Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 38

Sponsored Links

PAGE THIRTY-EIGHT*

 

Miqewa Hajiya tayi ta zugewa Umaimah rigar jikinta ta sanya hanunta ta ciro nononta ta dago yarinyar ta sanya mata a bakinta yarinyar ta kama tana tsotsa ya zubawa nonon nata ido yanajin wani shauqi da feeling na bijiro masa da sauri ya miqe ya fita daga dakin don ya fahimci zamansa zai iya haifae da matsala ko wanne lkc zai iya kai hanunsa ya cafki nonon ya taya yartasa sha.

Related Articles

 

Gidansa ya nufa yayi wanka sannan ya fara sanar da abokan arzikin sa anyi masa haihuwa matarsa ta haihu harda hotunan da yayi da bebyn ya dora a status dinsa na WhatsApp da Facebook aikuwa ya samu addu’a sosai zama yayi dirshen yana kallon bebyn da yayima huduba da sunan Hajiyansa Zulaiha yana kallon hoton yana hawaye yana Istigifari nadama yake da zuciya me tsarki tabbas ya aminta so masifa ne saboda sone umul aba’isin faruwar komai tsakaninsa da qanwar tasa amma meye ya sabbaba hakan? “Hajiya” ya fada a fili tare da cewa “itace taja mana komai amma yanzu laifina suke gani saboda nine mara gata”

 

Wayarsa ya dauka a karo na ba adadi ya kira layin Umaimah amma a kashe yasani koda a kunne take ba dagawa zatayi ba saboda ta dade da ajiyeshi da rayuwarsa a gefe gashi shikuma sai yanzune ma yake qara gasqata cewa soyayyarta itace take sarrafa rayuwarsa komawa yayi ya kwanta a kujera ya zubawa hotonsu ido lkcn farin cikinsu nanan bai gusheba shi abin ar mamaki yake bashi yanda yake hangen tsantsar qiyayyarsa a idon Umaimah Umaimah da a baya yake sarrafata da zuciyarta yanda yake so.

 

Da wadannan tunane² ya kwana da safe ya tashi ya shirya domin tafiya aiki saida ya fara zuwa yaga lfyr Umaimah da bebynsa daya laqabawa Shurafah sannan ya haura sama gurin Daddy daya dawo daga tafiya jiya da dare suka gaisa yayi masa barka kamar abin arziqi sannan yace.

 

“Alhmdllh babana Ina tayaka murnar samun qaruwar da kayi taya mace naji karar da kayiwa mahaifiyarku ka kyauta daka sanya sunanta wa baiwar Allan nan Shurafah so kamar yanda na fada maka lissafin da mukayi a baya zai canza ne bayan haihuwar Umaimah to alhmdllh ta sauka lfy saboda haka yanzu zabi biyu gareka kodai ka karbi yarka ka nemi wacce zata shayar maka da ita ko kuma ka rinqa biyan uwarta take shayar maka da ita”

 

Mamaki ne ya kusan kashe Hameed wannan fah shine tsugunu bata qareba ansai da biri ansai mage.
A sanyaye ya dago yace “amma Daddy na dauka cewa Umaimah koba itace ta haifi Shurafah ba ita me riqemin itace ta shayarmin da ita batare data nemi ko qwandala daga gurina ba….”

Daga masa hanu Daddy yayi yace “ai wai da take uwar tata shiyasa muka fada maka haka dama da ace ba ita ta haifaba ma aida mu da kanmu zamu bata ta shayar maka da ita saboda haka zabi ya rage naka idan ka yarda zaka rinqa biyane to wajibine duk wata ka kawo min 5 million na ciyarwa”

 

A matuqar mamakance ya dago yace “5 million fah Daddy me Shurafah zataci da har zata cinye 5 million a duk wata Daddy duk mutanen dake gdannan ma bazasuci 2 millions a wata ba balle jaririyar da aka haifa jiya?”

 

Shiru Daddy yayi ya dauki wayarsa ya fara latse² bayan yan sakanni aka daga yace “kuzo dukkanku inason ganinku a parlourn sama” yana fadin haka ya kashe wayar yaci gaba da duba wayarsa yana murmushi irin nasu na manya,
Shigowa sukayi suka hada ido ita dashi gabanta ya fadi sosai saboda wani kyau da taga yayi mata duk da ramar da yayi.

 

Daqyar ta iya samun guri ta zauna saman tumtum saida Daddy ya gama danne²nsa yace “Hajiya bashi yarsa” dagowa sukayi da sauri musamman Umaimah da taji mgnr kamar dirar kwarankwatsa a kanta.
Miqawa Hameed yarinyar Hajiya tayi jikinta a sanyaye hanunsa na rawa ya karba yana cije lebe wasu hawaye masu zafi suka zubo masa ya kwantar da yarinyar da taketa sharar baccinta a cinyarsa ya dago ya kalli Daddy yace.

