Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 42

Sponsored Links

XLII….
(42)

*MunayaMaleek is Five hundred via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566(idan baki shirya siya ba, don’t chat Me please)*

Hankalin Alhaji Dawood ya sake tashi musamman daya ji Muryar maman Edet tana cewa “Lallai sai ka aure ta, idan ba haka ba zan cigaba da tsine maka har jikokin ka, domin har yanzu abin bautar mu asari mandu na tsananin fushi da kai”

Related Articles

Ɗaya daga cikin mazan nan yace “idan ka yi taurin kai toh ka sani cewa mutanen kauyen mu zasu fito Domin ɗaukar wa Edet fansa, ba lallai ka fita daga kauyen nan a raye ba, lallai zaka aure ta ka biya sadaki, za kuma kayi duk wani abu da ma’aurata kan yi, sannan spirit (ruhi) din Edet zai bayyana zaka ganta da zarar abin bautar mu ta daura muku aure, sai ka zuba jinin bakin zakara a kan abin bautar mu sannan
ka tafi da matar ka, idan kayi hakan mun yafe maka”

Alhaji Dawood ya yi ƙasa da kansa, gumi na keto masa wanda har ta fara jike tsadaddiyar shaddar jikin sa, lallai ya fara girban abinda ya shuka tun a duniya, ta yaya zai iya yin dukkanin wanna abubuwan bayan shi din Musulmi ne, bai kuma ga tausayi ko imani a tare da su ba, nadamar irin rayuwar da yayi a Kuruciya yake, Hakan ya sanya hawaye fitowa Daga idanun sa.

Ya dago jin sun ce yana bata musu lokaci, hannun sa dake rawa ya haɗe su waje daya, yace “dan Allah ku yafe min, ku sassauta min, zan iya biyan ko miliyan nawa ne, amma bazan iya auren ta ba ko yin sadaukarwan jini ga abin bautar ku ba, domin Addinina yayi hani ga hakan”
Fafatawa suka shiga yi, amma Alhaji Dawood ya kafe bazai iya Hakan ba, har yamma suna abu daya, daga karshe suka nufi wajen abin bautar su domin jin ko ta amince da wanna bukata ta Alhaji Dawood.

A karshe dai suka rubuta masa dogon list din abubuwan da ake bukata na bikin, su doya, manja, barasa, gora, sa’a rago, zakara, Palm wine, kayan abinci da sauransu.
Gaba-daya lissafin kuɗin ya kai miliyan hudu da dori, bai ji komai ba ya biya domin yana matukar a yafe masa, tun a daren suka Fara bikin, gagarumin biki suka shirya mutane da yawa sun hallara, kamar ba dare ba, Alhaji Dawood na Daga gefe yana kallon su, a yau ya kara tabbatar da cewa lallai jahilci na nan har yanzu, a tunanin sa kowa ya waye da ilimi da addini ashe akwai dubban mutane da suke cikin jahilci, domin abinda da suka kira da biki ya kazance, an kuma cuci kalmar *biki* ina ma zai iya daukaka kalmar Allah ta hanyar kiran su izuwa ga Muslunci, amma baza su saurare shi ba tunda shi din mai laifi ne a gare su, duk da cewa sun furta kalmar yafiya a gareshi, ina ma malaman addini zasu zo wanna kauye da lallai sun yi babban jihadi domin Mutanen na hanyar bata.

Komawar tasa bai samu ba a ranar, ya kira Maleek domin sanar masa amma babu network, haka ya kwana a garin, sai a washegari ya shirya domin tafiya, ya sanya wa maman Edet damin kudi a hannun ta ta ki karba, yayi jim a tsaye, Duk da yana tausayin kansa, amma yafi tausaya wa maman Edet, jin alamun bai tafi ba yasa maman Edet tace “ka tafi, har raina na yafe maka, amma bana bukatar komai naka” tace hawaye na zuba a makatattun idanun ta.

jikin sa a sanyaye ya bar kauyen, domin duk da yayi abinda suke so hakan ba yana nufin komai ya wuce ba, lallai zai cigaba da yin addu’a da neman tuba wurin Allah domin ya yafe masa, lallai hakkin mutum, musamman irin na Edet ba wasa bane, lallai Iyaye ya kamata su farga, kada su Cutar da koma waye domin hakkin ba lallai ya tsaya iya kan su ba, har tattaba kunnen su zai iya shafa, kada kuma su raina hakki komai kankantar ta, yana addu’ar Allah ya sa abin ya tsaya iya nan.

