Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 33

Sponsored Links

*BOOK 1 PAGE 32*
*MIJIN MALAMA*
_littafina na kuɗi idan kina so ki biya ki karanta…. 08119237616 ko yayane kada ki karanta free without my permission please siyan littafinmu shi ne nuna soyayya a garemu🫂_

*Ƙaddarar mace abace mai wahala musamman ƙaddarar za dinga maka gori da ita, ana ganin kamar ganganci ne ko kuma kai ka ɗorawa kanka ba yin Allah bane🥹 Yadda da ƙaddara shi ne cikar imanin mutum, Ubangiji bai baka abu ba hakan na nufin abin nan ba alheri bane a gareka da rayuwarka, ƙaddara na tafiya da lokaci shi kuma lokaci ne abu ne da baya jira, hakan na nufi ita kanta ƙaddarar ba tabbatacciyya bace, akwai lokacin da zai zo ta zama tarihi… Wani jinkirin alheri, rasa abu baya nufin rasa rayuwarmu hakan wata dama ce da Ubangiji ya baka wajan gane laifinka da kuskurenka, wasu suna sakaci da addu’a, wasu kuma rashin biyayya ga iyaye, wasu kuma ruɗin ƙawaye, wasu kuma ƙaddarar ce dai…. Idan aka haɗa zamu fahimci gabaɗaya lokacin kowa ne bai ba, da zarar lokaci ya yi komai zai zama shuɗaɗɗen, cimma manufa bashi iyawa ma, cimma nasara da tsayawa akan ra’ayinki shi ne cikakken mutum. 🌚 NO MAN IS THE MAN WITHOUT A WOMAN🫰🏽🤘🏼*33
Murya na rawa ya ce “Don Allah ku tausaya mini wallahi ban taɓa son ta ba, balle na ce zan aureta, why should I? Allah kuka aura mini ita mutuwa zan yi mana son ta, bana ƙaunarta, kada ayi mini auren dole” Ya faɗa His voice was shaking. Yanayin yadda kowa ke binsa da kallon mamaki ya sanya shi ƙarasawa gaban Uncle Isma’il ya ce “Kun sai dai ni ba mahaukaci bane? Balle ayi mini uzurin taɓin hankali, I don’t know what is going to happen to me, I don’t know when this happened…..,” Tass! Mama ta ɗauke Alpha da mari, without letten him to recover ta ƙara sauke masa wani wanda ya sanya shi yin baya sai kuma ya dawo ya tsaya da ƙafafuwan shi dafe da kuncinsa tayi pointing ɗinsa da yatsa ta ce. “Idan ƙwayar ku ta sojoji ta faɗa maka ba daidai ba, ko allurar da ake muku to gabaɗaya haukanka ya zama na banza a nan, kayi kaɗan kayi tsararo bamu haifi ɗan da zai juyamu ko ya raina mana hankali ba, We are your parents, you are the child we gave birth to, we have the power to pass the sentence on you….” Mama ta ja ƙwafa ta ce “Let make it clearly for you, idan harni na ɗauki cikinka wata tara, na haifeka na baka nono na, naci kashi da fitsarinka wallahi wallahi ko zaka mutu ka farko sai ka auri Majeederh aurenka da ita a gobe babu fashi” Ta faɗa Sounding very angry. “…. Mam….”
Alpha’s Expression softened slightly as he looked at her ya juya ya kalli Majeederh wanda take zaune kamar anda sata, bata ko motsi sbd tsananin tashin hankali ruɗu da fargaba, da kuma tu’ajujjin abinda yake shirin faruwa da ita, An fasa aurenta? Kuma ranar ɗaya kasance saura kwana ɗaya a ɗaura? Ko dai ba ita jin ake nufi ba? Fizgota da Alpha ya yi ya sanya ta dawo daga hayyacinta ta dinga kallonsa kamar zautacciyya a hargitse ya ce “Kiji tsoran Allah Majeederh ki faɗa musu gaskiya, tunda nake na taɓa cewa ina son ki? Yaushe na sameki nace zan aureki kada ki bari a cutar dani ina da wacce nake so” Majeederh ta girgiza kanta tana jan jikinta baya ƙirjinta na ɗagawa sama tana dafe saitin zuciyarta ta ce “Me ya sa zaka zaɓi tuzartani a lokacin dana saka rai da samun ƴanci kamar ko wacce mace? Me ya sa zaka samun son abin dana fidda rai da samun shi? Me ya sa ka dawo da kwaɗayin kasancewa ɗaya daga cikin matan da zamu martabar aure bayan kasan ba haka bane? Me na yi maka a rayuwa daka nemi ɗaukan fansa ta hanyar da zuciya ba zata iya ɗauka ba? Me ya sa ƙaddara zata juya ta zo mini ta hanyar da ba zan iya jure mata ba?