Hausa NovelsNi da Almajirina Hausa Novel

Ni da Almajirina 8

Sponsored Links

NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)

Episode 8

Ina kwance rijib rufe da abin rufa, HajjahKaka na kusa dani sai tofin addua take min, sai muka ji salmar Baana.

Related Articles

HajjahKaka tace ga fa tsinanen… kawai ta hangama baki tana kallon sa, tama kasa karasa maganar dake bakin ta, can ta kallo ni tace Falmata ina Baana? Ba de Baana ne ya zama wannan tokareren kato ba?

Murmushi da be shirya yi ba, Baana yace inda watu?

Inna lillahi wa ina ilaihir rajiun Baana ne ya koma haka sai kace basamude ? Ah lalle kam tunda kun dauki hanya kafurci dole ku koma kama da kafuran farko, yanzu Falmata, Almajirin naki ya koma haka? HajjahKaka tayi maganar tana kare masa kallo

Takowa ciki Baana yayi, ya nufo inda nake, HajjahKaka tayi saurin dakatar da shi, ko da bani da kafa walh baka isa ka zo kusa da Falmata nayi shiru ina kallon ka ba. Kai ba kungiya koma me ka shiga Falmata tafi karfin ka..

A kausashe Baana yace ta samu taci abinci kuwa?

Ciki da mamaki HajjahKaka tace wai ko ba Baana ba ne me warin gawasa? Yo dan ka shiga wata training tsiya, ba shi ze hana na cima mutunci ba, yaushe kayi klin har ka fara wanka da buroshi? Ina zuwan Falmata ne? To tsaya ka ji wannan takarda da kudin da kuka kawo a banza dan ni jikata ba tayi aure ba ehe.

Wani irin mugun kallo ya bita da shi da yasa HajjahKaka shan ruwan jinin jikin ta, a kausashe Baana yace HajjahKaka zan iya jure kome amma banda shiga tsakani na da matata duk wanda yace zai rabani da ita to zai bakunce lahira yana fadin haka yaciro wayar sa daga aljihu ya kuna video sannan ya kawo wayar daf dani

HajjahKaka tuni ta natsu dan daga maganar sa zaka gane cewa he meant what he said.

Inna lillahi wa ina ilaihir rajiun please don’t do this to me, they’re all I have, nayi magana ina kuka, baice dani kome ba, sai mikewa da yayi ya nufa idan abinci yake, ya dauki plate ya zuba hade da hadowa da ruwan sha, ya dawo in da nake ya ijeye gabana, umurce ni yayi da na tashi na ci, ba shiri na mike na fara ci ina hawaye

Sai da na cinye kome tass kafin ya bani ruwan na sha, HajjahKaka kam sai ido dan abin ya bata madaukacin mamaki.

Idan kina son mahaifin ki da kaninki su rayu to ki zama a raye idan bahaka ba,ba iya su zan taba duka dangi ki zan kashe. Baana yayi maganar da authority

Zanyi duk abin da kace but please don’t hurt them, nayi magana ina kuka mai cin rai.

Hmmmm kin sha magani? Yayi maganar with a straight face.

Amsawa nayi da eh.

HajjahKaka ki kula min da matata na baki amanar cinta da shanta in har bata ci abinci sau uku a rana ba sai na fasa kafar ki da bindinga.

To li’illah fi quraish, kai kar fa kaga nayi kuri ina kallon ka,ka dauka jan idonka yayi tasiri akaina?to wa ke tsoron mutuwa? Wani dare ne jemage bai gani ba?
Kabi ni fa a hankali kar na zazzaga maka buhun bala’i da wani fuska agun kamar jikaken pampers na yara.

Murmushi da be shirya yi ba, Baana yayi, mutum ba kafa sai baki yayi magana cikin ransa kafin yabar daki..

Yana fita na dawo kusa da ita ina mai kuka, HajjahKaka Walhi yasan inda su Najib da Abba suke, yanzu ya nuna min video su.

