Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 8

Sponsored Links

Kwantar da kanta tayi a kafaɗarsa tace “promise?” Murmushi yayi ya ɗora hannunsa akanta yace “nayi alƙawari”kaɗa manyan idanunta tayi farare tace “shikenan nima nayi” wata wawuyar runguma yayi mata da saida tasa ta jin wani maganaɗisu ya dirar mata tundaga Tsakiyar kanta har babban yatsan ta sun ɗauki second’s masu yawa a haka sannan kowanensu ya samu janyewa ɗan’uwansa taja numfashi tace “zan shiga ciki” jinjina mata kai yayi ya buɗe motar ya ɗauko wata babbar leda cike da kaya ya miƙa mata yace Asha kwalliya lfy”

 

Karɓa tayi tana masa gdy ya nufi motarsa itama ta nufi gdan ta shiga da sallamarta Mama da Hasina suna tsakar gida Mama na bawa Hasina labarin Alh Mu’azzam da yazo gurin Hanisa ɗazu ta wulaƙantashi har tana faɗin kinga fah kajin can da nake ɓararrakawa shine ya kawosu da iyayen turaruka da ya shigo gaisheni kuwa dubu Hamsin ce yabani yace “Tallen ma yana neman alfarmar ta daina ɗauka ta zauna a gda shi Indai zata saki jiki dashi babu abinda bazai mana ba”
Murmushi kawai Hanisa tayi ta zauna tana duban Hasina itama itan take kallo suka dubi ledar data shigo da ita a tare Mama takai hannu ta janyo ta buɗe suka zaro idanu ganin wata arniyar waya me manyan kuɗaɗe ƙirar Samsum a cikin kwalinta sai kayan shafa mayuka masu babbar daraja sunkai kala goma da turaruka suma na alfarma sai wani ɗan ƙaramin akwati a cikin ledar har suna rige²n ɗauka tsakanin Mama da Hasina Mama ta buɗe tare da ƙaro idanunta waje tace “sarƙa ɗan kunne da zoben gold Ni Aishatu Hanisa waye me wannan kyautar darajar ahayyeee yau ina ƙirga ruwan alkhairi yau da dama muka tashi a gdannan….”
Tashi Hasina tayi tabar gurin zuciyarta na halbawa da ƙarfi tsoro firgici da tashin hankali haɗi da wani tuƙuƙin kishi ya taso mata a fili tace “Me hakan yake nufi kenan? Ni Ni Hasina nice budurwarsa Amma baiyimin kyautar girma ba sai ƙanwata yayiwa to hakan yana nufin meye?” Hanisa dake shigowa ta amshe da cewa nima tunanin daya ɗarsu a zuciyata kenan Yaya Hasina saidai ni ina ganin kamar ke yake nufin na kawowa kayan tunda ni babu wata alaƙa tsakaninmu bayan ta abota daya roƙeni muka ƙulla yau….”

Related Articles

 

Haka Allah yayi su ko kaɗan basason ɓataran junansu wannan tasa Hasina saurin mazewa tace “Kyautarki ce My jinin jiki duk wanda ya kyautata miki Ni ya kyautawa musamman Abdu da nake jinsa a ƙasan zuciyata nasan girmanki da nake nuna masa a gurina shine yasa shima ya zaɓi faranta miki da haska rayuwarki kiyi amfani da duk abinda ya baki nasan zakiji daɗinsu” Janye idanu Anisa tayi daga kallon Yayar tata tace “Tunda muka taso muka sabarwa kanmu mutum ɗaya baya mallakar wani abu face ya zama mallakin ɗayan Yaya inajin a raina zan iya sadaukar da komai nawa don ganin kinyi farin ciki a rayuwarki kamar yanda ya zamana kema komanki bakijin ƙyashin mallakamin don rayuwata ta haskaka Yaya ki riƙe kayannan a gurinki zan rinƙa jin namu ne mu biyu idan kika barni dashi kuma bansan yanda zanyi ba ko kin manta kece madubina ne abin da kikayi shine yake haskamin nima abinda zanyi”

