Yanci da Rayuwa 22
Arewabooks;hafsatrano
Page 22
***Tunda Mummy ta samu labarin uban kudin da aka tattarawa Noor din ranta ke baci, tana sane taki fara hado lefen da AJI ya bata kudi yace ta hada dan bata jin zata iya kashewa yar talakawa wannan uban kudin shiyasa taki siya duk da kuwa tafi karfin kudin amma bakin ciki da kyashi ba zai barta ba.
Da daddare suka yi waya da AJI ta wayar Asim dan shi a tsarin sa ba’a masa kira sai dai shi idan dan kansa yayi raayi ya kira toh. Maganar àbinda ya faru sukayi tana jin wani nishadi a muryar AJIn hakan kuma dama shine tsarin ta, zatayi amfani da Noor din ta karya tasirin Rafeeq din a wajen AJI da Asim din dan haka ne zata samu cikar burin ta. Karyar da murya tayi cikin kissa da kisisina tace
“Inaga me zai hana ya dauko matar sa kawai, idan yaso kafin lokacin bikin sun kara fuskantar juna.”
“Kinyi tunani me kyau, gwara su saba din duk da dai dama ba wai auren soyayya bane ba, auren cikar buri ne kawai.”
“Na’am?” Tace jin abinda AJIn yace sai kawai ya saka dariya sannan yace
“Akwai wani abu ne? Ko kin tsargu ne?”
“A ah ba komai wallahi, banji me kace bane ba.”
“Auw toh, yanzu zan kira shi na sanar dashi lallai ya dauko matar sa, zan saka Alhaji Mudi ya kira Alhaji Isma’il din ya sanar dashi tsarin mu.”
“Toh shikenn hakan yayi.”
Suna ajiye wayar ya dauki tasa wayar bayan ya mikawa Asim tasa ya shiga number Rafeeq din ya kirashi. Yana tsaka da tashin hankalin kiran AJIn ya shigo, ji yayi kwata kwata baya son magana da kowa a lokacin sai ya kasa daukar wayar har ta katse, tana katsewa wata ta sake shigowa, ya riga yasan AJI idan har yayi niyyar abu toh fa sai yayi shi yanxu idan be dauka ba, ba zai kyale shi ba har sai ya daga ya kuma sauke masa fada sannan ya fadi abinda ya kira yace sannan ya kashe. Dagawa yayi yana dafe da kansa da yake masa kamar zai rabe biyu cikin muryar sa da tayi wani irin dashewa sosai yace
“Assalamualaikum.”
“Wa alaikasalam. Ango kasha kamshi.”
AJI yace cikin sigar tsokana kamar bashi ba, runtse ido Rafeeq din yayi yana jin kamar da gayya AJIn ya fadi hakan tunda yasan shi sarai ba wai wasa yake yi dasu ba.
“Barka da dare AJI.”
“Barka dai ango, kana lafiya?” Karo na farko kenan da AJIn ya tambaya lafiyar sa tunda aka fara wannan dambarwar
“Alhamdullillah.”
“Toh madallah, sai kaji kuma abu ya juye ko? Toh damu hakan muke so dan ba bata lokaci zamu tsaya yi ba, yanzu ma kiran ka nayi nace maka lallai kaje ka dauko matar ka..”
“Idan min dawo sai ayi duk shagalin da za’a yi, dan dole ne ayi biki irin wanda ba’a taba yin sa ba a kasar nan.”
“In sha Allah.” Yace a takaice yana fata da burin AJIn ya katse wayar amma sai ya dora
“Mun baka zabin mu, idan har kana da taka zabin idan na dawo sai ka gabatar min da ita, na duba idan na tabbatar da dacewar ta da kai, zan je da kaina na karbar maka aurenta.”
“Nagode Allah ya kara girma.”
“Amin Amin, Allah yayi maka albarka.”
Ji yayi kamar an bugi kafafun sa da karfe ko katako me karfin gaske, jikin sa ne yayi wani irin sanyi. Ya dade yana burin jin kalmar daga bakin AJIn, ko da kuwa ta wasa ce sai gashi ya ji ta a lokacin da yake ganin kamar akwai rashin kyautawa a abinda akayi masa din.
“Ka kula sosai da duk hakkokin dake kanka a matsayin ka na namiji kuma shugaba, duk da dai bana jinka amma dole na fada maka, girma ne ya hau kanka yanzu dan haka dole sai kayi takatsantsan, kabi komai a tsari.”
Idan yace maganganun AJIn basu shige shi ba ko daya yayi karya, tabbas sun shige shi kuma sunyi tasiri matuka a gareshi har yake jin wani kaimi da karsashi na maye gurbin abinda yake ji a dah din.
“Allah yayi muku albarka baki daya.” Muryar AJIn ta sake riskarshi yana tsaka da tunanin yadda maganganun suke fita daga bakin AJIn zuwa kunnen sa cikin wani amo dake nuna tsantsar kulawa a cikin muryar AJIn.
