Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 19

Sponsored Links

Arewabooks@NoorEemaan

Xix…
(19)

Numfashi ya sauke, tausayin Munaya na kara mamaye zuciyar sa, a Wani bangaren kuma damuwar halin da dan’uwan sa ke ciki ya dame shi, wayar sa ya janyo yana duba wasu mahimman sako, Sam baya son yin bacci, yana son ganin farkawar Maleek.

Related Articles

***
Mummy
_11:50pm_
Farinciki ya cika zuciyar ta, domin ta san a yau matsalar ta zai kau, zata kashe kishiyar ta na tsawon shekaru talatin da wani abu, ruwan jikin ta take tsanewa a hankali tana murmushi kana ta dauko dan karamin kwalba mai dauke da turaren maiko.
” _Kada kiyi kuskuren haduwa da wani, lallai ya zamana da shi kadai zaki yi tozali, domin dl a ƙarfin turaren nan ya wuce tunanin ki, da zarar ya shake ta hankalin sa zai gushe ya susuce Miki hhhhhhh_” Muryar malamin tsubbun da ya Bata maganin ya shiga amsa kuwwa a kunne ta, sai ita ma tayi dariyar a fili tamkar sabuwar kamu tace “tabbas zan mallake ka Maleek a yau, ina ji a jikina ƙarshen wahala ta yazo, ban da matsala da Shakur, na san ya jima da bacci, this is the perfect time Maleek, I’m coming for you” ta karasa tana bin jikin ta da turaren mai matukar ƙarfi, bayan ta kammala ta saka Wata yololuwar riga tamkar yarinya, ta fesa mouth spray kana ta buɗe dakin ta a hankali ta fice zuwa na Maleek.
Shakur ganin sha biyu tayi yasa ya mike domin zuwa dakin Maleek, ya san by now giyar zata sake shi.
Cikin wani shauki daya fara diban Hajiya Sa’adah ta ɗora hannun ta kan handle din kofar Maleek zata tura, a kuma daidai lokacin ne Shakur ya ƙaraso Wajen.

“Mummy!” Shakur ya fada yana kau da kansa gefe domin shigar Hajiyar sa’adah tayi matukar muni, ya kuma ga rashin dacewar hakan, koda yarta ce mace bai kamata taje mata da wanna shigar ba balle namiji.
Duk wani nishadi da shaukin Hajiya Sa’adah ya tsaya cak a lokacin da Muryar Shakur ya ratsa dodon kunnen ta, wani tukikin bakinciki ya tsaya mata a makoshi yayinda taji kamar ta shake shi ɗan haushi, idanun ta ta runtse, kalmar malamin tsubbun na kara ratsa dodon kunnen ta a karo na biyu, ta riga ta tasan komai ya baace mata.

“Lafiya mummy ina zaki a daren nan?” Shakur ya kara tambaya ba tare da ya kalle ta ba, domin baya fatan ya sake tozali da surar ta kamar yanda yayi kuskuren gani a farko.
Cikin rudewa amma tayi kokarin dakewa tace “ammmm ammm my boy zan duba hankalina ya kasa kwanciya da irin baccin da yake yi”

Shakur ya sauke numfashi kana yace “He’s fine mummy, gajiya ce kawai, dan Allah ki tafi ki kwanta”

Kamar ta rusa kuka haka ta ji, amma bata son musu ko yin wata magana da zai tona asirin ta, hakan yasa ta bar Kofar dakin, amma bata tafi gaba-daya ba ta tsaya leka shi ko zai tafi ta samu ta shiga wajen Maleek din, domin tamkar turaren ma ya kara Mata jaraba, so take ta kasance da Maleek a yau, ko ta samu sauƙin abinda take ji a jikin ta da ma zuciyar ta.

Shakur ya bada tazarar mintuna biyu kana ya kalli hanyar data bi da kallo, a lokacin Hajiya Sa’adah ta leko kanta ko ya tafi ta ga ya juyo sai tayi saurin mayar da kanta, kana ta lallaba ta koma dakin ta domin rufuwar asirin ta.

