Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 6

Sponsored Links

🍇MunayaMaleek 🍓

 

_by NoorEemaan_📚✍️

Related Articles

Vi…
(6)

Numfashi ta sauke a lokacin data ga likita ne ke tsaye a kofar gidan su, ta taka a nutse zuwa gaban likitan wanda ya ke tsaye kusa da motar sa ya kafe kofar fitowa da ido, da alama sumayin fitowar ta yake.

A sanyaye tace “ina yini” bayan ta isa gareshi.
Cikin sigar wasa yace “Bazan amsa ba, bayan ko sunana ba ki sani ba”
Munaya ta dago fararren idanun ta da Yawan kukan da take yasa ya rine ta zuba wa doctor, Da ace a lokacin baya ne, da a ce Amnah’n ta na raye da tayi dariya daya ce hakan, sai dai a yanzu farin cikin ta yayi kaura ba kuma ta san yaushe zai dawo ba, tayi kasa da kanta tana murza sirarran yatsun ta.
Doctor kuwa ya fahimci yanayin ta, ya kuma mata Uzuri yasan is not easy manta abu irin wannan musamman ita da akwai shakuwa tsakanin ta da kanwar ta, ya mata Uzuri, amma yana son ya zama silar rage mata damuwa, domin a kallo daya ya mata ya hango tarin ramar da ta yi, ya kuma san har da zaman kadaici ke kara mata damuwa, ya saki ajiyar zuciya a bayyane yace “ya karin hakurin mu?”
Munaya taji kuka na son kufce mata, ta daure tace “alhamdulillah!”
Doctor ya kara cewa “Allah ya jikan ta da Rahama, Allah yasa mutuwa ta zamo hutu a gare ta”
Munaya ta kasa amsa wa, kukan da take kokarin rike wa ya kufce mata, ta saka hijab dinta ta rufe fuskar ta dashi…

Likita ya rufe idanun sa yana yana jin yanda sheshekar kukan ta ke fita na taba zuciyar sa, ya bude idanun sa yace “ooh Munaya kuka kuma? Ki hakuri, Amnah bata bukatar kuka a yanzu, addu’a kadai take bukata daga garemu, kiyi hakuri Please”

Munaya ta shiga jinjina kanta yayin da ta saka hannun ta innocently tana goge fuskar ta.

Tsawon mintuna uku suna a haka kana doctor yace “daman na zo ne domin mu yi magana sosai Ni dake, sai dai har Yanzu na ga You re not your self, so zan bari next idan na zo sai muyi maganar”

Munaya ta jinjina masa kai alamun “toh” ya bude seat din bayan motar sa ya fito da ledoji guda biyu ya mika mata na farkon mai dauke da tambarin *amrish delicious snacks* yace ” ga wannan kayan kwalama ne na taho Miki da shi” Munaya ta girgiza kai hadi da cewa “Nagode”
Ya bata rai sosai yace “ai ba roko na kika yi ba, kuma in dai Kin dauke ni yayan ki kamar yanda na dauke ki kanwata toh ki karba” ya karasa hadi da mika mata ledar… Bata da kuzarin jayayya da mutum a halin da take ciki hakan yasa bata ƙara cewa komai ba.
Ya mika mata dayan leda da fadin “wannan kuma kudin ki ne wanda kika bari a office dina”
Kirjin Munaya ya buga sosai a lokacin data yi tozali da ledar data zuba kudin asibitin Amnah a ciki, taji tamkar an fama mata ciwon da ke ranta, ta daure ta karbi ledar tana jin wani tukuki a ranta, ta juya a sanyaye ta nufi cikin gidan, tana daf da shiga gidan ta ji Muryar likita yace “amma Munaya ina kika samu kudi mai yawa haka cikin kankanin lokaci?”
Wani murmushi daya fi kuka ciwo ta saki, hawayen da take ƙoƙarin rikewa suka balle mata, ba tare da ta juyo ba tace “i sold my virginity doctor, budurcina na siyar domin samawa Amnah lafiya, soyayyar kanwata ya rufe min ido har na manta cewa Allah shi ke rayawa ya kuma kashe, tsananin son da nake wa Amnah da kuma burin ganin ta rayu dani yasa na manta cewa babu wanda ya isa ya samawa bawa lafiya fa ce Ubangijin daya hallice shi, i so much hate my self, na tsani kaina doctor, ina kuma rokon Allah ya yafe min laifin dana aikata” Munaya ta karasa cikin kukan mai karfin sauti daya taho mata kana ta nufi cikin gidan da gudu. Bata da kowa, babu Wanda zata fadawa damuwar ta domin taji sauki a ranta, amma a Yau data samu ta fadi wani abu, she felt a bit relieved. Sannan bazata iya masa karya ba, toh karyar me zata yi da zata gamsar da shi dalilin samun kudi har 3.9m a cikin abinda bai fi awa biyu ba?.

