Yanci da Rayuwa 12-13
Arewabooks; hafsatrano
Page 12-13
***Maimakon ya fita kamar yadda yayi niyya sai kawai ya koma falon ya zauna yana jiran fitowar su. Wayar sa ya ciro yace Saddam su jirashi sai 9 zai fito ya kashe ya hard’e yana jiran wanda zai fara fitowa. Aneesa ce suka fito tare da Ummita saboda suna da lectures 9. Ba wanda ta lura dashi har suka isa dinning area yana kallon su takaici na sake kume shi. Hadin salad ne kawai a wajen sai kayan tea da ko yaushe dama suna nan daga nan babu komai.
“Kan bala’i, babu komai akan table din ai.” Aneesa tace tana rike baki.
“Benn…” Ta kwala masa kira da sauri ya karaso wajen
“Sorry ma ina karasa arranging kitchen din ne.”
“Ina breakfast dinmu?” Tace tana hade rai
“Baki iya girki bane da kanki? Ko dole dole sai an dafa an ajiye muku kuna yaya mata.” Yace yana daga zaune a in da yake. Sai lokacin suka lura dashi a zaune
“Yaa fa school zamu fita.”
“Sai ku tashi da wuri ku hada breakfast, kalle ku manyan mata daku sai an dafa muku abinci.”
Shiru sukayi Aneesa kamar tayi kuka gashi bata so yayi mata fada sam. Asim ta raina amma Rafeeq kam bata isa ba. Tsaki yaja kawai sannan yace
“Ku fara shirin dafa breakfast kafin ku tafi school dan ita dai na sallame ta.”
Turo baki tayi yana kallonta, ta wuce drawer dake dinning area din ta ciro musu cornflakes da bowls guda biyu suka zauna suka hada suka sha Ummita dai bata ce uffan ba saboda tana tsoro dan tun dama ita Rafeeq ba magana yake mata ba bare yanzu da ransa yake bace. A tsattsaye suka sha cornflakes din suka fice ya rakasu da ido yana jan tsakin takaicin rayuwar sangarcin da yayan masu kudi irin su suke yi, wanda yake sa wa su kara jin suna da banbanci da talakawa har su dinga taka su suna bautar dasu da yi musu dictating abinda ya shafi dukkan rayuwar su.
Cigaba da zaman sa yayi a wajen yana jiran Hajiyar gidan dan baya so ya tafi ta samu damar ci wa Noor din mutunci gwara ta san shine ya hana ta yasan babu yadda zatayi dashi dole ta hakura dan ba kasafai ya fiya saka baki a abubuwan gidan ba amma duk sanda ya saka toh fa kowa sai ya ji a jikinsa.
Rolex watch din dake daure a tsintsiyar hannun ya kalla, a kalla ya shafe kusan awa guda a zaune, duk da haka be ji a ransa zai iya tafiya ba idan har ba fitowa tayi ba. Karin mintuna goma akai sai gata nan ta fito cikin shirin ta kamar kowanne lokaci, yar gayu ce da kwalisa ta ajin farko gashi duk sanda zaka ganta toh fa tana cikin ado da kawa, zata iya kashe ko nawa ne akan sutura ba tare da taji komai ba. A mamakance take kallon sa dan batayi tunanin ganin sa a wajen a zaune ba, fuskewa yayi bayan ya karanci yanayin mamakin da ta shiga. Mikewa yayi yana zura hannun sa cikin aljihun rigar sa sannan yace
“An tashi lafiya?”
“Lafiya lou, kana da bukatar wani abun ne?” Ta jefe shi da tambayar dan tasan tabbas akwai abinda ya tsaida shi din kuma tasan ita yake jira.
“Yes, maganar me dafa abinci ne.”
Sai yayi shiru yana jin zafin kalmar da ya kira ta dashi. Da sauri ta kalle shi, zai yi magana ya hango Asim na nufo wajen su yana gyara links din rigar sa. Fasa fadar abinda yayi niyya yayi sai yace
“Please ki sallameta, abincin ta babu dadi a samo wata.”
“Yawwa, shikenan ma tunda ka gaya mata da kanka, Mummy please a chanja ta, Feeqq baya son abincin ta.”
“Naji, zan ga me zanyi akai.”
