Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 21

Sponsored Links

*21*

 

Tsawon kwanaki biyu da farkawar hammad aka sallameshi sabida jikin nashi yayi sauƙi.
Sede zahra ita bata jin daɗin yanayin yayan nata,sabida gaba ɗaya kunyarta yakeji baya son su haɗa ido.

Related Articles

Jameel ne ya ɗaukosu a asibitin ya kawo su gida sannan yatafi da zummar gobe ze dawo.

Suna shiga cikin falon zahra taja hannunshi zuwa ɗakinshi,sede ita abun da bata gane ba koya suka haɗa ido kuka yake ta rasa gane kan lamarin.

Ɗakinshi ta kaishi,sannan ta juya ta koma nata ɗakin domin tayi wanka.

Bayan duk sunyi wanka sun kimtsa ne taje ɗakinshi tasameshi zaune ya rafka uban tagumi,zame hannayensa tayi sannan ta zauna akan ƙafafunsa,hannayenta tasa ta sakalo wuyansa tace cikin shagwaɓa”yayana wai kode bakaji sauƙin bane?”

Kallonta yayi da hawaye cike da idanunsa yace”Naji sauƙi mana”

“to me yasa kake kuka?”tasake masa tambaya.

“tausayin kaina nake shiyasa”

‘to ka kwantar da hankalinka ay ina tare da kai yayana”

“kin min alƙawarin duk sauyin yanayi bazaki gujeni ba?”ya tambayeta cikin marairaicewa.

Dariya tayi ta faɗa jikinshi tace”yayana kenan to ni da na aureka dan ina sonka to ina zani,ay muna tare har abada”.

Sosai ya tattaro natsuwarshi yace,”to shi soja me ulcer meyasa bazaki yafe masa ba?”

ay kamar wacce ya mintsina,zimbur ta miƙe daga kan cinyar tashi,hawaye na bin idonta,tace”ay wannan baƙin karen har abada ba yafiya tsakanina dashi,ni yaya don Allah kar ka sake min maganarshi”ta ƙarasa maganar cikin kuka.

Janyo ta yayi jiki ba ƙwari ta faɗa jikinshi sannan ta saki kuka me sauti gwanin ban tausayi.

rarrashinta ya shiga yi yana ɗan bubbuga bayanta gamida hura mata iska a kunne.

Sannu a hankali tayi shuru ta dena kukan,suna nan zaune aka kawo musu abinci daga gurin mummy.

Zubo musu zahra tayi suka ci suka ƙoshi,sannan kowa ya nufi ɗakinshi domin gudanar da ibada.

Hammad zafin da zuciyarshi ke masa yafi gaban tunani,ya rasa ta ina ze ɓullowa zahra ya shaida mata shine wanda yay mata fyaɗe,tsoron ta tsaneshi yakeji,shiyasa damuwar tai masa yawa.

Haka suka kwana kowa a ɗakinshi,hammad yadda yaga rana haka yaga dare ba tare da ya runtsa ba.

Gari na waye ba,yayi wanka ya kimtsa sannan ya fice a gidan batare da ya mata sallama ba ya nufi gurin jameel dan yazo ya warware masa damuwarsa.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*wasun ku basa da uzuri a rayuwa,nace muku ina tare da mara lfy,to surukatace aka kawomin in kula da ita,tsakani da Allah se in barota inzo inta saku nishaɗi,in na samu lokaci ne ko tayi bacci se in ɗan rubuto,amma kunƙi kumin uzuri*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button