Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 36

Sponsored Links

MIJIN MALAMA it’s a paid book, pay before you read…… For me information via WhatsApp number 08119237616Ya gara zama ya ce “Allah ya na gani na ga ji da ganinki a cikin gidan nan ba aure, gorin dangi ya Isheni ba zan jure ba, ba kuma zan lamunta ba, shekaru 31 kina haɗa kafaɗu da mahaifiyarki? Gabaɗaya ke ɗaya ya rage a dangi ƙannen bayanki suna gidan mijinki” Da tashin hankali kawai take bin Abbu da idanu ta kasa koda jan numfashi domin a ƙirji komai ya tsaya mata, zufa na yanko mata all over herself, kullum tana jin ciwo a zuciyarta, bata da burin daya shige tayi aure amma kuma bata da ikon aurar da kanta ai? Ciwon dake damunta kullum ƙara yawa yake This pain was different, it was draining and excruciating painful, and soon it stopped abruptly. Abbu ya ce “Kina ji na?” Ta ɗaga masa kai a hankali ya ce “Good, Tun kafin na nuna mini The other side of me ki shiga hankalinki, ko mazan auren ki ka rasa? Kawai kin tsaya zaɓe da ruwan Idanu” Majeederh dai bata ce komai ba, domin sama sama take jin maganganun mahaifin nata rai ɓace ya ce “Get out, ki fari na sake miki maganar fito da mijin aure” A sanyaye ta ce “Kayi haƙuri Abbu” Zata miƙe ya ce “Sit down”
Ya kalleta sosai sosai cikin magana ta fahimta tsakanin uba da ƴar shi ya ce “Mene matsalarki?”
Ta yi ƙasa da kanta, tsayin shekaru 31 bai taɓa zaunar da ita ya ce meke damunta ba, sai yanzu da komai ya ƙare mata “When all is gone” to yanzu ta ce me? Bayan faɗar bata da wani amfani, it’s too late to cry. Cikin tsawa Abbu ya ce “Ina magana kina ji na?” Ta girgiza kai ta ce “Lokaci ne bai ba Abbu, ka yi haƙuri” Abbu ya ce “Eclty, ni ne kike cewa lokaci ne bai yi ba? To buɗe kunnenki da kyau ki ji” Ya gyara zama ya ce “Wallahi wallahi ki fita daga idanuna, dana matsa miki a shekarun baya ki yi karatu ai saboda rufin asiri mu ne nothing more, yanzu i have what i want, kin rufa mini asiri yanzu kema ki rufawa kanki kiyi aure hankalina zai fi kwanciya, Hawwa’u am telling you as your father lokacin da zan ƙara miki maganar aure zaki sha mamakina wallahi Allah” Yana faɗin hakan ya miƙe tare da shigewa bedroom ɗinsa ya barta zaune kamar gunki. “Majeederh!”
