Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 20

Sponsored Links

MIJIN MALAMA
PAID BOOK
0811923761622
Mutumin dake zaune cikin motarshi ya zame idanunsa daga cikin nata a hankali ya rufe Ido yana jin abin da Latifa Omar ke faɗa. “You surprised me, Aliyu” Yana jinta dai bai ce komai ba, Latifa Omar ta ƙara cewa “Zuwan bazata har haka? Bayan am not in a dreams, kuma ba dare ba balle na ce?” Aliyu ya buɗe idanunsa cikin gajiyawa a gajarce ya ce “To ya na iya? My heart beating so faster” murya bata fita sosai ya ƙare maganar. Ganin Majeederh na ƙoƙarin shige su bayan daman tare za su fita ɗin ya sa ta ce “2 minutes please” Fita tayi da sauri harta isa ga Majeederh tana riƙe hannunta ta ce “Me kike ƙoƙarin yi? Bayan kinsan ke nake jira kada ki bari ƙwaƙwalwarki ta daina aiki ko ta samu matsala sbd tuna-ne-tuna-ne” Kallonta kawai Majeederh ta yi ba tare da ta ce komai ba. “Kizo muje, ya ce hanyar B.u.k ɗin zai yi shi ma” Yadda Majeederh ke kallon Latifa Omar yasa ta fahimci kusan dalilin kallo. Murmushi ta yi ta ce “Uhm I knw ur problem Majeederh, kina tsoran what those few people are going to say, right? Ai na faɗawa Baba ko waye kuma Abbu ma ya sani you can ask idan baki yarda ba, kawai if you trust me you have to believe” Majeederh da fararen Idanunta wanda suka kuɗe kawai ake gani,ta juya su a taushashe ta ce “Ke macace, ita mace sirri ce, sirrinki tsaraicinki ne, ki riƙe shi kamar tazugenki” Latifa Omar ta saka dariya mgn ɗaya kawai Majeederh za ta yi mai cike da ma’ana da azanci ta ce “Ok zan riƙe da hannu bibbiyu, Majeederh sbd ke na ce zai kaimu, nasan Abbu bai baki kuɗin mota ba, kuma is like compulsory to you na zuwa karɓo form ɗin, ki yarda dani in sha Allah nothing will happen as you think” Kafin Majeed ta yi magana ta yi gaba abinta hakanne kawai zai saka ta taho. Ta cikin madubin motar yake ƙare mata kallo har ta buɗe ta shiga sai a lokacin nauyin da zuciyarsa ke masa tun daren jiya ya saki, ciwon kan ya yi nasa waje. A ransa yake mamakin yadda ko kwalli bata sakawa cikin Idanunta. Key ya yi tare da yin reverse kana ya ɗauki hanyar da zata kaisa B.u.k new side…. Sun yi nisa sosai babu abin da ke tashi sai maganar Latifa Omar, Aliyu ya ɗan ya tsuna fuska yana tunanin yadda abu kamar wasa yake neman zamar mishi gaske, ya ce yana son Latifa Omar amma baya jin aurenta a ran shi duk da furta a baki, ya rufe idanu ya buɗe saman kwalta his heart disappointed him. Ya kasa daurewa ya ce “Na zama drivern kurma” Latifa ta ce “Kurma? Yana driver idanunsa rabi da rabi akan madubi ya ce “Ur friend, Jiddatul-khairy” Latifa ta buɗe ido kana ta juya ta ce “Malamarmu, Malama Majeederh mijin da zan aura ba sai anja masa aji? Ba gaisuwa” Aliyu-haydar ya ce “Hakan kuma ba halin Malaman ƙwarai bane” Duk tana jin su sai da suka gama surutu da wajan minti biyu suka ji ta ce “I don’t want interfere” Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Aliyu ya sauke lokacin muryarta ta sauka cikin kunnenshi, ba zai iya cewa ko ranar daya fara ganinta ya ji muryarta ba, sbd baya cikin nutsuwarsa ji yake kamar new Aliyu akai a lokacin ba shi Aliyun ba, sai ya ji kamar bai taɓa jin murya irin haka ba in his whole life, sanyi, nutsuwa, haƙuri da kamalarta duk ta bayyana cikin maganar da tayi ta kalmomin da baza su gaza biyar ba. Suna zuwa cikin B.u.k ɗin Majeederh ta fita babu jimawa ta dawo lokaci Aliyu na zaune hannunsa riƙe da Swn water yana sha ganin yadda ta yi tsaye ta kasa knocking Glasses ɗin motar yasa gently ya saka hannu ya fito daga cikin motar yana zuba hannu a aljihu tare da juyawa ya dinga ganin Students different department suna ta zirga-zirga. Ya kalli Majeederh ya ce “Jiddatul-khairy, you are too…” Da sauri ta ɗaga kanta a tunaninta ko yau Allah zai sanya wani namijin ya ce tana da kyau, saɓanin Uncle Isma’il da yake cewa tana da kyau da kuma ƴan-uwanta mata sai ta ji ya yi shiru ya ce “Kin gama ne?” Ta