Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 23

Sponsored Links

XXIII…

*Arewabooks@NoorEemaan*

“Hello! Hello Munaya kina jina?”
“Eh mami ina jin ki, ya aiki?”
“Alhamdulillah, ya jiki, ba abinda yake damun ki ko?”
Munaya ta kalli katon cikin ta a sanyaye tace “bakomai Mami”.
“Toh ki ci abinci sosai, sai mun dawo ko” barrister Abrar ta faɗa tana katse kiran, kana ta kalli matar dake zaune tare da ita a office din tace “cigaba ina jin ki”
“In gaya miki Yaya Aaban ya kira ni ya min tas wai lallai ni na zuga ki aka shigar da ƙarar nan, na dinga mai rantsuwa bani bace, yace bai yarda ba matarsa ba haka take ba. Daddyn su Maheer me zai yi in ba dariya ba” matashiyar mata mai suna barrister Hanan wacce ta kasance kanwa ga mahaifinsa su miemie, sannan Babbar aminiya ga barrister Abrar ce ke wanna maganar.
Barrister Abrar tayi dariya sosai, tace “ai idan aka biyewa pureheart wallahi yaron can zai ci bulus, abinda kuma bazan taba yarda da shi ba kenan, na kasa gane wani irin mutum ne shi yaron sam babu tausayi a tare da shi wallahi, kin san har yau bai nemi yarinyar nan ba, balle ya san halin da take ciki, sai bawan Allah Kanin sa da ke yawan zuwa, so nake Kafin ta haihu a yanke masa hukunci, wanna Shari’ar da akai ta dagawa ne yasa aka samu tsaiko kan shari’ar Munaya, ban taba tunanin za’a dau lokacin har haka ba, an so cin galaba a kai na, amma alhamdulillah Allah ya bani Nasara”
“Hmm ke dai sai godiyar Allah. Ni kaina bana son ya samu sassauci wallahi, ai ban san haka abin ya munana ba sai da na gan ta a zahiri”
Barrister Abrar ta girgiza kai kawai alamun abin na damun ta matuka.
“Kuma har yanzu bata yarda an yi mata awo ba bare a san gender din babyn?”barrister Hanan ta yi tambayar da katse shiru da office din ya ɗauka.
“Wallahi bata yarda ba, ina fara maganar zata saka kuka, sauƙin ta ma doctor Abbas na duba ta a gida, banda haka ko shopping fa bata yarda mu fita tare, kayan yaran ma unisex kawai na sisiyo, amma na fahimci dalilin ta, sam bata son haduwa da Kowa a wanna halin, tana gujewa maganar bakin mutane ne, kin san duk wanda ya ganta a wanna condition ɗin tofa sai ya fadi albarkacin bakinsa, ba Kuma wani Abin bane zai fara jan hankalin mutane illa karancin shekarun ta, amma abinda yasa hankalina bai tashi da rashin zuwan asibitin ba shine ko muna zaune haka zaki ga cikin ta na yawan motsi, rannan har yara suka yi ihun murna, sai fa su zo su sata a gaba suna jiran jikin ya motsa su ji dadi”
Barrister Hanan tayi dariyar yarintar su miemie, yayinda ta hasaso yanda ta ga Munaya ta lalace a zuwan da ta yi gidan yayan na ta, baka ganin komai sai cikin, karancin shekarun ta ya kara bayyana.

Related Articles

****
Tun bayan da aka kawo masa takardar sammaci daga kotu ya zuba wa farar takardar ido mai dauke da tambarin *supreme court*
Ba wai tsoron Shari’ar yake ba, fargabar sa iyayensu, wani hali zasu shiga idan suka ji dalilin shigar da ƙarar? Bai iya karya ba, ba kuma zai taba ba, dole ya fadi gaskiya, amma kuma hakan zai karye zuciyar iyayensu, musamman Alhaji Dawood.
Ɗa ma Alhaji Dawood din baya kasar ya san Hajiya sa’adah zata yi iya yin ta Wajen ganin maganar bata je kunnen sa ba, sam baya kaunar damuwar iyayen su, balle kuma ace shi ne sanadin damuwar su, ba yanda za’a yi ayi shari’ar nan shi da Shakur, Dole iyayen su zasu sani, sanin su kuma na nufin karyawar zuciyar su.
Ya lumshe rikitattun idanun sa da suka kada tamkar jan gauta yana juyi cikin kujerar dake gaban table din sa cikin nazari, dogayen yatsun sa biyu dafe da kansa daidai inda jijiyoyin kansa suka fito rudu-rudu.