Zuciyarta ta kirata, ta yi saurin ware idanunta tana dafe ƙirjinta. Zuciyar tata ta ƙare cewa “Nutsu Majeederh, think about that, wai kina da saurayin ne ma?” Waya taɓa cewa yana son ki? Balle ya yi tunanin sanyaki a gidansa matsayin matar aure ta sunna?” A razane Majeederh ta girgiza kanta, cike da tashin hankali tana sauraren abinda zuciyarta ke faɗa mata, ta yi shiru jin ta ce “To kenan yanzu ya zaki? Shelar kan ki za ki yi ko yaya? Kinga dai bakya son ɓacin ran Abbu ya zame miki dole neman mijin aure…..,” Da sauri ɗaya zuciyar ta buge ɗayar ta ce “Ji banza, ke dai ƙwaƙwalwarki bata aiki kamar mai shan miyar kuka, banda awon igiya ce ke kamar Malama Majeederh ce zata yi shelar kanta? Kuma shi Abbun bai san ƙaddara bane? Waye ya jefata wannan halin tun farko? Ba son zuciyarta bane da neman abin duniya? Do what is right not what’s easy, yadda ya dama zaka zai shanye abinsa, tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa akan doka! Dole abu ya yi haƙuri domin shi ne silar faruwar komai shi ne ya haddasa mata jinkirin auren, by the way Ubangiji hakan jarabta mu, kuma shi aure lokaci ko ita Majeederh ce zata aurar da kanta? A wannan zamanin bafa ita kaɗai ce take da wannan matsalar ta rashin aure ba, jarrabawa ce! Kuma zurfin cikin ki ya yi yawa Majeederh You have to do something, do something Majeederh! Biyyar da kikewa Abbu is too much….,”
Kamar zautacciyya haka Majeederh ke sauraren shirar zuciyoyin nata guda biyu, da mai faɗin gaskiya da mai kushewa tana ɗora ta a tubalin da zai kai ta halaka. Kyakkyawar zuciyar ta ce “Oh! Kina nufin ta wulaƙanta mahaifinta kenan? Daman haka ya dace ɗan halak ya yi wa iyayensa? Ba Abbu da yake mahaifinta ba, ko Mami idan ta yi magana dole Majeederh ta yi mata biyayya, mai haƙuri shi ke da riba a wannan rayuwar, na tabbar Ubangiji ba zai taɓa barin Malama Majeederh ta haka ba, dole akwai wani rabo da tanada mata albarkacin biyayyar da takewa Mahaifinta, rabonta yana ta wani ɓangaren” Majeederh ta yi zuru domin tafi gasgata maganar kyakkyawar zuciyar, muguwar zuciyarta ta ce “Hoo ƙaaasa! Yau ga bikin zuwa babu zanin ɗaurawa, waya hanata auren tun fil azal, lokacin yana wagairawun bai ajjiya ko sisi ba, a matsayinsa na uba wanda zai fita ya nema ya ciyar da iyalansa amma ya jingina ƴar cikinsa mai tsafta da kamala matsayin jarinsa, ya sadaukarwa duniya ita idanunsa ya rufe, kuɗi kawai yake so arziƙi yake nema ta ko’ina sbd yanzu ta tara masa ya shiga jerin masu kuɗin Kano shi ne zai ce ta fito da mijin auren? Ya ja mata ƙaddara sai su amsheta da hannu bibbiyu, rayuwar Majeederh ta shiga cikin lack of parents careless, Takaicin Uba zai iya kai ruhinta zuwa kushewa, yanzu daya tilasta mata kawo mijin aure idan zuciyarta ta buga fa? Kawai ki share mahaifinki ki ci-gaba da sabgar gabanki ya je ya ci kansa, Allah kaɗai ya san yadda zai da shi” Da hannu bibbiyu Majeederh ta toshe kunnuwanta, sosai maganganun da zuciyoyinta suke, suke mata amsa kuwwa a kunne! Jikinta har ɓari yake yana wata jijjiga. Kyakkyawar zuciyar ta ce “Amma ke baki da lissafi, da kina da shi ba kya ce haka ba, komai yana da sanadi Ubangiji ya ƙaddarawa Majeederh Jinkirin aure, amma Abbu shi ne sila, idan mutum ya kauce hanya addu’a ake masa idan da rabo ya dawo, abu ɗaya Majeederh za ta yi ta ci-gaba da addu’a, sadaƙa da yawaita azkar, kuma shi Imran ƙilan ƙaddararta da tashi daban shi ya sa a lissafin ƙaddararta babu auren shi, abu guda ɗaya ne ke ɓata mini rai da Majeederh yadda take yin shiru shirun nan, yaran cikinta na rainata ta ci uban kowa ta tattaka kowa, ta kuma cigaba da kare mutumcin kanta…” Ceceku ce aka shiga yi tsakanin zuciyoyi biyun! Kowa yana son Majeederh ta ɗauki shawararsa, ta saka hannu ta rufe kunnenta tare da sakin wani irin gigitacciyar ƙara ta zume wajan a sume…. Misalin 12 na rana, ta shiga buɗe Idanunta wanda sukai mata nauyi, a hankali ta saka hannu ta dafe gefen kanta dage barazanar tarwatsewa.
