Mijin Malama Book 2 Page 39
Kwantar da Majeederh ya yi tare da zubewa kansa a ƙasa tunaninsa ya tsaya, baya da kuzari ko fahimtar wanne kalar yanayi yake ciki, kowa na parlon kuka yake musamman Maman Alpha data san irin mugun son da Majeederh kewa Khalil, gashi an wayi gari yau babu shi a duniya, ya rasu ya barta da cikinsa, ya barta da so da ƙauna haɗi da farin cikin daya fara ɗanɗana mata, ta samu kwanciyar hankali asalin ƙibarta wacce ba a san da ita ba ta bayyana, farinta na larabawa ya ƙara fitowa ga wani buɗewa da ƙugunta ya yi, ga wani irin fitanannen kyau da tayi wanda ko a kwanakin baya shi kansa Khalil kallonta kawai yake, tuna wannan abu sai ya ƙara masifar ɗagawa Maman Alpha hankali, Majeederh ba zata ɗauka ba,ba zata taɓa yarda da rashi da fahimtar mijinta Khalil ya rasu ya barta ba, Zaytoon bata uhm bata uhm’uhm sai ajiyar zuciya take saukewa musamman idan idanunta ya sauka akan tokar gawar Khalil, a tarihi bata taɓa jin ko labarin halin uba kamar Mr President ba, balle wasan kwaikwayo ko irin labarin hikaya na littafan Hausa ɗinnan. Roohan dake ganin Khalil kamar sa’an shi yafi sauran gigicewa domin bama asan inda hankalinsa yake ba, tunda ya yanke jiki ya faɗi, Mami zaka ɗauka Raihana ce ta mutu saboda kukan da take, Khalil wani irin mutum ne mai shiga rai da tarin nagarta, sanda zai fara baka sha’awa duk da irin halinsa kai bama zaka sani ba. Dr aka kirawo har gida ya duba Majeederh ganin har yamma bata motsa ba, ya sauke numfashi a hankali ya ce “I am sorry ta samu heart attack ne, dalilin labarin da bata taɓa tunanin ji ba” Uncle Isma’il ya jinjina kai ya ce “Mene mafita?” Dr ya ce “A guji abinda zai ƙara sawa ta gasgata mutuwar mijin nata, tunda a yanzu idan ta farka gani zatai kamar mafarki tayi kuma zata ganshi” General Alpha da saukar shi kenan domin su Uncle har sun kwana, a hankali ya kalli Dr ya ce “Zuwa yaushe kake ganin zata farko?” Dr ya ce “Bana ce ba, ana buƙatar zuciyarta ta samu hutu amma zata iya kwana biyar ciff kafin ta dawo hayyacinta” Sallama Dr ya yi musu, Mai martaba Ajlaal baya cewa komai, kwana ɗaya tak ya fita hayyacinsa ko ruwa sai dole yake kaiwa bakinsa, a ranar kuma mahaifin Ƙhulud wanda yake ƙani wajan Takawa Sultaan ya sauk’a a ƙasar daman bai fiya zama ba, shi ma ya kalli Dr ɗin bai ce komai ba. Wajan ya yi shiru a hankali Arzaan ya ce “Kafin kwana biyar ɗin a saka malamai yi mata sauka da rubutu na haƙuri da dangana” Uncle Isma’il ya ce “Wannan shawarar tayi kuma abin dubawa ce” Arzaan ya sake cewa “Zan shiga Harami In sha Allah, yarinyar nan zata iya samun taɓin hankali” Abbu kansa a ƙasa baya furta komai sai kiran sunayen Allah. Ƙhulud Arzaan na wajan Gimbiya ita da Mami domin har yanzu bata farko ba, Clara bin komai take da idanu ta kasa yarda wai Ddmaster bom mahaifinta ne, idan ta tuna wai da bakinsa yake ƙara bata confidence na kwanciya da maza da kawo mata su, ya mayar da ita cikakkiyar karuwa Mai lasisi sai ta ji wata iriyar faɗuwar gaba. A kwana na huɗu Barrister Aliyu Sufyan