Munaya na kwance kasan tayis, domin tunda cikin ta ya kara girma ba inda ke mata dadin kwanciya kamar ƙasa, tana a haka aka turo kofar dakin ta, Junior ne, ta sakar masa murmushi ya tako a hankali ya zo wajen ta, ya durkusa a gaban ta, cikin maganar sa da bata fita yace “Anty muyaya, baby” ya dora hannun sa a kan cikin ta.
Munaya ta zuba masa ido, kwalla ya ciko idanun ta, ta ɗora sirarran hannun ta kan na Junior ta rufe idanun ta, a daidai lokacin da cikin ta ya wani motsa Junior ya zare hannun sa yana dariya, Munaya ta bude idanun ta, hawaye suka gangaro tare da murmushi, ba wai murnan cewa cikin ya motsa ba, farinciikin da Junior ya shiga ne ya sanya ta hakan, ya hau jikin ta yana goge Mata fuskar ta, kana ya tabe baki irin na yara shi ma zai yi kuka, ta kwantar da kansa a kafadar ta tace “na daina ka ji”
Ya jinjina mata kai yana mayar da kansa ya kwantar, bayan Amnah Munaya bata taɓa jin son wani yaro Kamar Junior ba, kamar yadda yake son ta haka ita ma take kaunar sa.

***
Shakur ya fito haraban gida rataye da jakar sa, yau da motar Maleek yake sha’awar zuwa lecturing, ya buɗe back seat zai ajiye jekar sa mai dauke da muhimman abubuwan sa ya hango farar takardar, ya ajiye jakar zai rufe motar, amma tunanin sa ya sake kai wa kan takardar ya dauko hadi da bude ta, gabansa ya yi mummunan bugawa daya karanta headline din rubutun, ya zagaya dayan bangaren cikin sauri ya bude motar ya shiga, hannun sa na rawa tamkar shi aka turo wa sammacin yayi dialing number’n Maleek…
“Tun yaushe aka turo maka takardar nan?” Shakur ya faɗa ɓacin rai muraran a Muryar sa.
Maleek dake zaune a office ya dafe kansa, shaf ya manta bai dauke takardar a mota ba, bai so Shakur ya gani ba.
“I’m asking you!” Shakur ya daka masa tsawa.
Ya runtse idanun sa, slowly yace “yau kwana hudu”
“And You kept mute, baka yi komai a kai ba, baka da hankali ne Maleek? So kake su daddy su ji ko me, innalillahi wa Inna ilahirin raju’un.
“Shak…..” Sam bai saurari Maleek din ba ya katse kiran, hankalin sa a tashe ya tada motar ya bar gidan, mai Gadi ya cika fal da mamaki ganin Shakur a haka, abinda bai taba yi ba, musamman gudu a mota.
Maleek ya bi wayar da kallo ganin Shakur ya katse kiran.
Ya jefar da wayar, ya mike yana zagaye office din.
Babu wasan zagi a tsakanin sa da Shakur tun yarinta, amma tunda Shakur ya budi baki ya zage shi yau Lallai ransa ya kai makura a ɓaci.
yana iya jure komai amma baya kaunar ɓacin ran kanin sa, ya furzar da iska mai dumi daga bakin sa, duk abubuwan nan laifin Munaya yake gani, ita ta tarwatsa masa k’yakkyawar rayuwar sa, taya bazai tsane ta ba? Bayan ta saka suna faɗa da Shakur din sa, ga wata matsalar Kuma ta ja masa wanda zai lalata zaman lafiyar gidan su.