“Sannu Hawwa’u” Muryar Anty ta sauka a kunnuwanta. Ta ya motsa fuska a hankali ta miƙe zaune tana jingina da jikin frame ɗin gadon bedroom ɗinta, cikin son nuna ta ji sauƙi ta ce “Ina yini? Yanzu kika zo”
“I haven’t been here long” Anti ta bata amsa cikin ƙasa da murya sai kuma ta ce “Meke faruwa dake har haka?”. Majeederh couldn’t speak sai da Anti ta ce “Kina da ilimi, kuɗi, hankali, kyau, amma duk da haka da sauranki baki gama cika mace ba”. Anti ta yi shiru can ta kuma cewa “I’m starting to get tired of seeing you in this situation,It is good that now you are married and you are in your husband’s house, Majeederh duk wani ɗaukaka da da iliminki a banza yake, macen da bata san komai ba wacce take gidan mijinta sai anfi ganinta da girma da daraja, sai anfi martabata fiye da komai, Abbank Uncle Isma’il shi ne ya turo ni ya ce na faɗa miki ya gaji idan ya haɗu dake ba zaki ji da daɗi ba, You’re a darling ke abar so, kina da kyau” Murmushi kawai Majeederh ta yi wanda ya fi kuka ciwo ta kalli Anti ta ce “Mene amfanin kyau? Wallahi ban taɓa fariya sbd ina da kyau ba, ina tausayawa duk wata mace mai kyau”
“Kyau abin so ne Majeederh” Majeederh ta runtse Idanunta ta ce “Bai ƙare ni da komai ba, wallahi da na san inda ake sauya fata daga fara zuwa baƙa da tuni na yi, na gaji da duniyar nan Anti” Ta faɗa tana riƙe ƙirjinta hawaye ma ya gagara fito mata. Anti ta ce “Kin gaji da duniya ga shi duniya na son ki, Majeederh mazan aure kika rasa ne?” Kanta a ƙasa ta kasa cewa komai Mami dake zaune looking so worries ta ce “Ta yani tambayarta Maryama, ni dai ba ruwana dole na ja baya idan ina matsa Majeederh za ta yi zaton dan bani na haifeta bane wallahi,to me ma zan ce? Nan nan wata Neighbor ɗinmu ta zo ta mini ta tas kamar uwata, zagi kala-kala tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin tashin hankali irin na ranar ba” Ta yi jim! Sai kuma ta ce “To akan me”
“Uhm, ta tsuniyar gizo ai bata shige na ƙogi, cewa ta yi wai bata yarda da Majeederh ba, gani take gantali kawai take a duniya shi ya sa bata damu da aure ba” Anti ta ce “To fa, ita wa kenan? Ina cewa akwai zabga zabgan ƴan mata a gidan wata ma ta yi Arba’in kamar uwata wallahi, amma ita ba taga na gabanta ba sai munafurci a ɗaure a ƙugu? Mutane basa kashe wutar dake ci a gabansu sai na wani? Baka da gadon mutum yana da gadon maganarka, to da izinin Ubangiji ba zamu ga wannan mummunan ranar ba, wani hanin ga Allah baiwa ne” Mami ta ce “A to, munafurci ne kawai irin na mutane wallahi Maryama, nan ta zo ta wata yaƙunanniyyar atamfarta duk gansa kuka, ai kana ganin wannan matar kaga zubin munafukai Inyami take kowa?” Anti dai bata ce komai ba. Ta juya kan Majeederh ta ce
“Ki tausayawa kan ki, ki tausayawa mana dan Allah Majeederh, zaɓen miji yanzu ba naki bane, duk wanda ya fito da niyyar aurenki kawai ki amince masa As long as you trust his morals, his behavior, his mind and his religion”
Kallon Anti kawai Majeederh take domin bai ɗaki shiyasa inda yake masa yayyu, wai ba a yarda da ita ba? Babu wanda ya taɓa riƙe hannunta sai Ajlaal shi ma kuma ta yi Asstagafirullah! Ta ja masa Allah ya isa kuma har azumi za ta yi bisa hakan wani ƙato ya riƙe mata hannu. Ta rufe Idanu “Ban ya fe ba Ajlaal” Anti ta ce “Waye haka?” Ƙasa magana ta yi sai a lokacin ta kifa kanta in between her legs ta shiga rera kuka kamar ƙaramar yarinya takaici da baƙin cikin Ajlaal ya cika mata zuciya.
