Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 38

Sponsored Links

XXXVIII…
(38)

*MunayaMaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, evidence of payment to 07082281566 (idan baki shirya siya ba, dan Allah don’t chat Me)*

Ji yayi da farko kamar bacci yake yi yana mafarkin Mutuwa, ya ganshi yana kuka an masa wanka an ɗaɗɗaureshi a cikin mayafi har an zura shi a kabari.
Yana a haka ya cigaba da jin Kamar yana mafarki ne, har sai da yaji kabarin ya matse shi, yayi ihu amma sai yaga ba wanda ya ji ihun nasa.
Ya dinga jin takun mutane suna watsewa har ya zamana an barshi shi kaɗai a ƙarƙashin ƙasa, sai yaga an dawo masa da ransa sai ya buɗe idon sa cikin farin cikin cewa ya gama mummunan mafarkin da ya keyi.
Sai dai yana kallon jikin sa sai ya ganshi cikin likkafani sai ya fara tambayar “ina riga da wandon dana kwanta da su, ya na ganni tsirara yanzu?.

Ya kara tambayar “a ina nake, ina ne wurin nan? Yaya nakejin ƙamshin ƙasa da kwaɓeɓɓen laka ta ko ina, wai me ya kawo ni nan ne?”
Shiru bai samu amsa ba Daga nan ya fara fahimtar ashe a ƙarƙashin ƙasa yake da gaske, ba mafarki yakeyi ba, ashe fa lallai ya mutu ne, innalillahi wa inna ilaihi raju’un.
Ya wani yi ihu yana ƙiran sunayen jinin sa, Daddyn sa, yarsa, har ma da Munaya ya kira amma ba wanda ya amsa, a madadin haka ma maganar dawowa take tana amsa kuwwa a kunnen sa, tabbacin Babu mai jin sa.
Sai ya tuna Allah, shine kawai zai iya taimakon sa, ya kama kuka yana ƙiran sunan Allah yana roƙon sa gafara, yana cewa “ya Allah na tuba”, ya kara ihu cikin firgici da tsoro irin wanda bai taɓa ji ba a rayuwar sa ta duniya.

Sai ya tuno wani wa’azi da yaji inda malamin ke cewa “Idan Allah ya sa kai mutumin kirki ne a gidan duniya Mala’iku biyu masu kyakkyawan kama za su zo su kwantar maka da hankali su ɗebe maka kewa.
In kuma ya kasance mutumin banza ne a gidan duniya to Mala’iku masu mummunan kama za su zo su ƙara razana shi su kuma azabtar da shi” malamin ya kara da cewa
“Yazeedur Raqqaashiy ya karbo Hadisin daga Anas bn Malik (R.A) yana cewa
“Watarana Mala’ika Jibreelu (A.S) yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) awani lokacin da bai saba zuwa masa ba.
Yazo, gaba dayan launin fuskarsa
ya sanja, Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa mai yasa naga launin fuskar ka duk ya sanja haka?”

Mala’ika jibril Yace “Ya Muhammadu (S.A.W) nazo maka ne a wannan lokacin da Allah yayi Umarni da Masu hura wuta su cigaba da hura ta.
Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Azabar Kabari gaskiya ce, kuma Azabar Allah ita ce mafi girma, to bai kamata yayi wani farin ciki ba har sai ya tabbatar da cewa ya samu tsira daga wannan”.

Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa “ya Jubreelu, ina son ka siffanta min yadda jahannama take”.