_”Allah na roke ka, kasa biyayyar da nayi ma iyayena ta zama wani tsani na samun haske da farin ciki a rayuwa ta.”_
Adduar da ya dinga nanatawa kenan a lokacin da ya kai goshin sa kasa, cikin kankan da kai yana me tattaro dukkanin nutsuwar sa, yana fata da burin Allah ya amshi adduar sa, Ya dube shi Ya dubi halin da yake ciki ya kawo masa dauki.
A duk lokacin da ka shiga wani matsi na rayuwa ko tashin hankali, ka kuma maida dukkan al’amarin ka ga Allah, tabbas zaka ga sauki da haske, hakan ce ta faru dashi, daren da ya raba yana adduoi ya samu sauki sosai har ya tashi ya shirya shirin zuwa office, yana shiryawa yana tuna umarnin AJIn wanda ya tabbatar da dole ne ya cika shi, amma ba zai iya zuwa da kansa ba,zai tura su Saddam da Mummy din idan yaso su yi abinda ya dace dan baya jin zai dawo gidan yau da wuri ma akwai àbinda yake so ya karasa.
Suna hanyar office din ya kira Aneesa, yace ta kaiwa Mummy wayar, tashi tayi ta je ta kai mata yana kan wayar.
“Ya Feeqq ne.” Tace tana mika mata wayar. Murmushi ne ya subucewa Mummyn irin na mugunta sannan tace
“Son, sai yanzu ka tuna da uwar taka?”
“Ina kwana?”
“Lafiya lou ango kasha kamshi, jiya kuma sai kaki dawowa gidan, duk da nasan ka samu labarin abinda ya faru.”
“Eh na dawo late ne, shiuasa.”
“Ba laifi ai, kasan kai yanzu ango ne baka laifi.”
“AJI yayi min maganar dauko ta.”
Yace yana jin nauyin kalmar
“Ok eh munyi maganar jiya.”
“Ok, ayi duk abinda ya kamata.”
“An gama, ango.” Ta fada tana dariya. Kashe wayar yayi ya jefar da ita a gefensa ya kwantar da kansa jikin kujerar motar ya lumshe idon sa.
***Tana makale jikin kofar dakin tana sauraron wayar da Baban yake, tunda suka fara maganar ta fuskanci kan maganar duk sai jikin ta ya kara yin sanyi, komawa tayi ta zauna a gefen gadon ta jiki a mace ta tallafi kuncin ta da hannun ta biyu,bata san me yasa ba, duk sai taji bata da wani karsashi akan maganar auren, kwana biyu kenan har yanzu wayar Asim din a kashe take, gashi ita yanzu ba wayar whatspp a hannun ta bare ta duba shi online, duk sai taji hankalin ta be kwanta akan maganar auren da komai ba.
“Shikenan kuyi magana dasu.”
Yace yana ajiye wayar, sannan ya kwala mata kira. Tasowa tayi ta fito wajen Baban ta zauna ya kalleta.
“Nasan kinsan duk abinda yake wakana ko? Kin kuma ji maganar da mukayi da sama’ila.”
“Naji Baba.”
“Yawwa, toh kiyi hakuri kowanne bawa da yadda Allah yake tsara masa rayuwar sa, sannan dama duk daren dadewa in dai muna da rai da lafiya dole ne zakiyi aure, abinda nake so dake shine ki nutsu ki rike mutuncin ki sannan ki girmama mijin ki da iyayen sa, a duk binciken da nayi yaron bashi da matsala ko kadan mutumin kirki ne, ina kyautata zaton kinyi sa’a samun miji na gari kamar yadda nake addua a kullum idan nayi sujjada, dama shine fatana da buri na, nayi alkawari idan aka dan kwana biyu, zan dauke ki na kaiki wajen dangi na, dana mahaifiyar ki, dama nayi alkawarin duk ranar da Allah ya cika min buri na, na aurar dake zan kai musu ke, su ganki sannan su tabbatar da Allah ne me rayawa kuma babu wanda ya isa ya katse maka rayuwa idan har Allah be yi ba.”
Kukan ta ne ya karu sosai, ta kara bude baki tana yin sa sosai. Tun sanda ta budi ido ta ganta a duniyar nan, bata ganin ko daidai da rana daya da mahaifin nata ya nuna gajiya wa ko sarewa akan dawainiya da ita, shi yake mata komai tun bata san kanta ba, har ta mallaki hankalin kanta, ta zama mutum be taba gajiyawa da ita ba, ya kan boye damuwar sa domin ya sanya ta farin ciki, baya taba bari ta zubar da hawayen ta sai dai idan a bayan idon sa ne, shine uwarta shine ubanta shine abokin ta kuma shine komai nata, dashi ta ke rayuwa bata saba da kowa ba, bata saba da mutane masu yawa ba dan haka ne ma rayuwar ta a gidan su Asim bata taba damun ta ba dan dama ta saba. Shafa kanta yake yana murmushi a hankali yana jin yadda kukan nata yake fita
“Baabaa…” Ta kira sunan sa cikin muryar kuka
“Ke fa sokuwa ce, menene abun kukan?”