Ta riga ta manta da wani Alpha domin shi ne mutum na farko daya tuzarta ta a duniya, She laid back down to rest but couldn’t. Tears of fear, betrayal and sadness streamed down her cheeks, and she knew that her life had been altered completely……
ZAZU Restaurant, Sultan Road Giginyu Nasarawa.
Suna zaune saman wasu haɗaɗɗun kujeru wajan wani gefen ruwa dake gudana, su wajan biyar ne kana ganinsu kaga tantiran marasa jin magana, wanda suka gagari kowa, abu mafi jan hankali a gare su ko wanne yana da class ɗinsa, ka taɓa ɗaya goma su hau kan ka, basa ɗaukan raini basa gudun abin magana, sun mai da jami’an tsaro kamar abin wasan su, Police station kamar shiga restaurant suka mayar da shi ko beach ko club… They’re all education natured enough, gabaɗaya kuma a Gang team ɗin Bad boy Abraham shi ne ƙarami, amma yafi ko wanne girman jiki da tsare idanu, baya ɗaukan raini baya son munafurci, idan ya faɗi magana haka ne domin baya ƙaunar ƙarya yafi son gaskiya ko zata kashe sa ko ta ja masa wata masifar, wani irin masifaffen jan aji ne da Abraham Bad boy, basu taɓa ganin dariyarsa ba, gashi da wani irin fikira ya ƙware wajan yin zane….. Abinci ne birjik a gabansu da difference types of drinks a gabansu, ga Shisha ga wine. Taj ne ya ce “John yarinyar ta ci banza kenan?” Ya faɗi hakan cikin turanci. Nan da nan fuskar John ta sauya ya ce “How do you think I will forgive her?” Taj ya yi dariya ya ce “To You didn’t take any action akanta” Wani lalataccen murmushi John ya yi ya ce “Tomorrow is Luna’s birthday, I will call her the club where the birthday will be held” Sai a lokacin Joshua da hannunsa yake riƙe da Luc Belaire Rose Ya ce
“Sai ka yi mata me?” John ya ce “I will rape her, and I will beat her to death” Ambaton Fyaɗe da akai ya sanya tsigar jikin Abraham ta shi tana zubewa, baya ƙaunar jin kalamar bare har ya ji ana faɗin za a aikata, gashi dai ƙaton arne amma bai son ƙazanta ko kaɗan. Ya ɗago kansa da wani irin sexy eyes ɗinsa wanda sukai wani irin kalar launi kamar na mage haka zubin halittar idanunsa suke, ga girar shi kamar zata haɗe lips ɗinsa da suke jajir ya taune, jikinsa sanye da Tommy Hilfiger T.shirt Maroon, da Levi’s crazy jeans iya qiwwa, ga wasu gargasa kwance lub daman dark skin ɗinsa wacce take ɗaukan idanu sun yi gwanin sha’awa, six-pack ɗinsa sun kama rigar hakan yasa ya yi wani ƙato irin mazan nan ne wanda ko kallon mace sukai sai ta kusa yin fitsari a wando don tsoro. Ya saka bandana a kansa hakan yasa sumar ta Kwanto har goshinsa idan kaga Abraham ba zak taɓa ɗaukan farin namiji ba, irin colour ɗin su ake wahalar samu…. A hankali yake jujjuya drink ɗin Gold berg wanda shi ne favorite drink ɗinsa. Bai ce musu komai ba sbd he’s not interesting da conversation ɗin na su. Ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious sai tashi yake a jikinsa. Taj ya yi wata mahaukaciyar dariya ya ce “Wallahi kaci uwar Shegiya ka yi mata fata-fata” Joshua Shi ma ya yi murmushi ya ce “I support you, the girl has no shame, kama yi ƙoƙari da zaka iya goga fata da ita, datti gal” Taj ya ce
