Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 49

Sponsored Links

Aisha Baby Novel: Wani tattausan murmushi ya yi mata yana ɗan ware idanunsa kaɗan, a hankali Majeederh ta mayar masa da martanin murmushin da ya yi mata ba tare da sani ko tsammanin hakan ba, ya zame idanunsa ya juya yana kallon wanda ke taɓa shi yana masa magana a hankali. Majeederh ta gyara nutsuwarta idanunta a ɗan lumshe bayan daidaita numfashinta da kuma sanin cewa camera ce a kanta ta numfasa tare da cewa“Ƙaddara! Idan na ce ƙaddara; ina nufin wani abu da Ubangiji ke jarabtar bawansa mumini da shi, ko da hakan ya kasance wani ne silar faruwar ƙaddarar ta mutum. Komai ya faru da mutum a rayuwa nufin Allah ne da kuma sahalewar shi, no matter what happens to you, you can’t run from your destiny, ba ko wacce zuciya ce ke iya jure jarabawar Ubangiji dangane da rayuwa ba, mafi kyakkyawar zuciya da tsaftata ita ke yarda ba mutum ne ya ɗora mata abinda ya faru da ita ba, Ubangiji ne!. Gabaɗaya muna rayuwa da ƙaddarorinmu ne, inma muyi nasara akan su, inma suyi akanmu, cimma nasara a rayuwar waninka ta hanyar ganin bayansa wannan zato ne irin na masu ɓauɗaɗɗiyar zuciya, cimma nasara da yaƙini ga cigabanka na rayuwarka mai zuwa shi ne matakin farko na zama nagartacce da gina rayuwa ta gobe”
Majeederh tayi shiru saboda yadda zuciyarta ke rawa da gaske, bawai tsoran camera ɗin take ba, yadda duk ɗago fararen Idanunta da zata yi sai taga narkakkun idanunsa kwance a fuskarta, fuskarsa ɗauke da wani irin shu’umin murmushi mai kwantar da zafin zuciyar ko wacce ƴa mace, ta ja numfashi ta sauke tana mai janye idanunta daga gare shi, she wonder why he keep his eyes on her? Ta riƙe kanta da kyau tana buɗe hannayenta tare da ɗan jingina da chair ɗin da ke juyawa da ita ta ce “Destiny!”
Ta ɗora da “destiny, fate, and lot mean a future that someone or something will have. destiny and fate both suggest that the future has been decided or planned by God. destiny often suggests a future that includes something great and important, Destiny ita ke jan mutum zuwa ga victory ɗinka na abinda kake son Achieving a rayuwa!” Halima Ben Umar ta ce “Haka ne, victory nasara kenan shi ke kawo Achieving na goals long term and short terms, kuma shi ke jan ragamar rayuwa, amma Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Me ya sa aminiyarta ta kasance mutum na farko wajen wargaza rayuwarki? Menene ya ja hakan?” Kai tsaye Majeederh ta ce “Soyayya! Love is our true destiny. We do not find the meaning of life by ourselves alone, daban nuna mata so ba, da bata tsaya a gefena ba, da ban nuna mata so ba wata ƙila da abinda ya faru dani bai kasance hakan ba, da ban nuna mata so ba da ban kasance da mijina wanda ya zama silar wanke damuwa da raɗaɗin da zuciyata take ba, da ban nuna mata so ba wakila da Dr Ibrahim-Khalil bai zama mijin malama ba, da ban nuna mata so ba watakila da ban san wacece ita ɗin ba, da ban nuna mata so ba da wala’alla ban haɗu da dangin mahaifiyata ba, da ban nuna mata so ba babu shakka da ilimin da nake da shi a yanzu tarihi zai zama…,” Hawayen daya fara taruwa a Idanunta ne ya sanya ta yi shiru tana haɗiye abinda take ji akan Latifa, bata son rauninta ya bayyana, amma Latifa ta riga data kassara rayuwarta, ta mata tabo, irin tabon da ba zai taɓa gogewa ba, tabon da aka zana shi da baƙin fenti maimakon baƙar tawada.
