Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 10-11

Sponsored Links

Arewabooks;Hafsatrano
Page 10-11

*AINAM DRINKS AND MORE*

Assalamu Alaikum
Hajiya ta kinada labarin kayan Egypt da muke kawowa kuwa to in baki sani ba matso ki kusa kiji AINAM DRINKS AND MORE mun kawo muku kaya na gani na fada na gayu wa inda sai wance da wance ake gani dasu ba kano made bane kunsan a koda yaushe burinmu mu kawo muku unique abu.Available ne ba jira zakiyi akawo ba ina Kebbi State,muna bada sari muna aikawa ko ina,duk abinda kike bukata hajiyata ki latsoni kawai wa.me/2348146766440
Ko baki siyaba yanzu kiyi saving number ta murika ganin status din juna
Nagode

Related Articles

 

***A nutse yake biye dashi har zuwa sanda ya samu waje ya zauna akan daya daga cikin kujerun alfarmar da aka kawata falon dasu. Yana zama ya zare glasses din idon sa ya ajiye akan wani silver tray da aka ajiye masa domin ajiye ire-iren abubuwan sa kanana. Kallon Rafeeq din yayi yana daga gefe yana jiran ya gama zama sosai sannan ya zauna. Da hannu ya nuna masa waje da nufin ya zauna. Sai ya zauna yana sadda kansa kasa.

“Ina Wakili?” Ya tambaya yana daukar tv remote ya kunna.

“Ya dan fita but nasan ba nisa yayi ba, a kirashi ne?”

“Kyale shi. Ya kaga aikin?”

“Alhamdullillah, sunyi kokari sosai banga wani failure ba, but we need to do better a sales management.”

“Good, kayi handling wannan.”

“In sha Allah.”

“Toh, magana ce dama akan dawowar ka, tunda ka dawo inaso ka hada hankalin ka waje daya,idan nace hade hankali waje daya ina nufin kayi aure, hakan zai kara maka nutsuwar kula da business din mu.”

Shiru yayi gabansa na faduwa, duk da yasan hakan yana cikin plan din AJIn amma be dauka da wurwuri haka ba, ta ina ma zai fara? Be shirya ba sam tunda har yanzu be ma san a wanne matsayi yake ba. Kansa ya sadda kasa ya kasa cewa komai Ajin na lura da shi da yanayin sa

“Ko babu matar ne, na samo maka?” Yace masa da gatse duk da yasan komai akan Rafeeq din.

“Zan kawo in sha Allah. Nagode Allah ya kara girma.”

“Kwana biyar zuwa sati daya na baka, kasan bana son aja time ana shiririta, idan ka gaza kawowa sai a lalubo maka a dangi.”

“In sha Allah.”

“Madallah, zaka iya tafiya.” Yace yana mike kafa ya dauke hankalin sa kachokam ya maida kan TV kamar bashi ya gama magana ba.

“Allah ya kara girma.” Yace bayan ya mike din yayi hanyar fita yana jin dan ragowar farin cikin da yake ciki yana ficewa gaba daya. Har ya kai kofa zai fita mahanar AJIn ta dakatar dashi

“Ka sani bana son yar kananan mutane, ka samo yar babban gida kuma yar manyan mutane, kasan hausawa sun ce kowacce kwarya da abokin burmin ta, ban gina rayuwar ku akan haka ba, investing nayi akan ku dan haka ne ma ba zan dauki duk wani shirme ba.”

“In sha Allah.”