Doctor ya fi mintuna goma a tsaye cikin matukar mamaki, lallai bai taba jin abinda ya daga masa hankali irin abinda Munaya ta fada masa ba, yaji ransa ya kai kololuwa a ɓaci, yana jin tamkar kanwar sa ta jini ce abin nan ya faru da ita, a fusace ya shiga motar sa ya tayar ya bar layin.

MALEEK!!!
Tun bayan faruwar al’amarin nan ya rasa nutsuwar zuciya, domin har sai ya sha barasa, tunanin sa ya gushe yake samun saukin zuciyar sa, ga Shakur da har yanzu baya kula shi abin ya ƙara damun sa.
Kamar yau zaune suke a dinning table su ukun, har da mummy, sai dai zaratan samarin babu annushuwa a tare da su, mummy dake serving din su breakfast sai a yanzu ta lura basa hira cikin kaunar junan su kamar yanda suka saba, Domin tun bayan dawowarta daga gidan malam ta shiga damuwa mai yawa, domin har karyan rashin lafiya tayi ta dinga zaman daki, domin idan tace zata bari su hadu da Maleek a ranar da abin ya faru komai zai iya faruwa har ta kai ta tona rufaffen sirrin dake zuciyar ta, wanda hakan zai sa komai ya lalace mata har ta kasa cimma burin ta.
Ganin shirun yayi yawa yasa tace “daddyn ku yace next week zai dawo” ta fada hoping zasu yi murnar da suka saba a duk lokacin da daddyn nasu zai dawo kasar, amma sai ta ga sabanin hakan, Shakur ne ya yi Karfin halin cewa “Allah ya dawo da shi lafiya” kana ya dire mug din hannunsa, ya mike hadi da cewa “na tafi mummy” bai jira amsar ta ba ya fita, nan mummy ta kara tabbatar da cewa something is fishy, Amma ta san bazasu fada mata abinda ke faruwa ba, domin ba a shiga tsakanin su, tun suna yara masu rike sirrin junansu ne, ta gwada Maleek dake juya cokali cikin mug mai dauke da coffee tace “my boy meya faru tsakanin ka da dan’uwan ka?”

“Ba komai mum” ya amsa hadi da mike wa shima ya fita.
Mummy tace ” i Said it, na san bazai faɗa ba, haka zalika dan’uwan sa” sai ta mike zuwa wajen window ta yaye labulen, daidai lokacin da Maleek ke kokarin bude motar sa, Shakur daya zo ta baya ya ɗan buge shi a baya, Maleek ya juyo, Shakur ya jefa masa hararan wasa, and then Maleek smile widely hadi da rungume dan’uwan sa, domin yasan tunda yayi hakan ya sauko daga fushin da yake dashi.
Shima Shakur ya rungume shi, domin yayi missing din sa kwana biyun nan, duk da ya ji matukar haushin abinda Maleek yayi, amma dan’uwan sa ne , is only brother, kuma hannun ka baya taba rubewa ka yanke ka yar, komai munin halin sa jinin sa ne” ya raba rungumar da cewa “muje ka fara ajiye ni a school sai muyi magana a mota” Shakur ya karasa maganar da zagayawa bangaren mai zaman banza.
Mummy ta koma da baya ta zauna kan kujera, ta na jin ina ma ina ma ta ji abinda suke cewa, ta shiga duniyar tunanin hanyar cimma burin ta.

