Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 10

Sponsored Links

PAGE TEN*

 

Da sauri Umaimah ta fara qoqarin janye jikinta daga nasa amma yaqi sakinta cafka Sadiya takai mata yayi wani juyi da Umaiman yamai da ita bayansa qanaamesa tayi ta saki kuka jikinta yana rawa saboda tasani yau kashinta ya gama bushewa sake kaiwa Umaimah wawura tayi ya riqe hanunta tare dayi mata wani murmushi yace “kada ki tabamin qanwa Sadiya batada wani laifi jirine yake daukanta shine na riqeta…” Hanu ta daga ta daukeshi da mari cikin bala’i tace “qarya kake Abdulhameed dama na dade Ina zarginka da Umaimah yaudai Allah ya tona maka asiri ashe abinda kukeyi kenan cin amanata kukeyi Hameed ka rasa dawa zakayi lalata saida Umaimah yarinyar dana raineta naci wahalarta Hameed menayi maka mena rageka dashi da zakake lalata da Umaimah yarinya qarama me hakan yake nufi? Ashe gsky abinda Nihal ta fadamin taganka kanashawa Umaimah nono nace qarya ne ashe cinyeta kakeyi Hameed yarinyar daka Raina tun batasan kantaba yanzun ita kake zina da ita ita kake qwaqwulewa meye hakan Hameed ni dama nasan ba wani meeting daka tafi kanacan kana iskancin kane….”

Allah ne ya bata saa ta cafko hijjab din Umaimah ta fincikota da qarfi ta wani wujijjigata tayi jifa da ita cikin rashin saa ta kifa saman wani dutse da aka ajiye a gurin ta qwallah wata razannanniyar qara da gudu ya nufota ja yayi da baya da sauri yace “na shiga uku Sadiya kin kasheni jini Sadiya jini take zubarwa a tsorace ta juyo daidai lkcn ya dago Umaiman da tayi doguwar suma yabi jikinta da kallo jini take zubarwa sosai ya qara qanqameta ya saki kuka yana jijjigata yana cewa “kada ki mutu Baby don Allah kada ki bari muyi asarar babyn mu kada cikin nan ya zube inasonsa Baby plz..”

Yanda yake mgnr kadai zai tabbatar maka da lallai baa cikin hayyacinsa yakeba kuka yake sosai yana jijjigata yana kiran “ki tashi Umaimah ki tashi don Allah kada ki mutu ban fadawa duniya matsayinki a gurina ba kada ki mutu kina kallona a matsayin mazinaci Umaimah kada ki mutu bamu cika burin kakanmu da iyayenmu ba Abba ya mutu da burin ganin zuri’ar mu ya mutu yana fatan zamanki a wannan matsayin yabada wasiyyar ko bayan ransa kaka ya tabbatar da dauruwar aurena dake kakanmu ya cika masa burinsa kafin yabar duniya Umaimah don Allah kada ki mutu saimun haifi danda zamusa masa sunan mahaifin ki aurena dake hadin Allah ne shine ya hada”

Tsoro ne ko tashin hankali yasa Sadiya yanke jiki ta fadi oho faduwar tatace ta fargar da mai gyaran fulawar ya nufo gurin da sauri ganin Hameed din rungume da Umaimah wacce take kamar matacciya ga jini sai malala yake ta qasanta yanata gursheqen kuka kamar wani mace ne ya tashi hankalinsa ya matso da sauri yace “ya salam maigida jininta zai iya qarewa akaita asibiti” sai yanzu hankalinsa ya fara dawowa jikinsa ya miqe ya dauketa cak kamar wata yar jaririya yasata a mota har yaja motar Sadiya tasha gabansa tana layi tace wlh baka isa ka fita da ita daga gdannan ba yau saidai koni ko kai ko ita na rantse da Allah baku isa kuci amanata ku fita lfy ba aure tab billahillazi baka isaba Allah ya tsine uban Wanda ya fasa wlh dagaku har danginku sai kunsan kunci amanata” tana fadin haka ta nufi cikin gdan a guje kamar mahaukaciya.