“Abinda nake tunani kenan, kaga idan kana son jin daɗi da more wa ka samu babies ɗin Brazil, idan asalin kyau ne most beautiful ladies in the world jeka duba Ethiopia…. Matan Nigeria are not romantic at all, shiyasa soon zan bar wahalalliyyar ƙasar nan” John ya taɓe fuska ya kalli Abraham ya ce
“Are you okay, Bad boy?” Ya yi masa banza kamar ba da shi ake ba. Wani a cikin su ya ce “Wai fa ko sau ɗaya Bad boy bai taɓa sanin mace ba” Taj ya ce “He’s not romantic, kamar baya da lafiya” Sai a lokacin ya ɗago fitanannun idanunsa ya zuba akan Taj cikin wata husky voice ya ce
“Ko!” John ya ce “Haka ne ma, baka da lafiya” Ya miƙe tsaye yana feeling kansa, ya ce “Maybe”
Taj ya ce “Soon zan sanyaka yin haka, na baka wata mahaukaciyar Alcohol” Cak Abraham ya tsaya tare da zubawa Taj idanu calmly ya ce
“Da na ci uwarka, kashe ka zan Dog!” Ya juya kan John ya ce “Let me make it clearly for you, ka sake kayi rapping wata ma rantse da Jesus sai na yanke maka abar, try it” Yana faɗin haka ya yi gaba walking full of peace and tranquility. Gang team ɗin suka bisa da idanu, ganin yadda ake musu gadara kamar ubansu, and he just 16 yrs.. Motarshi ya nufa Hyundai Ioniq 6 black colour, har zai shiga ya ji ana hayaniya cak ya tsaya jikinsa ya fara tsuma da idan da akwai abinda aka jarabci Abraham da shi bai shige abu biyu ba, yana mugun son yin faɗa musamman wanda bai shafe shi ba. Da wani sarrafa ya nufi direction ɗin yana zuwa yaga wasu maza guda biyu cikin kakkausar murya ya ce “Heee what’s going on?” Wani ya ce “Faɗa suke” Guy ɗin ya nuna Wani ƙyakƙyawan mutum ya ce “Wannan bawan Allan ne ya ɗan bugi motar wannan wai ko Joseph sunan shi? Shi ne ya fara zaga-zage” Abraham bai jira jin wani abu ba gabaɗaya jikinsa ɓari yake ya damƙi hannun wanda aka ce Joseph ɗin kafin ka ce me ya ɓalla masa hannu, ya ƙara damƙar ɗayan ya ɓalla wani irin ihu Joseph ɗin ya yi yana jin kamar zai mutu. Wani ya ce “Kai Mahaukaci ne? Haka ake raba faɗa” Ko inda yake bai kalla ba ya juya abinsa zuwa mota ya ja da wani irin 150 yabar cikin Zazu ɗin. Bar Aliyu ya sauke numfashi yana mamakin zafin zuciya irin ta wannan gwalilin yaron yafi tunanin ma mahaukaci ne….. Tun a Main parlour Abraham ya fara fatali da komai jikinsa duka rawa yake da wani irin karkarwa. Grandpa ya sakko yana mai ɓoye photon Zanen fuskar Abbu da aka kawo masa ɗazo, so yake ya saka aiwa Abbu Mahaukacin duka tunda ya taɓa masa lafiyar Grandson ɗinsa, yasan kuma Abraham ba zai taɓa bari ba shi yasa zai yi asirrin ce. Ya dinga bin Abraham da idanu kafin ya ce “Mami ko?”