…” Ta girgiza kanta duk wannan abun jikinta ƙyarma da ɓari yake kamar mai shirin yin jijjiga ta zube a ƙasa saman ƙafafuwanta tare da rarrafawa ta riƙe ƙafar Alpha ta ce “Ko a lissafin ƙaddara ban taɓa lissafa zuwan wannan ƙaddarar ba, ka tausaya mini ka aureni kuma aure zaɓin zuciyarka, zan zauna da kai a haka koda baka so na, koda zan zama ƴar aiki a cikin gidanka dakai da matarka, wallahi ba zan iya jure wannan ƙaddarar ba fasa aurena da zakai daidai yake da tsayawar numfashina” Majeederh ta ƙara ƙanƙame ƙafafuwan Alpha ta ce “Tunda na buɗe idanu naga kana damuwa da duk wata damuwata naji babu wanda ya dace dani sama dakai, zuciyata ta ƙauna ce ka Yaya, ƙauna mara algus ina sonka zan zauna da kai komai wahala, ƙunci, damuwa,takura ka rufa mini asiri kamar yadda Allah ya rufa maka kada ka muzanta ni kada ka sanya na sama abar kwatance a dangi da kuma unguwa ka dubi girman Allah ka amince da aurena wallahi da bakinka kazo mini da maganar da……,”
“Stop it, stop!” Alpha ya faɗa yana janye ƙafarsa daga gareta ya ce “Wallahi ba zan iya aurenki ba, baki mini komai but i can’t be your husband, i don’t love you anymore ki barni na aure wacce nake so ni ko zan takura miki ba zan iya aurenki ba ni ma kiyi mini wannan rufin asirin” Ya faɗa yana riƙe kansa da hannu bibbiyu.
Majeederh ta kallesa irin kallon ka rusa mini rayuwata kafin ta ce
“What have i done to deserve this from you?? Wallahi ina sonka ni” Aaliyah ce ta tashi tare da ƙarasawa wajan Majeederh ta ce “Anti Jeederh ki barsa Allah zai kawo miki naki rabon, ya yi haka ne domin ya kunyata ya sanya ƙaddararki ta ƙara tsamari” Majeederh ta girgizawa ƙanwata kai ta ce “No Aaliyah ba zan iya jure gorin aure a wannan lokacin ba” Kuka sosai Aaliyah take kamar ranta zai fita, tana tausayawa halin da yayarta take ciki. Anti girgiza ƙafa kawai take lokaci zuwa lokaci take jan ƙwafa, Abbu tunda aka fara maganar ya sunkuyar da kansa ƙasa baka iya gane yanayin da yake ciki, wai ƴar cikinsa take durƙoshe tana roƙan wani ya aureta? Me ya yi mata da zata nemi tuzarta shi har haka? Mami ta yi jigum idan ranta ya yi dubu to ya yi tsatsa ya lalace, kana ganin yadda idanunta ya yi jajur zaka san zuciyarta a kusa take. Uncle Isma’il kallon Alpha kawai yake, Uncle Bello ya dubi ɗan nashi ya rasa me zai ce masa he really disappointed him. Innati zare idanu tayi kana ta ce
“Komai yana da lokacin, lokacin bayyanar hakan ne ya yi kada ku damu, gaggawa aikin shaiɗan nasan za rina ansaci zanin mahaukaciya na jima da ganin wannan rana” Ganin babu wanda ya ƙara cewa komai ya sa Uncle Bello ɗaukan wayarsa ringing ɗin farko aka ɗauka cikin sauri ya ce “Liman kayi haƙuri an samu matsala a invitation card ɗin nan, ɗaurin auren ƙarfe 9:00 na safe sai a sanar a masallaci” A gigice Alpha ya kalli mahaifinsa ya ce “Abba me na yi maka da baka son farin cikina? Wallahi kuka aura mini Majeederh zan kashe kaina” Wani Mahaukacin mari Uncle Bello ya sauke Alpha kafin ya dawo hayyacinsa Mama ta ƙara sauke masa wani, ganin haka yasa Widad fashewa da kuka sosai ganin yadda ake marin yayan nata Uncle Bello ya nuna Alpha da hannu ya ce “General Ajzan-Alpha Bello Khan wallahi yau ko da gawarka ne sai an ɗaura aurenka da Hawwa’u” Alpha ya juya ya kalli Majeederh ya dawo ya dawo ya kalli Uncle Bello muryarsa bata fita ya ce “Sai a ɗaura da gawar tawa”
Yana faɗin haka ya fice daga cikin parlourn, Majeederh ta miƙe zata bi bayansa sai a lokacin Anti ta ce “Kada ki kuskura ki bi bayan wanda bashi da imani” Uncle Isma’il ya miƙe da hanzari ya ce “Kada Alpha ya cutar da kansa fa?” A takaice Uncle Bello ya ce “Rabo dashi daidai nake da zamaninsa, he really disappointed me ya nuna bashi da biyya ban isa da shi ba” Kafin kowa ya yi magana aka ji faɗuwar abu gabaɗaya suka juya Majeederh ta faɗi babu numfashi a ƙirjinta…..