Sai yace “Na’am. Hakika Allah maɗaukakin Sarki yayin da ya halicci Jahannama, yasa an hurata tsawon Shekaru DUBU. Har sai da ta zama JA -JAWUR.
Sannan aka sake hurata tsawon Shekaru DUBU har sai da ta zama FARI – FAT!!
Sannan aka sake hurata tsawon shekaru DUBU har sai da ta zama BAKI – KIRIN!!!.
Tana nan har yanzu BAKI KIRIN ce, mai
tsananin duhu ce.Harshen Balbalinta basu mutuwa ballantana Garwashinta.
Na rantse da Girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za’a bude misalin kofar allura daga wutar Jahannama, Wallahi sai dukkan Ma’abotan doron duniyar nan sun kone baki dayansu saboda tsananin zafinta.
Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za’a ratayo tufafi guda daya daga tufafin ‘Yan Wutar Jahannama a makaloshi atsakanin Sararin Samaniya, da sai dukkanin Ma’abotan doron kasa sun Mutu baki dayansu saboda tsananin Warin wannan Tufafin.
Da kuma zafin dake tattare dashi. Babu wanda zai yi saura acikinsu don tsananin abinda zasu riska na zafin wannan tufafin.
Na rantse da girman Ubangijin da ya aiko ka da gaskiya amatsayin Annabi, da ace za’a dauko zira’i guda na Sasarin nan na ‘yan wuta (wato CHAINS din da ake daure su dashi sannan a dinga jansu a kan fuskarsu)
Wannan Wanda Allah ya ambata Acikin Alqur’ani, a dorashi bisa wani dutse daga duwatsun duniyar nan, da sai dutsen ya narke ya zagwanye har zuwa Kasa ta bakwai.
Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya amatsayin Annabi, da ace za’a ajiye wani mutum a mafa’dar rana ana yi masa azaba, da sai wanda yake mahudar rana ma ya kone kurmus saboda bala’in zafinta. Zafinta mai tsanani ne. Zurfinta mai nisa ne.
Tufafin cikinta na karfe ne. Abin shan cikinta HAMIMU ne (tafasasshen ruwan azaba) da kuma ruwan Gyambo.
Mayafan cikinta kuma an yankosu ne daga Wutar.
Tana da Kofofi guda bakwai, Kowacce kofa tana da wani yankin cikinsu da aka tsaga mata, zasu shiga ta cikinta daga Mazaje da mataye”.

Sai Manzon Allah (saw) yace “shin kofofin nan irin namu ne?”

Sai Jibreelu yace
“A’a sai dai ita kofofin abude suke, wata kofar tana kasan wata.
Tsakanin kowacce Kofa da wata kofar, tsawon tafiyar shekara SABA’IN ne.
Kowacce kofa ta ninka wacce take sama da ita a tsananin azaba har ninki SABA’IN.
Za’a rika kora makiyan Allah cikinta. Kuma duk sanda aka koro wasu (‘Yan wuta) zuwa wata kofa, Zabaniyawa ne zasu tarbesu da Sarkoki da Sasarai. Za’a zira musu Sasari (chains) ta cikin bakinsu sai ya fito ta duburarsu.
Sannan za’a daure hannunsa na haggu ajikin wuyansa, hannunsa na dama kuma za’a fasa Kirjinsa dashi aturoshi ta cikin zuciyarsa sai ya fito ta bayan kafadarsa. Sannan ahada a daure da wancan Sarkar.
Kowanne Dan Adam za’a hadashi tare da shaytani guda acikin Sarkar Sasarin, Sannan arika Jansa akan fuskarsa (acikin Garwashin wutar da kuma dagwalonta) Mala’iku kuma suna Jibgarsu da Gudumomin Baqin Karfe.
Duk lokacin da suka nemi fita daga cikinta saboda bakin ciki da wahala, Sai a sake dawowa dasu cikinta”

Sai Annabi (S.A.W) yace ma Jibreelu (R.A) “Shin su wanene mazaunan cikin wadannan kofofin?”