da Almustapha da Hajia da Papi suka zo yiwa Majeederh gaisuwa sai dai yadda suka risketa ya ɗaga musu hankali ainun, Barrister Aliyu da General suka kalli juna ba wanda ya yi magana, a lokacin kuma tuni Allah ya cirewa Aliyu son Majeederh kallon ƴar uwa kawai yake mata. A daren ranar suna zaune a parlor suka ji an buɗe ƙofa an fito gabaɗaya suka kalli Majeederh dake tsaye tana dafe kanta dake sara mata, bata ganin kowa a parlon sai idanunta daya sauka akan Khalil dake zaune saman kujera ya harɗe ƙafa yana danna waya, ta marairaice fuska ta nufi wajan da sauri tana cewa “Man” Sai taga Khalil ya juyo yana mata wani irin sassanyan murmushi mai laushi ya ɗaga mata gira. “Ina ka je Khalil? Ka tafi ka barni” Maman Alpha da Mami da Zaytoon suka kalli juna, Majeederh ta faɗa kan kujerar ta shiga dukan ƙirjin Khalil yana karewa ta saki wani irin raunataccen kuka ta ce “Ka zautar dani, daman na san kana nan karka sake mini haka zan iya mutuwa, wallahi mutuwa zan yi don Allah Khalil karka sake tafiya, idan zaka tafi sai dai mu tafi tare” Pillow take ta duka wanda zaton ta Khalil ne kamar yadda idanunta ke shaida mata hakan, Maman Alpha ta miƙe tana riƙeta ta ce “Majeederh mene haka? Ina ilimin naki” Da wani irin yanayi take kallon Maman Alpha sai kuma ta nufi hanyar fita ganin Khalil tsaye a bakin ƙofa yana miƙo mata hannu ta taho su tafi, Maman Alpha ta riƙeta sosai tana kuka ta ce “Ki yarda Allah ke rayawa shi yake kashewa, ki yarda Khalil ya rigamu gidan gaskiya…,” Ta girgiza kai ta miƙa hannu ta ce “Wallahi bai mutu ba, ba zai taɓa mutuwa ya barni ba, ku yarda dani gaskiya nake faɗa muku, Mijina yana raye yana duniya wallahi yana nan, gashi can yana ɗaga mini hannu yana kirana mu tafi tare” Zaytoon ta ce “Hawwa’u wake halittar Mutum?” A hankali ta ce “Allah, amma wallahi tallahi Khalil bai mutu ba, na ji ajikina ALLAH ne shaida Khalil bai mutu, wallahi bai mutu ba don Allah Granny ku barni naje wajen mijina ko mutuwar ce a binne mu tare” Sunga tashin hankali domin hauka tuburan Majeederh ke yi, tana rungume jikin Abbu yana mata addu’a a hankali kuma Roohan ke mata firfita bayan an samu ta sha ruwan rubutu wanda aka haɗa da ruwan zam-zam bacci ya ɗauketa a jikin Abbu tana sauke ajjiyar zuciya. Abbu shafa kanta yake, ji yake kamar yafi kowa jin zafi da raɗaɗin abinda ya samu, idan ya tuna abubuwan daya dinga ma Khalil sai ya ji zuciyarsa ta raunata, gashi harya koma ga Ubangijinsa bai nemi yafiya wajansa ba. Aka ɗauke wayarta da duk abinda zai sanya ta dinga ganin Khalil karatun K’ur’ani kullum ake saka mata, sauka tako’ina ake mata, Gimbiya ta dawo gida har yanzu hango yadda wutar dake cin naman Khalil take, rashin maganarta ya ƙaru, bata da walwala kullum tana part ɗinta, shugaban jam’iyyar na ƙasar Germany ya sauka domin shi ya gama zaton Gimbiya ƴar Germany ce tana da komai dake nuna kasancewarta cikakkiyar ƴar ƙasar, wani abu ya ɗarsu a ransa yana jin kamar zata iya maye gurbin mijinta wajan zama President of Germany.
Some Year’s later.
