Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 11

Sponsored Links

1kne 0811923761612
Jiri ta ji yana ɗibanta, kanta na juyawa zuciyarta tayi mata nauyi, wani abu ya tsaya mata a ƙahon zuciya, al’amarin daya kusan haifar mata da ɗaukewar numfashi na wasu daƙiƙo. Ta tsaya cak ta zama kamar wata statue, kallon Uncle Isma’il kawai take tana ƙara son jin gaskiyar abinda yake faruwa. Ganin kamar bata hayyacinta ya sanya Uncle Bello dake tsaye gabanta ya sanya hannu ya kama nata cikin nutsuwa da tattausan harshe ya ce “Shiga ciki, domin igiyar aure ke zagaye da ke yanzu” Abraham was spaceless kalma ɗaya ya iya ganewa shi ne “Aure”
Wannan dalilin ya sanya gurbataccen tunaninsa da rashin cikakkiyar sanin zallar Hausa ya sa tunaninsa ya yi ƙaura daga fahimtar abinda Uncle Bello yake faɗa.
“Uncle?” Ya furta cikin wata murya wacce zai wahala ka fahimci me ya sauya masa murya. Uncle Bello bai iya kallon Abraham ba ya juya yana faɗin. “Alhaji Isma’il talk to him” Uncle Isma’il ya ce “In sha Allah”
Yana faɗin haka ya ja hannun Malama Majeederh zuwa cikin gidan Uncle Isma’il, Abraham yana tsaye yana bin kowa da jirkitattun idanunsa wanda azabar abinda zuciyarsa ke ciki ne ya haifar da sauyawar launin su, ya ƙara rungume kyakkyawan Ɗan shi Ibrahimul-khalil wanda ya yi luff a ƙirjinsa yana barci kamar ya samu bayan Majeederh.
Ganin Uncle Bello ya shiga ciki da Malama Majeederh ya sa Abraham ya bi bayan su In his footsteps, like a full-fledged Muslim. Irin tafiyar nan ta cikakkun musulmai.
Bayan tafiyar su, cikin kamala da nuna isa irin na Uba da nuna bar martabar ƴar shi g dangin miji Uncle Isma’il.
“Allahamdulillah, da farko zan fara da yiwa His Excellency addu’a Allah ya bashi lafiya ya kuma tashi kafaɗonsa albarkacin Ubangiji” suka amsa da “Amin”
“Na biyu, ina son ku fahimta muna so da ƙaunar ƴarmu kuma zamu amsheta da hannu bibbiyu a duk sa’ilin da ƙaddara ta faɗa mata, abin nufi bi ma’ana bamu baku auren Hawwa’u a sbd ta rasa mijin aure ba, duk da ƙaddara ta kifta tare da yin kutse a cikin nagartacciyyr rayuwarta ba hana masu neman aurenta zuwa garemu da buƙatar su ta yin hakan ba, duba da shekarun baya duk yadda take a kame a nutse amma babu wanda ya taɓa furta kalmar “so” a gareta balle maganar aure ya shiga, kana taga Allah yana nasa, tayi imani hakan ƙaddara ne mu duka mun yi, sai gashi a yanzu daya kamata ta rasa mijin aure sai kuma maneman suke ƙoƙarin yi mata yawa, kaga babu mai yin haka banda Al-hakkamu sarki kowa da komai, mai juya ƙaddara zuwa abu mai kyau, mai jarabtar bawansa da jarraba mai wahala” Uncle Isma’il ya da kata kana ya kalli Shugaban Jam’iyya wanda yake tamkar Uba ga His Excellency Abu-turab. Ya ce
“Ina fatan wannan dalilin ba zai zama hujjar da za a gorantawa Majeederh ba, ba zai zama tubalin da za a gina shi a gidan aurenta har a hanata sakewa ba, Shi ne ya ganta ya kuma amince zai aureta a hakan nan, wanda har yake ƙoƙarin jefa rayuwar shi cikin garari, ina da tabbacin ba za a taɓa samun matsala daga Hawwa’u ba, haƙurin ta ya shige yadda kuke tunani, tana da zurfin ciki” Dattijon ya numfasa ya ce “Haka Uba na gari ya kamata ya kasance, kuma mun amshi amana zamu riƙe babu abinda zai sameta domin da ɗa da dukiya na Allah ne, ƙaddara kuma kamar riga ce zata iya faɗawa kan kowa, kada ka damu zanwa His Excellency magana da zarar jikinsa ya samu”
“To, madallah madallah dai” cewar Uncle Isma’il.