Sai Mala’ika Jibreelu yace “Kaga Kofar nan wacce take chan Karkashin Kasa, ita ce mazaunar Munafukai da kuma wadanda suka kafirce daga Mutanen Annabi Eisa (A.S) (Wadanda aka ce kar su boye abinci amma sukayi taurin kai suka boye). Da kuma Mutanen Fir’auna.
Ita kuma wanna wutar sunanta “HAAWIYAH.
Sai kuma Kofar nan ta biyu, wadanda zasu shiga cikinta sune MUSHRIKAI. Kuma sunanta AL-JAHEEM.
Kofar ta uku kuwa masu bautar taurari ne zasu shiga ta cikinta. Sune mazaunan cikinta. (awani wajen ance zasu zauna tare da masu wasa da sallah). Kuma sunan wannan wutar SAKAR.
Kofar wuta ta hudu, ta nan ne IBLIS (L. A.) zai shiga cikinta tare da Mabiyansa da kuma Majusawa masu bautar Wuta.
Kuma sunanta LAZAA.
Kofa ta biyar kuwa ta cikinta YAHUDAWA zasu shiga. Kuma sunanta ALHUTAMAH.
Kofa ta shida kuwa, NASARA ne zasu shiga ta cikinta. kuma sunanta SA’EER”

Daga nan kuma sai Mala’ika Jibreelu ya sunkuyar da kansa yayi shuru, ya kasa cigaba da magana saboda jin kunyar Manzon Allah (S.A.W).
Sai Manzo (S.A.W) yace masa
“Shin ba zaka bani labarin ko su waye mazaunan cikin wanna Kofar ta bakwai din ba?”

Sai Jibreelu yace “Sune Ma’abotan Manyan Zunubai daga cikin al’ummarka. Idan har suka mutu basu tuba ba”

Nan take Sai Sayyidina Rasulullahi (S.A.W) ya
fadi ya suma!

Sai Mala’ika Jibreelu ya dauki kansa ya dora akan cinyoyinsa har sai da ya farfado sannan yace
“Ya kai Jibreelu lallai musiba-ta ta girma! Kuma bakin cikina ya tsananta, yanzu ashe akwai wanda zai shiga wuta daga al’umma ta?”.
Sai yace “Eh amma Ma’abotan Manyan zunubai daga cikinsu”
Daga nan Sai Manzon Allah (S.A.W) yasa kuka, Mala’ika Jibreelu ma yana kuka…!!!.

Hankalin sa ya kara mummunar tashi, tsoro da firgice ya mai rubdugu, sai Kuma ya ga Shakur tsaye da fararen kaya yana cewa “ya kai dan uwana ka tuba, ku tuba kafin lokaci ya kure muku domin lokaci baya hannun kowani bawa!”
Daidai nan ya bude idanun sa a firgice, zuciyar ta shiga tsalle, ya kalli yanda ya cike sharkaf da gumi tamkar an yi masa wanka da ruwa, ya kai idanun sa ga gadon ya hango Shakur a kwance idanun sa biyu yana kallon sa.

Yace “sha… Shakur!” Yace cikin sarkewar murya.

“Na’am!” Yaji Shakur ɗin ya amsa da irin amon sauti irin na Larabawan Asalin Muryar sa radau tamkar babu abinda ke damunsa yayinda fuskar sa ke fidda murmushi.

Maleek ya saki ajiyar zuciya daya fahimci ashe mafarki yake yi, ya dafa kansa yana komawa jikin kujerar da bacci ya dauke shi dazu, ya kalli agogo ya ga karfe 2:35am na tsakar dare ne, ya dafa kansa yace ” it’s a dream!”

“Me kace?” Shakur ya tambaye shi, maimakon ya amsa wa Shakur ɗin sai yace “kana lafiya Shakur? Babu inda ke maka ciwo?”

“Eh sosai ma, ban taɓa jin karfi kamar yadda nake ji yanzu ba, meka gani?”
Shakur ya tambaye shi.

Maleek ya ƙara sauke numfashi domin ya shiga firgici da mafarkin da yayi, kasancewar shi din ba ma’abocin yin mafarki bane, bazai iya tuna mafarkin karshen da yayi ba saboda dadewa”

“Kayi shiru, ko tunanin ta kake” yace yana dariya.

Maleek ya kalle shi, bai bashi amsar tambayar da yayi masa ba yace “Meyasa zuciya ta taki amincewa lafiyar ka lau?”