 

“Na yarda zan rinqa badawa Daddy ka taimakeni kabar yarinyar nan a gurin mahaifiyarta idan na tafi da ita bansan ya zanyi da ita ba ko kuma ka mayar mana da aurenmu mu raini yarinyar nan cikin kulawar da duk wani da me gata yake samu a gurin iyayensa….” daukeshi da mari Daddy yayi yace “zaka tashi ka barmin gurin nan da shegiyar yarka kosai naci mutuncinka”

 

Miqewa yayi a matuqar sanyaye ya matsa gaban Umaimah da take kallon Daddyn tana mamakin furucinsa kalmar shegiyar daya Kira Shurafah da ita tafi komai dukanta ya dora mata babyn a cinyarta cikin kuka me ban tausayi yace “Koda kowa na duniya zaiqi Shurafah bai kamata ta rasa gata biyu ba nawa da naki Umaimah ni namiji ne banida nonon dazan bawa Shurafah ta rayu dashi kada kibada qofar rabaki da yarki da qaddara ta qadarta mata zamowa me rangwamen gata duk da nasani a gurin gama garin mutane take me rangwamen gata amma a gurina me cikakken gatace saboda na yarda itadin qaddara tace Umaimah babu wanda ya isa yayi maka wannan kyautar bayan Allah kuma bakida tabbacin sake samun wani bayan ita ta yuwu ita kadaice rabon dake tsakanina dake karki manta Umaimah kinsani komai yana faruwa ne bisa buwayar buwayi gagara misali badon hakaba dasai kice ya zaayi muna matsayin ma’aurata mu samu yarda bata sunnah ba to wannan kadai ya isheki misali ganin damarsa ne hakan ta faru Umaimah na roqeki kada kibada qofar banzatar da rayuwar yarinyar da bataji ba bata gani ba laifi nawane naji ayimin hukunci a kankin kaina amma kada ya shafi Shurafah dan Allah Umaimah…..”

 

Wata tsawa Daddy ya sake doka masa yace “wlh tallahi Hameed idan baka bacemin da yarinyar nan a gurin nan ba sainayi maka abinda baka taba tunani ba” jikinsa har bari yake ya miqe ya dauki yarinyar ya rungume a qirjinsa yana wani kuka mecin zuciya ya juya ya kalli Daddy yace “hakan ma na gde daka bari aka raini cikinta a gidanka amma kasani Daddy wannan zata zama rana ta qarshe da zaka rasani nima zanbar maka gdanka kuma Shurafah zatabar maka gdanka bari na har abada”

 

Yana fadin haka ya juya zai fice Umaimah tayi saurin riqo qafarsa cikin kukan tashin hankalin abu biyu rabuwa da yarta qwaya daya tak a duniya tace ““Ina neman alfarma daya Daddy baa matsayina na mahaifiyar Shurafah ba a matsayina na yar’uwar mahaifinta ta jini wacce zan iya fansar rayuwata da tasa ina neman izinin shayar masa da yarsa batare dako sisin sa ba Daddy na roqeka kayimin wannan alfarm…..”

 

Daka mata tsawa Daddy yayi yace “wlh baki isaba Umaimah saidai ki tashi kibishi tunda kin zabi farin cikinsa akan nawa kin fifita darajarsa da matsayinsa akan nawa to kitashi maza ki hada kayanki kibisa bana buqatar ganin shegiyar yarinyar nan a gdannan” bata iyajin kalmarsa ta qarsheba ta toshe kunnenta tare da sakinsa ta fashe da wani gigitaccen kuka me firgita zuciyar me imani tanaji tana gani ya juyo ya kalleta shima yana kuka daidai lkcn yarinyar itama tasa kuka da alamun nono take buqata amma ya juya ya fice da sauri ta miqe tana hada hanya zata bishi Daddy ya ruqo hanunta ta kuma rushewa da kuka tace.

 

“Tun safe Daddy Shurafah batasha nono ba ka taimakeni kabarni nabata koda shine na qarshe da zatasha daga jikina……” Dauketa yayi da wani gigitaccen mari tayi qasa ta zube yaraf ta qara dora hanunta a kanta ta rushe da kuka tace “shikenan Daddy ka rabani da yata qwaya daya tak a duniya….” Miqewa ta sakeyi da gudu ta nufi window daidai lkcn da Hameed ya kwantar da yarinyar a kujerar me zaman banza ya shiga ya tashi motar a guje yabar gdan har lkcn kuka yakeyi.

 

Zamewa tayi ta zauna a qasa tama manta da dinki akayi Mata soyayyar da da mahaifi ta mantar da ita ciwon komai sai ciwon rabuwa da yarta, saboda tsabar kuka har muryarta ta dashe Daddy ya tsallake ta ya shige dakinsa inda ta miqe tana hada hanya ta fita daga dakin ta fara taka matattakalar benen amma bata iya sauka ba jiri ya debeta tayo qasa luuuuuu daga saman ji kake tim ta fado tsakiyar parlourn qasan kamar matacciya Hajiya dake zaune take gursheqen kuka ta taso da gudu hakan yayi daidai da fitowar Kaka dake baccin asara a daki……

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/21, 9:52 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *GIDAN UNCLE*

 

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button