Har ran shi bai ji daɗin shigar da mahaifiyar sa tayi ba, ko kadan bai yi wani bahaggon tunani a kanta ba, sai dai rashin dacewar shigar ta ɗaya gani, kenan da bai zo ba haka zata shiga, ya girgiza kan sa hadi da sauke ajiyar zuciya kana ya ɗora hannun sa kan handle din kofar ya tura ciki.
Mintuna goma kenan da tashin Maleek, yana zaune bakin gado hannun sa biyu dafe da kan sa, cikin sauri Shakur ya ƙaraso kusa da shi yace “Maleek ka tashi? sannu ka yi wanka ko za ka yi sallah kanka zai rage nauyi”
Ba musu kuwa ya mike ya shige toilet ya sakar wa kansa ruwan sanyi, ya ɗan jima kadan kana yayi brush hadi da alwala ya fito daure da farin towel, he was looking so fresh and handsome karfafan jikin sa ta sake bayyana ya bude wardrobe ya dauki Kayan baccin sa ya saka, ya fesa turare kadan kana ya kabbara sallah, duk da cewa abu ƙalilan ya sani kan addini da Alqur’ani amma a nutse yake tabbatar da sallolin da ake bin sa, duk da yana kuskure musamman idan yayi ruku’u bayan ya iddar, sai ya ji kan sa ya rage nauyin, ya zauna kan sa a kasa shi ba lazimi ba, shi ba addu’a ba ya dai yi shiru, Shakur ya mike ya fita ya dauko masa fresh milk, ya duba inda suke ajiye magunguna su ya dauki Panadol ya kawo masa, ya karba ya watsa a bakin sa kana ya shanye fresh milk din tas ya ajiye robar.

A hankali Shakur yace “bro!”

Maleek ya dago idanun sa da suka fara dawo da hasken su ya kalli Shakur, ba tare da ya amsa ba. Shakur ya dora da cewa “promise me ba zaka kara shan giya ba har abada, no matter what”

“I promise” Maleek ya amsa cikin husky voice ɗin sa daya dan dashe.

Shakur ya sauko kasa ya zauna kan sallayar da Maleek din ke kai yace “kayi hakuri da irin maganar dana gaya maka, Amma ka fahimce ni Maleek, ban fifita Munaya a kan ka ba, illah halin ko in Kulan da kake nuna wa kan halin da take ciki na matukar min ciwo, Ni da kai mun san cewa kaine silar duk halin da take ciki amma You kept mute, at least ko dan darajan jaririn cikin ta show some concern please, Ina kara baka hakuri a karo na biyu”
Maleek ya sakar wa kanin sa murmushi daya tsaya iya saman labban sa alamun komai ya wuce.
Shakur ya dauka cewa Maleek din zai masa magana kan Munaya amma yaji shiru, Shakur ya gama aiyanawa a ransa cewa bazai kara faɗa da Maleek kan Munaya ba, sai dai a sannu zai dinga nuna masa illar abinda yake yi.

*Mummy*
Kan gadon ta ta zube ta fashe da kukan bakinciki, zuciyar ta tamkar an watsa mata narkakiyyar dalma, baya ga rashin cikar burin ta har da makudan kuɗaɗen data kashe a dan karamin turaren nan, dubu dari takwas bokan ya karba a wajen ta, bayan ya bata tabbacin ƙarfi da tasirin da turaren zai taka a cikar burin ta, sai gashi Shakur ya lalata mata komai, kuma yace mata matukar wanna aikin ya lalace bata cika burin ta, tabbas babu magani ko asirin da zai taba cin Maleek, irin wanna kalaman waccan malamin tsubbun Hajiya maimoona ya fada mata, ga wanna ma ya maimaita mata, tunda haka ne mezai saka ta dinga bata kudin ta a Banza, wata hanya ya kamata ta nema, domin ta gaji da chachar kudin da take da sunan neman biyan bukata.

Mikewa tayi zaune tana jan majina ta lalubo wayar ta, lambar Hajiya maimoona kawar ta ta kira, wacce ke tare da abokin masha’arta a gadon ta na aure, a dan fusace ta daga wayar, zata katse saboda bata son wani ya katse mata jindadin ta, amma ganin lambar aminiyar ta Sa’adah yasa tilas ta Daga saboda ta san da wata a kasa, haka kawai Sa’adah bazata kira ta a daren nan ba, “Gwaurowa ya dai hhhhhhh” ta fada tana sakin dariya.
Haushi ya cika Sa’adah ga takaicin abinda ya faru da ita, kamar yarinya sai ta saki kuka, Hajiya maimoona ta sauka daga kan saurayin da zata iya haifar sa tace “innalillahi, ke Sa’adah kar dai ki ce min kan yaron nan kike kuka ba ko kunya?”

