Mijin Malama Book 2 Page 50
Aisha Baby Novel: Khalil ya sake rungume Gimbiya yana jin kamar ya shige cikinta ya huta wani irin kewarta ta saukar masa tare da mamaye jikinsa, ƙofofin zuciyarsa suka bubbuɗe da soyayyar Ummien nasa, idanunsa sun yi jajur saboda yadda a karo na farko tun bayan sanin wace mahaifiyarsa ya ji tana kuka, a hankali hawayenta masu zafi suke sauka a bayansa wajen wuyansa, ta ƙanƙame shi da kyau kamar zata sake yin cikinsa ta haife shi, a hankali a kuma nutse tana babbuga bayansa tana shafawa saboda jin yadda yake sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri, wata na korar wata.
“Ummieeeyyy” Iya abinda bakinsa ya furta kenan, saboda bashi da ƙarfin zuciyar da zai faɗi abinda yake saman harshensa a yanzu, ya sake rungumeta, wata gamsasshiyyar nutsuwa na sauka a jikinsa, sai yanzu ya ƙara tabbatar uwa, mahaifiya rahama ce, dole wanda ya rasa tashi ya zubar da hawaye.
“Ibrahim? Khalil yarona”
Gimbiya ta furta a kamalance tana jin dukkan wata damuwar zuciyarta na shekara wajen uku ta yaye nan take, zuciyar ta wanke tare da yin fari daga duhun damuwar da Mr President ya sanyata “Kana raye? Zan sake ganinka?” Yadda take maganar da ƙyar zaka san cewa ba ƙaramin ƙarfin hali tayi ba wajen furta kalaman, Khalil ya ɗago a hankali ya zubawa mahaifiyar tasa ido, shi mamaki yake wai ita ta haife shi? Ya ɗan yi Miskilin murmushi kafin ya ce “Allah bai ɗauki raina ba, ina tare dake, zan ji daɗin uwa Ummie” Sharr! Wasu hawayen suka sake sakko mata a hankali tayi murmushi mai laushi ta ce “Ya Allah!” Ta kama hannunsa tana tattaɓa shi ya riƙe hannunta ya ce “The real Ibrahimul-khalil is back, your son ɗanki ya dawo” Da sauri ta sake jawo shi ta rungume a wannan sa’ilin kasa riƙe kukan ta yi, ta sake shi bisa umarnin zuciya. Majeederh dake tsaye ta yi ƙasa da idanunta hawaye na zuba a cikin idanunta, lallai uwa! Daban take a cikin rayuwar yaranta, yadda Khalil ya narke jikin Ummie kaɗai ya isa ya fahimtar da ita yadda ya yi kewar mahaifiyarsa, ta rufe ido tana jin soyayyar mahaifiyarta fulani na ƙara sauka a zuciyarta ko wanne motsi tayi sai ta tuna da ita, bata san soyayyar uwa ba, babu rabon kuma zata samu ɗin Ubangiji ya fita sonta tunda ya ɗauke ranta ya barsu. Jin an kira sunanta a taushashe ya sanya ta ɗaga kanta Gimbiya ta gani riƙe da hannun Khalil tana kallonta alamar ita ke kiran nata, ta nufeta jiki a sanyaye da sauri twins da Yaa K suka mara mata baya, tana zuwa Gimbiya ta ce “ke fa ba Daughter-in-law ba ce, you’re my daughter ko baki auri Khalil ba” Kunya ta kama Majeederhn ta sunkuyar da kanta Khalil ya ɗan shafa kansa speaking calmly a taushashe ya ce “Ummie ki rungumeta itama” Gimbiya ta kalli Khalil sai kuma ta ɗauke ido ta ce “Come closer dear” Ta haɗa su ta rungume a jikinta tana rufe ido a ranta ta ce “Alhamdulillah!”
