Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 40

Sponsored Links

0/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: “Zuleehart? Aure? Da yara kuma har uku? Wanne irin wasa ne wannan mara daɗin ji, you’re my neighbor not my daughter-in-law” Zuleehart ta ƙaraso ciki, kyawawan yaran suka biyo bayanta da sauri, Bilal, Dina, Waheed, Maman Alpha ta dinga kallon Bilal dake tsananin kama da General ta durƙusa kanta a ƙasa hawaye na zuba a idanunta ta ce “I am sorry General, bani da zaɓi na gaji da zaman ɓoye kai na, na gaji da rayuwa daga ni sai yarana, na gaji da zuwa gidan nan matsayin maƙociya bayan ni surukar gidan ce, na gaji da ɓoye Bilal i am tired of everything”. Uncle Isma’il
Ya ce “Kai na ya ɗaure”
“Dame?” Uncle Bello ya furta idanunsa akan Bilal
“Bello kana ji fa? General ke da aure har da yara uku? Bayan duka mun san baya da shi sai yanzu?” Zuleehart ta girgiza kai while hawaye na sake zuba akan fuskarta ta ce
“Ask him Uncle, ba zan masa ƙarya ba, bana da kowa a ƙasar nan, dalilin shi nazo” Uncle Isma’il ya ce “Alpha” General dake kusa da Majeederh ya ɗago kansa ya zubawa Uncle duk ya yi zuru zuru
Uncle ya ce “Mene gaskiyar lamari? Da gaske matarka ce? Su ɗin yaranka ne?” Yaya Bilkisu dai bata uhm bata uhm’uhm sai Innati ta ce “Bama sai ka tambaya ba, kana ganin tsageran yaron nan kasan jinin soja ne, shi kenan ka rungumi matarka ka sake kululu uban kowa ya huta” Sai kuma ta fashe da kuka wiwi ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ubangiji kayi mana magani, tunda uwata tayi cikina ta haifa, nayi cikin wasu na haifa ban taɓa ganin masifa irin ta jiya ba” A taƙaice Abbu ya ce
“Innati, ki bari muji abu ɗaya” Tayi saurin cewa
“Yanzu Audil azizu maganata ka mayar amshin shata?” Clamly ya ce “Kiyi haƙuri”
Girgiza ƙafa kawai take, Uncle Isma’il ya sake kallon Alpha cikin kakkausar murya ya ce “Ina magana kana tsare ni da Idanu? Abinda Yarinyar kenan ke faɗa gaskiya ne?” General ya juya ya kalli Majeederh wacce kanta ke ƙasa, tsoro yake ya furta “Eh” ta ce ya yaudareta ya mata kishiya ko taƙi accepting auren nashi, tunda ya auri Majeederh bai ga dalilin da zai sanya ya yi wasa da damar shi ba, Zuleehart kallon Alpha take wanda yaƙi yarda ya kalleta.
Kau! Uncle Bello ya saukewa Alpha wani gigitaccen mari, wanda ya sa ya ɗan dafe fuskarsa, cikin faɗa da bala’i wanda ba a taɓa jin Uncle Bello ya yi ba ya ce
“To! Ban haifi ɗan da zai raina mini ɗan uwa ba, da har ana magana kanawa mutane kunnen uwar shegu, who are you? Dame kake taƙama da gadara? Eh?”
“Bello” Uncle Isma’il ya kira sunan ƙaninsa, yana ɗaga masa hannu, alamar ya saurara abi komai a sannu, ya lura Shock da damuwa ne ya yiwa Alpha ɗin yawa, a karo na uku ya sake cewa “Ya zama last time da zan tambayeka, who is she?” Kansa a ƙasa ya ce “She’s nothing, but a human being” A gigice Zuleehart ke kallon shi da wani irin masifaffan tashin hankali, jikinta na rawa da ɓari ta kasa cewa komai . “Ba matarka bace?” Ya girgiza kai, Maman Alpha kallon Bilal kawai take koman shi iri ɗaya ne da General. “Buɗe baki za ka yi kai bayani, ya akai ta ce matarka ce? Wannan yaran fa? Kamar da kuke da wannan fa?” Ya nuna Bilal. Alpha ya ce
“I know nothing, kama kuma tsarin Ubangiji ne, she’s not my wife!”