“Sorry Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, idan kina kuka duka zaki samu hawayen muna son muyi learning daga cikin ƙaddarorinki” cewar Hafsat A.b Hamza. Majeederh ta yi murmushi kawai tana sauke numfashi juya idanunta ta yi ko zata hangi Khalil ta samu ƙarfin quiwa amma ko inuwar shi babu, ta yi ƙasa da kanta hannunta riƙe da tissue ta ce
“Tun bayan faruwar abun ban taɓa magana da kowa akan abinda Latifa tayi mini ba, even my husband Khalil, ban taɓa baƙin ciki a rayuwa irin baƙin cikin da na ji a sanda gaskiya tayi halinta ƙarya ta ƙare ba, fitila ta haska mini aminiyar dana yarda da ita,ita ce responsible na abinda ya faru dani, ta wargaza mini rayuwa, ban taɓa yarda ko gasgata Aminiya na baƙin ciki da samun aminiyarta ba sai yanzu, I have been ashamed! Ni da kaina ina jin kunya na buɗe baki nace wacce nayi trusting ɗinta ɗari bisa ɗari ita tayi mini haka, and do you know what?” Ta share hawayenta ta ce “Abu zai faru dani, kuma she’s the first person da zan faɗawa ta bani shawara ashe duk kashe kaina nakeyi, sai yanzu nake tuna me ya sa ta ce na gudu na bar gidan mahaifina? Meyasa a lokacin baya ta saka na shafe fuskata da baƙi da sunan wai ko maza za suga kyauna? Amsa! Bata ƙaunar mu jera fuskata a buɗe gani take kamar ina disashe tauraronta ne, ta durƙusa akan ƙafafuwanta tana kuka, “wai na auri mijinta bata son ganina haka ashe she was just pretending! Babu hakan a zuciyarta, ban san adadin shekarun dana ɗauka tare da asirinta a jikina ba, ta sanya na zama mujiya a idanun maza, basa ganin kyauna basa ganin nagartata, ina zama wata kala a idanunsa, suna shakkar tunkarata da sunan soyayya, wanda hakan ya ja mini JINKIRIN AURE, nayi shekaru 35 a gaban iyayena cike da tashin hankali da damuwa, na sha suruta daga wajen ƴan uwana, mutanen unguwa da jama’ar gari, ana ce mini karuwa, ana cewa mai kuɗi nake so, ana cewa neman maza nake so shi yasa bana son aure…,” Daidai nan ta fashe da wani irin raunataccen kuka tayi saurin rufe fuskarta da tafin hannunta, wani irin kuka take mai ban tausayi kai kace yanzu ne komai ke faruwa,People’s bad comments about her in the past had an effect on her heart. Hafsat A.b Hamza da Fatima Jajere tuni suka fara kuka saboda akwai abin tausayi a labarin Majeederh, an kassara rayuwarta tako wanne ɓangaren wanda kuma ƘAWA ce silar komai. kuka tayi sosai wanda ya ja musu yanke recordings for some minutes domin samun nutsuwar zuciya.