“Brother” Clara kuma Fatymerh ta kira Khalil tana murmushinta irin na Ummie, Khalil ya kalleta sosai suke kama da ita bambancin kawai ita fara ce komai nasu iri ɗaya ne, nata zubin halittar na mace ne, shi kuma nasa namiji. Ta sake murmushi ta ce “Ko na ce Biyunina” Ya ɗaga mata gira da dukan kafaɗarta sai kuma yi yi mata rungumar gefe (Side hug) Kamar an masa dole ya ce “Sweetheart” Fatymerh ta yi murmushi ta ce “You’re welcome Kspider” Ya lumshe idanu ya buɗe, ya kalli Zizi da Badi da suke ta kallonsa jikinsu duka a sanyaye sai ya miƙa musu hannu da gudu suka rungume shi suna cewa “We miss you alot Kspider, Welcome back to the kingdom, among your relatives and parents” Khalil ya yi guntun murmushi iya laɓɓansa kafin ya juya ya kalli Majeederh yaga harta shige motar da Ummie take, ya tsaya cak da mamaki domin basu saba haka ba Ummie ta kalle shi sai kuma ta ce “Me?” Ya ɗan yatsuna fuska ya juya zuwa motar da Fatymerh Clara ke ciki, ya tarar su Al’hussain na ciki ya kwanta a bayan motar yana lumshe idanunsa zuciyarsa na bubbuɗewa na fargabar abinda ya aikatawa Jee har ta raba mota da shi, har suka isa cikin Palace idanunsa rufe ko tari bai yi ba, yana jin wata sarewar Algaita na tashi mai sanyi da daɗin saurara sounds ɗin na musamman kamar yadda ko wacce masarauta kalar Algaita ɗinta daban yake, wanda Sarkin Busa ke yi ya gada kuma wajen iyaye da kakanni, Khalil ya tsani duka irin wannan shi kaɗai sai siririn tsaki yake jaa. Majeederh na fitowa daga motar ta bi masarautar da kallo wata kamala, nutsu izza da isa irin ta masu jinin sarauta na game jinin jikinta, a ranta tana yiwa Ubangiji kirari rashin sani ya fi dare duhu sau biyu tana zuwa cikin Palace ɗin nan ba tare da sanin cewa gidan grandparents ɗinta bane, ashe duk wata soyayya da Ƙhulud Arzaan ke nuna mata jininsu ɗaya,ita ɗin ƴar uwarta ce, Lillahi wahidur Qahhar, buwayi gagara misali banda Al’hakkamu waye zai yi wannan? Ta goge hawayen dake bin idanunta, yadda take tunani haka Khalil ke yin nasa shi da keɓantacciyar zuciyarsa, ya karɓi Musulunci wajen Uncle ɗinsa, ya kalli Mahaifiyarsa ba tare da sanin matsayinta a wajensa ba, ya zauna cikin danginsa ba tare da saninsu da nasa ba, komai yana zuwa bisa tsarin Ubangiji da kuma yadda yaso. Ya lula duniyar tunani ya ji an rungume shi ta gaba data baya ya buɗe idanu, Mai martaba Ajlaal Sultaan ya gani tsaye a gabansa ya rungume shi idanunsa na rinewa, Rohaan ya sake rungumesa ta baya, Zaytoon kasa magana tayi sai kuka data fashe da shi, Majeederh da Ƙhulud Arzaan suka rungume juna, farin cikin ganin Khalil da Ahalinsa ya wanke zuƙatan Granny da sauran, nan da nan aka fara shirya kayan buɗe baki na musamman ga baki na musamman wanda ba’a zaci zuwan nasu ba, musamman Dr Ibrahimul-khalil.
Har dare lokacin kiran Magriba a ƙasar Saudiyya Khalil bai sanya matarsa a idanunsa ba, sai yaran kawai yake gani hakan ya dame shi yana son ya ji wanne hali take ciki, gefe guda kuma ganin Ummie a parlour ya hana shi tambayar Majeederh, haka kurum Ubangiji ya sanya masa jin nauyi da shakkar Ummie ɗin hadda kunyarta. A hankali ta ajiye azkar ɗin hannunta ta kalle shi yana zaune saman dadduma ya ɗan kishingiɗe idanunsa rufe hannunsa ɗaya akan haɗaɗɗan kushin a lokacin sai ta gan shi bashi da maraba da Ajlal ta jima tana kallonsa kafin ta ɗan yi gyaran murya, Khalil ya buɗe gajiyayyun idanunsa tare da kallon Ummie a taƙaice ta ce “Idan kayi buɗe baki, sai ka zauna zaman jin mulki”
Ya zare idanu sosai ya ce “Mulki?” Ta haɗe rai ta ce “Eh, naga sarautar kake ji da ita yau” Ya ɗan kwaɓe mata fuska domin shi baya son wata sarauta bashi da wani zaɓi wanda ya shige hutawa, tunda ba gun aiki za shi ba, kuma ba zai iya zaman surutu da kowa ba da Jee na nan shi ne za su yi hira mai daɗi irin ta mata da miji. Ta kalle shi da kyau ta ce “Ibrahim” Ya kasa amsawa idanunsa dai na zube a kanta ta ce “Bakai kake da ikon zaɓar sarauta ba, sarauta ke zaɓar mutum kuma ta riga data shiga jikinka ta zame maka jinin jiki, either you like it or not, kai ɗin jinin sarauta ne kuma kana son ta” Ya girgiza kai kawai yana miƙewa tsaye tare da dawowa kusa da Ummie tareda juyawa gabaɗaya a taushashe kamar zai mata raɗa ya ce “Goodness, takura ce” bata ce masa komai ba,ya miƙe zuwa sashin da aka basu har ya shige ya dawo yana shafa kai, Ummie ta miƙe tana gyara zaman lafayar jikinta ta dube shi a tsanake ta ce “Lafiya?” Ya ce “Ummie irin takalmin Uncle Ajlaal” Ta ce “Ya yi me?” Ya kasa cewa komai ta ce “Kai kuma da baka son sarauta mene haɗinka da takalmin sarauta?” Ya juya da sauri yabar wajen, a tare Mai martaba Ajlaal Sultaan shi da Prince Rohaan suka fito suna tsaye hannunsu riƙe da Dabinon ajwa Khalil ya fito cikin wata kyakkyawar jallabiya mai zare shuɗi irin zanen jikin sarauta ne da ita, yadda yake a tsaye saman ƙafafuwansa zaka kula da yadda ya kerewa Mai martaba Ajlaal Sultaan a tsayi girma da faɗin jiki, Rohaan ya ce “Mijin Malama an fito?” Khalil bai ce komai ba, addu’ar daya koya wajen Majeederh yake nanatawa a ƙasan zuciyarsa a haka yana tsaye Alhassan da Al’hussain suka fito da Yaa K gabaɗaya jallabiya ce a jikinsu irin ta mahaifin su Khalil, Ajlaal da kansa ya ɗauki Alhassan Rohaan ya ɗauki Al’hussain Khalil ya kama hannun Babban ɗansa kuma takwaransa Ibrahim Khalil.