girgiza kai tana addu’a a zuciyarta Aliyu yana son ya ƙara jin muryarta ya ce “Mene ya faru? Me bada form ɗin ne baya nan ko?” Har ranta ta gaji da magana ga yunwa sosai take ji ga kewar Little da rashin sanin inda yake ta marairaice kamar za ta yi kuka sosai ta ce “Uhm ba nan bane” Aliyu ya ware ido hadda riƙe ƙugu ya ce “Oh ni Haydar sai aka ce ina?” Batai magana ba har Latifa ta fito daga cikin motar ta ce “Meke faruwa nan?” Aliyu ya yi mata shiru Majeederh ta ɗauke kai can ta ce “Murtala way” Murmushi kawai Aliyu ya yi ya ce “Oh Kano state ministry of education, i think Government office?” Ya faɗa yana duban Majeederh “To yanzu can zamu kenan? Domin idan muka koma gida ba wannan form ɗin mun shiga uku wajan Abbu kwana zai yi yana faɗa” Aliyu ya ce “Waye?” Kai tsaye Latifa Omar ta ce “Her father” Sosai ran Majeederh ya ɓaci Latifa na son nunawa Aliyu Mahaifinta masifaffe ne ko yana takura musu ta ɓata fuska duk da ba’a ganin yanayin nata. Cikin Aljihu ya saka hannunsa ya ji ba kuɗi ya juya yaga babu wani pos a kusa da su, babu cash da sauri ya juya mota tuna cewa kamar ya bar kuɗi ciki jiya daya siyi Popcorn 2k ne ya miƙawa Latifa ya ce “For transport, ku yi amfani da shi wajan napep ina da shari’a 1:00” Latifa ta ce “Ok bye” Ya girgiza kai kawai jin ko godiya babu bawai kuma damuwa da hakan ya yi ba, Majeederh ya san ba za ta yi magana ba…..
Sun jima cikin haɗaɗɗen office ɗin na commissioner for education ɗin, kafin a hankali su ji an shigo duk suka miƙe tsaye ya nemi waje ya zauna, magidancin mutumi ya zauna saman kujera, babba ne mai shekaru amma kuɗi sun zauna rayuwar daula ga hutu da kwanciyar hankali plus jin daɗin rayuwa. Ya amsa gaisuwa ya ce “How can I help you?” Majeederh ta yi ƙasa da kanta a hankali ta ce “Sunana Majeederh Abdul’aziz Khan, ance na zo na amshi Form na scholarship ɗin da akai mana al’ƙawari ranar Candy da Musabaƙa” Ya jinjina kai ya ce “Ok” Kana ya shiga jawo file gefe ɗaya kuma yana danna waya ya ce “I, Alhji Aliyu S, Commission for education” Bayan sun amshi form ɗin ya haɗa su da wani ya yi musu bayani, Sai dare Majeederh ta ci abinci towon masara biyar kuɓewa bushasshiyya bacci ɓarawo shi ne ya ɗauketa. Washegari babu inda ta fita sbd ciwon kai da zazzaɓi tana ta kiran number Akeeth shiru a kashe. 5days left da yamma ranar laraba tana zaune a ɗaki tana tunanin hanyar da za ta yi cigiyar Little sai kawai ta yi ta sauke application ɗin facebook ta buɗe Acct da full name ɗinta Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, ta saka photon Little cikin uniform da rubutu mai tsayi da ma’ana, tausayi da neman taimako. Comment ɗin data gani ya ɗaga hankalinta zuciyarta tayi nauyi, ta ji kanta na juyawa komai ya yi mata zafi, ta ƙara buɗe Idanunta akan comment ɗin da aka ce mata “Ke aure ya kamata dake, shekaru sun ja” Ta cillar da wayar tana miƙewa tsaye kena kowa ya san bata da aure? Me ya sa ake son goranta mata yin aure ne? Ita zata aurar da kanta ne ko ita za taga namiji ta ce tana son auren shi? Ta ƙarasa gaban madubi ta shiga kallon kanta Majeederh ba zata iya tantance da gaske tana da kyau ko bata da shi ba, tasan dai ita fara ce ba ruwanta da Powder, kwalli, lipstick kullum fuska a rufe cikin liƙab sai duguwar riga da take sawa ko ƙaton hijabi. Ko dai gwada fita za ta yi babu wannan abubuwan? Idan ta fita hakan zata samu wanda zai ce yana sonta? Ta yi shiru… Washegari Alhamis bikin Widad ya kama yau za a fara za su yi Arabian night. Gabaɗaya suna zaune a parlourn gidan Uncle Isma’il, ga Uncle Bello ga Abbu sai Yaya Bilkisu da Innati. Uncle Isma’il ya ce “Na fahimci matsalarka Abdul’aziz, sbd baka da ɗa namiji shi ya sa ka ɗauki Majeederh kamar namiji? Tunda ita ce babba, duk abinda yake faruwa na sani, kawai zan maka cewa ba ka yi kanka da ƴarka mai hankali adalci ba, Majeederh does not deserve this Abdul’aziz, idan karatu ne kaima kana iya faɗaɗa naka kaje ka ƙaro