A nutse yake tuki kan kwalta, Shakur ya kalle shi yace “ka min alkawarin ka daina shan giya”
Maleek ya rage gudun da yake, yace “zan yi kokarin dainawa Shakur, ka san I’m addicted to it, dainawa bazai yiwu a take ba, but zan yi iya kokari na wurin dainawa”
Shakur ya jinjina kai, ya san Maleek baya karya dan a so shi, kuma shi mutum ne irin open minded basa boye abinda ke ransu, duk da ba surutu ne da shi, a lokuta da dama ya kan kuma ce “Bazan taba yin abu domin wani ba”

“Amma kayi kokari saboda lafiyar ka da Allah, kasan haramune ko?” Maleek ya jinjina kai.
Shakur ya kara cewa “Sai alkawari na biyu amma sai Munaya ta dawo aiki zan faɗa maka, ina jin rashin lafiyar kanwar ta ne yasa bata yi resuming ba, amma hopefully zata iya dawowa this week”

Maleek ya dage kafadar sa, daidai lokacin da suka iso *Nile University* inda Shakur ke lecturing, Shakur ya sauka suka yi sallama.

****

A hankali Cikin rashin kuzarin da har yanzu bai dawo mata ba take tafiya, sanye take da dogon hijab dinta onion color, Saboda yanda tunani ya mata yawa ko nisan tafiyar bata gani, kafar ta yayi bututu. BAYAN ta iso Company’n Maleek Nura mai gadi ke tambayar ta ko lafiya kwana biyu bata zuwa, ta ce masa lafiya a takaice, bata ko biyewa surutun sa ba, ta nufi bangaren da office din Maleek yake, a yayin da take taka matatakalar benen komai daya faru a ranar ya shiga dawo mata, ta daure zuciyar ta domin bata son yin kuka, bayan ta isa ga kofar glass ɗin tana jiran kofar ta buɗe a lokacin ta hango Maleek zaune a had’add’en office din sa cikin sigar suit looking so smart and handsome as ever, taji mugun tsanar sa ya kara cika mata zuciya, har take jin tamkar ta rufe shi da duka, daidai lokacin da kofar ta bude kanta, a daidai lokacin ne Maleek ya dago rikitatun idanun sa ya zuba wa Munaya ko motsa su baya yi, fuskar sa dauke da wani yanayi da ba zai fasaltu ba, Munaya ta tako zuwa tsakiyar office din sa, ta fito da hannun ta dake cikin hijab mai dauke da ledar kuɗin nan ta jefa masa har ya daki fuskar sa, raunin ta ya fito fili Sosai, ta fashe da kuka, ta kasa daurewa tace “I hate you with passion! Azzulumi Ga kudin ka nan na dawo maka da shi, Amnah is dead, kanwata ta mutu, meya amfanin kudin ka a gareni, nayi nadamar baka budurcina, Allah ya saka min abinda ka min ban yafe maka ba Maleek!” Ta karasa maganar cikin dacin murya, kana cikin sauri ta juya ta bar office din.

Maleek!
A hankali bacin ran jefa masa kudin data yi a fuska da bakaken maganganun data masa ya rikide izuwa wani yanayi, yanayin da bazai fasaltu ba, saboda kai tsaye mutum baxai iya karantar fuskar sa ba, ya fi maka da wanda maganar Munaya ta tabashi har ya darsa masa wani abu a zuciya, musamman daya ji kalmar mutuwa a ciki, yet fuskar sa a dinke tsaf wanda kai tsaye mutum bazai iya karantar yanayin sa ba… Ya shiga murza hannun sa cikin na juna cikin sauri sauri ya mike zuwa kofa tamkar zai bita, sai kuma ya dawo ya nufi dakin da yake hutawa, inda a nan ne komai ya faru tsakanin sa da Munaya, kai tsaye ya nufi gaban cctv Camera ya zauna, ya yi tariya zuwa ranar daya kusanci Munaya, a yau ya nutsu ya kalli tun daga farko har karshe, idanunsa suka yi matukar kadawa zuwa jajawur tamkar an watsa masa jini cikin su…

