Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 34

Sponsored Links

Khalil na shiga parlon Abbansa bai bari suka hada ido ba, yana tafiya a hankali ya zauna saman lallausan Carpet dake kasa, yayi gathering courage yace “Barka da dare Abba” Shirun da Abban nasa yayi yasa a hankali ya daga kai ya kallesa yaga jaridar hannunsa kawai yake dubawa, ya sunkuyar da kansa, bayan kusan minti biyu Abba ya ajiye jaridar hannunsa yana kallonsa a takaice yace “Wani international joint ventures na wata daya zaka min handling a Zanzibar, and the business isn’t new to you, you know everything about it, so u can chose to stay there in Zanzibar or come back to Nigeria weekly, bayan kayi min sorting komai zaka iya komawa duk inda ka fito ka ci gaba da rayuwarka since it’s the best for you and you are okay with it, i will neva beg you to come stay here!!” Yana gama fadin haka ya mike ya shiga dakinsa Khalil ya bi sa da kallo, sai gashi ya fito da files ya jefa masa nan kasa yace “Everything u will be needing is there, u can leave my sight now” Khalil ya dau files din a hankali yace “In sha Allah, Nagode Abba” Daga haka ya mike ya nufi kofa Abban nasa ya bi sa da kallo har ya fita, yana fita ya juya suna hada ido da Abba, Abba yayi saurin juyawa ya shiga bedroom dinsa. Har Khalil ya shigo parlon Mami na tsaye ta kasa zaune sai kai komo take a dakin, she is so disturbed and worried, Allah ya sa kiran alkhairi yake masa, tana ganin Khalil ya shigo ta nufesa da sauri tace “What did he say to you??” Khalil ya mika mata files din hannunsa ta amsa tana dubawa da sauri, can ta kallesa tace “What about this?” Yace “He wants me to be in charge” Mami ta dinga Kallonsa babu ko kiftawa can tace “He said so?” Khalil yace “Yea” Murmushi tayi ta rungumesa tana hamdala a zuciyarta amma ta kasa cewa komai hawaye ya cika idonta, ta sakesa tace “Yanzu yaushe zaka tafi?” Khalil yace “I need to prepare” Tayi kasa da murya da damuwa tace “Zan so ka shirya first thing in the morning ka bar gidan nan kafin wani yayi noticing dinka, har yanzu basu san u are around ba, nasan shi ma bai sanar masu ba” Khalil bai iya yace mata komai ba, ta goge idonta tace “Shigo ka ci abincin yanzu, i am so happy at this good news” Ta kama hannunsa suka wuce can bedroom dinta, tsaye tayi bakin kofa da mamaki tana kallon Nihad da ko motsi bata yi daga inda take ba balle ta ta6a abinda Mami ta zuba mata a gabanta, Mami ta kalli khalil tayi kasa da murya tace “Are you sure zata yarda ta kwana nan son? She hasn’t taken anything yet, are sure baxaka duba ko da akwai flight going to kano a yankar mata ticket ba?” Khalil dai sai kallon Nihad yake, Mami tace “Do so before it’s late plss, kasan wasu nature ne hakan basu sakewa a wani waje ba gida ba, so kar a takurata” Juyawa tayi ta fita daga dakin, khalil ya duka dab da ita yana kallonta, kin yarda su hada ido tayi, lkci daya yaga hawaye ya ciko idonta, still looking at her yayi kasa da murya yace “Where u offended in anyway?” Ta kallesa sai kawai ta fashe da kuka sosai, cikin karfin hali tana magana da kyar tace “Don Allah… Kayi hakuri ko a motor park ne ka kai ni ka sa ni a motar Jigawa in tafi wajen Aunty Jamila, don Allah kayi min wannan last alfarman” Tana kuka me ban tausayi ta fadi hakan, sai kuma ta hade kanta da gwiwa, yana ta kallonta kafin yace “An maki wani abu ne a nan din da za ki tafi jigawa?” Ta daga idanuwanta da