Majeederh na zaune a saman dining bayan ta gama zubawa kowa abinci dake daman ita tayi, Rohaan ya kalli plate ɗin Khalil lafiyayyen ƙosai ne wanda ya ji ƙwai da kayan ƙamshi, sai kuma kunun gyaɗa wanda ya ji madara sai nau’in kayan itatuwa ya ce “Ya mu duk kika zuba mana abinci shi kuma sai kayan ruwa?” A tare Ummie da Majeederh suka ce “Dare ne ai, sun masa nauyi” Roohan ya ce “Ya Allah ka aurar dani ka kawo wacce zata ce tana so na” A tare Zizi da Badi sukai dariya gabaɗaya sun yi zuru-zuru saboda basu taɓa zama da yunwa sai wannan shekarar ba. Ƙhulud na kallon yadda Khalil ke bin Majeederh da kallo yama kasa cin abincin ita kuma taƙi yarda ya sanya idanunsa a nata, Ƙhulud Arzaan ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce
“Na’am, Majeederh kike kira Granny?” Jee ta ɗago kanta ta kalli Ƙhulud Arzaan ta ce “Malama Majeederh Granny na kiranki fa, tun ɗazu maybe ba kiji bane” Majeederh ta miƙe daman ta gama abinda take Ƙhulud ta kalli Khalil tare da kashe masa ido ɗaya, ya shafa kai yana ɗaukan ragowar kunun gyaɗar da yake a cup ya miƙe tsaye hannunsa ɗaya zube cikin Aljihu Zizi ta ce “Baka gama cin abincin ba Kspider” Bai juya ba balle ya bata amsa, Ummie bata ce komai ba domin tasan me zai aikata,ta kalli Zoya da Zohal da twins ta ce “Kuzo muje, zaku harami?” Suka ɗaga mata kai da sauri ta kwashi yaran zuwa sashinta.
A hankali Majeederh ta shiga bedroom ɗin Zaytoon idanunta ya sauka akan Granny wacce take kwance saman bed ɗinta tana bacci dalilin maganin data sha, gyara mata kwanciya tayi tare da juyawa ta nufi waje a daidai wani corridor wanda aka kashe hasken wajen ta tsaya tana lalubar hanya, tana ƙoƙarin tafiya ta ji an rungumeta ta baya, ta sauke ajiyar zuciya gabanta na faɗuwa sosai ƙamshin turaren shi ya jima da bayyana mata waye, sun jima haka kafin ya juyo da ita gabansa bakinta na rawa ta ce “Ka sake ni?” Ya yi mata shiru sai sake matseta ya yi a ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali, ta fara kokawar kwacewa ya san kuma hakan na nufin ta yi fushi ne, ya ɗan kurɓi kunun hannunsa tare da ajiye cup ɗin saman window ya damƙo kanta yana haɗe fuskokinsu waje guda laɓɓansa a saman nata, Majeederh ta buɗe baki da niyyar yin magana ya yi saurin juye mata kunun bakinsa hakan ya haddasa mata yin shiru bisa dole ba dan tayi niyya ɗin ba, ya sunkuya tare da ɗaukanta ya bi ta can ƙofar baya ya nufi sashinsu da ita, idanunta rufe tana sake kwantar da kanta a lafiyayyen ƙirjinsa tare da shaƙar ƙamshin turaren shi na Boadicea The Victorious mai kwantar mata da zuciya,a nutse a hankali kuma ta buɗe maƙoshinta tare da shanye kunun ɗaya juyewa mata, har daɗi da garɗin gyaɗar suka mamaye bakinta.