ilimi, idan ma hakan kake so ta yi why not ka fara yi mata aure first sai karatu ya biyo baya, kaga da mijinta da komai babu wata fargaba, amma Fisabilillahi ka ɗauki Majeederh wacce take kan shekarunta na balaga tun daga Nigeriya zuwa Misira? Kasan halin da zata kasance a tsayin shekaru takwas ɗin da za ta yi? Yanzu ko namiji ne ka sadaukarwa ilimi shi ba tare da tunanin lafiyarsa ba?” Abbu ya kalli yayan nasa Uncle Isma’il ya ce “Lafiya kuma? Ina tunanin ai akwai kulawa ta makaranta?” Uncle Isma’il ya ce “Ok bari na na fito maka a mutum, idan Majeederh ta buƙaci namiji makaranta zata bata? Ko maza zata fara bi? Ka haifi yarinya a cikinka amma You don’t even know abinda ke damunta, da abinda take so ba, Majeederh Allah ne kawai yake kula da ita kuma shi ne ya bata yawon da take da shi, gata ƴar fari ga babu kulawar uwa data uba a wajanta” Sai a lokacin Yaya Bilkisu ta ce “Allah na tuba gata dai kyakkyawa amma ai babu mai ganin kyanta bata da kaya sai duguwar riga kamar haihuwar Larabawa, ai Allah ne ya san manufar Fulani da tace ka aurar da ita tun tana 15 amma kaƙi, ka ci mana wasiyya Allah ya sanya ta fito da kabari tai maka fatalwa sai ka fahimci tashin hankalin da take ciki” Innati ta zare idanu ta ce “A’a ba amin ba wannan kuma ai fatan tsiya ne meye kuma fatalwa ana zama lafiya abi dai komai a nutse tunda shi ya ce karatun take so ku zuba masa idanu idan yana laifi sai ya yi, duniyar gabaɗaya nawa take? Allah na tuna ya rubuta ya ajjiye komai ya faru ya shirya amsa” Uncle Bello ya ce “In sha Allah babu abin da zai faru, da dai ya barta tayi auren shi ne kawai” Abbu ya ce “Aure fa baya bari ayi karatu by the way waye ya ce yana son aurenta na hana?” Duk su ka yi masa shiru haka dai taron ya tashi ba fahimtar juna tsakanin Abbu da Uncle Isma’il da ƙaninsa Uncle Bello, familyn Khan maza ba su fiya yawa ba mata duk sun fi yawa. Majeederh na parlour ta yi shiru tana kallon yadda ƴan matan suke shiryawa cikin abayas baƙa Ruma jiya Imran ya bata, Raihana ma saurayinta ne ya siya mata, Aaliyyah kuma Majeederh ta siya mata da kuɗin albashi. “Anti Jeederh ba zaki ba?” Majeederh ta kalli Ruma ta ce “Eh” Aaliyyah ta ce “Amma me ya sa Anti Jeederh?” Ta yi musu shiru kawai Mami ta ce “Hawwa’u me ya sa baki son shiga cikin ƴan uwanki ne?” Ta ce “Ba komai” cewar Majeederh tana rufe ido Mami ta ce “To Allah yana kallo na yi nawa yin, Majeederh idan kana da kyau ka ƙara da wanka amma dai kuma ta wani ɓangaren kina da gsky tunda duk kin girme su sai dai ko Sahar” Aaliyyah ta ce “Kai Sahar ɗin ce sa’ar Anti Jeederh? Naga na girmeta da shekara ɗaya ma” Mami ta ce “Ji ƙuruciya to ai duk wanda ya yi aure ya zama sa’anta yanzu hirar da za ayi da Sahar waye zai yi da Majeederh?” Majeederh ta miƙe tare da shigewa bedroom ɗinta zuciyarta a cunkushe ji take gwarama kawai ta tafi karatun ta huta zuciyarta ta samu salama. Gidan Uncle Isma’il akaiwa decorations ya yi kyau sosai bride mate da friends ɗinta sun yi kyau aci make up, ga abokan ango sun kyau yawancin su classic ne masu aji ilimi ga wadata ta iyaye. A hankali Majeederh ta sako ƙafarta cikin harabar gidan kiɗa na tashi zuciyarta sai rawa take for the first time data zo event har haka, wanda kuma bayin kanta bane tabi ragamar zuciyarta akan abinda take jin kamar shi ne daidai, abaya ce mai ƙaton hannu a jikinta ga faɗi da take da shi ta yi mata yawa sbd ramewar da tayi, tayi rolling kanta a hankali ta saka hannu ta zame liƙab ɗin fuskarta a karo na farko in her whole life data cire liƙab a gaban maza tafiya ta fara yi zuwa wajan, gabaɗaya idanun jama’ar wajan suka dawo kanta duk wanda ya ganta sai ya taɓo na kusa da shi ya nuna masa Majeederh daga mazan har matan, ta ci-gaba ta shiga cikin wajan tana zuwa dab da wani matashin mutum tun kafin ta ƙarasu ya juya da sauri kamar yaga Aljana yabar wajan jiki na rawa……

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button