 

Hakanne yabashi damar figar motar a guje ya nufi Abdullahi Wase specialist hospital yana zuwa aka karbeta aka shiga da ita emergency duk inda sukayi binsu yake kamar wani zautacce daqyar Dr Saleem ya lallasheshi ya zauna a reception din ya hadakai da gwiwa cike da tashin hankali ji yayi an tabashi ya miqe da sauri yace “na shiga uku ta kasheta ko Dr?” Murmushi Dr Saleem yayi yace “ka kwantar da hankalinka bata mutuba munsamu nasarar tsayar da jini amma akwai buqatar wani jinin da gaggawa saboda ta zubar da jini sosai” ajiyar zuciya yace “alhmdllh cikin jikinta fah?” Girgiza kai Dr Saleem yayi yace “saidai muyi hqr wannan ya lalace muyi addu’ar Allah ya kawo wani me albarka” wasu hawayene suka zubo masa yace “shikenan tayimin sanadinsa ya zube” dafa kafadarsa yayi yace “karka damu zaa samu wani da wuri bamuda lkcn wannan yanzu jini muke buqata” hanunsa ya miqa masa yace “ka diba wanda zai isheku” janshi yayi suka nufi Lab din cikin saa jinin nasu iri dayane zama yayi aka dabe leda biyu sannan suka nemi daya aka siya suka fita har dakin yabisu har yanzu tana kwance kamar gawa Dr Saleem ya daura mata jinin nurse din dake kula da ita ce ta kalli Umaimah ta kalli Hameed tace “yallabai qanwarka ce ko matarka?” Dr Saleem yace “nima abinda ke raina kenan wannan aikin mijine yallabai samada shekara ashirin nake aikin kula da lfyr iyalan Alh Adamu Hameed Shuwa a tsayin shekarun nan Umaimah autar Hajiya ce qanwa a gurinka amma kuma naga wani baqon lamari tsakanin jiya da yau”

 

Lumshe idonsa yayi ya kwanta a gadon dake facing din na Umaiman ya zuba mata ido yace “qanwata ce kuma matatace iyakar abinda zan iya fada muku kenan” murmushi nurse din tayi tace “kamar ku kadai ta Isa ta bayyana hakan…” banko qofar da akayi ne yasasu miqewa da sauri a tsorace ya nufi gadon da Umaimah ke kwance ya nuna Sadiya dake shigowa da hanu yace “kada ki qaraso nan ki tsaya anan wlh idan kika bari na waiwayoki zakisha mamaki idanma baki sani ba ina qara sanar dake Umaimah matata ce ta sunnah wacce take iya dauke lalurata Sadiya kiyi a hankali kada ki dauki haqqin marainiyar Allah batajiba bata gani ba wlh batada laifi saboda itama batasan da aurena akanta ba….”

 

“Ina ruwana Hameed kai wannan ta shafa cin amana ba ni zakuci amana saboda kai tsinanne ne mayaudari maci amana azzalumi ni zakaci amana ka fakemin da wata qaryarka wai matarka ce to na rantse da Allah ba matarka ba ko uwarka ce saina kasheta saidai Khadijah ta dawo duniya ta haifi wata kuma kaima saika tafi inda ta tafi…” Zabura tayi a guje ta nufi gadon Umaiman yayi wani tsalle ya tareta tare da riqeta ga dukkannin qarfinsa ya hankata baya ta fadi Tim a qasa kafin yayi wani yunquri ta kuma tasowa ta fakaceshi ta haye ruwan cikin Umaimah shima kanta yayi a guje ya tunkudata qasa ya zare belt din wandon jeans dinsa yace “wlh kika qara tabata sainayi miki abinda bantaba yimiki ba kashe yar mutane kikeson kiyi Sadiya me tayi miki wanne irin haukane wannan kawai don takasance matata to ki sani aurena da Umaimah hadin Allah ne haukanki bai isa ya rusheshi ba abinda yasa na boye aurannan kenan saboda nasan ke mahaukaciya ci shigowar Hajiyansa ne yasashi yin shiru da bakinsa gadan² tayo kansa kafin ya ankara yaji ta daukeshi da wani gigitaccen mari ya dafe gurin da sauri ya dago kansa yace “Hajiya…” sake zabga masa mari tayi tana kuka tace.