Da wani irin sauri Zuleehart ta kalli Alpha, tashin hankali, ruɗu, gigita, suka haɗe mata lokaci ɗaya cikin kuka ta ce “General kasan me kake cewa? Kasan me bakin ka ke furtawa? Kana cikin hankalinka?” Cikin tsawa ya ce “Kin sanni ne? Wani ya turo ki? Sharri zaki mini? Kin taɓa jin labarin nayi hauka? Yaushe na aureki? Mene hujjarki na auren?” Tayi baya kamar zata kifa da sauri yaran sukai kanta a tare lokaci ɗaya suka ce “Maaa!” Bilal yazo wajan General ya riƙe hannunsa ya ce “Abbie, Maaa Abbie” General ya runtse idanunsa can kuma ya dakawa Bilal wata gigitacciyar mahaukaciyar tsawa ya ce “Leave” Bilal ya fashe da kuka, Zuleehart hooking brain ɗinta yayi na wani lokaci ta kasa yarda ko gasgata abubuwan da suke faruwa, yau ita General ke faɗawa haka? Ta rabu da iyayenta saboda da shi? Tayi sadaukarwa mai yawa dalilinsa? Tun baya hayyacinsa har yasan waye shi? Ya bata labari ta yarda dashi, ya mata tayin soyayya ta amince masa, har aure? Kenan ya yi haka ne saboda ya manta da Majeederh? Gudun kada depression ya kama shi? Ta durƙushe cikin tashin hankali ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Kuka take kamar ranta zai fita ta kalli General ta ce “Ka ji tsoron Allah, ka tuna akwai ranar mutuwa ka duba yaran dake tsakaninmu” Ya miƙe kamar zai daketa yana nunata da hannu ya ce “Kee! Stay away from my life, ban sanki ba, baki sanni ba idan burin ki haɗani da matata ce you decieve yourself, yara kuma ban haɗa komai da su ba” Ta kalli Majeederh ita dai Majeederh duk wannan tashin hankalin baya kanta, damuwarta ta ya isheta. Zuleehart tayi murmushin takaici ta ce “Haka ku Hausawa kuke, manta abu baya muku wahala, cin mana, yaudara, da rashin ƙima da darajar aure da matayenku, kuna wasa da zuciyar mata” Ta share hawayenta tana riƙe hannun Dina ta ce
“Ban dawowa, duniya nan zaka gani, lokaci al’ƙali” Ta danne zuciyarta ta ce “Yadda ka sama silar zubar hawayena, In sha Allah sai Majeederh ta zama silar zubar naka hawayen, yadda kayi wasa da zuciyata In sha Allah haka Majeederh za tayi da taka, yadda ka raunata tawa haka taka zata tarwatse, In sha Allah, In sha Allah idan har bani da hak’ƙi akan ka, Allah zai saka mini tare da zu’riata” Ta girgiza kai ta ce “Da yardar Allah ba zaka taɓa samun wacce zuciyarka ke so ba, da yardar Allah ba zaka taɓa samun farin ciki a soyayya ba, da izinin Ubangiji sai soyayya ta sanya ka wahala Allah ya ɗanɗana maka so da daɗin da zaƙin soyayyar wacce ba zaka taɓa samunta ba a rayuwarka” Tana faɗin haka taja hannun Bilal dake ta kuka ta ɗauki Dina, Waheed ya riƙeta suka fice daga cikin gidan. Maman Alpha ta miƙe tare da yin waje itama at the same time.