Khalil na zuwa ya kwantar da ita saman gado ganin tana ƙoƙarin tashi ya bi bayanta ya danneta da ƙirjinsa tayi saurin rufe Idanu tana damƙe damtsen hannunsa muryarta na rawa saboda hancinsa da yake goga mata a dugan wuyanta ta ce “Ma…man cikina, our baby” Ya sassauta nauyinsa yana zame abayar jikinta hannunsa ɗaya ya sauka a kan mararta data fara girma sosai daga nan kuma ya fara shafa dugwayen ƙafafuwanta idanunta rufe jikinta ya fara ɗaukan rawa ta ce “Let go of me?”
“I won’t” Ya furta a taƙaice kafin ya mirgina gefe yana jawota ya ɗorata saman ƙirjinsa, hannayensa rungume da ƙugunta ta baya wanne ya haɗa da nasa ya manne waje guda, bakinsa a kunnenta yana fesa mata numfashi mai zafi ƙamshin kunun na fitowa saboda ko brush bai yi ba, bayanta yake shafawa a hankali har ya samu nasarar ɓalle rigar jikinta ta rage sai Inner wears, jikin Majeederh ya saki domin Khalil ya san duk abinda tafi ƙauna a nutse a taushashe kamar mai raɗa yana ƙasa da muryarsa ya ce “I’m sorry” Ta yi masa shiru ya sake cewa “please” Ta buɗe ido tana kallonsa kafin ta ce “Sorry for?”
“My mistake” Ya mirgina kai yana tallafo fuskarta ya ce “Na miki ihu gaban mutane, babban damuwata gaban yaranmu” Ta ɗan yi murmushi ta ce “It’s ok” Ya shagwaɓe mata fuska yana kwaikwayon muryarta ya ce “Kiyi haƙuri i won’t do it again, ina tsananin son ki kuma shi ne sanadi ALLAH YANA GANI, and ba laifi na bane”
“Laifi na ne kenan?”
Ta tambaye shi tana tsare shi da sexy eyes ɗinta wanda nan take suka sake sauyawa Khalil lissafi ya kasa furta komai sai lip’s ɗinta daya fara zagayewa da hannunsa ta ce “You don’t trust me, kana tunanin zan iya cin amanarka ne? Idan zan ci me ya sa lokacin da ake zaton ka mutum banci ba? Sai yanzu, da nake ganin ba zan iya rayuwa babu kai ba? Da nake ganin ka riga ka cike dukkan gurbin zuciyata da soyayyarka, da nake ganin ka zama silar yaye damuwata, sai yanzu da hankalinmu ya kwanta, babba abu kuma ina sonka amma shi ne zaka mini ihu a gaban mutane harda ma John?” Sai kawai ta fashe da kukan shagwaɓa tana buga ƙafa da yarfe hannu tare da girgiza jikinta, hakan yasa gabaɗaya na jikin nata motsawa Khalil ya ƙarasa susucewa ya rarumota ya rungumeta sosai yana sauke wani irin numfashi a kiɗime ya fara sauke mata wasu Single Lip Kiss, breathing ɗinsa na sauka a zafafe, so yake ya rarrasheta amma sam bai san ya zai yi ba, ita kanta Majeederh sai data tsorata, tun tana dauriya ta fara ture shi zufa ta wanke mata jiki a gigice a kuma wahale ta ce “Cikina, marata” Maimakon ya saketa tunda ya samu abinda yake so amma kamar ta ƙara masa ƙarfi ne ya sake mata Leave a Mark Kiss, yana ficewa daga hayyacinsa jikin Jee ya fara saki ta raina kanta yau asalin Dr Ibrahimul-khalil take gani, wasu irin hawayen so da ƙaunar mijinta suka dinga fita daga cikin idanunta, tasan baya hayyacinsa da tuni ya fahimci halin da take ciki kuma daman tarata ya yi ta wannan hanyar yake son rarrashinta can ƙasa ta ce “Ya Allah kada kasa Khalil ya yi sanadin fitar cikin nan” idanunta na rufe hannunta ya saki, gudun ruwan da Khalil ya ji a cinyoyinsa wanda suke fita da zafi ya dawo dashi cikin hayyacinsa, ya zame daga jikinta da ƙyar wani buɗe Idanu ya yi lokacin da idanunsa ya sauka akan bedsheet ɗin da cinyoyinta jini yake fita daga jikinta harda guda-guda a gigice cike da tsoro ya tallafota yana “I am sorry Sexy mama, na rasa tunanina” Da ƙyar ta ce “Ka kira Ummie karmu rasa babynmu khalil….,” Wani gudan jini ne ya sake fitowa wanda ya sanya Majeederh ƙanƙame Khalil jikinta na rawa.