Majeederh na zaune idanunta ƙurr akan yaranta guda biyu da suka kasance duka maza, babu inda suka bar Mahaifinsu marigayi Khalil, kamar ya yi kaki ya tofar saboda masifar kamar da suke, fatar su kamar ta ƴan Ethopia ko Mali ga wata kalar suma a cuccure, shekaru wajan biyu da wata shida da rasuwar Khalil ana ganin kamar ta manta da shi ne, amma babu wani abu daya dangancin zaman su wanda ya shafe daga kanta, the romance,the love, the memory was still fresh, and it will be with her forever. Gashi wai har yaran sun fara tafiya? Dake zafin nama ne dasu gasu da farin jini masifar gata suke samu, a hankali ta share hawayen daya gangaro daga cikin idanunta, babu tashin hankalin dake damunta yadda su Uncle da Mai martaba suka kasa fahimtar ta, har suke tunanin zata iya rayuwa da wani namiji ba Khalil ba? Duk wanda zata aura gangar jikinta kawai zai samu, amma ta ma zuciyarta al’ƙawarin ko hannunta bai isa ya riƙe ba, kamar yadda yake mallakin mijin Malama haka zai dinga kasancewa, har ta mutu su haɗu a lahira wannan wani al’ƙawari ne na zuciyarta, komai dake jikinta mallakin ruhin Khalil ne. Uncle Isma’il ne ya shigo yana gyara zaman babbar rigarsa, fuskarsa ɗauke da murmushi a hankali kuma Uncle Bello ya shigo sai kuma Mai martaba Ajlaal suka nemi waje, Uncle Isma’il ya kalli Majeederh a hankali ya ce “Ma sha Allah, kamar yadda na ɗauki niyya kuma na cika a yau juma’a a yanzu an ɗaura aurenki da ɗan uwanki Alpha, ga sadakin ki” Ya miƙa mata kuɗin, ta kasa karɓa kanta a ƙasa ya kira sunanta a taushashe ya ce “Hawwa’u?” Hawayen daya gani kwance a fuskarta ya sanya jikinsa yin sanyi, tausayinta ya kama shi muryarta na rawa ta ce “Uncle kuyi miki haƙuri ku raba auren nan don Allah” Uncle Isma’il ya ce “A raba? Auren? Are you sure da bakinki kike furta hakan? Yayanki Alpha ne fa?” Ta girgiza kai jikinta na rawa ta fashe da kuka ta ce “Uncle ba zan iya kula da wani miji ba, ba zai samu abinda yake so ba, rayuwata ta jikkata, zuciyata ta raunana gangar jikina kawai zai samu, bana son shiga fushin Ubangiji da ɗora masa nauyin abinda ba zai iya ba” Ta zame daga kan kujerar ta durƙusa gaban Uncle Isma’il ta riƙo tagwayen yaranta masu masifar kyau kamar Zain_Abeed, ta juya ta kalli Hussain da Alhassan ta nuna musu Uncle Isma’il ta ce “Ku bawa Uncle haƙuri, tell him zuciyata ta ruhin Papa ɗinku ce, ku faɗa masa kune rayuwata, kuce masa karya haɗa ni da wani, beg him” Ta haɗe hannayenta bibbiyu, Alhassan da Al’hussain ganin yadda Mimi ɗinsu tayi dake suna da masifar wayo shekara biyu ba wasa ba, suka haɗe guntattakin tafin hannunsu tare da rausayar da kansu gefe, cikin gwaranci suka ce “Piyis Uncle” Alhassan ya kwaɓe fuska kamar yadda margayi mahaifinsu yake, a nutse Uncle Bello ya fice daga wajan, Uncle Isma’il tausayin Majeederh da yaran nata suka gigita masa tunani wani irin rikitaccen tashin hankali ya ruftowa zuciyarsa, amma how long zasu zubawa Majeederh idanu? Mutuwa gaskiya ce, hisabi wajibi ne, dole tayi aure ko dan samun nutsuwar zuciyarta.
“Majeederh kiyi haƙuri, aure an riga an ɗaura, faɗuwar wani tashin wani, waman ƙaddarallahu hakƙa ƙadrihi, bamu isa mu sauya miki zanen ƙaddararki ba Hawwa’u, bamu da zarafi ko ikon yin haka, Ubangiji daya ƙaddara samuwar ki a duniya ya fiki sanin dalilin ɗauke Khalil daga rayuwarki, babu mamaki rabo ne ke kira, kin san idan Rabo ya rantse babu wanda ya isa ya shata layi, Matsayinki na Musulma dole Kiyi imani da ƙaddara” Ya sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, zuciyarsa na harbawa sosai ganin yadda Alhassan ya kafe Uncle da idanu ya haɗe fuska sosai, gani yake kamar shi ke saka Mimi kuka. “Shin ba kiga uwar yaron ba? Ta amshi ƙaddara ta cigaba da rayuwarta? Ba kiga Biyunin Khalil ɗin ba? Kiyi addu’a tare da moving on ki cigaba da rayuwa, Alpha yana sonki kuma zai kula da rayuwarki da yaranki” Ya girgiza kai ya ce “Shekara biyu? Baki mance ba? Anya? Haba Majeederh kamar baki yadda da ƙaddara da Imani da ita ba?” Ta rungume yaranta sosai musamman Alhassan dake huci shi ɗaya ta ce “Ko shekara ɗari akai ba zan mance mijina ba, ko ana mutuwa ana dawowa na mutu na dawo ba zan manta Man ba”