 

“dama abinda yasa ka dage sai anbaka ita kenan Hameed irin taka amanar kenan me yaja hankalinka harka lalata tarbiyya marainiyar Allah na tabbata Umaimah bazata taba banzatar da tarbiyyar da kayi mata ba saidai kai ka banzatar da taka itama ka lalata mata tata meye ribarka Hameed qanwarka ka lalata harda ciki Innanillahi wa innah ilaihir raji’un wannan wacce irin baqar rayuwace wacce irin qaddara ce Hameed da kanka da kanka ka ketama Umaimah haddi ka cucemu Hameed kaci amanar maraici bazanyi maka baki ba amma da sannu zaka girbi abinda ka shika” tunda ta fara mgnr kansa na qasa harta gama ta juya ta nufi gadon da Umaiman takekai ta ruqo hanunta cikin tausayawa tace “Allah ya isanki Umaimah Allah ya isar miki” miqewa Sadiya tayi ta kalleshi tace “zaka dawo ka iskeni har gda wlh saidai koni ko kai azzalumi”

Yanajinta amma bai iya tanka mataba harta fice zuciyarsa mugun tafasa takeyi yasan duk bayanin da zaiyiwa Hajiya bazata saurareshi ba saboda haka yaja jikinsa ya fita ya zauna a kujerar dake qofar dakin, daidai lkcn da Umaimah ta bude idonta ta saukeshi akan Hajiya ajiyar zuciya Hajiyan tayi tace “sannu kinji Umaimah” daga Mata kai tayi cikin sarqewar murya tace “Hajiya ki tafi dani gdanki Aunty Sadiya da Uncle zasu kasheni wlh Hajiya kasheni zasuyi” kama hanunta tayi tace “wa ai dama kin gama zaman tsinannen gdannan ni dama tun farko banso zamanki ba dandai wannan azzalumin ya nace ne kuma Daddyn ku ya goya masa baya yanzu ga abinda gari ya waya” kwallar dake zubo mata Hajiya ta share mata tace “kiyi hqr wlh saiya gane kuransa wannan ai zalumci ne shekaran jiya yaje yake fadamin wata shashashar mgn saboda Daddyn ku yace yabarki ki fitar da miji bayan Daddyn ku ya tashi yake cemin wai yayi miki miji ashe abinda yake nufi kenan Allah ma ya rufa mana asiri da cikin ya zube da munga ta kanmu don wannan me raayin riqau din ba bari zaiyi a zubar dashi ba macuci kawai”

 

Abinka da zuciyar mace duk saitaji babu dadi aibata Uncle din da Hajiya takeyi lumshe idonta tayi daidai lkcn daya dawo dakin yace “Hajiya ta farka ne?” Tsawa ta buga masa wadda tasa Umaima bude idonta tace “ban sani ba dan iska mara imani ubanka zakayi mata idan ta tashin kaga Abdulhameed idan baka fita daga rayuwar Umaimah ba wlh saina sallama ka…” kallonta Umaimah tayi taga yanda yake zubar da hawaye tace “Kayy Hajiya kibari don Allah kinga fah kuka yake don…” bige bakinta Hajiya tayi tace “eh lallai gskyr hausawa da sukace baa dan iska daya wato ke har tausayin wannan annamimin bawan kikeyi ko to zan qyaleki dashi idan ya gama daibe albarkar jikin naki a banza kya nemi tudun dafawa kuma wlh kaji na rantse saikayi dana sanin abinda ka aikata tunda kaci amana ka rubuta ka ajiye amana sai tacika”

