Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 22

Sponsored Links

XXII…
A hankali Alhaji Dawood ke saukowa daga jirgin sunfarin Turkish airlines fuskar sa dauke da murmushi ganin sa Finally a kasar sa ta gado, bayan shekaru masu yawa daya diba a ƙasar masu jajayen kunnuwa, numfashi ya sauke kana ya shaki iskar garin mai cike da ni’imar dad’i, murmushi ya gagara boyuwa a kyakyawa kuma dattijuwar fuskar sa, yayi kewar iyalan sa, danginsa, hadi da abokan arziki ba kadan ba, more especially SA’ADAH din sa, wacce yake kyautata zaton tayi fushi da shi ne sosai Saboda zaman da baya yi a ƙasar sa, duk da bata gaya masa cewa tayi fushi ba, yayi tunanin hakan ne, domin a shekarun baya tana damuwa da zaman sa a kasar waje, sannan tana yawan neman sa a waya, amma yanzu kam ko bai neme ta ba, ita ma bazata neme shi ba, a takaice dai ta daina dokin sa kamar baya, wanda baya jin dadin hakan, shiyasa gadabaya tunanin sa ya dawo gida, kuma dawowa na dindindin yayi, ya san zata ji dadin wanna labarin tunda bai sanar mata ko ya’yan su ba so yake yayi suprising din su, hakan yasa kai tsaye motar haya ya samu wanda zai kai shi gida.
Basu wani jima ba suka iso gidan, ya sauko janye da trolly din sa Bayan ya sallame mai motar kana ya karasa jikin gate din sa ya kwankwasa, “waye nan” mai gadi ya fadi daga ta ciki yana nufar gate ɗin, a daidai lokacin da Alhaji Dawood ya sake kwankwasa gate din cikin rashin sani mai gadi yace “kai! wai waye haka ne kurma ne baya magana ne?”
“Nine Ahmadu” Alhaji Dawood ya faɗa.
“Innalillahi wa Inna ilahirin raju’un” mai gadi ya fada yana bude gate din cikin rawar jiki, tamkar zai kwanta a Kasa yace “Alhaji ka gafarceni, wallahi ban san kai bane”..
Murmushi Alhaji Dawood yayi yace “mun same ku lafiya?”
“Lafiya Lou ranka ya dade, Sannu da zuwa”
Daidai lokacin shi ma mai kula da flowers ya zo gaida Alhaji yana karban trolly dinsa, Alhaji Dawood ya bi haraban gidan da kallon hadi da kallon yanda flowers din suka ƙara kyau alamun suna samun kula, ya kalli mai kula da flowers din yace”aikin ka na kyau!” Cikin washe baki mai kula da flowers din yayi godiya kana ya yi gaba da trolly din, Alhaji Dawood na biye dashi, Ahmadu yayi saurin cewa “a huta gajiya Alhaji”
“Nagode” Alhaji Dawood ya amsa masa.
Mai gadi ya sauke numfashi, yana jin haushin kansa, duk da Alhajin bai yi fushi ba, amma shi kam ya zama uncomfortable, ya murza bakin sa hannu kana ya koma bakin gate ya zauna.
Hajiya Sa’adah na zaune kafafunta a harde tana chatting yayin da take kora sanyayar orange juice da ta sa yar aiki yi mata, ji take duniyar babu ya ita a jindadi domin shawarar da Hajiya maimoona ta bata yayi mata hundred percent she just can’t wait dare yayi, anjima kadan zata fita siyo desire tablets din, wanda zata zuba masa a favorite smoothie din sa.
“Aha! Daga ina kuma wanna trolly din?” Hajiya Sa’adah ta fada wa mai kula da flowers daya shigo ba tare da ta amsa sallamar sa ba, kafin yayi magana, Alhaji Dawood ya bayyana cikin falon, yaron ya fice Abin sa.
Wayar hannu Hajiya Sa’adah ya sulale ya fadi a kasa Sakamakon ganin Alhaji Dawood, wato bata taɓa bakin gani irin na yau ba, ta ma kasa Magana sai bin sa take da kallo, ji take kamar ta kurma ihu ko xata ji Dama dama domin the moment she set her eyes on him taji tamkar an watsa mata tafasasshen ruwan ne a jiki, meke faruwa da ita ne? Sai burinta na Daf da cika komai zai warware mata, “kai da sake” ta fadi tana girgiza kai ba tare da ta san cewa maganar ta fito fili ba, balle ta san Alhaji Dawood ya iso gabanta har ya dafa ta ba, “Are you okay Sa’adah?” Maganar sa kenan data dawo da ita tunanin ta.