Ya juya zuwa ga P.a Hammad “Hammad kai abokin Abu-turab ne na ƙwarai, kasan halayyar shi mai kyau da akasin haka, ba ina doubting akan shi ba ne, ina son sanin mene halinsa wanda ya dace ace ko wane Uba ya sani a matsayin wanda zai bada aure?”
Hammad ya yi shiru kai a kai a ƙasa. “Ka ji tsoran Allah, a maganar aure ba wasa ba batun kuɗi da mulki babu wanda bashi da zuciyar da zata iya kai shi zuwa wani bigirin na sauyin hali, faɗa mini gaskiya” Ya ɗago kai tare da zubawa Uncle Isma’il idanu kafin ya ce.
“No!, actually no, he’s innocent bashi da matsala” Uncle Isma’il ya yi murmushi ya ce “Allhamdulillah” shugaban Jam’iyya da Dattijon su kayi godiya sosai, tare da nuna farin ciki na auren Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, da Governor Abu-turab Alƙasim. Sai Hammad motoci suka shiga kai tsaye kuma Government house sukai.
Tsaye Ya samu matar shi Hajiya Luba sai masifa take,ya ja ya tsaya tare da yin shiru yana son jin wannan masifar ta mece. “Fisabilillahi duk kin cika kunnen jama’a? Hala ke da Sona ne?”
“A’a, ni da Uban Sona da Jawaad ne, yanzu abinda ku ka aikata ya yi daidai kenan? Kamar kuna neman kai da Majeederh sai a ɗaura mata aure sama taka without her permission? Meke damunka tana da iko na zaɓawa kanta wanda take so take ƙauna kuma ai a bari ko yaye yaron tayi?” Uncle Isma’il ya ce “Tab ɗin, wannan masifar taki bata da gurbi yanzu, zuciyar fulani ta motsa kyaci kanki to” ta yi saurin tarar shi da
“Muci kan mu tare dai, naga alama shi His Excellency ɗin ka kewa baƙin cikin gyaran Fulanin Gombe, yadda ka susu ce a kaina ka ke takaicin ya ji haka?” Ya hangame baki tare da riƙe haɓa ya ce “Haba ko da na ji, cewa zaki Soyayyar da nake miki ba banza ba, to maza maza karya asirin da ki kaiwa zuciyata ina buƙatar ƙarin aure” ta maka masa harara irin ta wasan miji da mata sam bata ji daɗin hawan ƙawarar da su ka yi wa rayuwar Majeederh ba. Tana buƙatar hutu da nutsuwa tana buƙatar sanin waye zai so ta, so na gaskiya waye ba zai gorantawa ƙaddararta ba. Uncle Isma’il bai tsaya da maganar ba ya ce “Ki ji tsoron Allah Hajiya Luba, ashe shi ya sa kullum ki ke zaune daram a zuciyata, shi ya sa kullum nake ganinki tamkar alawa mai tsinke a leda, Oh! Ni Alhaji Isma’il Khan, Allah na tuba ka yafe mini ina da arziƙin yin mata huɗu amma sharrin matan fulanin Gombe ya hana”
Duk yadda Hajiya Luba ta haɗe rai bai hanata yin murmushi ba ta ce “Stop kidding me, ban ji daɗi ba, ban ji daɗi ba kuma still ban ji daɗi ba, yarinyata nada gata a bari ayi mata auren gata mana? Kuma batun ta tare yau babu shi” Uncle Isma’il dariya yake sosai he’s so friendly
“To me ƴa, ai sai dai ayi haƙuri aikin gama ya gama kada ki manta daman ita ba mai son bidi’a ba ce, ki yi haƙuri ko wacce mace darajarta ɗakin mijinta, a yanzu babu abinda Hawwa’u take buƙata irin aure ta zama cikakkiyar matar aure, damar data rasa a baya ita ta samu yanzu, ki dubi Allah ki yafe mini amma ki janye batun cewa sai tayi yaye ai daman ba shayar da shi take ba” Hajiya Luba ta ce “Idan daɗin baki ne ba daga nan ba”
“Da shi na siye zuciyar ƴar mutan Gombe” su kai dariya ya bata side hug ta zaro ido waje irin ya haka?. A tsaye ya samu Abraham wanda ya kasa zama har yanzu yana riƙe da Ibrahimul-khalil, haka kawai zuciyarsa ke faɗa masa something bad was gonna happen to him, babban damuwar shi yadda a karo na biyu daya hango tashin hankali akan fuskar Maluma Jee. Gabaɗaya Uncle Isma’il ya mance da Abraham gabansa ya faɗi, musamman daya tuna shi Abraham bai san ƙaddara ba balle ya yarda ya kuma yi Imani da ita, cikakken mabiyin addinin Yesu ne na Injila. Ga Grandpa ɗin shi cikakken Pasto ne, zuciyar su a gurɓace take. Ya nisa tun kafin ya yi magana ya ji saukar muryar Abraham ya ce
