Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 2

Sponsored Links

2…….*
A raunace tana ƙoƙarin danne jaririn ta rarrafa zata riƙe mahaifinta, Abbu ya yi saurin ja baya yana nunata da hannu idanunsa sun yi jawur ya ce “Ɗan shege a cikin gidans? A tsakiyar parlourna Majeederh? Kina ta rayuwa da cikin shege a jikinki kina ce mana ciwo ne, ashe ni mahaifinki ki ka yaudara! Ki ka munafurta?”
Ya dafe ƙirjinsa abinka da farin mutum nan da nan fuskarshi tayi jajir.
“Allah ya isa, Allah ya isa tsakanina dake…,”
“Na shiga uku,Abbu” cewar Majeederh wacce ko motsi bata iyawa ga jikinta gabaɗaya jinin haihuwa ya wanke shi. Aaliyyah kuka take sosai ta durƙoshe gaban Abbau ta ce.
“Don Allah Abbu kada ka tsinewa Anti Jeederh, kada ka aibata ta ka ɗauki ƙaddara wacce zata iya faɗawa kan kowa, idan ka tsine mata da wanne zata ji, Abbu ka…,” Tsawa ya dakawa Aaliyyah ya ce “Aaliyyah da wanne suna ki ke amsawa a makaranta?”
Cikin tsoro ta ce “Aaliyyah Abdul’aziz Khan!” Abbu ya nuna Malama Majeederh da hannu ya ce “To daga rana mai kamar ta yau na haramtawa Majeederh amsa sunanta tare da nawa, na zareta daga cikin yarana, na haramta mata dukkan amfani da wani abu daya shafi sunana ni Abdul’aziz ko sunan familyna Khan” Tun da ya fara magana Malama Majeederh ta kafe mahaifinta da idanu zuciyarta ta fara daina aiki, Idanunta ya sauya tare da jirkicewa zufa ke yanko mata ta ko’ina jikinta ɓari yake, da sauri Ruma ta janye jaririn tare da sanya reza ta yanke masa cibiya,ganin Mabiya wato mahaifa bata faɗo ba ya sa ta nemi abu ta ƙulle jikin cinyar Majeederh.
Ruma ta saka hannu zata ɗauki jaririn domin ganin me Jeederh ta haifa Abbu ya ce “Ruma idan hannunki ya ƙara taɓa wannan shegen la’anannan yaron zan miki Allah ya isa kamar yadda na yiwa uwarsa”
“Kayi haƙuri Abbu” cewar Ruma. Mami duk abin da ake tana tsaye a gefe ta kasa cewa komai, idan ta kalli Malama Majeederh sai ta dawo da idanunta kan Jaririn.
Aaliyyah ta zube ta ce “Abbu me ya sa hakan? Zaka bawa Anti Jeederh tikiti shiga duniya da hannunka,bayan komai ta aikata kana da kamasho akai ba ita ɗaya ba, mene ya sanya zaka hofintar da MACE MUTUM kamar Anti Jeederh,ita ɗin haske ce, farin ciki ce ta ji da iya jarrabawar da take ciki ta rashin aure da kallon da jama’ar gari suke mata, kayi bincike Abbu, kada ka yi ladama a lokacin da bata da amfani”
Hannu ya sanya ya ɗauke Aaliyyah da mari yana huci ya ce “Ba zan taɓa ladama akan na rabu da wannan shaiɗaniyyar yarinyar ba, wacce ta cuceni ta cuci tarbiyyar dana bata, babu abin da zan iya cewa Majeederh sai Allah ya isa, ban yafe ba, ban yafe har na koma ga mahalaccina ba zan yafe mata ba” ya juya ya kalli sauran yaranshi da matarshi ya ce
“Ni Abdul’aziz Khan na yanke dukkan mu’amalar dake tsakanina da ƴata Majeederh Abdul’aziz Khan, ko da wasa ta ƙara ambaton sunana a matsayin ni ne mahaifinta wallahi sai na tsine mata, domin ni a wajena bata da maraba da gawa! Duniya ce ki je zaki gani”
Ba fatan gaskiya Majeederh take ba, ba kuma neman afuwar Abbu take ba, domin shi ɗin kaifi guda ne, amma tasan zai yi ladama a lokacin da bata da amfani kamar yadda Aaliyyah ta ce. Burin Jeederh shi ne Allah ya bayyana mata uban Jaririn nan, ko itama zata samu damar tsine masa, tayi masa Allah ya isa kamar yadda Mahaifin daya kawota duniya ya yi mata, ta yi masa mummunan fata a rayuwarshi ta yi masa addu’ar ɗaukewar dukkan wani jin daɗi walwala na tsayin rayuwa, damuwa da ƙunci su mamaye farin cikinsa, duhu ya maye gurbin hasken daya haska duniyarshi.