Sai ta rungume shi kawai ta fashe da kukan bakinciki da takaici, shi kuwa murmushi ya saki domin a tunanin sa farincikin ganin sa yasa ta a wanna halin…
Bayan ta ya shiga bubbugawa kana yace “ya isa, komai yazo karshe” Ya fada yana raba jikin su suka zauna kan kujera, ji take Kamar ta rufe shi da duka saboda har ranta wani mugun haushin sa take ji ganin ya bata mata duk wani shirin ta.
“Kamar baki ji daɗin dawowa ta ba, ko nayi laifi ne, fada min nayi gaggawar bada hakuri uwar yayana”
Saita kanta tayi ta yi murmushi daya fi kuka ciwo, tace “nafi kowa farincikin dawowar mijina, amma meyasa baka sanar mana ba?”
Murmushi yayi saboda jin dadin kalaman ta na farko zai bata amsar tambayar da ta yi suka ji shigowar Mota cikin gidan, babu jimawa su Maleek suka bayyana a falon, suka tsaya suka kallon Mahaifin su cikin mamaki da farinciki..
“What a surprise?” Maleek ya fada murmushi na meye gurbin fuskar sa dake daure tamau kafin yayi tozali da Alhaji Dawood, Shakur yace “indeed a surprise” yana dariya, Alhaji Dawood da farinciki ganin zaratan samarin nasa cikin koshin lafiya ya nufo su, suma suka taho gareshi, a tsakar falon suka hadu, ya haɗa dukkanin su ya rungume, idanun Hajiya Sa’adah kuri kan Maleek, the more tana kallon su the more take ƙara jin bukatar kasancewa da shi, wai meyasa ta auri Alhaji Dawood ne? she regret being his wife, a yanxu da yake tsaye tare da Maleek sai ta kara ganin tsufan sa, lallai sai yanxu ta kara tabbatar da cewa ya mata girma, Maleek ne daidai ita, ba mahaifinsa ba.
Ganin kamar sun manta da ita ta mike tana barin falon, domin cigaba da zaman ta zai iya sa ta fallasa kanta.
Sai da suka gama murnan ganin Alhaji Dawood kana suka lura cewa Hajiya Sa’adah bata falon. Maleek yace “where is mum?” Shiru ya ratsa dakin kana Shakur ya ce “may be taje dauko abu ne mu jira ta” ya dai fadi hakan ne ba dan yana da tabbas din hakan bane, ya kau da tunanin daga ransa yace “Amma daddy bazaka kara komawa ba ko?”
Murmushi Alhaji Dawood ya yi yana cewa “eh na dawo cikin ahalina kenan, sai dai zanna tura ku lokaci bayan lokaci domin ku duba min yanda companys dina ke tafiya a can, duk da cewa akwai amintattu dana baro kafin na taho, so it’s high time nima na huta hakan nan, tunda shekarun sun ja”
Jinjina kai suka yi suna murmushi, Alhaji Dawood ya kalli Maleek yace ” the business man, how’s your Company going?” Yanda yayi maganar a zoyale yasa MALEEK sakin murmushi yace “Great Dad”
“That’s Good, Kai fa Shakur ya lecturing din, har yanzu baka sha’awar business?”
“Alhamdulillah daddy, ina jin dadin aikin” jinjina Kai Alhaji Dawood yayi domin ya fahimci har yanzu Shakur din baya sha’awar business, and that’s cool, kowa da ra’ayin sa ba kuma ya tursasawa yaran sa yin abinda basa so, tunda kudin da yake karba mai tsoka ce, da haka ya cigaba da tambayar su yanda rayuwar su ke tafiya, hira tayi nisa har ma sun manta da Hajiya Sa’adah that’s yet to be back cikin su.
Ɓangaren Hajiya Sa’adah kuwa tana shiga dakin ta ta murza key, cikin rawar jiki ta dauki wayar ta, lambar Hajiya maimoona ta yi dialing, seconds uku kacal ta daga, Hajiya Sa’adah ta fashe da kuka sosai tace “na shiga tara Ni maimoona, anya ina da Sa’a kuwa? Hakika ban ci sunana Sa’adah ba, ina cikin tashin hankali, ya zanyi da so da sha’awar Maleek, anya zan same shi kamar yanda nake kulafuci kuwa, babu abinda ya taba bani wahala Kamar shi, haka zalika ban taba neman abu na rasa ba sai Maleek!”…
“Nutsu ki min bayani mana SA’ADAH, meya faru!” Hajiya maimoona ta fada daga dayan bangaren cikin damuwa.