Bai iya cewa da Hajiyan komai ba sai gaban Umaman daya matso ya kamo hanunta doke masa hanu Hajiya tayi tace “kul baka kiyayeni ba shashasha kawai babban kawai yanzu Hameed badon Allah ya duba maraicin yarinyar nan ya kawo shegen cikinnan daka kunsa mata ya zubeba daya zamuyi kenan to wlh ka fita daga idona na tsani halinka Hameed na tsani mutum maci amana baka moreba Hameed” bazai iya jure kalaman nata ba saboda haka ya juya har yakai bakin qofa ya tsaya yace “laifi nane dana boye muku gsky tun farko da ace na fada muku Umaimah mata tace da baku zargeni ba nasani Hajiya dole dama zan fuskanci wannan matsalar tunda nakasa hadiye qwalamata na sauketa akan Umaimah a lkcn da yake bai kamata ba kamata yayi ace na sanar daku matatace kafin wannan lkcn amma duk da haka inaso dake da Umaimah da Sadiya dama duk wanda yake zargina ya sani niba mazinaci bane Hajiya baki haifi fasiqi ba bantaba shuka a haramtacciyar gona ba kuma banacin itaciyar da Allah ya haramta min Hajiya koda ace ma zina nakeyi da Umaimah wannan ta faru yakama ace kuyimin uzuri nima dan Adam ne ba waliyyi bane ni inada buqatar inda zanke zuba ruwana idan na tara tun farkon aurena naso hana Sadiya aiki kukace ban isaba nasha kawo muku matsalata kuma kin kasa yimin maganinta sau nawa nazo nace muku inason qara aure amma saiku hanani kullum burinku na farantawa Sadiya wacce nine na daukota na kawota cikin family dinmu babu ruwanku da matsala babu ruwanku da damuwata Hajiya nayi hqr shekara bakwai Ina fama da matsala daya a halin inada wata matar bayan ita to me kikeso inyi idan ban nemi haqqina ba a gurin Umaimah shekara biyar tana matsayin matata ina rainonta Hajiya ko tari nake a asusun qasa yaci ace yayi cikar da idan na fasashi zai bani abinda nakeso Hajiya nasha fada miki Umaimah tanada miji kina daukan zancena wasa to ba wani bane mijinta nine matatace”

 

Yana fadin haka ya juya ya fice tare da jan qofar da qarfi a mugun fusace ya dauki motarsa ya nufi gdansa yana zuwa yayi parking ya nufi cikin gdan tun tsayawar motarsa tajishi saboda haka yana shigowa ta tareshi da bala’i tace “ai dama nasan dole ka dawo fasiqi la’anallahu wanda baisan Allah ba ka shammaceni Abdulhameed bantaba tunanin haka daga gareka ba saboda kaikam kwai dan akuya….” bata ida qarasawa ba ya dauketa da mari ta dafe gurin da sauri tace “kan ubancan ni ka mara Hameed tabdi wlh ka mari bala’i na rantse da Allah saika gwammace baka sa hanu ka mareni ba ihu kwarto jama’a kuzo ga kwarto Allah ya tsine maka Abdulhameed Allah ya isa tsakanina dakai azzalumi maci amana kisa tsaf saina kashe shegiyar yarinyar nan saidai idan bazata gdannan ba” murmushin takaici yayi yace.

“To dama wanne tsautsayine zai dawo da ita ta zauna dake itama ta samu yanci bautar da tayi miki a bayama ta rainon yayanki da kula miki da gdanki kina gantalin yawon aikin banza ta isa yanzu lkcn kula da mijinta ne itama da ita ta shayar dashi farin ciki tayi masa maganin matsalarsa dake kika kasa ta bashi lkcn da kika kasa bashi kinga dama jinin dake yawo a jikinta shine a jikina ita zata iya dani tunda irinmu daya bazata gaza kamar yanda kika gaza ba tana da dadi sosai” yana gama fada Mata ya shige dakinsa ya datso qofar yanajinta tana dukan qofar kamar zata balleta tana kiran sunansa harda na iyayensa tana qare masa zagi tare da tsinuwar diban albarka a haka yaran suka shigo gdan driver yaje ya daukosu suna shigowa dakin Umaimah suka nufa suna kiran “Aunty mun dawo zo kiga assignment dinmu ki kawo mana dakin ta nufa kamar mahaukaciya ta finciki charge dake jikin surket ta rufesu da duka kamar Allah ya aikota tana zaginsu tana fadin “dagaku har uban naku kutumar ubanku zanci ita ta haifamin ku tsinanniyar yarinyar da take neman rabani da ubanku to wlh duk shegiyar yarinyar dana sakejin ta kiramin sunan yarinyar nan sainaci wancan kwarton mazinacin fasiqin uban naku” yanajin irin tujarar da takeyi yasan duk dan ya kulata ne don haka ya bawa banza ajiyarta.

