Mijin Malama Book 1 Page 9
9……*
Yadda suka ɗaure Abraham a jikin sarƙa zaka ɗauka wani tantirin ɗan fashi ne ko kidnaper, ko irin mutanen nan masu muyagon harƙalloli. Suna zuwa suka cilla shi a mota tare da yiwa motar key.
“Ku daka ta” P.a Hammad ya faɗa yana ƙara sawa inda suke ya dubi Abraham wanda kansa yake sunkuye jini ya ɓata masa fuska.
“Mene matsayina?” Kai tsaye Captain ya ce “Kai P.a ne a wajan His Excellency” Hammad ya jinjina kai ya ce “Good, kamar matsayin P.a ya fi na mataimakin Gwamna, idan ya tabbata haka ne la shakka zaku bi nawa umarnin” suka kalli juna
cikin kuma rashin fahimta Captain ya ce
“Me kake buƙata?”
Ya ce “Ku kai Abraham gidana, ya zama sirri ni da ku kada ku kuskura akai shi Prison idan ba haka ba, ku ne zaku tabbata a can har ƙarshen rayuwa”
“Cin amana?” “Shi ma ita ya yi” cewar Hammad. Captain ya ce “I can’t, dole mu kaisa prison kamar yadda ya umarta”
“Nawa ya baku?”
“Mu ai ma’aikatan gwamnati ne, wannan shi ne aikinmu” Hammad ya yi murmushi mai kyau kafin ya ce “Mu ne Gwamnati ai, baka san inda rana zata faɗi ba gobe” “Kowa ya san ta yamma take faɗuwa” Captain ya tari numfashin Hammad da faɗin hakan.
“Zan baka 10Ms, zan faɗa maka yadda za kayi” ya yi shiru alamar tunani kafin ya ce “Sauran securities ɗin fa?” Hammad ya watsa hannu ya ce “Ɗauke shi, lokacin ya fara” Captain ya dubi abokan aikin nasa, ganin sun yi nesa da su hakan ya tabbatar ba su ji abinda suke tattaunawa ba. Tunaninsa ya rabo gida biyu shin ya amshi kuɗin? Idan ya amsa kuma ya ci amanar Gwamnansa, da ƙasar shi da kuma aikinsa. Amma miliyan Goma ai ba nan ba ce, babu wanda kuma zai sani.
Ya shiga motar, sauran securities ɗin ma haka kai tsaye suka fita daga cikin keɓantaccen gidan na His Excellency Abu-turab.
Hammad ya yi murmushi a fili ya ce “Kaci amnar maci amana kamar babu laifi? Ba zan jure ganin hakan ba, am sorry Best friend”
Abu-turab ya na tsaye da hannunsa wanda aka karya ya dubi Majeederh dake zaune tayi shiru ta sanya hannunta tsakanin cinyoyinta hakan na nufin tunaninta ya girmama har ya kasa ɗaukan ƙwaƙwalwarta. Abu biyu ya fi tsaya mata, kalaman mahaifinta Abbu, da kuma kalmar Abraham “I am the who raped her” hakan na nufin Abraham yaga surarta na ɗiya mace? Ya gama kallonta. Ta rutse idanu tana kiran sunan ALLAH. Yaron cikinta? Ɗan data raina? Ya yi mata Fyaɗe? Ya samar da cikin Khalil, ta ya ya hakan ya faru? Rabonta da shi shekara biyu, shin ciki yana shekara biyu ne? Ya akai har ya yi mata Fyaɗe bata sani ba? Yaushe hakan ta faru.
“Jiddo” Abu-turab ya kirata a ruɗe ganin yadda jikinta ke rawa kamar wacce take shirin yin jijjiga. “Ka da ki sawa kan ki damuwa wani ciwon ya kama ki, don Allah Jiddo listen to me ki bani dama, ki bani dama just one chance, please Jiddo Give me one chance”
Ta ɗago kai a nutse ta faɗaɗa kyakkyawar fuskarta speaking calmly ta ce “Your Excellency”
“Yes, Jiddo”
“Don Allah ka bani waje” ta faɗa murya can ƙasa idanunta na lumshewa.
Ya jinjina kai ya ce
“Zan fita,idan zaki farin ciki” yana faɗin haka ya yi waje yana zuwa wajan ƙofa ya juya ya kalleta sai kawai ya fice yana rufe ƙofar bedroom ɗin. Yana fita ta zame ƙasan lallausan carpet na ɗakin, zuciyarta tayi mata zafi ƙirjinta na ɗagawa sama. Tsoron t ɗaya kada bakin mahaifinta ya kamata ya sanya ta lalace kum ta bi duniya kamar yadda kalamansa suka bayyana haka, mene ya sa ya kasa yarda da ita ya kasa fahimtar ba zata taɓa aikata zina ba, ya kasa amincewa ƙaddara ce ta faɗa mata.
