Yanci da Rayuwa 20
Arewabooks; hafsatrano
Page 20
***Kwana biyu tsakani tayi ta jiran taji yayi mata maganar amma shiru, kyale shi tayi itama taga iya gudun ruwan sa yaushe zai fada mata. Normal suke yin maganar su kamar ma be san da maganar da Hajiya Maryam din tazo dashi ba, kyale shi yayi sai dai ta sake sosai dashi fiye da yadda suke magana a da kafin Baba ya sanar da ita maganar. Shi kansa ya ga chanji sosai hakan kuma yayi masa dadi har yayi deciding zai sanar da ita sirrin zuciyar sa sannan ya samu Mummy da maganar asan abinda ake ciki kawai zai fara zuwa wajen ta hira.
Apple over -ear headphone ne a kunnen sa yana tafiya zai fita daga part dinsu Aneesa ta tsaida shi, tsayawa yayi yana zare headphone din sannan ya harare yana tunawa da abinda ya faru ranar
“Mummy na kiran ka, tana part din AJI.”
Juya alakar fitar tasa yayi ya koma ta baya ya haura hallway din part din Ajin, a kofar ya tsaya ya cire headphone din sannan ya shiga yana saita tafiyar sa. Suna zaune gefen juna fresh fruits a ajiye a saman c-table din dake gabansu hannun Ajin na rike da green apple yana taunawa hankali yana amsa waya. Da hannu Mummy tayi masa alamar ya zauna, ya zauna yana maida kallon sa zuwa tv yana sauraron wayar da AJIn yake yana kyalkyala dariya kamar bashi ba.
“Baka da dama honourable, shikenan zan sanar da kai date din da za’a je aga iyayen, sai ku wakilce ni dan dama kune iyayen, dan inaga gobe zan yi tafiya zan kuma yi kamar 3weeks haka.”
“Toh shikenan, sai kaji ni. Nagode honourable.”
Kashe wayar yayi yana cigaba da dariyar farin ciki, kallon sa Mummy take tana tayashi dariyar
“Kinji wai honourable ne ke tsokana ta wai mijin minister, shine nace bansan yaushe akayi wannan maganar ba.”
“Ai akwai shi da tsokana.”
“Yanzu dai na wakilta su, sai a sanar musu da ranar da zasu je tambayar, zasu tafi da komai har sadaki dan tunda ba karamin gida bane kar a tsaya wani bata lokaci.”
“Hakan ma yayi sosai, Allah ya kaimu da rai da lafiya, ko baccin kirki kwana biyun nan bana iya yi saboda maganar nan, wai yau nice zan yi auran d’a, ai ba dan kace a bar hidimar bikin har sai ka dawo ba da yanzu za’a yi komai.”
“Hajiya kenan, yanzu dai ina Wakili?” Yace yana kallon Asim da yayi zuru yana jin hirar tasu da ya fahimci akan maganar auren Rafeeq ne.
“Gani AJI.”
“Yawwa, mahaifiyar ku kullum tana min korafin naki saka akan harkar kasuwancin mu na waje, saboda haka na yanke shawara gobe idan Allah ya kaimu zamu tafi Lagos ni da kai, daga nan zamu wuce Mexico.”
Washe baki mummy tayi cikin jin dadi tace
“Kai Masha Allah, shikenan kaga shima Rafeeq ai ya samu hutu,gashi zai angon ce ai dama yana bukatar ya huta.”
“Allah ya kaimu.”
Asim yace a sanyaye, be so tafiyar a lokacin ba amma babu yadda zai yi, dole yaje dan be isa yace wa AJI a ah ba. Tashi yayi ya fito sai ya rasa me ya kamata ma yayi ganin time din flight din nasu da safe ne karfe takwas, fasa fitar da yayi niyya yayi, ya koma daki ya dan dauki yan formal kayansa kadan a suitcase sai passport dinsa da wasu important abubuwan da zasu bukata saboda visa on arrival ne sai ya rufe ya ajiye sannan ya zauna yana duba schedules dinsa na gaba daya week din wanda dole ya ajiye su a gefe har sai ya dawo. Yayi niyyar zuwa ya ga Noor a goben suyi magana face to face yanzu gaba daya plan din ya rushe. Tashi yayi ya sauya kayan jikinsa ya feshe jikin da perfumes masu dadi da sanyin kamshi sannan ya fita, be tafi da kowa ba motar sa kawai ya ja ya nufi unguwar su dan baya jin zai iya tafiya be ganta ba, yana ji a jikinsa kamar wani abu zai faru kafin ya dawo gwara ya sanar da ita komai idan yaso ko waya ce sun cigaba da yi kafin ya dawo. Sai da yaje layin su sannan ya kira wayarta ga mamakin sa sai jin ta yayi a kashe, awa daya da ta wuce sunyi waya yanzu kuma a kashe ga wuta kuma a layin bare ya zata ko chargy tasa. Zama yayi a motar ya cigaba da gwada wayar har kusan minti talatin ta tura mata text message shima no reply shiru shiru har tara da yan mintuna sai kawai ya hakura jiki babu kwari ya tada motar ya bar unguwar.