Duk da kiran asubar da ake bai sanya ɗaya daga cikinsu ya motsa ba, ko wanne ka kalli fuskarsa za kaga tashin hankali musamman Dattijan mazan. Uncle Isma’il ya saka hannu ya sharce zufar data gangaro masa yana cire hular kansa ya ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Ya juya ya dubi Uncle Bello daya kasa cewa komai idanunsa ya yi jajur ya kalli Mama dake rusa kuka sosai ya ce “Wai mene ya faru mai zafi har haka da yaron nan zai mana wannan cin mutunci?” Mama ta share hawayenta ta ce “Idan ni na haifi Alpha da cikina to wallahi…..,” “A’a please” Anti ta tare ta da sauri wanda ya hana Mama ƙarasa faɗin abinda tayi niyya. Uncle Bello ya ɗago kansa ya ce “Ɗan cikina? Ɗan dana haifa Isma’ila?” Uncle Isma’il ya sauke numfashi ya ce “Dole akwai wani abu, yadda Alpha ya birkice kamar Mahaukaci sabon kamo zaka san something is fishy?” Jinjina kai kawai Mama take kafin suyi magana motar Abbu ta shigo cikin compound ɗin gidan Uncle Bello wanda aka baza rumfuna na ɗaurin aure, Abbu ya jima cikin motarsa kafin ya buɗe ya fito da sauri Mami ta fito tana mara masa baya, tun a balcony kafin su ƙarasa ƙofar parlour suka fara jiyo kukan Mama, Mami kamar zata kifa haka ta bangaje Abbu ta shige “Ba dai an fasa auren ba?” Abinda Mami ta faɗa kenan tana binsu da idanu, Abbu ya shigo tare da jingina da jikin bango can ya ce “Isma’ila, Bello na ji kira cikin gaggawa gashi ina ƙoƙarin rasa sallar asuba?” Uncle Isma’il ya miƙawa Abbu white paper ya ce “Read, karanta” Har Abbu yaƙi amsa sai kuma ya saka hannu ya karɓa tare da buɗewa hannunsa na rawa idanunsa ya sauka akan handwritten ɗin Alpha da yake cewa….