Yace yana ficewa cike da dana sanin dawowar sa kasar. Ya dade da jin AJI yana maimaita musu cewa investing yayi akan su tun daga karatun su da komai nasu, dan haka ne ma yake ganin dole dole su bi duk tsarin da yazo dashi ko da hakan ba zai musu dadi ba.
A daidai compound din gidan suka hadu da Mummy ta fito zata part din Ajin, wuce ta yayi kawai ba tare da yace komai ba. Kwafa tayi ta wuce itama tana cike da haushin sa. Yadda yake nuna kamar be san tana existing ba shine yake kara bata mata rai. A waje biyu ne kawai yake dan sakin jiki da ita, idan Asim na wajen ko Aneesa, amma da zarar su biyu ne sai yayi kamar be taba sanin ta ba a duniya.
Part dinsu ya wuce dan ya riga ya sallami driver sa dan be dauka zaman nasu takaitacce bane da Ajin. Saman sofa ya fada yana sauke nannauyar ajiyar zuciya me cike da tarin damuwa. A yau abubuwa biyu da suka rikita masa tunani sun faru cikin yan awoyin da basu gaza biyar ba. Da farko zaman ta a gidan su a matsayin yar aiki shine babban tashin hankalin sa, ta ya hakan ya faru, ta ina kuma zai fara bullowa al’amarin. Baya jin zai iya daukar hakan akansa tunda yasan me hakan yake nufi a gare shi, sai kuma maganar da Ajin ya bullo masa da ita ta sama ta ka, bayan ya riga yasan komai akan yarinyar da yake so tun fil’azal. Idan yace baya cikin damuwa yayi karya, sai dai shi mutum ne me iya dannewa da shanye damuwar tasa har ma ka gaza gane ainihin yanayin da yake ciki. Kiran sallah isha yasa shi mikewa yana tattare hannun rigar sa zuwa sama, ya wuce toilet ya dauro alwala ya fito zuwa masallaci yana ji da yakinin zai samu saukin damuwar sa idan har ya yi sallah ya zauna a ciki har zuwa sanda zai samu saukin abinda yake ji. Sai da ya kalli part din bayan kafin ya wuce, ya girgiza kansa yana sake jaddawa kansa dolen dole ta bar gidan duk da ya hango tashin hankali ta akan maganar wanda ya riga yasan dalilin hakan ya kuma san yadda zai bullowa al’amarin.
A masallacin ya tarar da Asim sai yayi joining dinsa sukayi sallar suka zauna a ciki har tara da rabi kafin su fito su wuce cikin gidan. Dinning area suka zarce Asim yayi serving nasa a kallon farko da yayi ma abincin sai da ta fado masa, ya lumshe idon sa ya bude su a hankali yana sake kurawa plate da warmers din gaban sa ido kamar me shirin gano wani abu. Taba shi Asim yayi ganin ya tafi tunani gaba daya.

“Lafiya?”

Yace yana zama a kusa dashi bayan ya gama zuba nasa dan babu kowa a wajen ma’aikatan duk sun wuce makwancin su.

“Wannan paper da ka bani dazu nake tunani akai, kasan na gano yadda zamu bullo mata.”

“Yawwa yayi, dama nima ina ta tunani akai.”

Spoon ya dauka karo na farko tunda ya dawo zai ci abincin gidan cike da karsashi ba tare da tsoron komai ba, ya saka shi a kan plate din nasa yayi Bismillah ya soma ci a hankali. Sai da ya cinye na bakin sa sannan ya amsa wa Asim din maganar sa da yayi karshe

“Da wuri zamu fita gobe inaso zan je wani waje by 12.”

“Ok Allah ya kaimu.”

“Amin, yaushe aka samu new cook a gidan nan?” Ya jefa masa tambayar yana sake yin spoon daya.

“An kwana biyu, bansan me yasa ba duk Mummy ta sallame su ta kawota.”

“Ok kun taba haduwa kenan.”

“Yes, no. Last time muna kitchen da Aneesa ta shigo zatayi aikin ta, ta saka wannan abun kaman Ninja yama sunan sa? Wanda ake covering face da komai sannan tasa socks ba zaka ce girki zatayi ba, da har nace ta daina sawa cox bana son abun nan sai kuma naga ta tsorota, sai na tausaya mata dan kasan Mummy tsaf zata koreta akan rules din da tasa mata.”

“Ok rules din Mummy ne dole tasa nikaf da socks?”

“Haka Aneesa tace.”

Ture abincin yayi baya bacin ransa na tasowa. Kallon sa Asim yayi ya kalli abincin sai yace

“Wai har ka gama?”

“No na koshi ne, babu dadi sam.”

“Haba dai, but ta iya sosai ai. Morethan sauran chefs na baya su da suke ma manyan chefs.”

“Ni dai beyi min ba, please ka fada ma Mummy a samu wani wannan abincin yana min wani iri, a sallameta kawai ma.”

“Ok, zan fada mata tunda baka so. But trust me da ka kara gwadawa zaka ji dadin abincin.”

“Be yi min bane ba kawai.”

“Shikena zan fada mata.”

“Na wuce ciki sai ka shigo.”

Ya wuce yana adduar Allah yasa Asim din yayi convincing din ta, a sallame ta dan ba zai dauki duk wani form of kaskanci ba da za’a yi mata.