“Trust me Maleek na warke, gobe ku cewa likitan nan ya sallame ni mu koma gida hakan nan, domin daga kai har Daddy kun yi duhu saboda zaman asibiti, gayamin yanda ni na dawo, na dawo kamar gawayi ko?” Shakur ya fada cikin nishadi.

“Shakur stop all this muyi maganar lafiyar ka”

“Kai nace maka babu abinda ke damuna nama fi ka karfi yanzu haka, matso muyi hira kada maganar ta tada Daddy”

A yau bai san Meyasa barkwancin Shakur ɗin baya dada shi kamar baya ba, ya kai idanun sa ga Alhaji Dawood daya kwanta, yanda ya takure zai tabbatar wa mutum da cewa baya jin dadin baccin.

Maleek ya tashi da kujerar sa ya dawo kusa da Shakur sosai, ya riko hannun sa daya ji yayi dan sanyi yace “sanyi kake ji ko?”

“A’a” Shakur ya amsa.

Maleek ya jinjina masa kai, ya ɗan kwanto kansa hannun Shakur din kamar wani Maraya.

“Gayamin ya kake jin ta a ranka yanzu?”

Cikin hanzari ya dago yace “wa?”

“The mother of your daughter ” Shakur ya fada.

Maleek ya balla masa hararan wasa.

Shakur yayi dariya yace “da gaske nake fa, ka tuna alkawarin daka min?”

Maleek ya jinjina masa kai.

Shakur yace “Please marry her, ka aure ta. Shine kaɗai zai faranta raina ko da bana nan”

“Toh ina zaka je da kake cewa haka?” MALEEK ya fada cikin daure fuska.

“Nima zan je nemo tawa masoyiyar” Shakur ya Fada cikin wasa.

Amma shi Maleek he’s damm serious Dan haka yace “A ina take? Sai na raka ka muje tare”

Shakur ya dawo serious, yace ” ina alkawarin da ka min”

“Shakur Please duk ka bar wanna maganar, nifa ta lafiyar ka nake yanzu”

“Maleek nace maka na warke, Ni dai ka cika min alkawarina, Kuma ko da bana nan tare da kai, ina so na kasance tare da kai, ina son a kowacce safiya bayan ka iddar da sallar asuba ka min addu’a, koda baka min kullum kana yi min ko sau biyu ne a sati kaji” ya fada da murmushi da kuma hawaye kwance cikin idanun sa amma basu zubo ba.

Kan Maleek yayi matukar daurewa, ya kasa gane kan inda maganar Shakur ɗin ya dosa, wani Irin strange feelings yake ji a jikin sa.

A sanyaye ya dago, damuwa fal fuskar sa yace “wani irin magana kake haka Shakur?”

“Toh na daina” yace yana murmushi.

Maleek a ƙoƙarin sa na son cire wani abu mai kama da fargaba dake tasowa daga can Kasan zuciyar sa yace “tell Me kana da budurwar?”

Shakur yayi murmushi sosai yace “Munaya, itace budurwa ta” tun Kafin ya karasa maganar sa Maleek ya dago kansa cikin sauri ya bishi da wani kallo.

Sai yace “ba zaka so ta ba, wacce bazata maka rashin kunya ba zaka so, that girl bata da kunya” yace yana cije labbansa cikin tuna abinda ta ce masa ranar da suka zo asibitin.

Shakur yayi dariya sosai yace “Maleek ko dai kishi kake? Amma ka san me munaya is a nice and obedient girl zaka fahimci hakan wata rana”

Maleek ya mai shiru, domin ya rasa yanda zai yi da Shakur da maganar yarinyar nan da yake yawan masa.

“Ina da wacce nake so a raina, amma ban taɓa gaya mata ba, kuma ina ganin lokaci ya kure min yanzu, a school da nake lecturing take, her name is Safeerah ” ya fada yana rufe idanun sa.