“What’s going on? Uncle?” “Nothing”
“Malumana, she’s crying” “She most” Abraham ya ware idanu yana ƙara rungume babyn a ƙirjinsa yana jin tamkar ya tsaga jikinsa ya mayar da shi sbd tsananin son da yake masa. Ganin kallon tuhumar da yake masa ya sa Uncle Isma’il ya haɗe rai, ya ce “Ba zamu shirya da kai ba, kuma ita Maminka ba dole tayi kuka ba acikin jama’a akan idanun manyan mutane dana mahaifinta ka sanya hannunka ka ɗauke ta? Sbd kai baka jin nauyin aikata abin kunya daman ka saba, ka ji ma da sanin bakwai jituwa da mahaifinta yadda ka mayar masa gida kamar wani muzuru duk sanda kayi niyya sai dai ka haura, to a hir ɗinka ba zan zuba idanun hakan ba, ko da wasa na sake ganinka inda Majeederh take sai na saɓa maka, banda abin kunya ba taci kashi da fitsarinka ta goyaka a bayanta ta yi maka wanka amma sbd….,”
“….. She’s not my mother” Unclu ya ce “Ba shakka” Abraham ya zube gaban Uncle kansa a durƙoshe ya ce cikin turanci “Na maka al’ƙawari sauya, zan zama yadda addininku yake son ya zama”
“It is too late to cry, Abraham” Abraham ya ɗaga gajiyayyun idanunsa kamar wanda ya sha ya yi tatul da basara ya ce “You’re kidding me, right?” Uncle ya yi shiru Abraham ya ƙanƙame Ibrahimul-khalil yana jin tamkar shi ya rage masa a rayuwa, daman tuntuni ya haƙura da mahaifina. Tausayinsa ya kama Uncle Isma’il ya ce “Kawo a kai mata ɗan?”
“…. No! Uncle help me kayi saving rayuwata, I love Mulumana, and am ready to convert to Islam ba zan ƙara taɓa Jeena ba sai ta zama halak a gareni” ya faɗa cikin turanci. Gabaɗaya ya rasa me zai ce.
“Ok, I’ll think about that” zan yi tunani akan hakan. Ya ƙara da “Kai mata babyn, ask her forgiveness sai ka je ka fara tunani idan kana son musulunta da gaske”
Ya miƙe cikin takunsa na isa kai ka ce cikakken Muslim ne yadda yake tafiya, yana tafiya arms ɗinsa na motsawa yana yin jikinsa har Mmk yake bawa Uncle Isma’il, ya yi kusan ukun Abuturab baƙar fatar jikinsa irin wacce ake so ɗin nan, so romantic and classic. Abraham is always stronger when he has Majeederh by his side, knocking ya yi ya daɗe kafin ya sanya hannu ya tura cikin kamo kalman da suka rage masa na Hausa ya ce “Salamu… Alayk” tana zaune saman kujera cikin abayar dake cikinta tun safe ta zura hannunta a tsakanin cinyoyinta sai girgiza ƙafa take slowly slowly, fuskarta tayi jajir kamar wacce ta ji ciwo haka ke tabbatar da ranta. ” I can’t believe this” Abraham said quietly. Da sauri ya ajjiye Ibrahimul-khalil ya zube gabanta tayi saurin ɗauke kai, girman Abraham tsoro yake bata, musamman idan ta tuna sanda yake yaro yana binta yana Mamina, gashi da son jiki da taurin kai baya jin magana bashi da tsoro. Ya jima da sanin rauninta ya san me sanyata magana ya san abinda zai sanya ta ji sanyi a ranta, but she hate him yana ganin ƙiyayyarsa a ƙwayar Idanunta. Ya rasa ta ina zai fara sbd sometimes bai wani iya rarrashi ba, One thing daya iya idan zai rarrashi mutum shi ne ya rungume shi, he just give a tight hug ɗin nan. Gently ya miƙe daga tsugunen da ya ke tare da fara zagaya ɗakin yana nutsa hannunsa cikin hargitsatsiyyar sumar kan shi. Da sauri ya yi kamar zai fita sai kuma ya sanya ƙafa da ƙarfi ya rufe ƙofar bedroom ɗin Majeederh tare da zura key ɗin cikin wandon shi….

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button