Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 28

Sponsored Links

28*

A falon ta yada zango tana turo baki gaba,ta juya mishi baya alamun tayi fushi.

Joystick ɗinshi ya maƙure a gefen cinyarshi,sabida kunyar zahra taganshi a hakan yakeji.

Related Articles

A hankali ya taka ya isa kusa da ita,ta bayanta ya tsaya,yace”tuba nake gimbiyata,pls a saurareni”maƙale kafaɗa tayi,murmushi yayi ya janyota jikinshi ya rungumeta ta baya ya ɗora kanshi kan kafaɗarta yana shinshina wuyanta yace”ayi haƙuri nace ko in fasa kaiki makarantar”

Da sauri ta juyo ta faɗa jikinshi,tana masa kukan shagwaɓa,tace”na haƙura yaya kaima kayi haƙurin karka fasa kaji”ta ƙarasa maganar tana zillo ajikinshi.

Ɗaukarta yayi cak suka,koma kan kujera,ya ɗorata akan cinyarshi,sannan yace”munyi shawara da jameel yace jarabawa kawai ya kamata kiyi,sabida kiyi saurin kammalawa ki shiga jamia,”ya faɗi yana latsa gefen cikinta.

Zillewa tayi tana dariya tace”duk yadda kaga ya dace yaya hakan zaayi”ta faɗi cikin nishaɗi.

Ƴar hira ce ta biyo baya a tsakaninsu,kamin tajashi zuwa ɗakinshi ta haɗa masa ruwan wanka.

Kayan daze sa ta ciro masa sannan ta fice a ɗakin,sosai hammad yaji daɗin ganin ta fito masa da kayan.shiryawa yayi ya fito zuwa falon.

Abinci sukaci,sannan suka dawo falo,yana ta mata hirar daɗin abincin,kallo sukayi sannan kowa ya miƙe ya nufi ɗakinshi,

To rayuwa na ci gaba da garawa,zahra tayi jarabawa har tasamu nasara a jamb ɗinta inda bata sha wiyar samun addmission a jami’ar Abuja ba.

Tuni hammad ya koma bakin aykinshi,inda aka turashi rivers state,tsakaninshi da zahra sede waya,sosai yake kewar matarshi sede dole ya jira ta girma dan la lurarshi tafi ƙarfinta sabida tayi masa kankanta.

A nata ɓangaren kuwa,zahra ƙawa tayi a makarantar data shiga me suna Husna.
Da farko zahra bata saki jiki da ita ba,amma daga baya tana sakar mata bayan ta karanci halinta.

Husna sosai take ƙara wayar da kan zahra inda ta koyar da ita yadda zata zauna da mijinta da dabarun zaman gidan auren.

Se yanzu zahra takejin haushin shishshigewa yayan nata da ta dinga yi,Ashe ba haka ake ba aji akeja,ayko tunda ta gano hakan seta sa shi ya raina kansa

Hammad sun samu hutu a gurin ayki,dan haka cikin zumuɗi da farin ciki ya nufo gida,tun da ya sauka a airport yakira zahra a waya”yayana ya kake?”zahra ta tambaya.

“lafiya lau princess,gani airport ki turo driver ya ɗaukeni”

Ba tare da mamaki ko murnar jin dawowar tashi ba tace”ok bari afaɗa masa” tana kaiwa nan ta kashe wayar,

Hammad tsaye yayi sororo da waya a hannunshi yana kallo,”kamar shi a gurin zahra yace gashi ya dawo amma ko murna batayi ba,kai may be bata da lfy ne”tunanin da yay ta yi kenan har driver ya iso ɗaukarshi.

Ya ƙosa yaga halin da zahran take,dan hankalinshi baa kwance yake ba.

Driver na isowa gida yay parking da sauri hammad ya fice daga motar ya nufi cikin gidan.

Zahra ko tun bayan data isarwa da driver sakon tayi maza tayi wanka ta kimtsa,acikin wasu riga da sket marasa maraba da tsirara.
Kwance take akan doguwar kujera,hannunta riƙe da remote tana sauya tashar da takeso..

Koda yayi sallama ya shigo,zahra bata motsa daga inda take ba,illa,ɗago kanta tayi ta dubeshi,sannan tace”wellcome bross”

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*To sabon sauyi acikin tafiya,😊akwai sabon novels ɗina dazan saki wata me kamawa in muna da rai da lafiya,sunan shi SHIMFIƊAR AURENA na kuɗi ne duk meso ze iya turo kuɗinsa tun yanzu naira 500 kacal,update biyu arana,safe da dare,insha Allahu, ku biya ku karanta daga jin sunan kunsan zaa ɓata hankalin dare,ga wanda yasan hannun surbajo yasan bazata bashi kunya ba karku bari abaku labari,SHIMFIƊAR AURENA,littafine daze kerewa kowanne,novel nawa,akwai tarin sirrika da magunguna acikinsa,dazasu fito da kimarki ta mace,sannan ga sirrin riƙe miji da ƴan uwansa,an baje kolin basira acikinsa,kisiya ki biya ki karanta,wannan soyayyar da akewa surbajo to afito a nuna ta akan SHIMFIƊAR AURENA,500 ne kacal*

*Zahra muhammed Nasir 2084024749 UBA*

*Whatsapp 07044600044 aturo shaidar biyan ta nan*

*Note bana adding a group kuma bana turo book pc in zaki shekara kina tambayar ɗaya daga ciki ba wanda zaki samu daga gareni,na jima ina faɗin banayi amma anki a fahimta,in baayiba kuce anyi wulakanci,*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button