“Meyasa kace haka? Dole ma zata so ka, because you are truly a rare gem, idan tayi gangancin kinka tayi wa kanta”

Shakur yayi murmushi ganin yanda komai Maleek sai ya nuna gadara da son girma, yace ” ba fa Dole, idan kuma taki fa? Tace bata son bakin saurayi ko miji?”

Sai da suka ji kiran asuba suka gane ashe sun jima suna hira, Alhaji Dawood ya farka saboda kiran sallar daya karade ko ina na asibitin kamar a ciki ake kiran sallar, Sai dai hakan baya rasa nasaba da shirun da ko ina ya dauka ne.

Alhaji Dawood ya mike ya shige banɗaki kana ya fito da alwala, kai tsaye ya nufi gadon Shakur “Barka da asuba dad, daddy”
Maleek da Shakur suka hade baki wurin fada, sai dai yanda kowa ya kira Daddyn ne ya bambamta.

“Mun tashi lafiya” ya amsa kana ya shiga tambayar jikin Shakur ɗin, ya Kuma ji dadin yanda yaga ƙarin kuzari a tare da shi.

Ya kalli Maleek dake kallon Shakur ɗin yace “je kayi alwala, sai mu saka Shakur yin tasa”

Maleek ya Mike kamar wanda aka zarewa jijiyoyin jikin sa ya nufi toilet, Shakur ya ɗauki wayarsa, ya shiga dinnawa, Tsawon mintuna biyar kana ya ajiye wayar, daidai lokacin shima Alhaji Dawood yaji Wayarsa tayi vibrating amma bai duba ba.

Maleek ya buɗe kofar toilet ya fito, sai ya ga Shakur ɗin na rike da counter’n yin tasbihi da alama lazimi yake, zai iya cewa a dukkanin rayuwar sa bai taba ganin mutum mai ibada kamar kanin sa ba tunda ba shiga mutane yake ba, Shakur baya da wasa da ibada even in the sick bed.

Maleek na sauke hannun rigar sa ya ji Shakur Cikin barkwancin sa yace “Malam ya haka? sai kallon na kake ko kyau na maka ne?”

Tilas Maleek ya murmusa, Alhaji Dawood yayi dariya irin tasu ta manya, ya zo ya daidaita sahun sa da Alhajin Dawood dake jiran sa, har zasu kabbara sallar yaci Shakur yace “Maleek!” Maleek ya waiwayo
Shakur yayi masa murmushi yace “Be a good boy okay? Ka zama yaron kirki, ban da fada” ya fada yana waving hannun sa wa Maleek kamar dai yanda ake wa mutum bye bye.

MALEEK ya zuba masa ido kawai, ji yake kamar ya koma jikin Shakur ɗin ya rungume shi ya yi kuka, bai taba sanin cewa yana da raunin zuciya ba sai bayan daya farka daga mafarkin da yayi, ga Shakur na masa maganganun dake kara raunata zuciyar ta sa.

Sallar daya ji Alhaji Dawood ya kabbara ne ya sanya shi juyawa ba dan Ya so ba domin yin Sallah.

A raka’ar ƙarshe cikin sujjada Maleek yaji karar faduwar abu, burinsa ya sallame Sallah ya ga menene, domin a sa’ilin da ya ji faduwar abun gabansa yayi mummunar bugawa.

Cikin Wani irin hanzari ya juyo, idanun sa ya sauka kan counter’n daya fadi kasan tiles, ya kalli Shakur sai ya ga idanun sa na kallon sama, kamar yana murmushi, ya kalli yanda hannunsa ya saki, ya mike da gudu ya karasa gadon yace “Shakur! Shakur!!”

Amma Shakur bai amsa ba. Ya riko fuskar sa a tafukan hannayen sa, cikin daga murya sosai yace “Shakur wake up!”

Sautin daya daga ne ya sanya Alhaji Dawood shima juyowa hadi da mikewa cikin sauri domin isa gadon”

🥺💔💔

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button