Kuka take son yi ku zuciyarta za tayi mata sanyi amma ta kasa sai ma wani abu daya tsaya mata a ƙasan maƙoshi da ƙyar take jan numfashi. A raunace ta ɗaga kai sama ta ce
“Allah na gode maka, Allah na gode maka da wannan jarrabawa, yadda kayo ni a Musulma mai yadda da ƙaddara Ubangiji ka sanya na cinye wannan ƙaddarar, zuciyata ta kasa jurewa Allah kai kasan abinda yake ɓoye Ubangiji idan rayuwata a wannan duniyar shi ne alheri ka tabbatar dani a raye ka bani haƙurin jure ƙalubalen cikinta, idan mutuwata ita ce hutu a gareni Ya Allah ka ɗauki raina a wannan lokacin, ka yafe mini kurakuraina ka kula mini da abinda na haifa” Ta rufe idanu tana ƙanƙame jikinta tana jan numfashi da ƙyar ta ce
“Asstagafirullah Ya Allah, Asstagafirullah, Asstagafirullah Ubangiji kana kallo,kana ji, kana gani albarkacin imanin da nayi da kai, albarkacin kare addininka da nayi, Ya Allah ka bani haƙuri kwatankwacin haƙurin da Annabi Luɗ ya yi da mutanensa, ka bani ikon jure yanayin rayuwa kwatankwacin juriyar da Annabi Yusuf ya yi, Allah ka bani ƙarfin zuciya wacce zan fuskanci ko wanne ƙalubale, kwatankwacin Yadda ka bawa Annabi Sulaiman ƙarfi ikon, Allah ka kula dani kwatankwacin kulawar daka bawa Annabi Musa a cikin gidan Fir’auna… Ya Allah Asstagafirullah!”
Jira take taga ta inda mutuwarta zata fara, amma shiru hakan na nufin rayuwata ita ce alheri a gareta.
Abu-turab na zaune ƙasan carpet ya sanya Mama a gaba hannunsa naɗe da bandeji cikin kulawa ta ce “Abu-turab me ka ke so?”
“Majeederh nake so Mama” ta ce “Nemi Soyayyarta idan ta amince ba zan hana ba”
Ya yi shiru ta ce “Idan baka da abun faɗa jeka, ka sani a gaba” ya kalleta ya ce “Kamar ba zata amince ba” Mama ta dube shi sosai tana duba yanayinsa ta ce
“Idan har baka sanya son zuciya cikin lamarinka ba babu shakka zata amince, ka yarda da kan ka shi ne kawai” tana kallon T.v ta ce
“fight for the truth, fight for your love, idan har ka faɗa mata wahalar daka sha akanta Majeederh zata ji tausayinka, sai dai bana son ta aureka don jin tausayi sai don cewa tana Son ka”
“Tausayi yana zama so”
“Inji ku Hausa ba, babban kuskuren da kuke kenan, gurbin tausayi daban na So daban go and search”
“Mama please ki….,”
Cikin faɗa ta ce “Abu-turab ba zan tilasta ƴar mutane ba, fita ka bani waje” ya miƙe jiki a sanyaye yabar bedroom ɗin, Jidda na nufar inda yake ya daka mata tsawa. Mama ta ce “Na gode Allah tunda ƴarka ce” yarinyar ta fashe da kuka sosai da gudu kuma ta nufi bedroom ɗin Majeederh ta sameta zaune inda take..
“Mami” Majeederh ta zubawa yarinyar idanu sai ta ɗan saki fuska ta ce “Call me Jidda”
“Dady ya ce Mami” Majeederh ta jingina da bed ta kallon yarinyar sosai tayi kama da mahaifinta. Jidda ta ce
“Ina son Daddy, kema kina son shi?” Majeederh shiru ba amsa ta ƙara cewa “Zaki zama Mamina?” Sai a lokacin ta ce “Ai ni Mamin kowa ce come here”
Barrister na zaune looking so worries ya ƙara ramewa ya yi baƙi kamar ba kyakkyawan matashin nan ba mai jini a jika. “Aliyu Meke damunka?” Ya dubi Hajia ya ce “Me kika gani Hajia?” Ta haɗe rai sosai ta ce “Why are you asking my question with a question?”