Bedroom dinsa ya shige ya murda key dan baya ma so Asim ya biyo shi ya hanashi samun damar more tunanin sa. Yana jin shi sanda ya taba kofar jin ta a rufe yasa shi wucewa dakin sa kawai dan dama shima a gajiye yake kwanciyar kawai yake son yi.
Rage kayan jikinsa ya sauya zuwa night dress yayi duk wasu night routines dinsa da ya saba ya wanke bakin sa da mouthwash me dadin kamshi sannan yazo ya haye gadon ya ja duvet dinsa har saman kansa ya rufe ruf yana fatan bacci ya dauke shi kawai. Duk kuwa yadda yaso yayi baccin kasawa yayi, da ya rufe ido ita yake gani sanda take masa magiya tana zubda hawayen ta me matukar tsada a gare shi. Tsaki ya dinga ja kawai daga kwance yana jin tsana da kyamar halin iyayen nasu fiye da a da da be gama sanin ciwon kansa ba. Me yasa zasu kaskantar da duk wani mutumin da yake karkashin su. Shi a ganin sa babu wani banbanci tsakanin masu arziki da mara sa shi, Allah ne yaso ya gansu a haka ba wai wayon su bane ko dabarar su. Dare sosai ya raba yana sakawa da kwancewa hakan ya haifar masa da wani irin ciwon kai me saka ka jin dum. Da kyar ya samu baccin ya dauke shi ta karfin gaske bayan ya lalubo maganin sa yasha.
Rashin samun isashen baccin da be yi ba da kuma tashin wurin da yayi ya kara taazzara masa ciwon kan amma haka ya daure ya tashin yayi wanka ya shirya cikin farar shadda kasancewar Friday ce. Sanda ya fito babban living room din gidan babu kowa duk basu tashi ba, har ya wuce zai fita sai ya dawo baya, ya chanja akalar tafiyar tasa zuwa kitchen din gidan.
A kofar yaja ya tsaya yana kallon bayanta tana tsaye tana aiki babu Hijab din a jikinta kasancewar safiya ce tasan har ta gama aikin ta babu wanda ya fito. Tun ranar da Asim ya hanata rufe kofar ta daina sai dai tayi aikin a haka dan tana tsoron lokacin da Mummy zata shigo ta same ta. Sai ya kasance da safe ne kawai take cire hijab din ta ajiye shi saboda bata sakewa sam idan tana aikin dashi. Kallon kitchen din yayi a tsanake cikin dakikun da basu gaza biyar ba, sannan ya maido da kallon sa kanta har lokacin bata juyo ba aikin ta kawai take hankali kwance. Duk da taji motsin mutum amma bata taba kawowa shi bane ba, duk tunanin ta Ben ne shiyasa ma bata damu da tsayawa daga aikin nata ba har ta kammala hada salad din ta juyo da nufin dora shi akan Island din sai kawai taga mutum ya tsaye yana kallon ta. Kwayar idonsa ta kalla cikin sakan biyu tayi saurin janye idon ta saboda wani irin abu me karfi data hanga kwance a cikin idon nasa da suke a matukar shanye kamar yana jin bacci.

“Ina kwana?”

Tace tana durkusawa har kasa kamshin turaren nan nasa na jiya yana bugo ta daga in da take. Taji kamshin tunda ya tsaya amma saboda tsabar yadda take jin kamshin tun jiya yasa tayi tunanin har yanzu din ma jin nasa kawai take yi. Maimakon ya amsa gaisuwar ta ta, sai ya shiga takowa zuwa cikin kitchen din kansa tsaya har ya iso daf da ita, ya wuce zuwa bayan ta kamar zai gota ta, sai yasa hannu ya ja igiyar data daure apron din da ita sai ji tayi ta saki gaba daya.

“Get out.” Yace yana lumshe idon sa.

Rasa in da zata yi tayi, gashi ya tare hanyar da zata wuce din ya kuma dauke kansa daga kallon ta yana jiran ta fice kawai dan ganin ta a haka ba karamin kona masa rai yake ba.

“Zan wuce.” Tace a hankali sai ya matsa kawai yana kara dauke kansa. Wajen da ta ajiye hijab din nata ta nufa ta dauka tana kokarin fita yace

“Ki fara hada kayanki, you are leaving this place.”

Zatayi magana yace

“Karki roke ni.”

Da sauri ta juya ta fice kukan na taso mata, kukan bakin ciki da takaici. Duk da ba wani zaman dadi take a gidan ba, amma tana jin son aikin ta dan shine garkuwarta, kuma a kalla babu wanda yake takura mata yawanci sai Aneesa itama ba ko yaushe ba. Hajiyar gidan ta kan dade bata leko kitchen din ba bare har ta ganta ma amma shi wannan tunda ya dawo yake neman duk hanyar da zai koreta. Me tayi masa har haka da yake kokarin ganin sai ya bata mata. Idan ya koreta ya zatayi da mahaifin ta da rayuwar ta?

_”Allah sarki Asim.”_

ta furta a hankali tana goge hawayen da take. Be nuna mata irin wannan tsanar ba ko da ya fara ganin ta a gidan. Yadda yayi mata a lokacin da taje neman alfarma wajen Hajiyar kadai yasa take jin shi din daban yake, ba irin halin yan gidan yake dashi ba. Sai gashi shi daga dawowar sa, ya dauki karan tsana ya dora mata, duk da babu irin hakurin da bata bashi ba amma kamar ma be san tanayi ba. Kukan ta, taci ta godewa Allah kafin ta kalli yan kayan ta dake dakin da basu da wani yawan kirki ta tattare su waje daya, ta zauna tana jiran tsammani.

🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
07040727902

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button