 

Murmushi sukayi suka rungume juna Hasina na shafa bayan ƙanwar tata tace “Naji Jinin jiki zan karɓi kayan kwalliyar na adana mana amma ki ɗauki sarƙarki da wayarki” saurin girgiza kai tayi tace “Aa banason sarƙa wayar kuma ki bani ta hannunki kiyi amfani da wannan irin taku ce Ni wannan ungwagwurar ta isheni” harararta tayi tace sai kiyi kuma Hanisa bazan karɓar miki waya ba kiyi amfani da kayarki sarƙar kuma idan bakiso a siyarta sai musai fili da kuɗin”
Sunci gaba da rayuwa me daɗi kamar yanda suka faro gininta tun farko yanzu abu ɗaya ke neman basu matsala shine ɗabi’ar su data bambamta duk da kasancewar kasuwar Hanisa ta buɗe alhazan birni sunata jewa akanta amma taƙi sakin jiki taƙi yarda ta saurari kowa mutum ɗaya take saurara shi ɗin ma jansa takeyi a ƙasa kamar kare shi kuma ya nace kullum cikin hidima yake yana jewa a hanya. Tuni ya gama siye zuciyar Mama batada zance saina Alh Mu’azzam yana ganin waya a hannun Hanisa amma ta hanashi numberta wannan yasa wani zuwa da yayi ya ƙudiri niyyar sai ya san yanda yayi ya ɗauke ta suka fita ya siyo mata wacce tafi ta hannunta.
Haka kuwa akayi yau yana zuwa suka gaisa da Mama yace mata yanason zasu fita da Hanisa, babu musu Mama tace “Kayyah Alh Mu’azzamu ai dakai da Hanisa duk ɗaya ne meye na neman alfarmar ai kawai umarni zaka bata” ƙasa yayi da kansa yace “ai dake naga har yanzun baya² takeyi dani taƙi sakin jikinta dani kuma fah Mama idan Anisah ta saki jiki dani ba itaba kema sai kin huta don yar Saudiyyar nan sai kinjeta kinyiwa wani alfarma shima yaje”

 

Wata uwar guɗa Mama ta saki tace “aikuwa dole ma ta sake Alh wannan alkhairi dake tunkaroni Hanisa ke Hanisa fito kuje shaffind da Alh maza karki ɓata masa lkc” Miƙewa tayi zuciyarta a hassale zatayi bala’i Hasina tayi saurin riƙe ta tace “Pls karmu raba hali a gabansa ya samu abin goranta miki na fuskanci mutumin nan da gaske yakeyi so yake kuyi rayuwa Hanisa ki bishi kiga gudun ruwansa kafin ki yanke masa hukunci”
Wata uwar ƙwafa taci tace “Banso kikayi mgn ba da kin barni dasu Allah Mama ta fara ƙure hƙr na Yaya tunda taga banason sauraronsa ta ƙyaleni mana bashida hali ne fah” sake ɗaga mata hannu tayi tace “nidai na roƙeki kije idanma wani abun ya nema Indai bai zarceba kiyi masa wlh akwai daɗi harka musamman in kika samu ingarman namiji Ni yanzu damuwata ɗaya bansan meye yasa kwata² sama da watanni ke tun ranar da tsautsayin nan ya faɗa miki har yau saidai muyi tsote² da Abdu ya daina cina Ni kuma na saba da ɗanɗanonsa me tsayawa a zuciya dama inason mu samu lkc nayi miki mgn naga kinada alfarma a gurinsa ƙilan ke ya faɗa miki laifina wlh na fara zargin kaina ko daɗina ya daina ji any way kije kawai koma mene zamuyi mgn idan kin dawo”…

 

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*AUREN SHA’AWA* Na kuɗine ,Zazzafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_

Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍“`♡♡

 

*OUM HAIRAN*
[12/16, 2:33 PM] Oum Hairan&Affan: *WATA KARUWA*

 

*OUM HAIRAN*

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button