Washegari suna zaune a parlour, lokacin ma dai tattaunawa suke dake kuma weekend ne, a hankali ta yi sallama ta shigo, suka kalleta Maman Alpha ta haɗe fuska, Latifa ta shigo tana tura wani tsohon mutum a wheelchair, suka dinga kallon mutumin Abbu kamar ya ganeshi sai kuma ya manta ina ya san shi. Maman Alpha ta ce “Mene ya kawo ki yau kuma? Maza tashi ki fita” Tana kuka ta ce “Don Allah ku saurareni, hakan zai sanya ku ƙara fita daga duhun da kuke ciki ta wani ɓangaren” Maman Alpha za tayi magana Uncle Bello ya ce “Bari muji meke tafe da ita ko?” Latifa Omar ta ce “Banga laifinku ba, na cancanci ko wane irin hukunci, son zuciya da kwaɗayi da kuma baƙin ciki ya jani zuwa cikin kabarina tun kafin lokacin mutuwata, ban kasance ƙawa Aminiya ta gari ba, duk abinda ya samu Majeederh ni ce sila amma ba komai ya zama laifina ba” Ta kalli Abbu ta ce “Abbu ka tuna wannan? Wani Alhaji Bashir da kuka yi maganar auren Majeederh akan Deal? Zai baka kuɗi ka bashi auren Majeederh?” Su Uncle Isma’il gabaɗaya suka kalli Abbu shi kuma ya dinga kallon Alhaji Bashir, Latifa Omar ta ce “Shi ne wannan, ga nan ya karɓi nasa hisabin duniyar, ka hana shi auren Majeederh bayan ka amshi kuɗin shi, akan gurɓatacciyar zuciyarsa ya sace Majeederh tare da reping nata, hakan ya faru ba tare da saninta ba, domin an gusar mata da hankali” Tayi ƙasa da kai ta ce “Maman Alpha idan kin tuna sanda bamu ga Majeederh ba tsayin sati har tace mana farkawa tayi ta ganta a asibiti to a lokacin akai reping nata, babana ya shirya hakan” Gabaɗaya suka kasa magana, Yaya Bilkisu ta ce “Ke mene haɗin ki da shi? Bayan Malam Umaru babanki?” Ta ce “Ni Adopted child ce, nima Shegiya ce bana da uwa shi kansa bai san wacece babata ba, yana da yara sunfi 30 yayi amfani da arziƙin shi ya yaudari ƴan mata da zawarawa da yawa, rabin yaran shi duka sikila ne kamar yadda Baby Khalil ya kasance sikila, Mijin Malama baya da alaƙa da baby khalil banda ta Kasancewar shi ɗan uwa, suna kama ne da Dr Ibrahimul-khalil saboda kasancewar, shi da Majeederh are cousins, baby khalil is my younger brother” Abbu ya kasa motsi, bai taɓa baƙin cikin kasancewar shi uba irin yau ba, yana ina duka hakan ke faruwa ne? “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” A fili ya ce
“Nawa ne kuɗin” Latifa Omar ta ce “Ba kuɗin ake buƙata ba yanzu, yafiyar Majeederh ni da mahaifina muke so, abubuwa sun mana yawa, duniya ta juya mana baya sai data bari muka gama jin daɗinta, naci amanar aure data mijina gashi yanzu nida haihuwa sai kallo amma yanke mini mahaifa, duka abubuwan dana shiryawa Majeederh ya dawo kai na, hatta aurenta da Khalil ni ce sanadi nayi zaton bashi da kowa, a gari kawai yake yana gantali, shi da gang team sai nayi zaton zata sha wahala idan ta aure shi, ashe bokana ya rufeni bai faɗa mini asalin waye Dr Ibrahimul-khalil mijin Malama ba” Innati ta miƙe tana dungure kan Latifa ta ce “Annamimiya, algunguma ƴar maza mai warin zina” Kuka kawai take, Alhaji Bashir baya motsi saboda paralyse shi kansa kuma sikila ɗin ce da shi. “Na yafe miki, dake da shi, but it’s over between us” Latifa ta ce “Na sani, kinfi ƙarfina kin mini nisa, don Allah don Annabi ki bani baby khalil na riƙe na dinga kallon yaro a gabana ko zan ji daɗi” Majeederh ta ce “Allah ya sauwaƙa, ki ɗauka bashi da haɗi daku, zan ma nesanta shi daku” Maman Alpha ta ce “Ai yara kike so? Sanda kike ta zubar da kyautar da Ubangiji ya yi miki bakya tunanin zaki iya son haihuwa Nan gaba? Hoooo ƙaaasa! An yafe muku tashi kuje” Fita sukai jiki a sanyaye Abbu ya dafe kansa dake juya masa.
