Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 36

Sponsored Links

XXXVI….
(36)

Hankalin sa a matukar tashe da yake zaune yanxu likita na masa bayanin maganin da Kuma side effect din sa, ya shiga tunani mai zurfi, ashe abun ya wuce tunanin sa, yanzu waye ya siyo maganin karfin sha’awa, shin matarsa Sa’adah ko ko dansa Maleek?

Gaba-daya kansa ya kulle so yake ya samu amsa tambayoyin dake dankare a ransa, so yake ya san tun yaushe ake wanna lalacewa a gidan sa. Likita da ya lura Alhaji Dawood Baya hayyacina sa ya tabo sa yace “Alhaji lafiya kuwa?”

Related Articles

“Alhaji Dawood yayi firgigit yana sakin murmushi yake yace “lafiya ba komai, toh na wuce doctor, nagode kwarai”
Da haƙa ya fita Cikin sanyin gwuiwa, likita ya bishi da kallo cikin nazari.

Da kyar Alhaji Dawood din ya iya tuka kansa, so yake ya zama strong domin Shakur, idan babu shi a raye wa zai kular mai da shi? Tunda bai yi sa’ar uwa da dan uwa ba, da ba haka ba da babu abinda zai hana shi ma a bashi dago a asibiti.

Irin abincin da likita yace Shakur zai iya ci ya shiga nema, ya samu ya siya masa citrus fruits da
Kuma abinci daya sha vegetables, har ya shiga mota sai Maleek ya fado ransa, duk yanda yake jin haushin sa da tsanar abinda yayi masa amma Sai daya sauka ya siya masa abincin shima, kana ya karasa asibitin.

Yana shiga dakin ya tarar da Maleek Zaune ya kurawa Shakur ido dake bacci, Maleek ya dago kansa, ya samu ya haɗe kalmar “welcome Dad”

Ko kallon sa Alhaji Dawood din bai ba, ya karasa gaban gadon, ya shafa kan Shakur ɗin kana ya ajiye ledar abincin, ya fice zuwa office ɗin likita domin ya tabbatar ya zo duba shi bayan ya tafi gida, so yake ya ji a wani hali jikin Shakur ɗin yake ciki, idan babu cigaba zai fitar da shi kasar waje.

Ɓangaren Hajiya Sa’adah kuwa, kwanan ta uku curr bata yi wanka ba saboda tashin hankali, har Wani duhu ta kara, a yau ta gaji da shan ruwan toilet da take, sosai yunwa ke kwakulan cikin ta, amma tsoron fitowa take ji, shirun da Alhaji Dawood ya yi bai dauki mataki a kanta ba yafi komai kara daga hankalin ta, ga ƙawar ta Hajiya maimoona bata kira ta din ba bare ta samu mafita.

Ta daure zuciyar ta ta fito saboda ta kasa cigaba da jure yunwar da take ji, sai data leka ko ina ta tabbatar babu kowa falon sannan ta fito, a gaggauce ta shige kitchen, indomiee da kwai ta haɗa, ta ɗauki lemon kwali ta sake komawa dakin ta.

Sai data cinye abincin tas ta kora da lemon ta dawo hayyacin ta, ta mike ta nufi toilet tayi wanka, ta fito ta saka atamfa ta zuba kwalliyar ta, sai kamshi take bazawa take ta dawo Asalin Sa’adah din ta.

Ta zauna ta janyo wayar ta, inda take adana hoton Maleek ta shiga, ta kafe shi da ido, ita fa bawai ta hakura da Maleek bane, buri da muradin da take da shi a kansa sai ma abinda ya karu, domin yanda take kintata halittar Maleek a da ashe ya wuce tunanin ta, ta kuma rage masa daraja, amma data gan shi a zahiri ta ji bazata iya taba rabuwa da shi ba, yanzu da Alhaji Dawood ya sani bata ki ya sauqaqe mata wanna auren na sa ba, domin idan arziki ne ta tara har bata san adadi ba, me kuma take nema banda ta samu saurayi mai jini a jika ya yi ta biya mata bukata, ga samari birjik amma kash babu wanda idanun ta ya makalewa sai Maleek, za kuma tayi amfani da duk wata kissa da kisisina wurin janyo hankalin sa gare ta.