 

Sai yamma liqis ya fito daga dakin yana daura agogo bata parlourn sai yaran suna zaune sai matsar hawaye sukeyi Nihal ce ta taso ta rungumeshi ta sake fashewa da kuka tace “Uncle me Aunty tayiwa Mom take zaginta kuma yau da safe bata bamu abinci ba da zamu tafi islamiyyah sai bobbo da biscuit Uncle yunwa mukeji Maliha har kuka ta rinqayi a makaranta saida Mu’allimah ta siya mata cheese sannan tayi shiru” ransa ne yayi mugun baci wai kamarshi ace yayansa suna fita basu karya ba kawai saboda sakacin uwarsu kama hanun yaran yayi yace “kuyi hqr Auntynku batada lfy tana asibiti kuzo muje kuganta sai kuci abinci acan” murna suka hauyi da tsalle da kansa ya cire musu kayansu yasa musu wasu ya jasu suka fice daga gdan suna zuwa asibitin ya nuna musu dakin suka shiga da gudu lkcn an cirewa Umaimah roba ta biyu ta jinin tana zaune ta jingina da pillow da gudu suka nufeta suna murna suna tsalle itama taji dadin ganin yaran saboda ta saba dasu koya ta yini bata gansu ba sai taji babu dadi haurawa sukayi saman gadon suka rungumeta Maliha tasa kuka tace “Aunty shine jiya Uncle ya daukeki kika tafi kika barmu kikaqi dawowa kiyi mana break yau sai haka muka tafi bamu karya ba nayita kuka a makaranta inajin yunwa” Nihal ce me wayo tace “Aunty kin rame kinyi fark meye yake damunki aka kawoki asibiti?” murmushi tayi vta shafa kansu tace “banida lfy ne amma naji sauqi da ganinku kunajin yunwa ko?” Daga Mata kai sukayi tace “no wonder indai yarana sunajin yunwa Ina ganewa Hajiya dake zaune tana kallonsu tana murmushi tace “kaji yan jakar uba ina iyayen naku da suka barku da yunwa” kawar dakai Umaimah tayi tace “mudai ki bamu abinci yarana suci Hajiya idan sunci sayi miki bayani” Nihal ce tace “mu Mom dinmu bata sonmu yau ma duka tayi mana saboda mun tambayi ina Aunty”

Daidai lkcn ya turo qofar ya shigo tare da sallama dago kanta tayi da sauri idonsu ya sarqe guri guda yanayi mata kallonsa me narkar da zuciya murmushi yayi mata tare da ajiye kayan daya dauko mata da shopping din da yayo yace “Hajiya sannu da qoqari yame jikin?” Ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata amsa masa abincin ta zubo jallop din shinkafa ce data wadatu da alayyahu da kifi banda sai qamshi takeyi ta miqawa Umaimah ta karba tare da zaunar da Maliha ta fara basu abincin a baki sunata zuba mata santi itadai batace musu komai ba saboda yanda takejin qwayar idonsa na yawo a jikinta muryar Hajiya ce ta katseta tace “idan kaga dama kaje Daddyn ku yana nemanka yanzun nan ya fita zashi gdanka” amsawa yayi da “to” ya miqe yace bari naje na biyasu kudinsu na dawo dakatar dashi Hajiya tayi tace “aa aikai ka gama aikinka saura namu ubanka ya biya komai” dagowa yayi da sauri ya kalleta yace “amma Hajiya…” Dakatar dashi tayi da cewa “karkace min komai Hameed wlh da zaka yarda ma daka daina zuwa inda nake saboda idan na ganka jinake kamar na kasheka”

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*

 

*🅱RILLIANT WRITERS* *ASSOCIATION* 🖊
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_

 

*GIDAN UNCLE*
( _Love and romantic story_)

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

 

*MALLAKAR*
👇🏻
*FAUZIYYA TASI’U UMAR*
*®FAUZAH*

 

Wattpad👉🏻 realfauzah

 

[email protected]

Alhmdllh a madadina da iyalaina munayiwa daukacin al’ummar duniya barka da shiga sabuwar shekarar gogerioun calendar duk da dai mu munci wata hudu a tamu ta musulumci Allah ya hadamu da alkhairan cikinta sharrikan dake tattare da ita Allah ya kade manasu yanda muka shigeta lfy Allah yasa muga qarshenta lfy idan kuma bamu da rabon gani to Allah ya karbi ranmu muna cikin musulumci muna masu aikata ayyukan alkhairi sannan yasamu a ceton Muhammadur rasulullahi (S.A.W).

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button