_”Dan Allah dan Annabi kayi hakuri, wallahi Amnah kanwata ce bata da Lafiya, yanzu haka tana asibiti unconscious, tana da brain Cancer, likitoci sun ce kudin aikin da za mata 3.9millon, dan Allah dan Annabi ka taimaka min kada na rasa kanwata, wallahi na yarda ko a albashina ne na yarda kana cire har na gama biyan ka kaji?”_

_” i hate you with passion, Azzulumi ga kudin ka nan, Amnah ta mutu, kanwata is dead”_…. Kalaman Munaya ke dawo masa daki-daki, kansa ya ɗauki caji, ya ji zuciyar sa tayi nauyi, ya rasa tunanin daya dace yayi, ya mike zuwa box da yake ajiye kayan mayen sa, har zai bude ya ji Muryar Shakur tamkar yanzu yake gaya masa _”promise me bazaka kara shan giya ba”_ ya ji jikin sa yayi sanyi, ya ajiye box din, lallai neman mafita yake, so yake hankalin sa ya gushe ya manta kalaman Munaya masu matukar daci agareshi, but yana son rage shan giya, saboda yayi wa Shakur alkawari, ko da bazai daina ba, but at least he should try ya rage ko yaya ne” ya saka hannu ya rufe fuskar sa tsawon mintuna goma yana a haka ya ji zugewar kofar glass din sa alamun shigowa, ya kuma san Shakur ne domin babu mai shigo masa kai tsaye ba tare da izinin sa ba…

“Bro!” Shakur ya faɗa bayan ya buɗe Kofar da Maleek din kan huta a ciki, a hankali ya cire hannunsa daga saman fuskar sa Wanda hakan ya bayanna Halin da yake ciki.
“Subhnanallah!” Shakur ya fada yana zama a gefen sa, cikin kulawa yace “what happen Maleek?”

Tsawon mintuna uku kana Maleek ya kalli Shakur straight into his eyes yace “she came”

Cikin rashin fahimta Shakur yace “who came…?” Sai kuma ƙwaƙwalwar sa ta bashi yace “oooh You mean Munaya?” Maleek ya kafe sa da ido ya kasa cewa komai, cikin murna Shakur ya cigaba da dacewa “where is she, ban gan ta ba, ko ka aike ta ne?” Domin yana matukar bukatar ganin ta.

“Ta dawo da kuɗin nan, and she said kanwar tavta ta rasu”

“Innalillahi wa Inna ilahi raju’un!” Shakur ya faɗa yana dukan hannun sa cikin na juna yanda maza ke yi, yana mai jin matsanancin tausayin Munaya, ya mike hadi da kamo hannun Maleek yace “let’s go find her bro, ya kamata muyi magana da ita” Maleek ya mike ba musu ya bishi, ko za a titsiyeshi da wuka ba zai iya fadin takamaiman abinda yake ji a zuciyar sa ba, sai dai ya san kalaman Munaya sun dake shi matuka.

A mota suka dinga zaga unguwanni da layuka ko zasu ganta, amma ko mai kama da ita basu gani ba, gashi babu address din ta, domin haushin ta da maleek ke yi bai saka ya bata form na employee bare a samu address din ta a ciki ba, haka suka dawo cikin sakin guiwa, musamman Shakur da shi bai iya boye damuwar sa ba, sosai hankalin sa ya tashi, kasancewar bashi da zurfin ciki.