Tsoron ta daya yanzu bata san kalar hukunci ko kuma me Alhaji Dawood din zai ce mata ba, amma zata jira ta gani,
Da wanna hankalin ta ya kwanta ta shiga kiran Hajiya maimoona sai dai number busy yake nuna mata.

Maleek kuwa tun ranar daya taka kafar sa zuwa asibiti bai ƙara fita ba, Shakur yayi masa magana kan bai kamata ya bar Companyn sa haka ba, amma ya ce babu inda za shi har sai Shakur ɗin ya warke, Shakur Yace ya tafi gida ya huta nan ma yace babu inda za shi, domin bayaso abinda zai sanya Alhaji Dawood ya kara jin tsanar sa domin yana ganin hakan a cikin idanun sa yanzu, baya amsa gaisuwar sa, Shakur kaɗai ke bashi farin ciki, duk da yana cikin halin ciwo amma bai so ya ganshi cikin damuwa.

Kamar yanzu shi da shakur din ke dakin suna hira, yanxu an cire masa oxygen din saura na’urorin dake jikin sa, Alhaji Dawood ya bude kofar ya shigo, Shakur ya kalli Maleek yace “Maleek jeka yi wankan ka since Daddy is here”

Maleek ya Mike, ya gaida Alhaji Dawood, amma bai amsa ba, yayi kasa da kansa ya debi kayan daya siyo sabar yanda bai son komawa gidan shi kadai, ya nufi toilet ɗin dake dakin.

Alhaji Dawood ya zauna kusa da Shakur yana tambayar sa jikin sa, maimakon Shakur ya amsa sai yace “Daddy Meyasa baka amsa gaisuwar Maleek ba?”

“Har kana tambaya ta Shakur, Duk wanna halin da kake ciki waye sila? just keep quiet please, bana son magana a kan shi da ma ita din”

Shakur yayi shiru yana kallon mahaifin na sa, bai taba Ganin sa da zafi kamar yadda yaƙe ganin sa a yanzu ba, ya sauke numfashi kana ya budi bakin sa yace “Daddy, Maleek bashi da laifi, bai san komai kan shirin mummy ba”

“Ban gane ba, bayan abinda idanuna suka gane min, yaro ne ko shashashan ina ne shi?, ooh no please Shakur” yace yana kulle idanun sa.

“Trust me Dad, Maleek yace min ta….” Nan ya shiga bawa Alhaji Dawood labarin abinda Maleek yace masa, ya san yin maganar Babu abinda zai janyo face sosa zuciyar Daddyn na sa amma yana son wanke Maleek din sa.

Alhaji Dawood ya yi ƙasa da kansa cikin dimbin al’ajabi, sai yanzu ya samu amsar da yake nema kan maganin karfin sha’awa daya dauka a kitchen, menene yayi wa Sa’adah, Meya rage ta da shi, ta rasa Wanda zata ci Amanar sa da shi sai dan cikin sa, hawayen bakin ciki ya zubo masa yayi saurin sharewa.

“Ya Abbas kana samun ya Shakur a waya kuwa? I’m worried, I hope yana lafiya” munaya da doctor Abbas ya kawo ta makaranta ta fada, tayi kyau sosai cikin fararen uniform din ta wanda ta daura bakin jallabiya a saman ta, siririn farin glass daya dace da fuskar ta ke sanye a idanun ta.

Abbas ya ce “nima bana samun sa, amma idan na ajiye ki zan tafi can school din da yake lecturing kila mu hadu”

“Dan Allah kaje karka manta” munaya ta fada cikin marairaicewa.

Yace “taya zan manta, Shakur mutumi nane fa, oya yi min murmushi”

Tayi masa murmushi, har dimple dinta ya lo6a yace “dama kina da dimples ban sani ba?” Ta saki dariya cikin jin kunya ta sauka daga motar.

Shima yayi dariya cikin son Munaya ya tada motar ya bar asibitin.