Related Articles

DEAR PARENTS.
_Bani da baki ko kalmar da zan muku bayani wajan fahimtar daku abinda nake nufi, amma na zaɓa mana hanya mai sauƙi da warware ƙullin da yake ƙoƙarin raba zumunci, ban kashe kaina ba, ban kuma zauna a cikinku na ɓata muku sunan family ba, more especially mahaifina, kayi mini komai a rayuwata ta duniya har kawo lokacin da nayi wayo na girma na mallaki hankalin kai na, Ina son Majeederh a matsayinta na ƴar uwata wacce jinina da nata suke yawo a jijiyoyin ko wannenmu, amma bana sonta ta aure bana ƙaunar zama da ita, akwai yarinyar da nake so a duk sanda kuka amince mini zan gabatar muku da ita a matsayin matar da zan aura kuma sirikar ku._
_Naso karɓarta matsayin mata kuma nayi muku biyayya, amma wallahi zuciyata ta kasa yarda da wannan ƙudirin idan na auri Majeederh ba zan iya sauke hakƙin aurenta akai na, zanta cutar da ita, zata zama bora a cikin gidana, zan wulaƙanta ta, wulaƙanci da human rights za su iya hukantani, zan muzantata, muzancin da babu macen da aka taɓa yiwa irinsa, zata zama baiwa a cikin gida, irin bayin da ba a samun su a yanzu sai ƙarnin baya irin bayin gidan sarauta ɗin nan, zata zama almajira a cikin gidan mijinta, To idan zan iya aikata mata duk wannan gwara ban aureta ba, nima ina mata fatan samun rayuwa mai ƴan-ci, ina gudun na tashi da ɓari ɗaya a shanye rana gobe ƙiyama_
_Babban Dalilia na rashin aurenta shi ne, Ni mashayi ne, ni mazinaci ne Majeederh bata dace da mutum mara tsafta kamar ni ba, ku yafe mini don girman Allah, kuji tausayina kada ku aibata ni, zan dawo duk sanda kuka yarje mini idan kuma mutuwata ta riskeni ina roƙan kuyi mini addu’a da samun dacewar Ubangiji!_

~G.A.B Alpha~

Abbu ya ɗauke numfashi lokacin da idanunsa ya sauka akan kalma ta karshe, date da time. A sanyaye ya ce “Yaushe ya tafi?” Mama ta ce
“Ya tafi ko ya gudu? Wallahi ƙarya Alpha yake baya Shaye-shaye, duk mutum bai hali irin wannan baya zama inda yake, ya tsani zin kamar yadda ya tsani fitar hawayena” Anti ta ce
“Me ya sa zaiwa kansa irin wannan tabon to?” Uncle Isma’il ya ce “That’s what i was thinking too” Wayar Abbu ce tayi ƙara ya ce “Ina zuwa” fita ya yi yana ɗaga kiran ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce “Thank you, na gode sosai” Ya kashe wayar kana ya dawo. “Yanzu mene abin yi?” Uncle Bello ya miƙe ya ce “Ku san hanyar daza ku bi ku kwantar da hankalin Majeederh, ita nake tausayawa wallahi da ina da wani yaron bayan shi da a yanzu ba sai anjima ba zan ɗaura masa aure da ita, Allah ne shaidata, Alpha kuma sam ba zan masa baki ba, amma zan ga illar bijrewa iyaye nasa kalar godiyar kyautatawar da mukai masa kenan” Yana faɗin haka ya fita gabaɗaya mazan fita sukai domin gabatar da sallar Asuba zuciyoyinsu babu daɗi. Mami ta kasa cewa komai domin ta girgiza da al’amarin, wani irin baƙon al’amari ne wannan? Only God knows! Bayan Anti tayi sallar Asuba bata jira mijinta ba ta nemi napep zuwa gida…
Wajejen huɗu na rana ta fara buɗe Idanunta da ƙyar, wanda sukai mata nauyi har lokacin drip ne manne a hannunta, ta juya kaɗan sbd ciwon da ɓarin kanta yake mata ga wani dishi dishi da take gani kamar mai hawan jini, da sauri kuma ta buɗe idanun tare da yin shiru tana ƙoƙarin tina mene ya kwantar da ita ciwo haka? Duk ƙoƙarinta na son ganin bata kwanta ba? “Sannu Anti Jeederh” Aka faɗa daga can gefe, ta juya suka haɗa idanu da Aaliyah da kuma Sona ɗiyar Anti ta ce “Ƙarfe nawa?” A sanyaye Aaliyyah ta ce “Huɗu da kusan minti goma” Majeederh tai shiru sai kuma ta ce “Huɗu?”
“….Ai an kwana har yamma tayi, don baki da lafiya ne” Majeederh ta ce “Kina nufin kwana na ɗaya kwance?” Ta bata amsa da “Eh” Daidai nan Anti ta buɗe ƙofa ta shigo tana kallonsu ta ce “Yaushe ta tashi?” Sona ta ce “Yanzu Anti” Anti ta ce “Sannu Hawwa’u” Ta ɗan yi murmushi tare da yin shiru a hankali kuma ta ce “Shikenan na zama matar Yaya? Ni ma nayi aure an ɗaura mini aure da Yayana General Alpha ko Anti? Allah na gode maka za a daina yi mini gorin aure ni ma nayi aure ƙaddarata ta zo ƙarshe….

*Mijin Malama it’s a paid book….. Subscribe before you Read🤓*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button