★★★
Munaya!!!
Bayan barinta office din maleek ta koma gida a kafa kamar yanda ta zo a Kafa, ta yi kuka sosai mara amfani, nadama kuwa ta yi shi babu adadi, ta rungume kayan Amnah da suke yan siraru cikin matukar kewar ta, a karshe ta shiga linke kayan daya bayan ɗaya, bayan ta gama ta zuba su cikin leda har da takalman ta, sai guda ɗaya data bari wanda ta siya mata ranar da ta siyi hijabai, ita kanta bata san dalilin ajiye takalmin ba, ta dai samu kanta da ajiye shi, ta sake fita babban titi, ta samu almajirai mata ta basu kayan sadaka da niyyar Allah ya kai ladan kabarin ta, haka ta juyo hanyar gida cikin sanyin jiki, iska na kada hijab dinta a yayin da take takawa, hakan ya sake bayyana loneliness din ta, domin kallon daya mutum zai mata ya hango damuwa, kadaici, da kewa a tare da ita.

★★★

“Ni na ga jaraba ni maimoona, Sa’adah zaki kashe kanki ne kan wanna yaron, toh wai in tambaye ki dole ni, bazaki iya hakura da shi ba” maimoona kawar mummy ke wanna maganar cikin jin takaicin kawar tata.

Mummy da ta dan yi zuru-zuru ta cire tagumin da ta yi, ta saki murmushin yake wanda yafi kuka ciwo da labb’anta da suka bushe, tace ” maimoon ke nan, bazan iya hakura ba, baki san waye Maleek ba, ni na san kalar namijin da nake farauta, toh bari ki ji abinda baki sani ba, wallahi na sha leken sa idan yana wanka bai sani ba, tashin hankalin da nake shiga idan na kalle shi yasa na daina leken sa, idan ana maganar namiji iya namiji ingarma mai kyakkyawar sura toh idan an samu my boy an wuce nan, ke dai bani mafita kawai, domin harkar malaman nan ba son shi nake ba, ke kika kwadaita min, gashi ya ja min matsala har kiwon da nake yi domin kaina kadai wata ce can taci moriyar sa”

Hajiya Maimoona ta ɗan harari mummy, domin haushin yanda ta kwallafa rai akan Maleek take ji, ta gyara zamanta, cikin salon duniyan ci tace “Toh kawai ki fito fili ki fada masa abinda yake ran ki, ayi a wuce nan, a toh shi yaro ne da zai ce bai gane karatun ba, idan ma bai gane ba ganar da shi, ki fito masa da abinda yake ranki, ki kuma kwadaita masa Sa’adah”

“Anya k’awata zan iya? Kina ganin ba za a samu matsala ba, kin san dai yanda suka shaku da Shakur sosai, ga shi da bin diddigi bana son a samu matsala” mummy ta fada.

“Wai ma wannan lusarin mijin naki meye amfanin sa, shine kullum yawon kasuwanci kasashen waje tamkar akan sa aka fara neman arziki” Hajiya Maimoona ta faɗa tana harare harare tamkar daddyn su Maleek ne a gaban ta.
Mummy maimakon ta kare mutuncin mijin ta sai tace “ke rabu dashi, ni mutumin nan haushi yake bani wallahi, gashi wai ya kusan dawowa, Ni Wallahi bana son ya rabe ni, domin baya tsanana min abin arziki, dashi da babu duk daya, ayi mutum bai iya komai ba, ga kudi dai a gida kamar zasu yi magana amma babu gams…” Mummy ta kasa karasa maganar cikin jin takaici har cizon yatsan ta take.
Hajiya Maimoona ta mike tsaye tana rataye tsad’add’iyar jakar ta hadi da sanya glass din ta, kallo ɗaya mutum zai mata ya hango budewar ido a tare da ita, ta kalli mummy tace “Sa’adah kiyi tunani sosai kan maganar nan, ki fito muraran ki nuna masa abinda yake ranki, shine kawai mafitar da nake hanga miki” ta karasa da barin falon mummy cikin takun kasaita irin na gogaggun mata yan duniya…

 

Wattpad@NoorEemaan
@Arewabooks @nooreemaan
Whatsapp:07082281566

 

Thank you for reading my story.

07082281566

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button