yau kawai mukasan juna baki saba daniba, amma dai kidena saka damuwa aranki karya jamiki wata matsalar kinji mai sunan kanwata” gyada mata kai tayi tana tunanin maganganunta zurfin ciki da rashin fadama Farida labarin Khaleel tun lokacin data hadu dashi shi yajawo musu wanan matsalar fa, da sauri ta kalli Husna ahankali tace “zan fadamiki please bayan nagama fada miki ki gayamin me kuskurena” murmushi Husna tamata tace “ok inajinki to” shiru tadanyi kafin tace “Ya Khaleel ne matsala ta” saikuma tai shiru kaman tana tunanin wani abu Husna tace “waye Ya Khaleel” dan ijiyar zuciya ta sauke sanan tace “mijina” shiru tasake yi sanan tadago kai tasake kallon fuskar Husna hakanan taji zuciyar ta ta natsu da ita ahankali ta shiga bata labarin tun ranan farko tada fara haduwa da Khaleel filla filla har zuwa yau da safe abinda yafaru tagama labarin duka tana matsar kwalla kafin ta kalli Husna datai tagumi tana kallonta, tagumi Husna tacire tareda sauke ajiyar zuciya tace “wlh Islam kin tafka uban rashin hankali, ai gwara ya sakekin tunda ke banza ce mara wayau” da sauri ta daga kai ta kalleta kirjinta na bugawa, hararan ta Husna tayi tace “eh mana bake mai yar uwa ba kinacema mijinki mai sonki ya sakeki akanta ai shikenan ya sakekin, wai inama yan uwan mummyki sukene da suka barki babu abinda kika iya na zamantakewa da daraja miji” kwalla ta share tace “Abbana humanitarian ne, yana zuwa gari gari yana bada taimako yana taimakon mutane, to lokacin dayaje Sudan wani gidan marayu anan yaga Umma na tana fama da sikla shine fa yaji yana sonta dayake shi AA ne saiya auro ta yataho da ita nigeria, Ummana batada yan uwa, Mummy kawai na san yan uwanta” sosai Husna taji tabata tausayi hakan yasa ta sassauta murya tace “Islam abinda kikama Khaleel wlh bai daceba ki rokeshi ya yafemiki tun kafin lokaci ya kure miki ke yanzu dayake nuna ya damu da Farida yakike ji?” Ahankali ta shiga rera kuka tunawa da yanda ya dinga koyama Farida kwallo jiya datayi da kyar ta tsayar da kukan ta kalli Husna da rinannun idanun nan tace “abun cizona yake sosai azuciya” dan dariya Husna tayi tace “bari namiki ta hausanki idan kika gansu tare abin na cizan miki zuciya shine kuma zakice baki sonshi, nan gabama zuciyar taki yagewa ma zatayi gabaki daya in kika cigaba da ganinsu tare, ko kinfiso kiyita ganinsu tare ne yana bata kulawa?” girgiza kai tayi “yariga ya aureki babu aure tskaninshi da Farida, kinriga kin tafka babbar kukure, kin kira mijin ki wicked sanan ki cemai shine yasaki aduk matsalolin nan dakike ciki Islam, mutumin daya zauna dake lokacin dakike ba mutum ba yasoki ahaka yabar aikinshi yana jinyanki, zamanin nan a ina ake samin namiji haka, keme yar uwa ko, to wlh tun wuri ki bashi hakuri kafin ki rasashi gabaki daya ko so kike ya sakeki kikoma ma Fahad ne?” Girgiza kai tayi tace “ni banmasan inda Fahad yake yanzu ba shiya koranmin shi, kuma Mum ta karbi wayana hala yanata kirana baya samuna” saikuma tafashe da kuka da kyar tai shiru ta kalleta tace “Maman Sadiq wlh zuciyata zafi takemin” “aike kikaja ma kanki zaki bata auran ki akan wayanda basu damu dakeba, keme yan uwa gashin kin dameshi ya kawoki yabarki dasu kinata shan wulakanci anma hanaki zuwa asibitin” ahankali tace “Yaya zan bashi hakuri yariga yace nai zamana agidan mu zai aiko min da takardar” murmushi Husna tayi tace “Khaleel na sonki bazai taba sakin kiba, kece dai yanzu zaki lallabo shi ki shawo mana kanshi, akwai hanyoyi daban daban da ake lallaba miji abashi hakuri yanzu dai tunda kina gidan kune kuma anhanaki zuwa asibitin balle ku hadu duk randa yazo zakici gayu sosai kije ki dane jikinshi ki rungumo kayanki kina mammatse shi da kukan kissa ki cemai kin tuba ya yakuri” nan Husna ta shiga bata shawarwari da dabaru na gidan aure da yanda zata shawo kanshi sai wuraren 1 takoma gida salla tayi tafito jin Abba ya dawo tareda Anty Hindu gaishe su tayi Abba yace “maisa baki biyo Mummy kinje asibitin ba?” “kaina ke ciwo Abba” Anty Hindu tace “kindai sha maganin ko?” gyadamai kai tayi, Abba yay murmushi yace “ai muna ma tareda mijin naki a asibiti yakecemana zaidan barki anan anturashi wani assignment a Lagos zaidan yi kwana biyu dafatan dai kinamai addu’a sosai ko?” gyada kai tai ahankali dan bazata iya magana ba ayanda kirjinta ke bugawa Abba yay murmushi yace” masha Allah haka akeso akodayau she mace takasance mai yawan yima mijinta addu’a da fatan alheri, jeki huta idan ciwon kan baidena ba kizo kifadamin saina kira likita yadubaki” gyada musu kai tasake yi sanan takoma daki bakaramin kuka taciba ranan yanzu shikenan sakin nata zaiyi shine yakema su Abba kwana kwana, bahalin taje gidan Maman Sadiq dan sunriga sundawo.

Abangaren Khaleel ko kadan baiji dadiba dayazo hospital din baigantaba yana zaune ne kuma sako yazo daga wajen aiki ana neman su a headquarter dinsu na Lagos zasuyi wani assignment shine ya fadima Abba zaidan barta anan dan gobe zai tafi Lagos din idan yadawo saiyazo ya dauketa Abba yamai fatan alheri washe gari yabi jirgin safe zuwa lagos cike da kewanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button