“Bana so na tafi, bana so na tafi na barka.”
“Toh mu tafi tare kawai.”
Yace yana dariya. Chusa kanta tayi a jikinsa tana cigaba da kukan. Da kyar ya samu tayi shiru sannan yace taje ta wanko fuskarta, ta shirya zasu fita wani waje. Tashi tayi ta gyara jikinta ta saka kayanta da Hijab suka rufe gidan suka fita.
***Yadda zuciyar sa take ta azalzalar sa da son ganin ta, ya kasa daurewa kawai yace wa Saddam suje unguwar tasu. Daga nesa sosai dasu sukayi parking kamar yadda ya saba ya zauna a motar yana kallon wajen yana tuna baya yana jin kamar ba zai iya cigaaba da juriyar da yake ba.
“Oga wai me zai hana kawai kasa mu sato maka ita kawai ku gudu daga kasar gaba daya.”
“You are not serious.”
Yace wa Saddam din, dariya ma maganar ta bashi kawai sai ya murmusa kadan.
“Allah sir, shikenan kaga an huta.”
“Mu wuce kawai.”
Yace yana kin bawa maganar Saddam din muhimmanci amma deep down yana jin dama zai iya hakan,da abinda zai yi din kawai kenan.
***Wani babban shagon furnitures Alhaji Isma’il ya je da kansa, ya karbi 30min ya duba kalar kayan da yake so yan ubansu sannan PA dinsa yayi payment sannan suka fito. Duk abinda yake yi so yake ya wanke kansa a wajen Baban duk da yasan abinda sukayi masa zai yi wahalar gaske ya manta har ya yafe musu amma dai zai cigaba da gwada saar sa tunda har da kansa ya neme shi ya kuma dora masa komai, shi kuma zai yi amfani da damar wajen ganin ya yi abinda zai wanka kansa. Kwana uku suka nema dama a basu su shirya komai duk da Mummy tace kar su sha wahala wajen zuwa da komai yadda idan ta tashi korar ta, daga ita sai kayan jikin ta zata yi gaba amma sai suka ce a ah dole zasuyi ma yar su abinda ya dace. Tsaki tayi tana raya sai kace wani abun arziki zasu kawo suke ta wani iyayi, Aneesa tasa ta gayawa Rafeeq din sai kawai ya bawa Saddam key din gidan bayan ya rufe bedroom dinsa ya je yayi lodging a hotel ya basu space suyi abinda zasuyi dan shi ba zai iya da iayyen su ba.
Tunda key yazo hannun Saddam ai sai ya shiga shirya abubuwan yadda yake so dan dama ya rasa yadda zai cewa Rafeeq din ya kamata a yi gyaran gidan amma yanzu da ya samu dama da go ahead dan yace masa duk abinda ya kamata ayi, ayi kawai. Tun daga kan furnitures din gidan da kitchen da komai sai da Saddam din yasa aka fidda su, aka siyo wasu aka chanja paint da komai hatta compound din gidan sai da yayi masa gyara na musamman. Daga shagon furnitures din gidan direct aka kawo furnitures din da Alhaji Isma’il ya siya bayan ya kira Baba yace za’a kawo masa ya gani amma sai yace a akai chan kawai sai yayi lissafi nawa ya kashe zai biya in sha Allah. Kashe wayar kawai yayi yana jin babu dadi yace akai chan din kawai.
Ana tsaka da aikin gyaran wajen suka kawo sai kawai aka shigar dasu aka hada komai zuwa washegari gidan ya dau saiti yayi wani irin masifaffan kyau daidai tsari da taste din Rafeeq din haka Saddam yayi komai. Rafeeq din ya kira ya sanarwa shi kuma ya kira Aneesa yace ta fadawa Mummy an gama. Tana fada mata tace tazo ta rakata suka taho gidan Rafeeq din, tun daga waje taga irin gyaran da akayi ma gidan sai da gabanta ya fadi, anya batayi shirme ba kuwa? Yar talakawa irin wannan ta shiga irin wannan daular anya kuwa? Daurewa tayi suka shiga gidan zuwa main ciki anan ne ta tsaya tana mamaki kala da haduwar kayan dake zube a falon uwa uba tsadaddun kaya yan ubansu. A rikice ta kira maigadi tace waye ya zuba kayan, anan ya fada mata daga gidan su amaryar ne aka kawo, sosai abun ya dake ta amma ta daure tunda tasan sun samu kudi sosai daga hannun abokan AJI sai kawai tayi concluding da shi sukayi amfani suka yi wannan kayan.