Mijin Malama Book 2 Page 47
“Ina son shi tun ban san yana duniya ne ko ya mutu ba? Ina son shi tun baya cikin rigar musulunci, ina son shi tun kafin na san cewa jininmu ɗaya, ina son shi…” Ta kasa ƙarasawa saboda wani irin abu daya caki zuciyarta, can ƙasan zuciyar tana jin kamar bata kyauta mata yadda ta buɗe sirrin da babu wanda ya san da shi ba, daga ita sai zuciyarta wacce kuma ita ce ma’adanar ajiye wani ingantaccen sirrin hijabin rayuwarta bakiɗaya.
Wata kunya ta ji ta lulluɓe ta, tare dayi mata hijabi wa gangar jikinta, tana jin inama wajen da take zaune ya tsage ta shige ciki? Amma ina! Duk yadda ta kai da yiwa bakinta linzami a yanzu bata da ƙarfin qiwar ci-gaba da riƙe hakan, raunatacciyar zuciyarta ta kasa riƙe kanta da cigaba da iya ajiye sirrin da yafi ƙarfin ta, an jima ana ruwa ƙasa na shanyewa, kamar yadda ta jima tana ajiye surruka da yawa, amma duk yadda takai da riƙe zurfin cikinta a yanzu bata da kuzari balle ta hub’ɓasa riƙe hakan.
“I love my husband Khalil! Irin son da ba zan iya furtawa ko gamsar da wanda yake tsagina, ji, ko saurarena ba, zuciyar dake son shi da gaskiya ita kaɗai tasan how much i love him” Ta goge idanunta tana riƙe yanayin da take ji da dukkan kuzarinta da ajin da take da shi, cikin nuna jarumta ta ce “Ina raye, ina numfashi kamar kowa, ina gani,ina ji, amma gani nake tamkar matacciyya ce ni a rami, haske nake ciki amma duhun zuciyata nuna mini yake kamar dare biyu ake!. Ban san cewa akwai wani abu da ake halitta a jikin rayayye ba, sai da na fahimci bayanni akwai halitta a jikina ZUCIYA, Na rasa sukuni na rasa meke mini daɗi a duniyata, zurfin cikin da nake da shi ya sanya ba kowa ya fahimta ba, gabaɗaya zaton jama’a JINKIRIN AUREN dana samu shi ne raunin dake raunata jaririyar zuciyata; zato ne kawai kuma mara inganci, tsammanin so da ƙaunar Abraham ita ke damuna, na ji kunya i have been ashamed, idan na tuna ɗan dana raina shi zuciyata ke so! So ɗin ma na aure” Ta kasa ƙarasa maganar saboda nauyin da kalaman sukaiwa halattaccen harshenta sai ta yi shiru kawai tana rufe ido.
“Ɗan uwana General Alpha Bello khan! Shi ne mutum na farko daya fara so na a duniya, ni kuma Dr Ibrahimul-khalil Abraham shi ne first love ɗina daga nan duniya har lahira, an ce so makaho ne (Love is blind) amma bana gani saboda a kullum da Idanun zuciyata nake son shi, yaushe na fara jin haka mene dalilin har yanzu bani da cikakkiyar amsa ni da kai na, tunani fal ya yiwa ƙwaƙwalwata murfi, tun a baya na furta ƙaddarori ne suke zagaye dani, ɓoyayyun mane mana da rashin sanin wanda zai zama mijin malama ya sanya na rasa madafa, sai dai komai na da farko yana da ƙarshe, kamar yadda tayi silar rusa farin cikina haka tayi silar haɗani da abokin rayuwa,iya hakan kaɗai zai iya sawa na yafe mata zunubanta idan ina da tabbacin tuban da zata yi” Khalil na tsaye kamar an dasa shi, kalaman Majeederh sun ɗaure masa jijiyoyin jikinsa, suna neman kassara masa zuciya, ya rasa kuma a wanne bigire ko tubalin zai ajiye wannan zancen nata mai shirin tarwatsa masa zuciya? A hankali ya sake duban lokacin yaga yaci ace suna airport yanzu gashi already John ya shige da su Alhassan, jin ƙafafuwansa na neman kasa ɗaukan gangar jikinsa ya sanya ya jingina da bangon wajen yana mai zuba mata narkakkun idanunsa masu cike da wasu kalar zantuka wanda baki ba zai iya furtawa ba, sai dai gangar jiki tayi aikinta wajen nuna zahirin abinda zuciya ke ciki.