“Tashi ki ɗauki shegen danƙi ki bar mini gida” Aaliyyah kamar zata haukace ta ce “Mami ki sanya baki don Allah, Abbu ina Anti Jeederh zata nufa? shin tana da gidan da ya fi wannan ne?” Sai a lokacin Ruma ta ce “Aaliyyah kada ki sanya na fara zargin kema kin munafurci Abbu” Aaliyyah ta juya ta kalli Ruma ta ce “Me kike nufi?” Ruma ta ce “Ina nufin abin da kunnuwanki suka je yi miki, kin jima da sanin Majeederh nada cikin shege ki ka ɓoye”
Wani irin mugun kallo Aaliyyah ta watsawa Ruma ta ce “Ki ji tsoron Allah, kuma akwai ƙiyama, Mami do something”
“Something?” Mami repeated. “Don Allah” Aaliyyah ta sake furtawa Idanunta ya kumbura sosai, tausayin Malama Majeederh ya kamata tasan tunda Majeederh ta kasa cewa komai hakan na nufin abubuwa da yawa.
Mami ta kalli Majeederh ta ce “Ki duba Majeederh babu alamar dana sani a idanunta, ni kai na da nake uwarta ta yaudareni, sai yanzu nake mamakin abin da ya hanata aure ashe mu muke hauka ita ta jima da sanin kan ɗa namiji shi ya sa babu littafin aure a cikin littafan da take wallafawa, kin ja mana abin faɗa”
Da sauri Abbu ya ce
“Ta jawa kanta dai, domin ban haɗa komai da ita ba, ta je hakƙin Addinin Musulunci ma kaɗai ya ishe ta, kafin na buɗe idanu ki fice daga gidan nan”
Zuciyarta tayi nauyi bata da hanyar kare kanta, fatan ta Ubangiji data yarda da shi,kuma take bautawa ya bayyana gaskiya ya wanketa a wajan Mahaifinta ko da ba zai amsheta matsayin Ƴa ba. Ta juya ta kalli Jaririn ko Jaririya domin bata san me ta haifa ba, amma tasan samuwar babyn na nufin wani abu! Only God knows.
Da hannu biyu ta ɗauki jaririn ta miƙe da ƙyar jiri na ɗaukarta, ga wani ciwo da cikinta ke mata har yanzu mahaifa bata faɗo ba. Kanta a ƙasa cikin wata murya mai tsananin rauni wacce ko fita ba tayi sosai sbd yadda numfashinta yake riƙewa ta ce.
“Me ya sa zaka mai dani Gawa bayan da rai a tare da gangan jikina? Bayan da numfashi a ƙirjina? Me ya sa zaka bawa duniya ni Abbu wallahi bana da laifi ban san samuwar cikin ba, ban san waye da wannan alhakin ba, ban san waye yake da sanya hannu wajan ruguza rayuwata ba, ban san waye ya zama silar rabani da Mahaifina, dangina, haɗi da farin cikina ba, zan tafi Abbu ina roƙan ka yafe mini a duk sanda gaskiya ta bayyana ko da ƙasa ta rufe mini Idanu, zan raini kyautar ALLAH, zan raini Raba Gardama shi ne hujjar da zata iya fiddani daga zargi, Allah ya haɗa fuskokinmu da alheri”
Aaliyyah ta cire hijabin jikinta ta sakawa Majeederh domin rigar barci ce kawai a jikinta, kuka take sosai tana faɗin. “Kiyi haƙuri Anti Jeederh bana da ikon taimakonki na kasa aikata komai kiyi…,”
Kuka ya ci ƙarfinta ta juya da gudu ta shige ɗaki ba zata iya ganin tafiyar yayarta ta ba.