***Sake saka battery tayi amma kemaimai wayar taki tashi, sosai ruwan ya shiga cikinta dan haka dole ta hakura ta cire komai ta bazata zuwa gobe ko zata tashi, tasan zai kirata tunda yanzu kusan kullum sai ya kirata da daddare sun dade suna magana dan haka duk sai taji babu dadi haka dai ta hakura ta kwanta sukuku Baba na lura da yanayin ta tunda wayar ta fada ruwa sai kawai yayi murmushi yana mamakin yadda har ta saba dashi haka.
Kasancewar tafiyar AJI ce babu bata lokaci ko da yayi sallar asubah be koma ba ya hau shiryawa dan yasan ko minti daya Ajin baya karawa akan time din da yace zakuyi abu, sai da ya kara gwada kiran nata still a kashe sai kawai ya hakura ya fito rike da suitcase din da sauri Jamal ya karba masa ya kai masa Range Rover din AJIn da zasu tafi a ita ya saka sannan ya rufe. Saman dinning ya zauna yana zama sai ga Rafeeq ya fito a shirye cikin blue black suit jacket da trousers sai white collared shirt da blue necktie kana gani kasan wani muhimmin meeting din zashi. Hannu ya mikawa Asim din suka yi musabiha sannan yaja kujerar kusa dashi ya zauna yana kallon varieties na abinciin dake kan dinning din. Chips kawai ya zuba da shredded Chicken ya hada da hot tea yaci kadan saboda safiya ce baya iya sskewa ya wani ci abincin sosai. Same abinda yaci shi Asim din ma yaci suka tashi a tare suka nufi part din AJIn.
“How many days zakuyi a chan?” Rafeeq ya tambaya dan tun a daren jiya AJI ya sanar dashi da tafiyar tasu.
“Ban ma sani ba wallahi, naji dai AJI na waya yana cewa zai yi 3weeks kafin ya dawo, bansani ba ko har da ni za’a yi 3weeks din.”
“Ok best of luck bro, ka kula sosai sannan ka saka ido a komai. Kazo min da report na duk abubuwan da kukayi sai mu duba su tare.”
“In sha Allah.”
A falon suka zauna suka jira Ajin ya fito suka dunguma suka fita tare yana gaba suna binsa haushin Mummy na karuwa ganin Lagos din ma sai an je da Rafeeq din da masifa ita bata ma san sanda ya fada masa ba sai yanzu da ta gansu tare take tambayar shi ina zashi anan taji wai ashe meeting din da za’a yi a Lagos din tare dashi zasu.
“Jaraba.”
Tace tana komawa cikin ganin motocin sun fice daga gidan. Su biyu ne a bayan black Range Rover din Rafeeq na ta duba wasu sakonni a mail dinsa shi kuma Asim duba wayar sa yake ko Noor tayi masa reply amma shiru, sosai abun ya dame shi amma sai ya danne har suka karaso airport din suka yi bording sai Lagos.
Karfe tara da rabi suka shiga meeting din na two hours ne dama daga nan suka fito zuwa hotel din da Rafeeq din zai zauna na kwana biyu, wanka Asim ya sake ya sauya kaya sannan sukayi lunch zuwa 3 suka sake fitowa suka je suka samu AJI a suite dinsa sannan drivers suka dauke su zuwa airport. Rafeeq na tare dasu har aka gama duk wasu formalities ya tabbatar sun yi bording sannan ya dawo hotel din.
***Ruwan da wayar tasha ya hanata kunnuwa dama ta gaji ta zama sai a hankali dan b3 din ma sai an masa ciko yake kai labari. Har sha biyu shiru wayar taki kunnuwa kawai sai ta tambayi Baban ta shirya tace zata kai gyaran Garki market ya bata kudi yace ta taho musu da dan abubuwan da zasu bukata. Tana fita Hajiya Maryam na shigowa sai dai wannan karon ita da wasu mata ne su biyu sai yaran ta dake mata aiki a restaurant dinta dauke da wasu silver flats masu kyau da kyalli sai wasu kwalaye manya suka dire a tsakar gidan sannan suka fita.
“Sannun ku da zuwa.”
Baba yace ya mike ya dan lallaba kafar ya dauko tabarma dayar matar ta karba ta shinfida suka zauna.
“Sannu Baban Fatima.”
“Yawwa Hajiya, kunzo lafiya?”
“Lafiya lou Alhamdullillah, ya kafa? Naga kafa tayi kyau Masha Allah.”