Mutumin ɗazu ya sake kallon Majeederh cikin yanayi na damuwa a hankali ya ce “Na yi sake, ɗan zaki ya girma why? Me ya sa kayi mini shigar sauri haka Khalil? Kasan yadda nake son matarka kuwa? Me ya sa tawa ƙaddarar da zuciyar ta rasa wacce zata so ko ƙauna sai MATAR AURE? Matar Auren ma da nasan Khalil ba zai taɓa sacrifice a kanta ba?” Ya riƙe kansa da hannu bibbiyu saboda juya masa da yakeyi a zaune yake ji yake kamar zai kifa saboda masifaffan tashin hankalin da yake ciki, zufa ta shiga yanko masa a fili ya sake furta “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ubangiji idan Majeederh alheri ce ka gaggauta kashe aurenta da mijinta na aureta, i don’t care da shekarunta, Ya Allah; soyayya da matar aure? Matar Dr Ibrahimul-khalil Abraham? Anya alƙiyamarsa bata kusa tsayawa ba?” Duk ya firgice ya fita hayyacinsa he looks so old amma ba mai lura da hakan saboda wani irin arziƙi da kwarjini, ya zaro hanky ya dinga share zufar dake tsastsafowa daga goshinsa tana sauka a fuskar shi. Jajere ta kalli Majeederh ta ce
“Mun sha ganin mutane ko nace mata da dama, wanda suke ganin kuskure ne ko rashin dacewar ko zubar da aji ne ka auri wanda ka girma, musamman irin tazarar girman naku ke da Dr Ibrahimul-khalil Abraham, ke ya kika ji kuma ya kika ɗauki abun? Ya surutun jama’a ya yi tasiri a zuciyarki?” Majeederh ta yi murmushi cikin tattausan harshe da kalami mai daɗi ta ce “Tunani akan cewa zaka burge mutane, wannan abu ne da ba zai taɓa yiyuwa ba, ko da ace rayuwarka zaka bada a kan su; ko da ace gaskiyarka zata fasa ƙirjinka ta fito,sam sam ba zasu yabeka ba, yafi maka ka saurari zuciyarka a kullum, mutanen da suke kewaye da kai sune suke sare maka quiwa a yayin da kaso aikata wani abu,sai kayi nasara a rayuwa sannan kowa ke son ƙulla alaƙa da kai, babu haramci akan auren wanda ka girma idan zai girmama ra’ayinka, ku girmama na juna, yana da wadata, da zuciyar nema, yana da kyakkyawar mu’amala abinda ake buƙata kawai nagarta da cancanta, idan gaskiya zaka faɗa, duk gaskiyarka ba zaka kai Sayyiduna Abubakar ba, duk ƙaryarka ba zaka kai Musailabatul kazzabu ba, munafurci sai Abdullahi ɗan Ubayyu ɗan salo, ƙarfi sai adawa girman jiki sai samudawa, muni sai Julaibibi, matar da akafi so a duniya ba kamar Nana A’isha matar Annabi Muhammad S.A.W, ƴar da akafi so a duniya babu kamar Nana Faɗimatu, Mulki sai Annabi Sulaimanu, kuɗi sai ƙaruna, talauci sai Mus’ab ibn Umairu shi ne wanda ya mutu likkafani bai ishe shi ba, idan taurin kai mutum yake ji da shi akwai su Ƙuddaru, duk iskancin da mutum zaiyi a duniya ba zai kai Hamana ba, a fito na fito da Allah sai shaiɗan, shi daman ba mutumci ne da shi ba, ya ce tunda aka fifita shi akan ɗan adam tabbas sai ya halakar da rabin su, Ubangiji kasa mu dace muyi kyakkyawar ƙarshe” Gabaɗaya suka amsa da amin. Kowa jikinsa ya yi sanyi Khalil dai wani irin nutsuwa yake ji idan ya kalli Majeederh kuma ya tuna matarsa ce sai yaga bashi da wani sauran buri a duniya. Ta gyara zama a hankali ta ce “To kuma duka wannan sai mutum ya tsaya girman kai don wanda zaka aura ko yake sonka yana ƙasa da shekarunka? Idan zanen ƙaddararku iri ɗaya ne fa? Idan iya rubutu ne ba kamar Annabi Isa, abi Annabi sau da ƙafa sai su Sayyiduna Abubakar Saddiƙu, a bada rayuwa saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama sai Umar Farouk, a yin kyauta sai Sayyiduna Usman Zannur, ayin aike a isarwa da Annabi saƙon shi sai Gadanga ƙusar yaƙi Sayyiduna Aliyu, to da yawan mutane suna take abinda yake farilla suna mai da shi sunna, sunnar ma wasu take ta suke, ban wani ji abu mai kama da damuwa ba saboda babu wani challenges dana samu game da hakan” Gabaɗaya suka jinjina kai cike da gamsuwa.