hawaye ke zuba tana girgiza kai tace “Ni bance an min komai ba” ya dau duk abincin da Mami ta sa mata a plate ya kai parlor sannan ya dawo yace “Fito ki ci” Tace “Ni na koshi” Yace “Fito nace” Mikewa tayi trying hard not to burst into new cry ta fito daga dakin ta tafi ta zauna inda ya ajiye abincin, ta hadiye wani abu da ya tokare mata throat da kyar, Yana kallonta yace “Now eat” Bata san sanda kukan ya subuce mata ba tana girgiza masa kai, ya hade rai yace “Kee” ta daga ido da sauri ta kallesa, ya durkusa yana kallonta, sai kuma ya ciro handkerchief ya mika mata, Da sauri ta sunkuyar da kanta, ganin har sannan mika mata handkerchief din yake ta kai hannu a hankali ta amsa, ta goge hawayen da ke zuba idonta da shi shi dai kallonta kawai yake, bayan ta gama goge idon ta daga kai a hankali tana kallonsa, ya sauke idonsa ya matsar da plate din abincin gabanta, ta kalli cokalin dake cikin abincin ta dauka ta diba ta kai baki a hankali ta fara ci, mikewa yayi ta bi sa da kallo har ya fita zuwa next parlor din, gaba daya taji baxata iya cin abincin ba, she has clearly run out of appetite, this is the third shock of her life so far, but this particular one is so strong and it’s about giving her heart attack, of all the shock, this made her felt bata da sauran hope a duniya, this made her loose all hope, she now believe she is now all by her self a duniyan, kwakkwaran wata daya ba ayi ba ta girgiza da lamari har kala uku, yanda take ji a ranta ta kara tabbatar da bata da wani sauran gata kuma a duniya, ganin komai take kamar mafarki amma ita dai tasan ba mafarki take ba, this is nothing but reality, bata ta6a jin ta tsani kanta duk abubuwan dake faruwa ba sae yau, she hate herself for everything so far, ta daure ta tashi da kyar ta mayar da duk abincin cikin warmer dinsu ta fito don tasan baxata ta6a iya ci ba, ta zauna kasa ta jingina da kujera, ko sanin hawaye na zuba idonta bata yi ba. Khalil na zaune first parlor da Maminsa dake waya da sister dinta, she is happily telling her that he is back, daga nan kuma ta kira aminiyarta warce kasar su daya and she is always there for her at all time, shi dai khalil kallonta kawai yake har ta katse wayar, Mami ta mike tace “An samu jirgin kuwa son?” Ya girgiza kai yace “Aa Mami” Tace “Toh gobe first thing sai kayi mata booking ticket kafin ka tafi koh?” Khalil bai ce komai ba, Mami ta koma can ciki, ba a dau lokaci ba sai gata da plate din abinci ta zubo masu, tare suka ci abincin, ya ci peppered chicken din kawai a maimakon pepper soup yace mata ya koshi, Mami ta kira Bilkisu ta kwashe duk abubuwan ta fita da su daga part dinta. Karfe tara da rabi Mami ta shigo parlon da Nihad take tana kallon Nihad tace “Toh ki tashi kiyi wanka don ki ji dadin jikinki ko?” Nihad ta mike tsaye ba tare da ta bari sun hada ido ba, Mami dai sai kallonta take, ganin ta nufi kofa tace “Ga bandaki nan a bedroom” Ta girgiza kai tace “Zanyi a na parlor” Daga haka ta fita daga parlon zuwa daya parlon wanda bandakin ke ciki, tayi hakan ne sbda la’akari da tayi da Mumynta, bata sharing bathroom din dakinta da kowa, khalil dake danna waya ya daga kai ya kalleta, tun da ta kalli iphone din hannunsa bata sake kallon direction din nasa ba, yaga ta shiga bandaki, Mami ta shigo parlon ta kirasa ya mike ya bi bayanta, suna tsaye parlon farko tace “Toh yanzu a haka da taki sakin jiki zan kai ta bangarensu Mimi?” Yace “Aa Mami ki yi mata shimfida kawai a parlor nan ta kwanta” Mami tace “Aa haba dai, ya zata kwana a parlor, abinda yasa kaga bance zata kwanta nawa bedroom din ba i am leaving it for you kai ka kwanta, ni zan je in kwanta wani wajen” Yayi Murmushi yace “Aa Mami ba sai kin bar min gadonki ba, kawai ki kwanta ni zan kwanta parlor, kema kinsan i prefer sleeping on the couch” Tace “Toh shikenan sai mu kwanta da ita a daki, let me get her sleeping dress wajensu Mimi….” Daga haka ta fita sai gashi ta dawo da sabuwar rigar bacci na Noor ta kai dakinta ta ajiye ma Nihad a gefen gado da tsadaddun spray biyu sannan ta fito, Nihad na fitowa daga wankan taki shiga dakin, shi dai yana ta danna wayarsa, ta rakube jikin kujera, Mami ta fito parlon zata ma Khalil shimfida, ganin Nihad a rakube tace “Baby shiga ciki ki shirya, za ki ga sleeping dress da turare na ajiye maki saman gado” A hankali Nihad tace “Nagode” Daga haka ta shiga dakin, Shimfida me lafiya Mami tayi ma Khalil a parlor na biyu, shi dai bin ta kawai yake da kallo, yasan yayi kewar Maminsa fiye da zatonsa, he so missed all this, har bedroom dinsa Mami kan shiga ta gyara masa back then, tana gamawa ya mike ya nufeta yayi mata side Hug cikin sanyin murya yace “Thanks Mamina” Tace “Ai kai ma zaka yi wankan ko?” Yace “Sure” Tace “Let me get u ur pajamas” Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo, sai kuma yayi murmushi ya shiga dakinta don shiga banɗakinta yayi wankan, zaro ido Nihad tayi ta rufe jikinta da kayan baccin da take kokarin sakawa ta durkusa kasa da sauri ta rufe fuskarta, ya sauke idonsa ya juya ya fita daga dakin, bandakin da tayi wanka ya shiga kawai, Mami ta ajiye masa pajamas din saman inda tayi masa shimfida bayan ta dawo ta tafi dakinta, dariya Nihad ta bata ganin yanda ta rakube kasa jikin dressing mirror bayan ta saka kayan baccin, Mami tace “To tashi ki hau gado ki kwanta” Nihad ta kalleta da sauri cause she never expect it, can tace “Aa zan kwanta a kasa” Mami tace “Common hau gado kiyi kwanciyar ki Baby” Shiru Nihad tayi sai kuma ta mike a hankali ta tafi ta hau saman babban bed din wanda furnitures dinsa kadai ma abun kallo ne, Mami ta dago mata duvet ta mika mata ta amsa ta rufe jikinta ɗon dakin yayi sanyi ta dalilin Ac dake kunne. Har kusan karfe dayan dare Nihad bata ga bacci ba, tuni Mami tayi bacci, da ta tuna wasu abubuwan sai taji hawaye me zafi ta gefen idonta na zuba, she wish she could rewind everything from the scratch, she wish many things didn’t happen, daga karshe da taga she needs to cry out ko zata samu saukin abinda take ji a ranta, cike da karfin hali ta mike zaune tana kallon Mami cikin duhu, a hankali ta lallaba ta sauka daga kan gadon ta tafi bakin kofar, nan ma ta tsaya tana tsoron kada kofar yayi kara idan ta bude har ya farkar da Mami, can dai ta runtse ido ta kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude, bata ji yayi kara ko kadan ba, ta fita ta kullo mata kofar, yana kwance parlon nan ma wutan a kashe yake, a hankali tana tafiya making sure she isn’t making any sound ta tafi ta bude dayan kofar ta shiga daya parlon, can wani corner ta tafi ta zauna tana shesshekan kuka cike da tausayin rayuwarta, hawaye kawai take wani na bin wani, tun da ta fito daga dakin Khalil da shi ma bai yi baccin ba ya bi ta da ido cikin duhun har ta tafi daya parlon, he can’t say why he is still awake may be over excitement