To sai akayi yaya? Ke fa kin fini sanin cewa kasan turai da nan ba daya ba, can a kan kashe bera wannan sai a maka ka makarkama to bare ace mutum, dallah manta da wannan bahon..

Ban ga alamar wasa ba a fuskar sa HajjahKaka. He truly mean it.

To ai sai kiyi, a haka zai ta tsorata ki har ya samu ya daga fatarin ki ya dura maki ciki,kin ga daga nan idonki ya bude,idan zaki daina wannan koke koke ki zama jan wiya tsaf zaki mallake shi dan naga yana mutuwar sonki ato wannan kuka ba shine ba, mu bakaken fata mun saba gwagwar maya da irin su. HajjahKaka tayi maganar tana goge min hawaye

Shiru nayi ina nazarin abinda HajjahKaka tace, can nace ya zanyi in zama in control of him?

Kiyi min da hausa yadda zan gane dallah, HajjahKaka tayi maganar cikin tsiwa

Ya zanyi na mallake shi? Nayi maganar ina kallon ta

HajjahKaka tace ahab cikin ruwan sanyi zaki mallake shi, sabida yana musiban sonki kuma zuciyar sa gaba daya kece, a hankali HajjahKaka ta dinga karanto min yadda zanyi har mu samu damar kubuta daga hannun su

Nafi minti goma ina nazari can, nace to shikenan HajjahKaka zanyi yadda kika ce indai hakan ne mafita a gare mu.

Ko ke fa? Amma da kin mayar da kanki Dodi minal Dodi sai abinda yace za kiyi? Ai wannan ba halin kanuri asali bane, ai tsoro ba naki bane Falmata.

To HajjahKaka zanyi yadda kika ce.

Oh oh Falmata ashe Baana kyakkyawar mutum ne? Jiba yadda yayi shadaudau dashi kamar ba Almajirin ki ba? HajjahKaka tayi maganar tana jiran abin da zance.

Nikam shiru nayi ina tunanin ya zata kasance idan shawarar HajjahKaka tayi tasiri agun sa,duk na kosa nabar nan, na koma gun Abbah nasan suna cikin damuwa.

Damasak
Gidan Dr Bukar
Ba karamin sha’ani ake yi a gidan ba, kasancewa yau ne yake aurar da babbar yarsa, gidan cike yake dam da jamaa ga kuma hadari ya hararo.

Wayar Ummu Salmah ne ya fara kukan kiran, cike da mamaki Ummu Salmah ta amsa kiran hade da cewa Ya Baanaliye ina ka shiga?

Ba tare da bata lokaci ba Baana yace kubar duk wani abu da kuke yi kubar gidan nan yanzu,ku tafi gida na cikin gari yana gama fadin haka ya yanke kiran..

Cikin rawan jiki Salmah taje ta same mahaifiyar su abin da yayan nasu yace,amma kowa yayi kunen kare da ita, ganin kowa yaki kulata ta deba ya’yan ta tayi gaba dasu dan ko ba ace ba tasan gari ba lafiya,

Suna tsaka da sha’anin Babagana dake fama da Zazzabi ya nufa parlor Baban nasu, kai tsaye yace Baba suna hanya kuma wa inan yan wani gari ne ba lalle su gane ni ba.

Cike da mamaki Baban yace su wa kenan?

Babagana yace sojojin jihadi, don Allah Baba ka tatara su, ku koma cikin gari, nima gudowa nayi daga kungiyar amma Baana yana can

Cike da mamaki Baba yake kallon sa,dan shi yakasa gane abinda Babagana yake nufi, ko de zafin ciwo yake sa shi sumbatu
Amma ya ga damuwa da fargaba rubuce a fuskar sa, ba shiri Baba yaje sanar da mutane ciki amma Atine tace sam ba inda zasu,

Yaya idan ma jitai jitai da kake ji a yanki Bama ne kake so ka bata wannan rana gaskiya zamu yarda ba.

Suna cikin magana kowai su kaji….

 

Pharteema(DMK)
THANKS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button