Hajiya Sa’adah na zaune a dakin ta, ta janyo wayar ta ta kira Hajiya maimoona, sai data kusan katse wa ta daga. Kamar bata son magana tace “Hello”

Hajiya Sa’adah ta jinjina kai, lallai duniya, ita Hajiya maimoona ke wa haka, ta share hawayen daya zubo mata tace “maimoona amintaka tace haka? Ke wacce irin mutum ce, ace har yarona ya rasu ko gaisuwa ba zaki iya min ba?” Daga can bangaren Hajiya maimoona tace “toooo Allah ya jikansa”

“Abinda ma zaki ce kenan? Nayi nadamar sanin ki a rayuwa, Bayan kece mai bani shawara, sai da ƙaddara ta fada min sai ki juya min baya?” Hajiya Sa’adah tace cikin kunar zuciya.

“Toh me zance, ko nina ce ki bari su ganki, ai sakacin ki ne ya ja miki, baki iya takun ki ba, shiyasa har haka ta same ki, na bar hanyar ki domin bazaki ja min ba ina more rayuwa ta”

“Abinda zaki ce kenan? TOH idan har sakaci ya saka asirina tonuwa, kema ki gani a kanki, zaki gani kema in Sha Allah”

Hajiya maimoona tayi wani shewa tace “ba abin ba bakar muguwa, I’m very smart, asirina bazai taba tonuwa ba domin Ni din ba lusarar mace bace, na iya takuna, kuma wanna ya zama kira na karshe da zaki min, ki fita hanya ta!” haka aminan junan suka yi baram baram, Hajiya Sa’adah ta yi kuka ba iyaka, dalilin meye wa rudin duniya da zugar kawa ya kai ta ya baro ta, sosai take nadama a kurarran lokaci.

Maleek kuwa sai da yayi wata uku curr sannan ya koma Companyn sa bisa tilastawar Alhaji Dawood.
Rashin fara’ar sa ya ninku, magana idan baya zama dole ba sam Baya son ta, hakan yasa ma’aikatan Companyn sa ke kaffa kaffa da duk wani abu da zai bata ransa.

Bayan shekara ɗaya. Wata ranar juma’a da Misalin ƙarfe takwas na safe Maleek yayi parking harabar gidan doctor Aaban.

Ya fito daga cikin motar kai tsaye ya nufi Kofar da Zai sada mutum da falon ya kwankwasa, ya lumshe idanun sa, sosai yayi kewar angel din sa, domin tunda suka zo addu’ar arba’in bai kara ganin ta ba.

Bude kofar da aka yi ya saka shi bude idanun sa daga tunanin ɗaya faɗa na tuno lokacin da suke zuwa da Shakur, barrister Abrar ya gani, yace “ina kwana”

“Lafiya Lou” ta amsa tana mamakin dama ya iya gaisuwa amma bata nuna ba, ta bashi hanya tana cewa “Bismillah”
Ya bi bayan ta hadi da zama a kujera, shiru ya ratsa falon kana ya budi baki yace “zan dan fita da angel ne”

“Okay” barrister ta amsa, kana ta nufi dakin Munaya, ya ɗan waiwaya yana dube-dube kamar mai neman wani abu sai kuma ya jingina Bayan sa da kujerar da yake zaune ya rufe idanun sa.

Barrister Abrar ta tarar da Munaya na styling gashin little Amnah da ribbons masu kyau yayinda take sanye da doguwar riga kanti golden yellow sosai tayi kyau. Little na ganin ta tace “Mami nayi kyau?”

“Inyee yanmmatan Daddy , kinyi kyau sosai”
Little ta washe kyawawan haƙoran ta irin na Maleek tana dariya, Munaya tayi murmushi tana girgiza kai.

“To kije Daddyn ki yazo” ai wani uban ihu ta saki, Munaya ta saka hannun ta ta toshe kunne ta dasu, barrister ta Fara dariya.

Wani tsalle tayi ta dane jikin Maleek, yayi saurin buɗe idanun sa Yana murmushi sosai, yace “my angel”

Sai kuma little ta bata rai, cikin turo baki irin yadda yara ke yi tace “Daddy mun bata ma, tunda baka zuwa wajena kuma”

Ya shafa fuskar ta, shi kanshi ya san mai laifi ne dan haka yace “I’m sorry my angel, ki yafe wa Daddy kin ji?” Ya san bazata fahimce shi ba ko da ya mata bayani saboda ita din karamar yarinya ce.