ne na cewar yau gashi a gida da Maminsa after some years, bayan kusan minti 7 ya mike a hankali, shi ma bai kunna wutan ba ya nufi kofar ya bude gently ya fita, ta direction da yake jin shesshekan kukanta ya nufa, kawai gani tayi wani abu da yayi mata kama da statue tsaye a kanta, er kara tayi a mugun tsorace ta mike xata gudu ya rikota, sai a sannan ta ji kamshin turarensa ta rufe fuskarta da sauri a jikinsa tana kuka a hankali, bayan few seconds yace “Saboda kiyi kuka kika fito nan?” Ita dai bata ce komai ba sai shesshekan kuka take tana Girgiza masa kai kawai, ya janyeta jikinsa yace “Zauna nan” ta tattaba bayanta taji kujera, hakan ya sa ta zauna a hankali, yana tsaye inda yake yace “Ki saurari duk abinda zan ce maki yanxu cause it’s for ur benefit” ita dae tayi shiru tana jin sa gabanta na faduwa, yayi kasa da murya yace “On no condition xa ki gaya ma wani a gidan nan relationship dinmu, that should be s secret between us har zuwa sanda xa mu cika ma juna alkawarin da muka dauka a baya” Nihad dai kanta na kasa, yace “Nace ma yan gidan admission letter kika zo amsa garin nan, so duk abinda zaki ji na gaya masu gobe ya zama hakan kema a wajenki” Nihad ta share idonta ta gyada masa kai kawai, ya kunna wutan parlon yana kallonta yace “Sai da safe” Bata yarda sun hada ido ba ta mike ta nufi kofar shiga second parlon Mami ya jira har ta shiga sannan ya bi bayanta. Washegari Nihad na tashi taga ita kadai ce dakin Mami, tana kokarin gyara gadon sai ga Bilkisu ta shigo, Bilkisu na murmushi tace “Ina kwana” Nihad ta sauke idonta tace “Mun tashi lafiya” Bilkisu tace “Ai da kin bar shi ma xan shigo in gyara, aikina ne” Nihad dai bata ce mata komai ba ta shigo ta fara abinda zata yi, Nihad ta fita parlor, tana bude kofar first parlor taga Mami da khalil a zaune parlon, Ta gaida Mami da ladabi Mami ta amsa mata da fara’a, ta kalli Khalil suka hada ido, ta kasa barin wajen bata gaishesa ba saboda Mami dake zaune, bata yarda ta kallesa ba tace “Ina kwana?” Yace “Lafiya, ga breakfast din ki” Mami tace “Bari a kai mata can parlon so that she will be comfortable” Yace “Aa za ta yi a nan” Nihad dai bata ce komai ba, can ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, ya nuna mata breakfast din dake saman tray, ta dauka ya nuna mata inda xata zauna, Mami dai sai bin ta da kallo take because she is so cute and meek, Mami ta kallesa tace “Amma ‘yar mai gidan da kake ce min kana zama wani lokacin a gidansa ce ko?” Khalil zai yi magana aka bude kofar parlon, Mimi da Noor ne suka shigo, suka yi wani ihu a tare ganinsa, daga inda yake zaune duk suka tafi da gudu suka rungumesa so happy seeing him, sai ga wasu set din Yan matan biyu Hanan da Farhana, su ma duk suka rungumesa so so happy seeing him, he couldn’t help it but smile don shi ma yayi kewansu sosai, Mami dai sai murmushi take, Mimi ta kalli Mami ta fashe da kuka tace “Mami mene ya sa zaki boye mana yayanmu ya dawo, Abba yace he’s been around since yesternight” Sai kuma ta fashe da kuka, Khalil ya jawota gefensa yana kallonta yana murmushi yace “Is there any diff between now and the yesternight” Tace “Yes of course, wallahi da nasan kana nan nima a nan zan kwana jiya, i soo miss you yayanmu” Tana fadin haka ta kara rungumesa tana hawaye, Nihad dai sai bin su take da kallo kana ganinsu kasan su ne ainahin rich kids din, duk Mimi ta fi kama da shi, Noor ma fara ce Farhana da