“Maimoon bazaki gane ba, ban taba jin bakinciki irin na yau ba, ina daf da cika burina a daren nan shegen yaron nan Shakur ya bata min komai”

“Ke ma Sa’adah taurin kai, tun tuni nace ki hakura da yaron nan kin ki, Ni Abinda yake bani mamaki shi ba ibadah yake kamar Shakur ba amma duk Abinda kike baya kama shi, na gaya miki ki hakura, ga yara nan masu jini a jika, amma kin tsaya kwadayi ke lallai sai Maleek uhmm haba sa’adah sai kace wata yarinya”

“Hmmm ni barni maimoona, bana son kowa sai Maleek, shi kadai nake da muradin kasancewa da shi, na ma daina bata kudi na a Banza, a zahiri zan fara nuna masa abinda ke raina cikin salo da kissa ta yanda ba zai iya tsallake tarko na ba”

“Yawwa ko ke fa, abinda ya kamata ki yi tuntuni kenan, kin tsaya shashanci, bare na san zai amince yaran zamanin nan ba idanun su a bude taar yake, kina masa tayi zai amince, saura kuma kar ki ja masa aji ki sakar masa jiki yayi saurin gajiya dake”

“Ke babu ajin da zan ja masa wallahi, ke kin san shekara nawa nake son kasancewa da shi kuwa?, ooh Allah na” ta fada tana matse ƙafafuwa.

Hajiya maimoona ta kyakyale da dariya, daidai lokacin da saurayin dake kwance a gado ya taso gare ta, tilas ta yi jifa da wayar ta suka cigaba daga inda suka tsaya.
Take mummy ta gane halin da kawar ta ke ciki, hakan yasa ta katse wayar, ta rufe idanunta cikin jin shaukin dama ita ta samu abinda take so, she can’t wait to be with Maleek, ranar farincikin ta bazai misaltu ba, a wanna daren bacci barawo ne ya yi nasarar daukar ta, ba dan ta shirya masa ba.

***
“Mami Allah zan iya, ki bari na yanka Miki” Munaya ta fada wa barrister Abrar wacce zuwa yanzu ta ɗan saki jikin ta.

Barrister Abrar wacce ke ji dadin yanda Abrar ke shiga cikin su yanzu tace “Nagode, zauna toh ki yanka” ba musu Munaya ta zauna ta fara yanka albasar, barrister Abrar na mata hirar mutumin ta junior sai murmushi take.
Daga baya ta ɗora da yi mata nasiha kan rayuwa, jikin Munaya yayi sanyi, nasihar barrister Abrar ya shige ta ba kaɗan ba, ta yi matukar nadamar biyewa zuciyar ta, amma zata cigaba da yin addu’a da neman gafarar Allah kamar yadda barrister Abrar ta bata shawara har taji nutsuwa a zuciyar ta.

*DOCTOR ABBAS*
Zaune yake a office din sa yana dan duba contact din sa yana kiran wadanda suka jima basu yi waya ba domin sada zumunci, yana cikin scrolling ya ga number’n Shakur kamar Yadda yayi saving da AA….

” Ya Salam” ya furta yana dafe kansa a lokacin daya tuna cewa yayi wa Shakur alƙawarin zai kira shi, ba bata lokaci ya danna masa kira.
Shakur dake tsaye gaban hall yana lecturing dalibai ya dakata a lokacin daya ji ringing din wayar sa, excusing kansa yayi ya fita daga ajin kana ya daga bakin sa dauke da sallama.

“Wa’alaikumu Salam, Barka da rana, nine doctor Abbas wanda ya zo Companyn ku da dan jimawa”

Cikin rawar jiki da murna daya fito a Muryar sa ya ce “alhamdulillah, kullum ina tsumayin Ganin kiran ka”

Daga can ɓangaren Doctor Abbas ya yi murmushi, Halin Shakur din na burge shi, ganin yadda yayi matukar damuwa da Munaya, ga uban gayyar daya aikata laifi ko a takalmin sa, takaicin Maleek din ya sake cika shi, ya kawar tunanin a ransa kana yace “afuwan, na sha’afa ne, ya al’amura?”

“Alhamdulillah Nagode, ko kuna tare da Munayan ne ka bani ita”

“A’a ina asibiti ne, amma gobe nayi alƙawarin mu hadu a asibitin da nake aiki da misalin uku da rabi sai mu je in da take, saboda ganin cikin ya fara tsufa na Kai ta gidan abokina mai iyali”

“Toh Nagode sannu da k’ok’ari, tabbas wannan duka aikin mu ne, amma mun gaza, an daura maka nauyi kayi hakuri, in Sha Allah Idan mun hadu ka min total na dawainiyya daka yi da Munaya zamu biya”

Daga dayan ɓangaren Doctor Abbas ya yi murmushi yana girgiza kai, bai taba ganin mutum mai iya magana cikin lafazi mai cike da girmama dan Adam kamar Shakur ba, sam baya da dagawa ko jin kai saboda suna da arziki, kawar da tunanin yayi, a fili yace “malam Abbas na ɗauki Munaya tamkar kanwata, so babu maganar biyana komai da zaku yi, sai mun haɗu goben” ya karasa maganar da kashe kiran a lokacin da idanun sa ya kai kan agogon dake manne a office din, mikewa yayi cikin gaggawa domin yana da operation da take jiran sa, gashi har lokacin ya gota da mintuna uku, kayan aikin ya sanya, ya fice zuwa dakin operation din.