Gently Malama Majeederh ta kalli Mami, ta juya ta kalli Ruma, da kuma Raihana wacce bata ce komai ba har yanzu. Ta jima tana kallon Mahaifinta kafin ta nufi hanyar barin parlourn jiri na ɗaukarta, tana jan ƙafa wacce ko takalmi babu ta buɗe gate tare da ficewa daga cikin gidan, kamar yadda take barin gidansu haka numfashinta ke barin ƙirjinta, ganinta na janye wa, jinta na raguwa, jaririn hannunta na neman ƙwacewa zuwa ƙasa.
Tafiya take jini na bin cinyoyinta, tafin ƙafarta na taka kan titi, tun tana jurewa har ƙafarta ta fara rawa jikinta ya saki ta ƙanƙame jaririn a ƙirjinta, slowly slowly ta fara ganin duhu a Idanunta tayi baya luuu! Zata faɗi a kayi saurin tare ta, ta faɗa jikin mutum ba numfashi a ƙirjinta.

Hospital
A hankali aka buɗe Ƙofar room ɗin tare da mayarda ita aka rufe slowly. Tsaye ya yi a kanta ya zuba mata narkakkun idanunsa ya ɗauki almost 5 minutes yana kallonta kafin ya ɗaga ƙafarsa a hankali zuwa gaban bed ɗin, ya ja kujera tare da zama akai, cikin nutsuwa ya sanya hannu ya ɗauki jaririn dake kwance yana motsi cikin tattausan showel ɗin da aka saka shi. Soyayyar Jaririn ya samu gurbi a zuciyarsa musamman da bai taɓa samun ɗan kansa ba, bai taɓa ganin gudan jininsa ba. “Ohh baby, your Dad is here” ya furta can ƙasa gudun kada ya tashe ta.
“His Dad?” Ta furta cikin magagin barcin dake ɗaukarta domin allurar bai gama sarkinta ba.
Ya ɗago kai da sauri ya kalleta ba ƙaramin harbawa zuciyarsa tayi ba, this is the first time da yaga fuskarta babu liƙab iya tsayin shekarun daya santa.
Kasa magana ya yi domin duk yadda zuciyarsa ke fasalta masa kyanta abin ya shige haka, musamman da tayi maganar kamar wacce bata hayyacinta idanunta rufe gashin idanunta sun kwanta luf luf gwanin sha’awa fuskarta ta ƙara haske.
“Kin farka? Ya jikin”
Muryarsa ta daki dodon kunnenta yanzu kam allurar ta gama sakinta ta buɗe manyan Idanunta da suka kumbura tare da sauke ganinta akan Aliyu Sufyan Alhassan. Ta runtse idanu yau ƙarya ta ƙare fuskarta available, Allah ya rufa mata asiri jikinta a rufe yake.
“Sorry, In sha Allah komai ya zo ƙarshe zan wankeki wajan Abbu be patient” bata kalle shi ba, domin ƙirjinta ya yi mata nauyi babu wanda ya sake magana har Aliyu ya ce “I love my son, i love both”
“Ka barni” ta furta a kame cikin sanyin harshe. Aliyu ya gyara zama idanunsa akan fuskarta duk da bashi take kallo ba. “You’re dreaming, ba zan sake kuskuren baya Jidderh,ba zan sake ba, ina son rayuwa da yarona tare da mother’s of the son”
“Ni guba ce, zan iya zama illa ga kowa” ya tari numfashinta ya ce
“Ban dani Aliyu Sufyan Alhassan, ban dani Jeederh” ta juya ta kalle shi kallon daya kusa zautar da shi hannunta ɗaya a ƙirjinta ta riƙe sosai cikin nutsuwarta da kamilalliyyar muryarta ta kame kanta sosai ta ce. “Baka da haɗi da ɗana, kada ka yaudari kan ka ka duba kusancinmu da Latifa ka barni” “Jeederh idan na barki ki ɗauka na bar duniya, Latifa kuma ta bani full opportunity na aurenki” cikin gajiya wa ta ce “ba zaka saman ba”
“Koda na halattawa kai na zama Uba ga danƙi? Wallahi Majeederh na shirya ɗaukan ko wanne ƙalubale akan ki, kuma idan wannan yaron zai sanya ki aureni zan je court ta mallaka mini shi,wanne Irin mallakawa ma? Bayan blood grp ɗina da na shi ɗaya ne, ko DNA text za a yi zai tabbatar da ni ne uban shi” Wayarsa ce ta fara ringing sunan Wife ya fito ya ɗan ja tsaki har kiran ya tsinke aka sake kira lokacin Jaririn ya fara kuka, picking call ɗin ya yi tare da saka wayar a hands free.