Hanan ne kadai haskensu bai kai nasu Mimi ba, Farhana sai kallon Nihad take keenly, can ta kalli Mami tace “Mami who is she?” Mami tace “Our visitor” Tambayarta ne ya ja hankalin sauran yan matan suka kallo inda Nihad ke zaune, Noor ta ɗan juya ido tace “Ohh She looks familiar” Hanan dai kallonta take babu ko kiftawa kamar me son gano wani abu, can ta ja Noor suka fita daga parlon tana zare ido tace “Kin tuna wata yarinya da video dinta ya tafi viral weeks ago?” Noor ta zaro ido bayan tayi recalling video din tace “Ohh yess!! exactly, wallahi suna kama sosai, i think baxan rasa video din a thrash bin dina ba” Tun da Khalil yaga sisters din nasa duk sun yi concentrating kan Nihad, yace “Ohk, ohk now, i need rest za mu hadu anjima a main parlor…” Mimi tace “Yayammu who is she, nima kamar na santa” Mami tayi dariya tace “A ina kika santa, banda karya Mimi” Mimi ta juya ta sake kallon Nihad da ta sunkuyar da kai gabanta na mugun faduwa don banda nude video dinta babu abinda ya fado ranta, mikewa Khalil yayi yace “Mimi za mu hadu anjima a main parlor, i said i need rest, ku fita” Sai ga Noor da Farhana sun shigo da gudu parlon, Hanan ta biyosu da sauri, Noor ta nufi Mami har tana tuntube tana mika mata wayarta tace “Mami u remember this???” Mami ta amshi wayar ganin video din da take nuna mata tace “Wai ba nace ki goge video din nan ba Noor? What is it still doing a wayarki?” Noor na zaro idanuwanta kamar za su fito tana nuna Nihad tace “Ba ita bace warcan” Mami ta kalli Nihad da sauri, sai kuma ta amshi wayar tana kallo, Kasa cewa komai Khalil yayi, Nihad da jikinta yayi sanyi kamar warce aka kwara ma ruwan sanyi ta kasa kwakkwaran motsi inda take zaune ta dinga bin su da kallo kamar warce tayi ma sarki karya, sai kuma ta sunkuyar da kanta with tears in her eyes, Mami ta kalli Khalil da sauri, sai kuma ta kara kallon Nihad, tuni Farhana ta tafi ta kirawo wasu set din yan mata biyu duk suka tsaya bakin kofa ko warce da wayarta a hannu, da ta kalli videon sai ta leko ta kalli Nihad baki bude, Mami da ita kanta jikinta yayi sanyi qlau ta kara kallon Khalil that is saying nothing, can ta hadiye wani abu tace “No, no may be resemblance ne kawai, ai akwai resemblance” Noor da Farhana suka wani gwalo ido har suna hada baki suka ce “Mami wallahi ita ce, the video is so clear fa ba wai yayi dishi dishi bane, ki duba mana ki ga, ita ce wllh” Da sauri Hanan ta tafi tana mika ma Mami waya wai don ta kara gani da kyau, Mami ta ki amsar wayar bata kuma sake cewa komai ba, Sajida tace “Ikon Allah, then who brought her to this house? Ance yar Maryam Abatcha American University ce fa” Mimi dake tsaye gefen Khalil ta kallesa a hankali tace “Yayanmu who is she?” Bai ce mata komai ba yana bin sisters din nasa da kallo ya nuna masu kofa yace “Ku fita” Farhana ta kyabe baki haka ma Hanan duk suka juya, Noor ma tayi ficewarta, Mimi ta dinga kallon Nihad dake ta hawaye, Ita ma ta fita daga parlon, Mami dai mutuwar zaune tayi a inda take. Daga karshe ta mike ta shiga dakinta ta zauna side din gado duk jikinta a sanyaye, a ina Khalil ya samo yarinyar nan har zai shigo da ita gidan nan? Bilkisu ta fito daga bandaki tana kallon Mami ganin yanayinta tace “Mami are you okay?” Mami tayi karfin halin cewa “Sure, ki tafi idan ina bukatarki zan kira ki Bilkisu” Tace “Toh Mami” Daga haka ta fita daga dakin, Har sannan Khalil na tsaye ya rasa abun yi, Nihad