“Alhaji ya dawo, ina zaune kwatsam sai ga shi babu sanarwa,taya zan yi abinda na tsara bayan ya zo”
“Mtsssswe! Amma kina bada Mata wallahi SA’ADAH, Ni fa na zata wani abin tashin hankali ne ya faru”
Waro jajayen idanun ta Hajiya Sa’adah tayi tace “yanzu wanna ba matsala bace maimoona?”
“Ta ina ya zama matsala, bayan kina dani, kawai Malama kin daga wa mutane hankali na zata wani abu ne, kinga babu abinda za a fasa daga yanda muka tsara, amma today is cancelled, ki manta da yau, domin ya dawo, kin san dole zai bukace ki tunda an dade ba a haɗu ba, ki bashi haɗin kai, gobe zamu tattauna yanda za a yi, ko ma na zo gidan”
Numfashi Hajiya Sa’adah ta sauke tana cewa “anya zan iya sakin jiki da shi maimoon, wallahi ina Gaya Miki tun lokacin dana saka dansa a raina na raina iyawar sa, wallahi haushin sa ma nake ji idan ya rabe Ni”
Hajiya maimoona ta saki dariya, tana mamakin wanna abu na SA’ADAH da mugun naci”
Cije le6e Hajiya Sa’adah tayi tace “Allah karki ji zancen wasa, ki daina dariya this is not funny at all”
Hajiya maimoona ta goge fuskar ta domin har da kwala ya xubo mata saboda dariyar mugun ta kana ta tsagaita tace “shikenan, ki yanda nace miki dai idan bakyaso ya zargi wani abu, because there’s no way ku dade baku hadu sannan yazo ki nuna baki san zance ba kin gane, yawwa sai anjima”
Mikewa Hajiya Sa’adah tayi ta nufi toilet, ta wanko fuskar ta ta fito, dai-dai lokacin Alhaji Dawood ya kwankwaso kofar, Hajiya sa’adah ta daidaita yanayin ta ta bude masa Kofar, ya riko hannun ta yace “ina ji a jikina Kamar kina fushi da dawowa ta SA’ADAH”
Tamkar yarinya ta marairaice tana cewa “ba kaine baka sanar da Ni zuwan ka ba, ban tanadar maka special dishes ba amatsayin Wanda ya yi doguwar tafiya” ta fada domin ta cire masa tunanin cewar bata so dawowar sa ba, duk da bai yi karya ba, amma she’s not gonna let him know that.
Murmushi yayi, yana jin dadin kulawar ta garesa yace “karki damu kanki matata, kin manta Ni din ba bako bane, so zanci duk abinda kuma zaku ci, kuma albishirin ki, na dawo Nijeriya gaba-daya”
Dam daram!! Kirjin Hajiya Sa’adah ya buga cikin tashin hankali, amma tayi jarumta wurin danne tashin hankalin ta tace “da gaske? Gaskiya naji dadi, Finally my husband is back home, barka da dawowa cikin ahalin ka” ta karasa cikin kirsa, amma in the inside she’s boiling tamkar tafasasshen ruwa daya debi awannin yana tafasa.
Godiya Alhaji Dawood yayi mata kana yace zai je dakin sa Domin dauro alwala jin kiran Sallah, yana umartar Hajiya Sa’adah da itama tayi Sallah, jinjina masa kai tayi, yana gama fita ta sulale ƙasa dafe da kanta, komai ya gama fice mata a kai, ta ɗauki waya zata sake kiran Aminiyar ta, sai kuma ta fasa ta jefa wayar kan gado, ta kwanta tana numfarfashi tamkar mai ciwon asthma, sallar da bata yi ba kenan har sai da ta ji shigowar su alamun sun dawo daga masallaci hakan yasa ta mike ta nufi toilet domin dauro alwala.

So sorry for the inconveniences… Wani uzuri mai ƙarfi ne ya rike Ni.💖

  1. Munaya Maleek is 500 ✍️✍️😘 contact
    07082281566 to subscribe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button