“Yes Grandpa” Ya faɗa yana kallon Grandpa, David ya ce “Na saka private Investigators amma shiru, ina tunanin wannan Mamin taka bata duniya ta mut…..” Kafin Grandpa ya ƙarasa Ya ji Abraham ya buga kansa da jikin wani Glasses yana faɗin “No!!!!!!, Mamiii…”
A hankali Majeederh ta duba agogon hannunta taga 12 saura minti goma, gabaɗaya ta manta akwai wani taro a B.u.k na gabaɗaya students ɗin makarantar musamman na Department ɗin Politics Democracy. Ta sauke ajjiyar zuciya a ɓoye a hankali ta kalli mutanen da suke gabanta ta ce “I can’t do that, abu ne na cakuɗeɗeniyya da mata, am sorry” Mutumin ya ce “Please Malama Majeederh Ngo ɗin nan tana buƙatar ki, zamu baki ko nawa kike so, kawai muna so kiyi aiki damu” Bata kallesa ba ta dubi wata ta ce “Kika ce me?” Matar ta fashe da kuka sosai ta ce “Ki taimaka mini, yarinyata aka aurawa wani yaƙunan tsoho saboda yana da kuɗi, gashi yanzu yarinyar ya ja mata masifa yayyun fitsari take sbd takura rayuwarta da yane kamar ɗan taure, gashi yanzu ya gudu wai ba zai iya zama da ita ba, wannan masifar duk Ubanta ya ja mata saboda son kuɗi ne da shi kamar ƙudan cizo” Majeederh was speckless hango kanta take matsayin yarinyar a hankali ta ɗan rufe ido ta buɗe ta ce “Zan kira ki weekend, ina da aiki yanzu thank you Inna” Ta amshi number Dattijiwar “Na gode na gode, Ubangiji ya jiƙan gobenki ya baki zuri’a ta gari ya raya miki su ya barki tare da mijinki” Majeederh dai ta yi shiru, Mai Ngo ɗin yin duniya amma taƙi tanka shi ya yi ƙwafa ya fice,daga nan ya fito tabar masu kula da Foundation ɗin nata ya shiga motar ta tare da yin Bismillah ta harba motar kan titi ta nufi B.u.k new side…… Hall ɗin a cike yake da manyan baƙi, masu kuɗin garin da jami’an tsaro da ƴan jarida haɗi da Lauyoyi na jihar. Yana can tsaye domin bai wani jima da shigowa ba, ya runtse idanunsa jin zuciyarsa na bugawa, ya wani kwaɓe fuska har zai juya ya ji wani ya ce “Malama Majeederh Abdul’aziz Khan is here” Attention ɗin Students ɗin sama da 300 ya dawo kan Majeederh dake tafiya cike da kamala kana ganinta kaga cikakkiyar mace mai nagarta, abayar jininta kaɗai ya nuna arziƙin da Ubangiji ya yi mata daga baiwarta. Mutumin ya ce “Allahamdulillah ita ce zata gabatar mana da addu’a daga ɓangaren musulmai, kafin mu je ga addu’ar zamu gabatar muku da sunanta da kuma matsayinta a makarantar” Da ƙarfi John ya ce “Allow her to speak” Gabaɗaya Students ɗin suka ce “Yes! Yes!” Ya ce “Ok zata yi bayani da kanta Malama Majeederh Bismillah” Tafi ƙarfin Minti biyu kafin ta ɗan yi gyara Muryar ta ce “Bismillahir Rahmanir Rahim, In the name of Allah….,” Cak ta yi shiru jin kamar ita ɗaya ake kallo, Da wani irin firgici Abraham ya ɗago kansa dake ƙasa zuciyarsa kamar zata faɗo bakinsa na rawa ya ce “Mami…?” Sai kuma ya miƙe yama manta su waye a wajan kuma daman shi mutane basa gaban shi, gaba ya bawa kunya ba baya ba, Gadan-gadan ya nufi wajan Majeederh takun tafiyarsa kuma ya ja hankalin mutanen hall ɗin, Majeederh na ƙoƙarin yin magana taga kamar an cillo mata mutum a gaba ta ɗago idanu slowly idanunsu ya sarƙe dana juna ta dinga kallon ƙwayar idanunsa bakin Abraham na rawa yana kwaɓe mata fuska ya ce “Ma…ma… Mami Jee…!” Sai kuma ya yi kanta gabaɗaya zai rungumeta….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button