Tace tana wuce su kawai. Bata ma san me zata ce ba kwata kwata, takaicin ta daya yadda Asim bashi da say din kansa sai abinda Rafeeq din yace. Tasan tunda suka fara haka toh fa dole sai sun sallametan, dole tayi musu abinda take so din dan ita kanta yarinyar ba wai ta kwanta mata bane ba, alfarmar Hajiya Maryam take ci, amma duk da hakan yanzu ba zata sallameta kai tsaye ba, zata san yadda zata bullo mata ta bar gidan ba tare da Haj.Maryam din taga laifin ta ba.
***Tare suka isa office sai dai ko zaman minti talatin Rafeeq be yi ba ya sake ficewa dan yana da wajen zuwa dama. Daga shi sai Saddam suka fita dan baya so yayi wani kuskuren da zai sake jefa ta cikin matsala komai zai gudanar dashi ba tare da ya bari AJIn ya sani ba.
“An gama komai?”
“Eh an gama, Ammar nasa ya kira shi a waya kuma yayi convincing dinsa, yanzu haka ma nasan sun dauko shi zuwa asibitin, duk wani arrangement da za’a yi an gama da bill da komai.”
“Nagode Saddam.”
“Ba komai sir, Allah yasa a dace.”
“Amin.” Ya amsa a chan kasan makoshin sa.
Sanda suka karasa asibitin su Ammar din sun riga sun karasa har Dr ya fara duba shi, office din head na department din Rafeeq ya wuce tare da Saddam dan dama abinda ya kawo shi kenan. Tarba ta musamman yayi musu ya basu waje suka zauna sannan ya yi musu bayanin matsalar kafar da kuma sauran tests da za’a masa a gano ainihin dalilin matsalar tasa, sosai Rafeeq ya gamsu da bayanin sannan yayi ma Dr din godiya suka fito yana jin a kalla yayi wani abu da zai faranta mata.
Dakin da aka bawa baban nata ya shiga, Ammar na tsaye kansa yana masa maganar ya kirawo wanda zai zauna dashi har ayi aikin sai gasu sun shigo.
“Welcome sir.” Ammar yace, mika masa hannu Rafeeq yayi suka gaisa sannan ya karasa gaban gadon da baban yake kai ya durkusa har kasa abinda yayi matukar bawa su Ammar din mamaki banda Saddam da ya riga ya san komai.
“Baba barka da wannan lokaci.”
“Barka dai, ya gida ya aiki?”
“Alhamdullillah Baba, ya kafar kuma?”
“Gata nan alhamdullillah, tunda mun zo nan zamu ga yadda Allah zai yi ikon sa, nagode muku sosai Allah ya saka muku da Alkhairi.”
“Amin baba, Allah yasa a dace.”
“Amin nagode muku kwarai, Allah ya raba ku da iayyen ku lafiya, Allah ya sa ku samu kuma masu yi muku. ”
“Amin.”
Suka hada baki suka amsa. Fita Rafeeq din yayi, yana fita Ammar ya sanar da Baba shine ya dauki nauyin aikin nasa.
“Allah sarki, ai da ka sanar dani tun wuri nayi masa godiya ta musamman.”
“Ai baya so ka sani baba, yanzu ma dan Allah ko zuwa yayi karka nuna masa ka sani, dan ransa zai baci akan hakan.”
“Allah sarki, toh shikenan ba damuwa, ba zan ce komai ba. Nagode nagode kwarai.”
***Relaxing yayi sosai a bayan motar kansa da yayi zafi ya ragu da kaso kusan talatin. Tunda suka baro asibitin yake jin sa sakayau har suka je sukayi sallar jumaa sannan yanzu suka dau hanyar komawa gida. Yana jin Saddam na magana da Asim dan shi kashe wayar sa yayi gaba daya dan baya so ma a kirashi. Suna gama wayar yace wa Saddam din ya kaishi gidan sa dake apo sai ya dawo ya dauke shi da chan yamma kamar karfe biyar haka zuwa da rabi. Da toh ya amsa suka fara biyawa ya shiga yayi masa order abinci sannan suka wuce gidan. Har ciki ya kai masa komai ya zube a falon sannan shima ya wuce gida ya dan samu huta kafin anjima din. Abincin ya dan chachakala ya zuba sauran a freezer ya dawo ya haye doguwar couch din dake falon yayi kwanciyar sa.