“Idan ni yake so ya samu,
Idan gangar jikina yake so gata nan, amma ba zai taɓa samun farin cikina ba, ba zai taɓa ganin walwalata ba, ba zai iya samun amincewa da yardata ba, da amincewata ya raɓi jikina ba, balle rabo ya rantse akai na, zuciyata ta ruhin Man ce, jikina na ruhin Khalil ne, farin cikina na Mijin Malama ne” Daga bakin ƙofa aka ce “A yanzu kuma ni ne mijin Malama, kenan na yi dace da duk zan samu haka daga gareki?” Majeederh ta runtse Idanunta da kyau jikinta duka rawa yake da ɓari, Uncle Isma’il ya fita Alpha ya ƙaraso gaban Majeederh, da sauri ta miƙe ya riƙe ƙafafuwanta da kyau ya durƙusa gabanta, shi kansa jikin nasa rawa yake saboda wani masifar shakkarta yake ji, ganin yadda ta ƙara riƙe kanta shirun ta ya ƙaru zai iya k’irga sanda ya ji maganarta tun bayan mutuwar margayi Dr Ibrahimul-khalil Abraham. Ya yi kasa da kansa wasu masifaffun hawaye masu zafi na sakkowa daga cikin idanunsa, jikinsa na ɓari yana wani irin runtse idanunsa a firgice cikin tashin hankali ya ce “Ni ne raba gardamar wanzar da farin ciki a wajanki Jiddatul-khairy, i love you so much, ki duba abubuwan da suka faru, ki yarda rabon samun Alhassan da Al’hussain ne ya sanya na bar gida har kika auri Khalil, ki yarda wani rabon ne ya kashe Khalil ya haɗani dake, ada shi ne mijin Malama a yanzu kuma ni ne mijin Malama, ina son ki tun kina zanin goyo, na wahala akan ki,kuma ina kan wahala, na rayu da wani mahaukacin son ki” Ta ƙanƙame Al’hussain, Alhassan kuma ya ƙanƙameta yaran duk basu sakin jiki da Alpha ɗin tun wuri, ta ce “Ba zan iya ba, wallahi ban iyawa, ina ma Ubangiji ya ɗauki raina ya kaini zuwa ga ruhin mijina? Ba zan taɓa iya cin amanar shi ba, kamar yadda ya buƙaci kar na manta da shi har duniya ta tashi ban mancewa da Man” Ganin yadda take kuka yasa Al’hussain fashewa da wani gigitaccen kuka, Alhassan kuma ya dinga kwaɗawa Alpha motar wasan hannunsa yana ture shi daga wajan ƙafar Majeederh, Alpha ya kalli Alhassan tears running down his cheeks ya ce “I am sorry my son, but i love ur mother i love her with all my heart and soul, i am madly in love with her” Da sauri ya miƙe tare da ficewa yana jin dole ya bar ƙasar nan da Majeederh ya mantar da ita kowa da komai hakan ne zai sanya ta yarda Khalil is no longer alive, as soon as tana Nigeria memory ɗin rayuwarta da Khalil ba zai taɓa gogewa ba. Yana fita Majeederh ta durƙushe tana fashewa da kuka ta kalli yaranta ta ce “Alhassan, Al’hussain bamu da gata, mun rasa garkuwa jagora kalli yadda ake mana?”…
U.S /Arizona.
Mayo Clinic. Da sauri ya ƙarasa shigowa reception na cikin haɗaɗɗan Hospital ɗin yana mai danna wayarsa a gaggauce, trouser ne jikinsa mai ɗan kauri saboda whether ɗin garin was very cool ga wata snow dake zuba, ya ɗora winter coat saman t.shirt ɗin jikinsa, kamar wani cikakken ɗan U.s ɗin har yanzu bai gama dawowa daidai ba, idan ya tuna yadda wuta ta cinye Joshua sai hankalinsa ya yi masifar tashi, yanzu da ace bai dabara zuwa da mota iri ɗaya ba, ya shiga kwana suka sauya direction shi da Joshua da tuni shi da Khalil zasu babbake? John ya sauke numfashi idanunsa akan baturiyar dake cewa “John?” Ya ɗaga kai ya ce “Yes” A hankali ta furta “Congratulations, After two years and six months, your patient recovered and he is awake…
[