“TOH na yafe maka”

Yayi murmushi kana ya sumbaci kamatun ta yace “thanks” ya mike ya riko hannun ta Yace “muje”

“Daddy, unguwa zamu?”
Ya jinjina mata kai.

Yana kokarin tada mota yaci tace “wai Daddy ina bakin Daddy na, bana ganin shi, Meyasa baku zo tare ba, Daddy tafiya yayi ko? Kullum mummy tana sallah sai inji tana kuka tana cewa Allah ya jikan ku Ummah, ya Shakur da Amnah, sai na ce mata kaiiiii mummy sunana fa kike kira, wai mene take cewa Daddy?” Little ta fada cikin yarin ta” Maleek yaji zuciyar sa ba dadi, ya tsakar mata murmushi mai ciwo kawai ya tada motar suka fice daga gidan.

*American International School of Abuja* nan ya tsayar da motar sa, makaranta ne mai matukar tsada, ya kalli little Amnah yace “zaki yi karatu ko?” Ta yi murmushin jindadin sosai tace “eh Daddy Ina son school” ya riko hannunta suka fita zuwa office ɗin shugaban makarantar akayi mata yan interview, ƙarshe dai aka sanya ta a pre-nursery one domin sun ganta so smart ga kuma surutun da alama kwakwalwar ta zai ja, nan ya biya kudin makarantar daya kai N3.2 Million.
Suka bata excerise books, textbooks, uniforms, sport wares da sauran Kayan amfanin makarantar.
Daga makarantar ya nufi supermarket da Ita, jaka, takalma da lunch box ya siya mata, hadi da kayan makulashe kana ya dawo da ita gida.

A lokacin da Munaya ta ga kayan tayi mamaki sosai domin she wasn’t expecting it, ashe zai iya daukar responsibility din sa a matsayin uba ga little Amnah, , she thought bazai yi ba, domin da ya Shakur na raye zata iya cewa shine ya saka ta ko bashi shawarar hakan.

Bayan little Amnah ta shigo da ledar kayan makulashen ta tace “mummy kije inji Daddy na”

“Ni?” Tace Cikin mamaki.

“Eh wai kizo”

Kiran me yake mata, ita me zata masa? Ta dai dauki hijab dinta ta saka, ta fito farfajiyar gidan, yana tsaye jikin motar sa, yanda ta ga fuskar sa a cure haka itama ta hade ta ta, ta zo dan nesa da shi ta tsaya, ya kalle ta kana ya ɗauke kansa yace “baki iya gaisuwa ba?”

Wani takaici ya kamata, ta kara haɗe ranta, ci kanka bata ce masa ba, abinda ya tsana kenan yayi magana a masa Banza.

Ya kara cewa “Kar dai ki koyawa yarinyata rashin kunya, i can see you lack respect”

Kasa kasa tace “ƙura ne yake cewa kare maye”

“Ya kalle ta cikin kankance ido yace “me kika ce, any way bana son ji, abinda zan ce miki shine a dinga shirya angel da wuri, ƙarfe bakwai daidai zan zo daukar ta ranar Mon…”

Ai bata jira jin rashin maganar sa ba ta bar wajen, sosai hakan yayi masa ciwo, ya cije labbansa kana ya bude motar sa ya fice daga gidan.

Ranar Litinin kamar yadda yace ya zo karfe bakwai daidai yana sanye da pyjamas red color da ratsin baki, little Amnah ta fito shirye cikin kayan makaranta tayi matukar kyau, kana ganin ta ka ga real definition of rich kid, ta rugo wajen babanta tana rungume shi, ya duka ya sumbaci kamatun ta yace “how are you angel?”

Tace “fine daddy” Munaya dake tsaye dan nesa da su tace “little zoki karbi Kayan ki”

Maleek ya rike hannun little ya kalli Munaya cikin ido yace “kawo mata”

Munaya ta tsaya tana kallon sa, sai kuma tace “ina ruwan ka TOH?”