***Tana zaune tana jiran tsammani har azahar ta kawo kai, tashi tayi ta dauro alwala sannan ta shirya ta nufi kitchen din kawai, ta shirya komai da zata bukata sannan ta dawo daki tayi sallah sannan ta koma ta hau aikin nata. Tana cikin aikin Mummy ta shigo kitchen din tayi saurin zubewa a kasa ta shiga gaishe ta.
“In kin gama ki sameni a ciki.”
Amsawa tayi ta fice ita kuma ta cigaba da aikin duk babu dadi, tasan dole akwai dalilin irin wannan kiran, abu ne me muhimmanci shiyasa bata kira ko turo kowa ba tazo da kanta. Kasancewar bata yi wani girki da safe ba yasa aikin yayi mata yawa dan hadawa tayi gaba daya ta dafa komai. Bayan ta kammala ta jera yadda ta saba ta tsaya tana jiran Ben yazo ya duba shiru, ta dade a tsaye tana jiran sa be shigo ba babu ma alamun yana nan. Fita tayi kawai ta je ta kai abinciin ta daki sannan ta nufi wajen Hajiyan. Sai da aka fara sanar da ita sannan aka ce ta shiga. Ba ita kadai bace a falon Aneesa da Ummita sai Laila da ta dauko su a school ta kawo su gidan. Hira suke irin tasu ta yayan manya masu ji da kansu musamman Laila da take jin babu ita a haduwa. Idon su akanta har ta karaso tazo ta zube a kasa.
“Ji zubin munafukai.” Laila tace tana jan tsaki.
“Haka take ai, sum sum sum kamar mutuniyar arziki.” Aneesa ta dora tana jan tsaki.
“Kin gama shirya komai?” Mummy ta tambaye ta.
“Eh na gama.”
“Me ya faru da abincin ki na jiya, yarona yace baya so ba dadi. Kinsan dama saboda su na dauke ki aiki nake kuma biyan ki kudi masu yawa ko?”
“Na sani.”
“Toh me yasa zakiyi sakaci har ya gano wata matsala.”
“Dan Allah ayi hakuri ba zan sake ba, zan kula sosai.”
“It’s too late.” Tace tana daukar wayar ta, ta kira ta sakata a handsfree.
“Where are you?”
“Ok.” Sai ta katse wayar
“Jiya Aneesa ta ajiye gold bracelets dinta akan Island din kitchen, kin ganshi?”
“A ah Hajiya, banga komai ba.”
“Karya kike waye yake shiga kitchen din idan bake ba, dole kin ganshi ai.” Aneesa tace tana hararar ta
“Kinsan yaran talakawan nan da bakin hali, ta gani kila daukewa tayi ta saka cikin kayanta. Haka wata househelp da Mami ta taba yi, ta kwashe mana komai ta gudu.”
Laila ta saka baki tana yatsine
“Wallahi ban dauki komai ba, ban taba daukar abun wani ba.”
“Karya ne, taso Ummita muje mu yi searching kayanta.”
“Ku muje.” Laila ma tace suka tashi suka fita.
“Idan har suka samu abun nan cikin kayanki toh zaman ki ya kare a gidan nan.”
“Wallahi tallahi ban dauki komai ba.”
“Rike rantsuwar ki, bari su dubo su dawo.” Tace tana gyara zaman ta. Kamar minti biyar sai gasu sun dawo Ummita rike da bracelet din Laila kuma da wani designer watch na Rafeeq me shegen tsada.
“Uhum, aina kuka samo su?”
“A kayanta Mummy, ta hade su waje daya da alaama tayi shirin guduwa ne ma.”
“Hadda wannan agogon?” Tace tana zaro ido.
“Hadda shi.”
“Shiyasa Rafeeq ya nuna sam batayi masa ba, ashe ya gano wani mugun hali nata da bamu sani ba, ganin wai Hajiya Maryam ce ta kawo ta yasa na rabu da saka mata ido, ashe ita tace bari kuga.”
Kuka take tunda suka soma magana, tabbas an yi niyyar a ci mata mutunci ne, bata da bakin kare kanta tunda sun riga sun shirya abinda suke so su shirya din, ta barsu da Allah kawai.”
“Jaira me kalar munafukai, bani wayar nan na kira Hajiya Maryam kar taji da wai, dan yanzu sai taga kamar nayi rashin kyautawa.”
🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥
*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!
Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,
Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶
YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano
AMATULMALEEK
Mamuhgee
Guda biyun 1k
Guda Daya 500
Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
07040727902