A hankali Khalil ya juya kujerar da yake zaune, bluetooth a kunnen shi yana jin komai dake faruwa, domin a jiya sai daya sanya wata na’urar ɗaukan sauti a gidan, ya kuma saita ta, idanunsa sukai jajur. John ya ce
“Mene amfanin ɓoye kanka ne? Yana da kyau su san mijin malama is still alive” Khalil baiyi magana ba, sai jijiyoyin kansa da suka fito tare da yin ɗoɗar a saman goshinsa, idanunsa sukai jajir John na lura da yadda naman jikin Khalil ke rawa, gargasar jikinsa ta mimmiƙe tsaye tana zubewa. Har John zai yi shiru sai kuma ya ce “Mene amfanin zuwa Orphanage ɗin nan kace zaka yi rayuwa cikin yaran da kake taimakawa?” Khalil ya miƙe tsaye yana dafe kansa John ya miƙe ya ce “Ko wajan Ummie ne ka….,” Bai ƙarasa maganar ba yaji Khalil ya ɗauke shi da mari ya damƙi wuyansa ya haɗe da jikin bango duka jikinsa rawa yake idanunsa sun firfito waje da ƙarfi ya ce “Shut up!” Sai kuma ya saki John Khalil ya dafe kansa a gigice ya ce “My head” Daidai nan Faɗimatu ta shigo da basket kyakkyawar yarinya cikin kamilalliyar shiga, John ya ce “Wife stay right there” Faɗimatu ta kalli John wanda sunan shi tuni ya koma Othman Zannur. Ta ce “Dear Yaya Khalil na kawowa abinci fa” John ya ce “Wife i said ki tsaya nan ko” Ta tsaya tana kallon Khalil durƙushe, John ya kama hannunta suka fice tare da rufe ƙofar, babban Orphanage ne, gidan marayun ya haɗu Khalil tun yana asalin bad boy ɗinsa ya gina, Faɗimatu a gidan ta tashi itama har zuwa lokacin da John ya aureta, yara ne sosai a gidan Khalil na mutuwar son su kamar rai haka kowa na Orphanage ɗin. Khalil ya jima zaune kafin ya miƙe tsaye ya ɗauki bottle water ya zubawa tsakiyar kansa, kamar ya kira Zaytoon ko Mai martaba Ajlaal haka yake ji, amma ya ɗauki niyyar sai ya yiwa kowa hauka duk wanda ya shiga rayuwar Majeederh dame ƙoƙarin raba shi da ita more especially GENERAL ALPHA BELLO KHAN. tsayin wata guda kenan kullum Khalil yana zuwa bedroom ɗin Majeederh, sai asuba yake guduwa ya razana Uncle Bello hade da General, Majeederh kuma taƙi yarda ta tare, ta yarda zata rayu da ruhin Khalil tunda yana sanyata cikin farin ciki, kuma har yanzu a tunaninta a mafarki yake zuwar mata, tayi wani irin kyau haske da ƙiba Maman Alpha har mamaki take, cin abicinta ya ƙaru shi da kan shi Khalil ya fahimci haka, har wata guda ba wanda ya san labarin Khalil na raye! Even his mother, Aaliyyah bata ƙasar ma bakiɗaya ita da Barrister Aliyu ya ɗauketa sun barwa Latifa gidan.

Yau ma kamar kullum Khalil ya hauro ta katanga ya sanya fararen kaya voyel ne fari tas da shi, kai tsaye direction ɗin da zai kai shi bedroom ɗin Majeederh ya nufa, ya zuge glass ɗin window ya diro, abinda bai taɓa gani ba ya gani, ya ganta kwance ta rungume Alhassan dake ta kuka zai sha tea cikin dare tana bashi kuma ya tarwatsa cup ɗin saboda ya ji haushi, baccin da ya yi kenan bai sha ba, Khalil ya zubawa fuskar Alhassan idanu ganin wata mahaukaciyar kama da suke da yaron, nan da nan ya fara loosing control ɗin shi, so da ƙaunar yaron ya wanzu a zuciyarsa, ya ƙarasa bakin gado ya zauna, a hankali ya kifa kansa tare pecking kumatun Alhassan yana buɗe idanu yaga yaron ya kafe shi da Idanu, sai kuma ya ɗauke shi ya rungume yaron kamar yasan babansa ne ya ƙanƙame shi yana sauke ajiyar zuciya, sun jima haka kafin Khalil ya goya yaron abayan shi dake Alhassan ɗan fitina ne irin babansa ya ƙanƙame shi, Khalil ya kama window ɗin ya dira yana jin Alhassan yana kyalkyala dariya a haka ya fice da yaron goye a bayansa…
[

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button