***
Zaune take jugum cikin zurfin tunani, domin sai karfe goma ta farka wanda tayi mamakin irin baccin da ta yi, ko fitar ya’yan na ta bata gani ba, ta San sun neme ta kila ganin tana bacci yasa suka tafi basu tada ta ba, amma ita ba haka taso ba, ta so yin tozali da muradin zuciyar ta Maleek, ga gidan ya zame mata so boring, ko dai zata biyewa Hajiya maimoona ne ta samu wani saurayi ta rage zafi wata zuciyar ta bata shawarar hakan.

Kamar mai tabin ƙwaƙwalwa tayi saurin girgiza kanta, a fili take furta “A’a bazan ci Amanar my boy ba, shi kadai zai mallake Ni, ko uban sa jikina yafi karfin sa wallahi”
Tayi shiru cikin nazari kana ta ɗora da cewa “dole na same ka my boy kafin dawowar Daddyn ka, zuwa lokacin ka zama ɗan hannu, wanda kai da kanka zaka dinga nema mana wajen da zamu samun nutsuwa da juna” ta karasa tana sakin murmushi mai sauti, domin ta gama hango komai zai tafiyar mata yanda ta tsara.

*WASHEGARI*
_3:20pm_

Tun uku da yan mintuna Shakur yazo bakin asibitin, ya faka motar sa a gefe yana jiran da rabi tayi sai ya kira doctor Abbas ɗin ya shaida masa ya iso, domin baya son damun sa ko shiga hakkin sa da tuni ya danna masa kira.
Ajiyar zuciya ya sauke, a lokacin da yake tunanin maganar da su ka yi da Maleek kafin ya zo.

” _Bro zan je wajen Munaya na gan ta, ko zaka shirya mu je ko gaisuwar kanwar tace sai ka mata_ ”

Maleek dake danna system ya tsaya cak, kana fuskar nan babu fara’a ya girgiza wa Shakur kai, ko uffan bai furta ba.

Shi ma Shakur bai kara cewa komai ba, domin da gaske yake daya ce yayi alƙawarin bazai kara fada da dan’uwan sa ba, zai cigaba da bin sa a hankali har ya amince ya gane gaskiya, domin har ransa yana da wani boyayyen kudiri kan su wanda yake fatan ya tabbata, hakan zai faranta ransa.

Maleek kuwa a lokacin da Shakur ya fita, sai ya ji ya kasa ci-gaba da yin aikin, gaba-daya nutsuwar zuciƴar sa ta yi kaura, komai ya daina masa dadi, yanayi ne da bazai misaltu ba.

” _She’s five month pregnant_ ” maganar doctor Abbas ɗin ta dawo masa, haka nan ya ji zuciyar sa ta buga daya tuna wannan maganar, ba wai tsoro ba, sam baya tsoron a sani, bacin ran iyayen sa ne baya so, kansa ya ji ya fara sara masa, ya ɗora kan a table din sa, ya shiga nazari.
**
Uku da rabi dot Shakur ya kira wayar Abbas, murmushi Abbas yayi a lokacin daya ga kiran sa, ya mike yana cire hand gloves din hannun sa, domin wani patient yayi wa allura, bai daga kiran ba, ya fita daga dakin da yake ya shiga office din sa ya wanke hannun sa da sanitizer, kana ya fito farfajiyar asibitin, ya kuwa hango shi zaune Cikin mota kafafun sa a waje, ya karasa wajen shi suka gaisa, Cikin wasa yace “ahhh wanna zumudi haka, TOH mu karasa masallacin can mu yi sallah sai mu wuce”
Shakur yayi dariya yana mara masa baya, ya san ɗaya fadawa doctor Abbas din karfe nawa ya zo nan da kila zai ce yayi gaggawa.
Bayan sun iddar da sallar suka dauki hanyar gidan doctor Aaban.

 

 

MunayaMaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566, thanks for your patronage.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button