Doctor Abbas yaje makarantar sai dai su ma sunce Shakur ɗin kwana biyu bai zo ba, bai kuma bada Dalilin rashin zuwan sa ba.

Doctor Abbas ya damu ainun, ba Kuma ya son zuwa Companyn Maleek saboda yanda basa shiri, sai tunanin zuwa wajen mai gadin Companyn ya fado masa, ya san zai samu wani bayani, kila tafiya Shakur ɗin yayi, bai gaya musu ba, sai dai yana zuwa Companyn ya samu labarin sun kwana biyu zasu ga Shakur ba, Nura mai gadi ya kara masa da cewa da cewa shima Maleek kusan sati Daya kenan baya zuwa, kan doctor Abbas ya kara daurewa TOH meke faruwa ne?.

Yayi wa nura godiya, sannan ya shiga mota, ya dauki wayarsa ya kara kiran wayar Shakur ɗin a kashe.

“Daddy Ina wayata ne? Ina son sanar da makarantar da nake lecturing su bani leave, sannan na fadawa abokan arziki kada hankali su ya tashi”

Alhaji Dawood yace “wanna gaskiya ne, Maleek ga mukullin mota, je ka ɗauko masa wayar”

“Okay Dad” Maleek ya fada yana karbar mukullin ya fita, bayan ya kawo wayar ya kunna ya meka masa, Shakur ya karba ya turawa makarantan sakon cewa bai da lafiya yana gadon asibiti tare da hakuri kan rashin sanar musu kan lokaci da bai Yi ba, sakon Munaya ya ga ya shigo wayar sa yayi murmushi ya nuna wa Maleek fuskar wayar yace “ga mutuniyar” Maleek ya balla masa harara, Shakur yayi murmushi daidai lokacin da kira ya shigo wayar sa ya ga lambar doctor Abbas ce, ya daga, doctor Abbas har da ajiyar zuciya saboda yanda ya damu sannan yace “haba Shakur, ina ka shiga ne haka, duk ka saka hankalinmu ya tashi”

Shakur yayi murmushi yace “afuwan tuba nake, bani da lafiya ne, muna asibiti ma Yanzu haka”

“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un, asibiti? Sannu Allah ya baka lafiya, kuna wani asibiti ne?” Doctor Abbas ya fada a dame.

“Ameen, Maleek yama sunan hospital din nan?” Ya tambayi Maleek din ba tare da ya katse wayar ba, bayan Maleek ɗin ya fada masa, shima ya sanar wa doctor Abbas ya ce gashi nan tahowa yanxu nan da haka suka yi sallama.

MALEEK ya kalli Alhaji Dawood yace “Dad ban ga su yaya Laraba ba?”

Alhaji Dawood ya sauke numfashi sannan yace “Maleek na rasa yanda zan sanar musu ne, ka san dole zasu tambayi Dalilin kwanciyar dan’uwan ka a asibiti, Bama wanna ba, idan suka zo suka ga daga Ni sai kai ke cinyar Shakur dole su nemi sanin gaskiya”

Maleek yayi kasa da idanun sa kawai, mamakin Hajiya Sa’adah na kara Kama shi, dama haka take? So heartless human being he has ever seen, ya kauda tunanin ta daga ransa, domin Sam baya son tunowa da ita.

Babu jimawa doctor Abbas din ya karaso asibitin, ya kadu da ganin halin da Shakur ɗin ke ciki Musamman na’urorin dake jikin sa, a tunanin sa normal rashin ne lafiya ne wanda bai wuce karin ruwa ba.
Kamar yadda Abbas bai gaisa da Maleek ba, haka shima Maleek ko kallon inda yake bai ba.

Doctor Abbas yaso kiran munaya, amma sai ya fasa domin ya san tana tsaka da karatu yanzu a makaranta, amma ya fadawa Shakur ɗin cewa zasu dawo da yamma, zai kawo su, da haka ya fice daga asibitin.

Da yamma kuwa sai ga barrister Abrar, doctor Aaban, Munaya, little Amnah, da su miemie, sai doctor Abbas.