“Before you pray, believe, before you speak, listen, before you spend, Earn, before you write think, before you Quite try, and before you die live, Assalamu alaikum” Daga nan program ya ƙare sukai sallama Majeederh ta miƙe tana sauke niƙab ɗin fuskarta hankalinta yana kan Khalil, sam bata lura da wanda yake zaune ya zuba mata idanu kamar ya cinyeta ba, tana zuwa ta kama hannun Khalil ta ce “Afuwan Ranka ya daɗe tuba nake” Ya kasa ce mata komai sai hannunta daya kama suka nufi waje, mota ya buɗe mata ta shiga shi dai kallonta yake ita kuma ta kasa haɗa Idanu da shi saboda kunya ya nufi wajen driver ya shiga ya jima zaune ya sake juyawa tayi saurin ɗauke kai sai kawai ya girgiza nasa kan murmushi yayi a taushashe ya nufi Lafiya Round a hanya ya kira John ya ce ya kawo masa su Alhassan sun riga da sun yi missing flight ɗin sai gobe. Majeederh ta riga sauka tana shiga Main parlour taci karo da Alhassan ya yi mata kaca kaca da milk cake a saman carpet cikin faɗa ta ce “Alhassan” A gigice ta miƙe tsaye jikinsa na rawa kansa a ƙasa ta nufe shi kafin ta ƙarasa tuni ya kwasa da gudu tana cewa “Stop, stop dear” Ina ya kama makaken windown ya dire zuwa bayan garden ta dafe kai a ranta tana jin yaya za ta yi da Alhassan yanzu? Gabaɗaya halin babansa ya ɗauka ya kwashe shi tas ta juya tun kafin su haɗa ido Khalil ya yi saurin haurawa upstairs yana shafa kai, shi da kansa ya san idan halinsa Alhassan ya ɗauka to wallahi za a sha fama, ta girgiza kai ta nufi part ɗinta wanka tayi tare da sallah ta nufi kitchen domin fara tunanin abinda zata haɗa na buɗe baki. Khalil na zaune a parlourn shi wajen dab da magariba sau uku yana zuwa bedroom ɗin Majeederh sai ta gudu shi sam ya rasa dalilin hakan sai kawai ya barta, a hankali ya jinjina kansa yana sauraren John dake cewa “Mun ware adadin mutanen da za a bawa zakkar, mun ware adadin mutanen da za a bawa kayan abincin, bayan marayun da muke da su…,” Kallon da Khalil ya yi wa John ya sanya ya yi shiru a hankali ya ce “how many times zance ba marayu bane?” John ya shafa kansa ya ce “Tuba nake, kai ne uwa kai ne uba” Khalil ya kame fuska John ya ɗora da “Suma an ware musu kayan sallar su, abincin azumi, dana sallah, Gidan Uncle’s ɗin Malama da gidan Abbu duka an kai musu kayan azumi” Khalil ya lumshe idanunsa ya buɗe calmly ya ce “Batun zakka, babu buƙatar ƙarawa mai ƙarfi, ƙarfi ok” John ya ce “In sha Allah, daman wasu masu kuɗin ke yin haka, ba za a bawa talaka zakka ba sai mai kuɗi” Khalil ya jinjina kai, John ya miƙe ya ce “Zan shige, sai goben” A taushashe ya ce “Abinci?” John ya zare Idanu ya ce “Rufa mini asiri da matata, azumin farko naci abincin a wani wajen ba wajenta ba? A’a zan shige yanzu kawai” Yana faɗin hakan ya ɗauki wayarsa da komai nasa, Khalil ya shafa kai ya miƙe gabaɗaya bashi da wani ƙwari a hankali suka sakko downstairs shi da John ɗin lokacin Jee ta gama komai tana tsaye gaban plasma tana jona bonner Alhassan yana leƙawa yaga me take domin ya haddace, ta yi wanka ta shirya cikin wata abaya lemon green ta mata kyau sosai fuskarta ta ɗan faɗa, Khalil ya yi kicin kicin da rai saboda kishi musamman da yaga tana murmushi mai taushi, john ya ce “Malama zan wuce sai goben” Majeederhn tayi jim sai kuma ta ce “Ba zaka yi buɗe baki ba a nan?” Ya girgiza kai ya ce “Idan kin sallama Dr ya biyoni muyi a wajen Faɗimatu?” Majeederh ta zare ido bata ce komai ba, shi kuma ya yi gaba yana ɗagawa Alhassan hannu, yana barin wajen Khalil ya nufi inda take kafin ya ƙarasa tayi saurin shigewa part ɗinta daidai nan kuma kiraye kiraye ya fara tashi a masallatai, hankulan jama’a