“Ah kafa Alhamdullillah wallahi, da sauki sosai.”
“Allah ya kara lafiya.”
“Amin.” Suka hada baki gaba daya
“Lafiya kuwa? Tun jiya nake kiran wayar ka a kashe haka wayar Fatima ma a kashe, dalilin da yasa dole na taho kenan.”
“Wallahi wayoyin ne sai addua, ni dama tawa ta lalace yau kusan kwana uku kenan, tata kuwa jiya da daddare ta fada ruwan chan shikenan taki kamawa yanzun nan ta fita kai ta gyara na dauka ma kun hadu a hanya.”
“A ah bamu hadu ba, yanzu ta fita kenan.”
“Yanzu yanzu kuwa.”
“Toh magana ce ta taso dama, kasan munyi magana nace sun ce zasu sanar ranar da zasu zo, toh jiya ta kirani tace gobe zasu zo, shine fa nayi ta kira na sanar sai kuma naji waya a kashe, dole na ture aikin gabana na taho.”
“Allah sarki, wallahi matsalar waya ce.”
“Toh yanzu ina muka kwana?”
“Eh na kira dan uwan nawa, munyi magana na sanar dashi komai. Yanzu zan sake kiran shi sai na sanar masa da zuwan nasu gobe.”
“Toh hakan yayi, ga wannan kayan nan, a tafi dasu chan gidan nawa gudnmawar kenan na sallamar bakin.”
“Kai Hajiya, wannan dawainiya haka, nagide nagode Allah ya saka da Alkhairi.”
“Amin ya Allah, babu komai me gidan ma na sanar dashi yace zai shiga duk sai a hadu a karbi tambayar. Inaso Fatima ta fito itama tamkar kowacce diya, dan haka dole sai munyi abinda ba zai zamar mata gori ba.”
“Haka ne, nagode kwarai Allah ya saka muku da Alkhairi.”
“Amin ya Allah.”
“Yanzu idan muka fita sai mu mika kayan chan kawai yafi azo ana tunanin Wanda zai kai, tunda gidan ba boyayye bane ba.”
“Wanne gida ne?” Matar da suka zo tare ta tambaya
“Gidan Alhaji Isma’il Gashash ne.”
“Ah dole kice ba boyayye bane ba, kamar a maitama yake ko?”
“Eh a chan yake.”
“Lallai.”
“Ku tashi muna da abubuwan yi sosai, bari mu koma Malam, duk yadda ake ciki sai muyi waya a wayar Fatiman idan ta dawo.”
“Toh ba damuwa, nagode kwarai ku gaida gida.”
***Yadda kasan Mummy ta jawo daren gari ya waye saboda yadda ta matsu gobe tayi, sunyi waya sau kusan goma ita da aminiyarta Hajiya Lubabatu suna sake kitsa wata tsiyar, duk yadda suka tsara haka abubuwan suke tafiya. Har Allah Allah take gari ya waye wakilan da AJI ya wakilta suje su nemar wa Rafeeq aure, auren yarinyar da babu wanda yasan asali da dangin su, talakawan gaske wanda AJI ya tsana yake kyama. Yarinyar kuma da shi kansa Rafeeq din yace baya so a sallameta, yarinyar kuma da Asim yake jin zai iya yin komai akanta. Na farko tayi nasarar chusa ma Rafeeq abinda baya so a matsayin matar aure haka kuma ta masa zabin ta yasan AJI ba zai taba ba sannan uwa uba zata samu nasarar raba alakar dake tsakanin Rafeeq din da Asim zata chusa gaba da kiyayya a tsakanin su ta yadda Asim zai yi duk yadda zai yi wajen ganin ya karbe ragamar komai daga hannun Rafeeq din sannan ya nuna masa tsantsar kiyayya irin wadda ta dade tana fata da buri.
Rafeeq na Lagos be dawo ba a ranar saboda ya gaji da Abujan so yake ya sake hutawa sosai kafin ya dawo at least zuciyar sa zatayi sanyi daga ciwon da yake addabar ta. Kiran sa Saddam yayi bayan Ammar ya kirashi ya fada masa komai dake faruwa yaji yaushe zai dawo Amma sai yace masa be gama abinda yake ba, yaso yace masa ya dawo amma sai kawai ya kashe wayar ya barshi rike da tasa a hannu. Murmushi yayi dan ya tabbatar idan har abubuwan da suke faruwa suka tabbata Rafeeq din sai yafi kowa murna duk a yanzu yana nuna baya son maganar kamar ma ya hakura amma yasan shi sarai karfin hali ne kawai. Be sake kiran nasa ba, sai ya kyale shi kawai yasan dai duk tsiya zai dawo ne, kuma kafin nan suna fatan komai ya tafi cikin tsari.
****Washegariiiiiiii