Muryar Latifa na rawa ta ce “Sweetheart kana ina? 3days without you ina ka je ina ta kiran number ka a kashe” ba yabo ba fallasa ya ce.
“Ya akai Latifa?”
“Wani abu mai kama da almara ya faru, na kasa sanin babin da zan iya sanya Malama Majeederh”
Aliyu ya ce “Just go to the point Wife” cikin damuwa Latifa ta ce “Majeederh ta haihu,na goya mata baya amma ta bani kunya ta sanya ina yawo da ita har ina kare cikin shege?” Ya tare ta faɗin
“Who told you that?”
“Ruma, ta kirani tun a daren da abin ya faru lokacin na tashi naga babu kai babu motarka, kwana uku kenan yanzu haka Majeederh ta gudu da ɗan gudun surutun jama’a kuma ta shaida ɗan shege ne, Ruma ta ce Majeederh ta bayyana musu cewa daga gidan Abbu ba inda zata sai gidan uban ɗan taci gaba da zaman karuwanci da shi”
Duk maganar da suke Majeederh na ji, tuni ta amshe ɗanta daga hannun Aliyu ta rungume shi,tana jin kawo yanzu shi ne kaɗai ya rage mata, shi zata kalla matsayin wani nata kuma zata kula da shi da dukkan iyawarta har kawo lokacin da gaskiya zata kure ƙarya.
“Ke yanzu kin Yarda Malama Majeederh Abdul’aziz Khan zata iya aikata ZINA?”
“Me zai hana Sweetheart? Tunda ga gaskiya ta bayyana kuma Allah ya isa tsakanina da ita, na gode Allah da ya sanya baka aureta ba, balle mu haɗa iri da shege” “Ba shege bane”
Da ƙarfi ta ce “Wallahi shege ne” cikin tsawa mai firgitarwa ya ce
“Latifa Omar idan ki ka sake sheganta mini yaro zaki sha mamakina, zan miki hauka zan nuna miki true color na” Majeederh ta dafe kanta a hankali ta miƙe bayan ta zare ƙarin ruwan da ake mata, ganin Aliyu ya juya baya yana masifa jijiyoyin kansa na motsawa ta sulale a hankali ta bar room ɗin rungume da jaririn nata.
Kamar mahaukaciya haka ta zama, Latifa ta hargitse tamkar zata cinnawa kanta wuta ta ce “Aliyu Sufyan Alhassan kasan me ka ke cewa? Mene haɗinka da yaron?” Cikin rashin damuwa kuma daman ya shirya amsar ko wanne ƙalubale ya ce.
“Yes that’s my name Aliyu, kuma baki taɓa jin nayi hauka ba sai dai ina dab da shirin manna bikin haukan ke, tunda ba soyayyar gaskiya ki ke nunawa Majeederh ba”
Latifa ta zari key ɗin motar ta ce “Don’t Tell me kana tare da Majeederh tsayin kwanaki ukun nan?” Ya ware hannu irin he don’t care ɗin nan ya ce.
“Yhh, Ina tare da Ɗana da matata, Majeederh is my wife….

 

08119237616*🌈MIJIN MALAMA🌈*

Nimcyluv Sarauta
*_Arewabooks@Nimcylub_*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button