Farin cikin ya bayyana a fuskar little Amnah data ga Daddyn ta, cikin ihun murna tace “yeeeeeee Daddy” ta zo ta fada jikin sa, ya rungume ta a kirjin sa yana jin son ta, sosai yaji dadin ganin ta domin yayi matukar kewar ta, Alhaji Dawood sam bai kawo komai a ransa ba, amma yayi mamakin ina yarinyar ta san Maleek, domin maleek ba son yara yake ba, ga kuma ya ga alamun shakuwa a tsakanin su, Munaya ce karshen shigowa hannun ta dauke da basket, wanda tayi wa Shakur ɗin abinci irin na mara lafiya, dogon hijabin maroon ne a jikin ta sai glass dake fuskar ta wanda ta mayar da shi na ado yanzu, kila dan ta ga yana matukar kara kawata fuskar ta ne, bakin ta ɗauke da sallama ta shiga dakin, gaban ta na faduwa, Alhaji Dawood ta fara hango wa ta karasa wajen shi ta durkusa tace “ina wuni, ya mai jiki?” Cikin jin dadin Alhaji Dawood ya amsa yana murmushi domin sosai ya yaba da tarbiyyar ta.

Ta mike ta ajiye basket din, idanun ta ya kai kan Shakur, ta zaro idanun ta ta cikin gilashin idanun ta, domin sosai zuciyar ta ya karye ganin yanda Shakur ɗin ya rame kamar ba shi ba.

Bata san lokacin da Wasu hawaye suka wanke mata fuska ba, tayi kasa da kanta, Shakur yace “Munayaa kuka kuma? Kar fa ki koyawa little Amnah saurin kuka” ya fada da wasa.

Munaya ta dago kanta ta kalli Shakur ɗin, bata taɓa ganin mutum mai karfin hali kamar sa ba, duk wanda ya kalle shi ya san yana jin jiki amma sai wasa da dariya yake.

Muryar little Amnah mai Zaki da kaifi ya karade dakin tace “bakin Daddy na in gaya maka wani abu, mummy ta iya kuka sosai ”

Shakur yayi dariya yace “toh kin ji ko? Ya kamata ki daina”

Alhaji Dawood yaji little Amnah ta burge shi domin gata yar karama amma sai bakin magana.

Abbas daya ji sabon abu yace “wato shi Shakur ne bakin Daddyn ki?” Ya fada da dariya.

“Eh mana, shine bakin Daddy na, kai kuma Daddy doctor, ga kuma farin Daddy na nan” ta fada tana komawa jikin Maleek da kansa ke kasa, ta kuma xillewa ta nufi wajen Alhaji Dawood tace “kai ina Daddyn ka da mummyn ka, ka ‘ga mummy na can, kuma ina da Daddys guda haka ” ta gwada uku da yatsun ta.

Alhaji Dawood ya riko hannun ta Yace “kece ke yar gata ce, ya sunan ki?”

“Sunana Nabeelah, amma little Amnah ake ce min”

“ALLAH ya miki albarka kin ji?”

Tayi dariya sai ta kara hawa jikin Maleek ta dane shi, ta kalli inda Alhaji Dawood ya zauna, tace “ka ga Dad…”

Abbas daya fahimci surutun Amnah zai iya tona asirin cewa Maleek ne mahaifinta yayi saurin cewa “Little yi shiru, karki damu bakin Daddyn ki, baki ga bashi da lafiya ba”

“TOH na daina” tace tana ɗora kanta a kirjn Maleek.

Shi kam Alhaji Dawood yaji komai yarinyar tayi na burge shi, ga shiga rai, ya Kuma yi mamaki kwarai da yarinyar ke cewa munaya ce mahaifiyar ta domin she looks so young.

Maleek ya mike zai fita, little Amnah tayi saurin riko hannun sa tace “zan bika Daddy”
Maleek ya saci kallon Alhaji Dawood ya ga little Amnah yake ta kallo yana murmushi, yayi saurin rike hannun ta suka fice daga Dakin.

 

Munayamaleek is 500 via3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566, thanks as you patronize.💖

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button