A hankali ya miƙe cike da nutsuwa yana gyara zaman sunglasses ɗin fuskarsa, yadda fuskarsa tayi jajur zaka san kukan da Majeederh take ya taɓa zuciyarsa da gaske, ba zai iya jurewa ba domin yana gab da samun matsala a kamalance ya fice ta ƙofar baya daidai nan kuma ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious ya karaɗe wajen hakan ya sanya director da camera man ɗin da suke kusa ɗago kansu zuwa gare shi, if they are not mistaken wannan shi ne mijin Malama, the ex-president son, jikan masarautar Saudiyya hamshaƙin ɓoyayyiyar mai arziƙin nan na ban mamaki, mamallakin kamfanoni kala-kala, uban marayu wanda ba a san adadinsu ba, Dr Ibrahimul-khalil Abraham Kspider, Mijin Malama. Khalil ya haɗe fuska sosai domin baya ɗaukan raini, sai kame kansa yake kallo ɗaya kuma a tsanake zaka yi masa ka gano ƙwayar idanunsa da take iri ɗaya data Majeederh, Khalil hannunsa zube cikin Aljihu ya yi wani irin sahihin kyau mai fusgar hankali musamman yadda yake lullumshe Idanu, ya juya kaɗan idanunsa ya sauka akanta ta kifa kanta a saman armchair tana kuka a hankali Silently, shi bai sam bai son loosing control ɗinsa akanta wajen wanda bai ma san miye so ba, balle damuwa da su, ya jima da sani kuma da fahimtar cewa ita ɗin dai, ita ce Rauninsa (His Weakness). Ba sauri yake ba yanayin yadda jikinsa ke motsawa so romantic and sexy zaka ɗauka sassarfa yake idanunsa buɗe amma kamar a rufe suke yadda yake lumshe su, ba zai iya cewa ga wanda suke wajen ba idanunsa Majeederhn kawai suke gane masa, bata yi aune ba ita dai ganinta tayi tsaye gaban mutum hannunsa ɗaya zube a bayanta ɗayan kuma ya ɗora a kafaɗarta yana zubawa fuskarta wani irin kallon na mai kama da tuhuma, ta kasa ci-gaba da kallonsa saboda idanunsa da sukai mata kaifi da gaske ɗin har lokacin kuma hawaye na bin fuskarta ta sake ɗago idanunta taga bai motsa ba ko ƙifta idanunsa bai ba ita kawai yake kallon bakinta na rawa ta ce “Ma…ma..” ta kasa furta komai saboda yadda taga ya buɗe mata Idanu sai kuma ya ɗan matse kafaɗarta irin “Speak up” ɗin ganin tayi shiru ya sa ya damƙi hannunta tare da fara tafiya da ita zasu bar daƙin da ake recordings shirin na Mata a yau.
“Man please” A taushashe ya furta “Uhm” ta riƙe hannunsa ta ce “Calm down dear” Rinannun idanunsa ya buɗe mata sosai ba tare daya furta komai ba ta kwantar da murya ta ce “Why are you here?” Ya ɗan saketa yana girgiza kai da hannu ya nuna mata kanta sannan ya nuna mata idanun dake fita daga cikinsu a taushashe kamar zai mai raɗa ya ce “muje” ta ce “Bamu gama ba” Ya zare mata Idanu ya ce “Ba buƙata” Baki ta buɗe za tayi magana ya yi saurin cewa “Hawwa’u!” Ta kalle shi a gigice tsoro ya mamaye zuciyarta bata san cewa tana jin shakkar Khalil ba sai yanzu, idanunta ya sake ciko da hawaye wanda kuma shi ne baya so harga Allah, Hafsat A.b Hamza ta ce “Sorry for the interference” Ko inuwarta Khalil bai kalla ba ya riƙe hannun Jee zasu bar wajen Hafsat ta ce “Matarka abar so ce, banga laifinka ba Dr Ibrahimul-khalil, amma zan so kayi mana afuwa zuwa sanda zamu ƙarasa wannan program ɗin please, mutane da yawa suna jiran irin wannan ranar don Allah don Annabi albarkacin azumin dake bakinka” Khalil har lokacin bai kalli Hafsat ba, idanunsa akan Majeederh ya durƙusa daidai kunnenta yana warming bayanta kamar zai rungumeta ya ce “Kome zakiyj, ki tuna” Tayi saurin kallonsa a taƙaice ya ce “Ki tuna, I love you!”