ya koma yadda za a jiƙa maƙoshi ya juya ya nufi part ɗinsa, wanka ya yi da alwala ya sanya tattausan voyel ɗin jallabiya ya zama irin baƙin Balaraben yana sakkowa yaga biyuni da yayansu Baby Khalil gabaɗaya cikin jallabiya ya kama hannun Baby Khalil ya ɗauki Al’hussain ai kuwa Alhassan ya saka ihu saboda kishi ne dashi bisa dole ya ajiye Al’hussain ya ɗauki Alhassan suka nufi masjid, Majeederh sallah ta yi itama ta shirya musu abinci a dining room tana Ajiye mug ɗin coffee ta ji an rungumeta ta baya a hankali ya kwantar da kansa a wuyanta, cikin sabon sonta da yake fisgarsa ya matseta a ƙirjinsa da kyau yana fesa mata iskar bakinsa a kunne a hankali ya ce “Guje gujen na mene?” Ya faɗa da ƙyar yana manna mata laɓɓansa masu sanyi, Jee ta yi shiru tana sauke numfashi ya sake matseta sosai yana jin kamar ya mayar da ita tsaginsa ya ce “Saboda kin tonawa kan ki asiri ke kika fara crushing nawa?” Ta yi saurin rufe ido abinda take ta gujewa kenan, ya yi murmushi yana jan kumatun ta ya ce “Shy Girl” Ya juya tare da nufar saman carpet ya zauna akan dadduma yana tanƙwashe ƙafafuwansa Jee ta ƙarasa inda yake zaune ta durƙusa ta ce “Ina yini?” Ya yi mata shiru sarai ya jita ta sake cewa “An sha ruwa lafiya?” Ya juya ya ce “Me?” Ta kasa Kallonsa ya miƙa mata hannu tayi sak sai kuma ta ɗora nata a kai sukai musabaha ya ce “Assalamu alaiki Uwar gidan Dr Khalil” Ta ɗan yi murmushi ta ce “Fatan kasha ruwa lafiya?” Ya matse hannun sai kuma ya ɗauki dabinon ajwa ya saka bakinsa ya sake d’akkowa ya saka mata, kusan a tare suka lumshe idanunsu saboda daɗi da garɗin haɗi zaƙin dabinon daya ratsa bakunannsu zuwa jijiyar dake bawa gangar jikin amsa kuuuwa da yanayin da take ciki, ta gyara zamanta Alhassan ya miƙawa Khalil hannu ya ce “Aby” Khalil ya hargitsa kai yana kama ɗan ƙaramin hannunsa sukai musabaha ya nuna Jee ya ce “Ka gaisa da matata Mimi” Alhassan ya miƙawa Majeederh hannu ya ce “Mimi” Ta kame kunnen shi ta ce “Wato kai dole ka nuna mini jinin Dr Ibrahim ne ko? A gado abinda ka manta ne kawai baka ɗauke ba? Allah duk sanda ka sake haura katanga kamar ɓarawo jikinka ne zai faɗa maka fitinanne kawai” Alhassan kallonta kawai yake, ta juya kan Al’hussain ta ce “Kai kuma sarkin haƙuri wannan haƙurin zai maka illa watarana” Ta kalli Baby Khalil ta ce “Kai kuma kana babba idan sun yi laifi baka san ka make su ba ko? Maza su rainaka kaga yadda zanyi da kai” Tana faɗin hakan tayi shiru ta fara haɗa musu tea ta bawa kowa bata sakawa Baby Khalil suger sosai ba, tana bawa Alhassan ya yi cilli da cup ɗin ya daki center table, tea ɗin ya zube cup ɗin ya fashe, Khalil ya yi saurin ƙasa da kansa domin gani yake kamar vedion ƙuruciyar shi ake nuna masa, Majeederh ta juya ta kalli mijin nata ya haɗe rai sai kawai ta fashe da kuka Khalil ya zare idanu ya kalli Baby Khalil ya ce “Friend kama abokan ka kuje part ɗinku now” Ya miƙe ya kama hannun Al’hussain, Alhassan yaƙi tafiya Khalil ya daka masa wata gigitacciyar tsawa tuni yabi bayansu, suna barin wajen Khalil ya zare jallabiyar jikinsa ya rage daga shi sai trouser faffaɗan ƙirjinsa a buɗe, ya zare abayar jikinta ya fizgota yana rungumeta a hankali a kunnenta ya ce “Kin zauna kina yiwa yarana faɗa tas, ban ce komai ba shi ne kuma zakiyi kuka?” Ya shiga zagaye lip’s ɗinta da yatsar shi tayi saurin cewa “Amma wannan gadon da ya yi na zuciya ba zan iya da shi ba” Ya tari numfashinta da cewa “Ya kike da ubansa?” Ta yi shiru ai kuwa ya bi ya danneta da ƙirjinsa ya saka hannu tare da ɓalle net ɗin bra ɗinta ya ce “Kukan shagwaɓa kike, bari gwarzon mijinki Dr Ibrahim ya saki me dalili….
[