“Da ruwana, domin yata kike so ta dauki abu mai nauyi, hakan kuma ba zai yu ba”

Domin ta kunsa masa takaici tace “sai ka samo mata yar aiki” ta fada tana ajiye lunch box da school bag din a nan inda take tsaye kana ta juya, cikin abinda bai fi taku uku ba ya cimma mata yace “mark my words, matukar kika cigaba da min rashin kunya kin kusan daina ganin ta, zan ɗauke ta daga gidan nan, zan kuma samo mata nannies ba daya ba” ya koma inda ta ajiye kayan ya duka ya ɗauka sannan ya nufi wajen motar sa domin baya son tayi latti.

Ɓangaren Hajiya Sa’adah kuwa, duniya yayi mata zafi, zaman gidan ya ishe ta, domin idan ba masu aiki ba ba wanda ke mata magana, ji take kamar ta bar gidan, amma tsoron sa take, domin barin ta gidan na nufin tonuwar asirin ta, wani amsa zata bawa mutane idan suka tambayi Dalilin mutuwar auren ta?

Wata Shida da fara zuwan little Amnah makaranta kenan, Maleek ya sake saka ta a islamiyya, domin ilimin addini da bai samu ba tun yarinta yake so yarsa ta samu, yana matukar kwadayin ilimin addini musamman iya karanta Kur’ani amma gani yake lokaci ya kure masa.

Kamar yau munaya ta shirya ta da wuri, kana itama ta shirya cikin uniform domin tana da school itama, ta yi kyau sosai, cikin uniform ɗin, ta saka farin glass, ta fito sak kamar malamar asibiti.

Sai dai har bakwai da mintuna biyar bata ji shigowar motar Maleek ba, ta kalli little Amnah tace “little zan bar ki tare da Mami tunda bai zo ba”

“Uhuhmmmm mummy ki jira yazo” little tace tana yin fuskar kuka.

Munaya ta ɗauki lunch box din little, sannan ta dauki jakarta ta rataya ta kuma rike jakar little Amnah a hannu, tayi wa Mami sallama suka fito farfajiyar gidan.

Daidai lokacin da wayar ta ya fara ringing, ta daga da sallama, daga can bangaren doctor Abbas ya amsa Cikin Muryar bacci yace “baby na kiyi hakuri, Bacci ne ya ɗauke Ni bayan sallar asuba”

Munaya ta sakar masa murmushi tace “ya Abbas ba komai fa, ai na san ka gaji sosai da sosai ne”

Shima ya sakar mata murmushi Hadi da cewa “amma gani nan zuwa, yanzu nan zaki ga na karaso”

Ta zaro fararen idanun ta ta kalli agogon hannun ta tace “ai zuwa lokacin na gama makara ya Abbas dina, ka bari xan hau napep, na ma fito, karka damu”

“Kin tabbata?” Yace mata cikin kulawa.

“Eh” ta amsa tana murmushi.

“Okay, I love you bye ”

“Love You too” ta amsa cikin kunya tana dariya, daidai lokacin ta ji mai gadi na bude kofa.

Ta saki ajiyar zuciya ganin motar Maleek, domin bata son makara ko kadan, cikin sauri Maleek ya fito daga cikin motar ya nufo Inda Suke tsaye, ya duka gaban little Amnah yace “my angel I’m sorry kinji yau Daddy ya sa kin makara, oya let’s go” yace yana karban jaka da lunch box ɗin little Amnah daga hannun Munaya da ko kallon sa bata yi ba, shima haka.

Little ta daga wa Munaya hannu itama ta yi mata bye bye kana ta nufi Kofar fita, ta gaida mai gadi, sannan ta bude karamin gate ta fice, tana cikin tafiya taji horn a bayan ta amma bata juyo ba, little ta cigaba da cewa “Daddy ka kira mummy mu tafi tare ” hakan ne ma ya saka yake mata horn amma take raina masa hankali bayan tana ji, suna zuwa daidai saitin ta little Amnah tace “mummyyy ki zo muje”

Munaya Ta girgiza kanta tana cigaba da tafiya cikin takun ta mai nutsuwa, yet mai daukar hankali.

“Dan Allah mummy ki zo ki shiga kinjiiii” little ta kara faɗa cikin magiya, Munaya ta yi gaba bata ce komai ba, ran Maleek ya ɓaci, shin me ta dauki kanta ne, saboda fushi ya wani ja motar da gudu suka wuce ta, ta bi motar da kallo tana tabe baƙin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button