Hanyar gidan doctor Aaban ya nufa, domin tunda ya ga takardar nan ya san barrister Abrar ce ta shigar da ƙarar nan, a yawan zuwan da yake gidan duba Munaya ya san cewa ita din babbar lawyer ce mai zaman kanta. Bazai iya imagining daddy da mummy sun ji cewa an shigar da Maleek ƙara ba, tashin hankalin da zasu shiga bazai misaltu ba.
Ya danna horn mai gadi ya bude masa domin ya gane sa yanzu, wanna karon bai jira an masa iso ba, ya shiga danna alarm din Kofar shiga falon.
Babu jimawa aka buɗe kofar, doctor Aaban ya gani bayan an buɗe kofar. Ya sauke kansa kasa saboda kwarjinin da yayi masa kana ya gaishe shi, doctor Aaban ya amsa yana bashi hanyar shigowa.
“Aha Shakur ne, sannu da zuwa” barrister Abrar ta faɗa murmushi dauke a fuskar ta, a tunanin ta wajen Munaya yazo kamar kullum.
“Zaune mana, lafiya dai?” Doctor Aaban ya yi tambayar ganin kamar baya tare da nutsuwar sa.
Ya kasa zama ya durkusa gefen barrister ya hada hannuwan sa waje ɗaya alamun roko yace “i make sound selfish, Amma wallahi babu son kai ko daya, zan iya cewa nafi kowa jin takaicin abinda Maleek yayi wa Munaya, da ina da iko dana sanja komai tamkar bai taba faruwa ba, ina rokon ki dan girman Allah ki taimaka ki janye karar nan, komai zai iya faruwa idan labarin nan ya je kunnen iyayen mu, dan Allah ki taimaka ki duba magana ta”
Barrister Abrar tayi kasa da kanta, abin ya Mata banbarakwai, babban saurayi kamar Shakur ke rokon ta kan laifin da ba shi ya aikata ba, gaba-daya ya rude har wata gumi ya haɗa saboda tashin hankalin, tayi matuƙar tausaya masa, amma kash bakin alkalami ya bushe.
Tunda Shakur ya fara magana doctor Aaban ke kallon sa cikin nazari har ya kai aya, tabbas duk wanda yake da kamar Shakur a ahalin sa ya more, domin shi din jajirtacce ne, mai sadaukar da komai nasa domin farincikin familyn sa.
Barrister Abrar ta bude baki zata yi magana ya dakatar da ita domin ya san amsar da matar shi zata bayar zai kara breaking zuciyar Shakur ne into pieces, ya kalli Shakur yace “kaje, i will talk to her”
“Duk da Shakur yaso jin ta bakin barrister Abrar domin hankalin sa yafi kwanciya amma bashi da zabi daya wuce ya mike, yayi godiya ya fice.

“Pureheart, ya zaka ce ya tafi, ka bari na gaya mas…..”
“Abrar ya kira ta da sunan ta na ainihi”
A duk lokacin daya kirata da hakan ta san maganar bata wasa bace.
“Na’am” ta amsa tana kallon sa.
“Ni zaki yiwa taimakon nan, ki janye karar nan, matukar na isa dake a matsayin miji, can You see halin da yaron nan ya shiga kuwa, even Munaya shari’ar nan zai yi affecting din ta, domin idan tana gaban alkali yana tambayar ta komai da take kokarin mantawa zai na dawo mata, wani hali kike tunanin zata shiga bayan yanxu kwanciyar ta ake so tunda cikin ta ya tsufa, ki janye karar nan please, idan kuma ban isa dake ba, sai na haɗa ki da Ammi”
Tun dazu jikin barrister ya gama mutuwa, maganar mijin ta Kuma has add to it, takaici ya saka kuka zuwar mata ta Kalli mijin ta tace “yanxu yaci bulus kenan, babu wani mataki da za’a dauka a kansa kenan? Taya za’a daina ire-iren waɗannan abubuwan idan ba’a hukunta masu yi domin ya zama iznah ga yan baya.
Doctor Aaban ya dawo kusa da matar sa cikin lallashi yake patting bayan ta yace “ya isa, ba dan shi zaki yi ba, domin Allah, munaya, da kuma shi Yaron nan ɗaya zo”
Ta kwantar da kanta a kafadar sa tace “Ni abinda yafi bata min rai shine halin ko in kulan da shi Maleek din ke nuna wa, for God sake sai wanda ba ruwan sa ne yabi ya daga hankalin sa, wani Irin mutum ne shi Maleek din nan Kamar ba zuciya ce a kirjin sa ba, kawai ya zauna a can without even caring”

“Ki manta da shi, surely zai yi nadama wata rana, Ni dai ki manta da shari’ar nan saboda zaman lafiya, da kuma kwanciyar hankalin Munaya”
Ta yi shiru kana tace” I’m not giving you a yes, sai nayi tunani a kan hakan pureheart”
Ya gyada kai yace “Nagode” da haka ya mike kana ya bar ta domin tayi nazari da kyau.
Munaya kam na daki a kwance sam bata san wainar da ake toyawa ba.

 

 

Me ra’ayin ku kan Page din yau? Magana nake da yan paid groups ba da yan bati sidan ba😂💔

MunayaMaleek is 500 via 3200689860 first bank Haruna Rukayya.
Shaidar biya ta Whatsapp number dina 07082281566.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button