“Ɗan Najeriya ne fa?” Almustapha ya bada amsa yana hararar Bar Aliyu Sufyan Alhassan. “Lafiya nake” “ƙarya ka ke, na san halinka dole da abinda yake damunka” Aliyu ya rasa me zai ce, ya faɗawa mahaifiyarsa damuwarsa tamkar ya tona sirrin aurensa ne, kuma zata tsani Matarsa Latifa Omar, amma seriously yana cikin damuwa ya mance when last da ya yi mu’amalar aure da Latifa, ya manta rabon da ya ji ƙamshin girkinta kullum abinci da ƙauri ya manta rabon da yag kitso a kanta, ya mance rabon da ya ji kalmar adawo lafiya daga bakinta. Yana buƙatar kasance da matarsa haƙurinsa ya fara gazawa.
Ya riƙe kansa, da mutuncinsa sbd gudun faɗawa halaka, amma irin su Latifa sune suke sanya maza neman mata da aikata zina.
“Ni banga abinda ka rasa a gidanka ba, amma ka sanya wa kanka damuwa akan wata ƴar iska haba Aliyu” Barrister ya kalli Almustapha ya ce
“Mai ɗaki ai shi yasan inda yake masa yoyo, ba zan hana ka aibata Majeederh ba amma ba kowa ake halinsa ba” Almustapha ya kalli Aliyu sai kawai ya miƙe tsaye. A tare suka fice daga cikin gidan nasu, Bar Aliyu ya yi Lodge Road wanda dalilin Majeederh ya kama haya a unhwhaty, shi ma Almustapha ya nufi hanyar gidansa. Maimoon na zaune ita da ƙawarta wacce suke neighbor da ita. “Maimoon kin ji daɗi, Allah ya baki miji wanda yake wada taki da komai na rayuwa” Maimoon tayi dry sosai ta ce “Allah sarki, wallahi bani da matsala da mijina saɓani bai taɓa haɗani da shi ba, yana da haƙuri sauƙin kai, sometimes na fisa rikici ma, gaskiya samun miji kamar Almustapha da wahala, yana da kare hakƙin aure da nasa, kullum cikin kyautatawa iyalansa yake” Maryam tayi murmushi ta ce
“To Allah ya bamu irin taki” “Haba ya bawa ƴan gaba dai, ke kina ɗakin mijinki ai ki ce kawai Allahamdulillah,kin san duk wani kwanciyar hankalin aure shi samun daidaito tsakanin ma’aurata, yarda da juna, haƙuri, tausayi. Ni kam i trust my husband” Shira suka ci gaba da yi. Suna zaune Maimoon ta ji anyi horn ta miƙe da sauri ta ce “To ga ɗan halak nan” Maryam ta ce “A’a zama bai ganni ba, lemme have my way” sukai dry kana sukai sallama.
Maryam na fita compound na gidan Almustapha na fitowa ya dinga kallonta domin bai taɓa ganinta ba. Ya shafa kai lokacin da take cewa “Sannu da zuwa”
“Thank you, can i know you?” Ta ce “Matar maƙocinka ce Habib”
“Oh, you’re too beautiful” Mamaki ya kama Maryam sai tayi ɗan murmushi ta ce “Harna kai Matarka Maimoon?” Ya yi murmushi yana kashe mata idanu guda ya ce “Haba waccar Dabbar?” Maryam ta zare ido ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un Matarka ka ke kira da Dabba?” Ya watsa hannu ya ce “Yes, Kinga bani number ki please” Number ta bashi ta shige tana Kaɗa masa jiki, ji ya yi kamar ya bi bayanta domin ya tabbatar mijinta baya gari.
Cikin dare Abu-turab na zaune ya samu sanarwar gaggawa an samu motar jami’an tsaron shi a wani gefen hanya, gabaɗaya jami’an sun mutu guda ɗaya ya yi saura Captain shi ma yana gadon asibiti. Misalin 2 na dare Uncle Isma’il na harabar gidansa yana duba jaridar ranar inda yake ganin cewa Governor yana asibitin Cameron domin duba lafiyar shi, kamar yadda aka samu sanarwar ta bakin mai kula da lafiyarsa. Ji ya yi an tsaya gabansa ya miƙe da sauri da ƙarfi ya ce “Abraham innalillahi,mene ya sameka…
MIJIN MALAMA
Book1 500
Book2 500
Mutum zai iya biyan book1 kafin a fara book2… Idan kuma yana da hali zai iya biyan 1k ɗin bakiɗaya. 08119237616 kuyi magana ta nan.*🌈MIJIN MALAMA🌈*
Nimcyluv sarauta