Yana faɗin hakan ya fice daga cikin wajen, Majeederh ta ji kamar ta bisa ta ji dalilin wannan fushin nasa? Bata da wani option wanda ya shige ƙarasa program ɗin, ta koma ta zauna zuciyarta ta kasa nutsuwa a wajen, ta kalli Jajere jin tambayar da tayi mata ta ce “Mutanen da muka yarda dasu harlau sune suke son ganin bayanmu, as i was saying ƙaddara ita tayi tasiri a rayuwata, bisa gudunmawar ƙawa da matar wan babana, bana da masaniyar cikin dana samu wanda jama’a suka dinga Allah wadai dani, amma a yanzu abu ɗaya zan faɗa muku wannan cikin ɗan da aka haifa ƙanin Latifa ne, mahaifinta shi ne uban baby khalil, ina lalube cikin duhu ina ganin ɗan uwana ya guje ni ranar aurenmu ashe shima ƙaddara ce ta faɗa masa, saboda kawai ba a son ganin farin cikina, he left me sanda nake tsananin buƙatar shi, ina da tarin masoya a ɓoye ba tare da na san waye zai zama Mijin Malama ba, JINKIRIN AUREN dana samu shi ne ya zame mini sanadin haɗuwa da inuwata, kuma na yarda wani jinkirin alheri ne,In addition, you can’t run faster than your shadow, slowly but surely” Ta riƙe hawayen idanunta da kyau ta ce “Na yarda ɗan uwana ba rabona bane, bayan wannan ƙaddarar mahaifina ya tsine mini yana ganin tamkar ina sane nayi cikin shege nake playing game a gidansa, abin mamaki ina haihuwa manema suka fito kala daban daban, a ciki hadda mijina a yanzu na auri Abuturab ina tunanin na samu inuwar da zan raɓa na samu nutsuwa ashe kura ce da fatar akuya, ba zance ga farin cikin dana samu a gidansa ba ko sau ɗaya, abu ɗaya na sani taimakon da ya yi mini, At his house, I was diagnosed with depression, na kamu da depression hakan yasa na kasa bacci a ko wanni dare tsinuwar mahaifina ke amsawa a kunnena, ya d’aureni yana bani maganin bacci saboda ciwon kan da nake, he turned me to a drunkard…,” Wani irin rikitaccen kuka ta fashe dashi wanda ya sanya Halima Ben Umar ta toshe bakinta saboda kukan da yazo mata, wanne irin hali mata suke ciki ne? Wacce kalar ƙaddara ce wannan irin ta Majeederh? Ta jima tana kuka kafin ta ce “Naga rayuwa amma yanzu Allhamdulillah! Ya zama tarihi” Halima Ben Umar ta ce “Ya akai mijinki ya amsheki a yadda kike?”
“He believed in destiny, Mijina; daban yake” Majeederh ta bata amsa a taƙaice, Halima Ben Umar ta ce “Mene alfanun auren wanda kika girma? Kuma tayaya kike iya yi masa biyayya duba da cewa tazarar da kika basa mai yawa ce?”
A duka tarin tambayoyin wannan ita ce tambaya mafi tsauri da Majeederh zata amsa, ta yi murmushi sosai ta ce “Me? Na yi girman kai wajen biyayya ga samun aljanata? bari na faɗa muku abinda ko shi mijina bai sani ba, wanda kuma personal issues na rayuwata amma yau zan buɗawa duniya gaskiyar lamarin” Daidai nan Khalil ya sake shigowa domin shi gaggawa ce da shi, shigowar shi ba daɗewa mutumin ɗazu ya shigo majeederh tayi tattausan murmushi ta ce “Wallahi wallahi wallahi, tun kafin Dr ya ce yana so na, nake son shi, so mai yawa son da bana iya bacci a lokacin ma bai san waye shi ba saboda ƙarancin shekaru ina son Khalil tun kafin na aure shi ina son Khalil tun yana bad boy ban tabbatar da ina son shi ba sai ranar daya dawo gareni a cikin B.u.k ranar taron da mukai a hall a gaban kowa….
[

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button