dai ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka, Bayan Bilkisu ta fita ya juya ya tafi dakin Maminsa, yana shigowa dakin ya kulle Mami ta mike tana kallonsa cike da tuhuma tace “Khalil wacece warcan yarinyar ka kawo mana gidan nan? Who is she? Menene alaqarku?” Yayi gathering courage yace “Mami calm down pls, yarinyar mai gidan da nace maki nakan zauna wajensa a kano ce, kuma ai na gaya maki dalilin da ya sa muka taho tare, Banda wannan babu wani dalilin Mami” Mami tace “Toh zan tura maka kudin jirgi ka siya mata ticket ta koma, ai ta gama abinda take ko?” Ya rasa abinda xai ce, Mami ta hade rai tace “Ko baka ji abinda nace bane?” Yayi kasa da murya yace “Mami bata gama ba, bata samu amsan admission letter din ba ma” Mami tace “Toh me kake nufi? Ka gaya min me kake nufi Khalil?” Ya marairaice yace “Mami karki manta gidan babanta fa nake all this while, bai san ni ba ya yarda da ni, yayi accomodating dina na zauna cikinsu for almost 10 months now” Mami tace “Yanxu ya kake son ayi khalil? Me kake son in fada a wannan issue din? Sai kace baka san mutanen gidan nan ba ko mance halinsu ne? wait first… Wai ma ita ce a video din nan ko ba ita bace?” Ya sauke idonsa kasa bai iya yace komai ba, Mami tayi masa tsawa tace “Baka ji na ne?” Cike da karfin hali yace “Ita ce” Mami tace “Nawa ne kudin jirgin, zan tura maka yanzu” Yana girgiza kai hankali tashe yace “Mami mun yi magana da mahaifinta kan cewa ta zauna nan gunki har ta karbi admission letter din tunda bai fito ba, Mami we can’t repay him this way, he is one of the nicest person i have met in life, kawai ka haifi yaro ne baka haifi halinsa ba, but her mother and father are down to earth, sun min abinda baxan mance su a rayuwa ba, sannan Mami duk yaran gidan mahaddatan qur’ani ne, kawai dai ita….” Sai kuma ya kasa ci gaba don ya rasa me xai ce, Mami ta fashe da kuka tace “Magana kake son ja min yanzu fisabilillah Khalil? A ina kake son in ajiyeta har ta zauna a gidan nan bayan kana gani duk yan matan sun shaida ita ce a videon nan kuma sun je su idar, sannan har shi Abbanku sae da ya tofa nasa a lokacin da ya ga video din nan kwanaki, he was so disappointed yayi ta addu’an Allah ya shirya mana zuri’a, sai kawai yau a ganta a gidan nan ba kuma kowa ya kawota ba kai?? Kai da kake da ta6o ta ko ina a gidan nan shine zaka kara shafa ma kanka kashin kaji? Check this out khalil, yaushe har Abban naka ya bukaci ka dawo da har zaka dawo tare da wannan issue din? Kayi min gata kayi ma kanka gata ka fitar da ita daga gidan nan kafin wani ya kara noticing dinta bayan kanninka, Plss take her out of this house Khalil”

Masu jira ina turawa su yi fowarding a dinga yi ana tunawa da hakki, ku kuma masu karantawa a bati amma fa a duniya yake bati, duk na gaisheku kyauta ya damuna?? Masu posting on Facebook, Hassan Basiru majia, Aminu Arthur and the rest, Hmm an dai ce prevention is better than cure, i warned first.

Nihaad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence via👇🏻

Related Articles

07087865788……

 

*Wato duk me son sanin wani turare Nihaad ke sakawa da ke sa Khalil jiyo kamshinta da ta gifta waje upon the hatred ya biyoni pc don abun sirri ne, nima shi nake sa wa Barrister ke jiyo kamshina tun daga gate, joke apart…, kuma saboda wannan kamshin ya min alkawarin daga ni ba kari* 🤓🥰

_SCENTMANIA_💯

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button