Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 30

Sponsored Links

Arewabooks hafsatrano
Page 30

***A darare ta kwanta daga gefen sa, be matsa mata ba dan yaga yadda yake a tsorace dashi sai ya kyale ta har sai da bacci ya dauke ta sannan ya matso ya gyara mata kwanciyar sosai a jikin sa.
Bacci sosai sukayi gaba daya Rafeeq zai iya cewa ya dade be yi bacci me dadin na ranar ba, shi ya fara farkawa bayan alarm din sa ya buga saboda yana tsoron makara ganin basu kwanta da wuri ba yasa ya saita alarm din. Hannu ya kai ya kashe ganin ta dan motsa baya so ta tashi. Da dabara ya mike yaje yayi alwala yazo ya fita zuwa masjid ya barta tayi baccin idan ya dawo sai ya tashe ta. Yana fita ta bude ido dan dama tun kafin alarm din yayi ta farka bata dai so ya gane ta tashi ne. Lallabawa tayi ta sakko daga gadon abun da ya faru na dawo mata vividly tayi saurin runtse idonta dan ko tunawa bata son yi. Dakin ta, ta lallaba ta shige sannan ta rufe kofar da key ta zauna a gefen gadon tana kuka. Jikinta gaba daya wani irin ciwo yake mata musamman kafafun ta sai da tayi kukan ta gama sannan ta lallaba ta shiga toilet ta sake hada ruwan kamar yadda yayi mata ta shiga tana lumshe ido dan zafin ruwan na ratsa ta. Sau uku tana fitar da ruwan tana sake shiga har ta danji daidai sannan ta fito ta dauro alwala ta dawo dakin tayi sallah.
Tana sallar ya murda kofar jin ta a rufe yasa shi juyawa kawai ya kyale ta dan ya lura tana bukatar space baya so ya kuma takura ta. A falon ya zauna ya kunna Sunna TV ana karatun al’qurani me girma cikin suratul Yusuf sai ya zauna kawai yana bi a hankali har ya soma gyangadi. Anan saman sofa din ya mike kafa ya kwanta yana kwanciya bacci ya dauke shi.
Karar door bell ce ta farkar dashi ya daga kansa da kyar yana kallon wall clock din yaga karfe tara har da rabi. Tsaki yaja kadan yana dana sanin kwanciya a falon haka dole ya mike ya nufi kofar ya bude yana kallon me bugawar.

“I’m very sorry.” Yace da sauri ganin fuskar Rafeeq din ba walwala sam.

Related Articles

“Drop it here.” Ya nuna masa gefen kofar daga ciki, ajiye basket din yayi ya juya shi kuma ya rufe kofar yana jan tsaki.
Kofar dakin ta ya kalla sannan ya kalli breakfast din wanda Mummy tasa aka kawo musu. Karon farko yaji be gamsu da abincin ba musamman da ya gano tana da wani motive akan auran nasu. Wucewa yayi kawai yaje yayi brushing teeth dinsa ya dauki wayar sa ya nufi dakin ta. Kofar a bude take ba kamar dazu ba, sai ya tura kansa ciki kawai bakin sa dauke da sallama.
Dakin a share yake fes an gyara gadon sai akwatin kayanta da ta dauko a dakin sa yana baccin ta hade su tsaf waje daya wanda ya siyo mata kuma ta zuba su a closet ta gyara ko ina dai har ta fito zata tafi fa ta kasa bude kofar falon kamar ya saka mata lock ko password bata dai gane ba. Ba kamar last time ba tana ja ta bude amma yanxu tayi tayi ta kasa ganin zai farka yasa ta jawo kayan ta dawo dakin tana kumbure kumburen.
Da ya shigo ko kallon sa batayi ba aka hada rai ciki ciki ta amsa sallamar ya kalli kayan nata dake gefe sannan ya kalli yadda tasha Hijab tuni ya gane abinda take nufi. Dariya ta bashi sosai har sai da ya dara abinda ya sake kular da ita ta cika tayi fam tana jin kuka na taso mata.

“Good morning my wife.”

Ya fada yana karasowa wajen ta, da sauri ta matsa kar ya taba ta, tana kumbura baki.

“Ni tafiya zanyi gidan mu.”

“Me yasa? Uhum?”

“Ba komai.”

“A ah dole akwai dalili, fadi min me yasa zaki tafi?”

Kallon sa tayi tana so tagane idan da gaske har fuskar sa yana so ta fada masa ne. Ganin yaci serious yana kallon ta yasa ta yanke shawarar gaya masa kawai.

“Dama.. ni na zata Asim ne mijin…”

Wani irin dip annurin fuskar sa ya dauke, yaji kamar ta dauki mashi ta buga masa a kahon zuciyar sa,ya dinga kallonta da wani irin yanayi na zallar bacin rai da rashin jin dadi.

“Asim ne mijin!? Tunda bashi bane ba zaki zauna ba? Shiyasa zaki tafi gida?”

Daga masa kai tayi alamar eh. Da sauri ya jingina da jikin bedside jin wata irin hajijiya na neman dibar sa tayi watsin mahaukaciya dashi. Kallon ta yake yana hango tsantsar gaskiar abinda take fada. Ransa ya kai kololuwa wajen baci, be sake ce mata uffan ba, ya juya ya fice daga dakin hade da bugo kofar da karfin gaske.

Zaman ta, ta cigaba da yi a wajen ba tare da ta damu da abinda ta fada din ba, tun abinda ya faru dadaddare ta yanke shawarar gaya masa gaskia kawai, ita Asim take so bashi ba, shi kawaii burge ta yake amma Asim shi da gaske son ta yake yi a gaban kowa kuma ya nuna,kuma tasan zai fi jin tausayin ta ma.

“Toh ke a ganin ki yanzu akwai wata sauran alaka tsakanin ki da Asim ne har yanzu? Ko kuwa kina tunanin dan uwansa zai rabu dake shi ya aura? Lallai baki da hankali.”

Wani shashen zuciyar ta ya tunasar da ita, sannu a hankali ta soma tunanin kirki da karamcin Rafeeq din, da wani irin halin sa da yasha banban da na sauran maza.
A tunanin ta zai dawo dakin ne a amma sa taji shiru, ganin zaman ba zai mata ba, yasa ta mike kawai ta sungumi kayan ta, tayo waje. Yana zaune yana shan coffee me zafi yana kokarin daidaita bacin ran da yake ciki ta fito. Yaji fitowar ta amma be juya ba, ya cigaba da abinda yake yi yana danne zuciyar sa har ta zo ta wuce shi ta nufi kofar. Sake kama kofar tayi ta bude amma taki buduwa tayi tayi yana jin ta ransa na kara baci

“Ka bude min.”

Tace da muryar ta kamar ta munafukai. Tashi yayi gaba daya ya bar falon dan baya so yayi mata abinda zai zo yana regretting amma tabbas tayi masifar bata masa rai. Kofar baya yabi ya fita daga main building din ya zagaya chan baya in da garden yake wanda yayi niyyar zagayawa da ita yau taga gidan sosai. Gefen wasu furanni ya zauna yana shakar kamshi da danshin wajen yana so zuciyar sa tayi sanyi kafin ya koma gidan.

***Duk yadda taso ta bude kofar ta kasa haka ta hakura ta dawo dakin tana kuka ta rafka uban tagumi gashi tana so ta kira Baba suyi magana tasan zai fahimce ta,amma switch off gashi ba wani iya operating wayar dama tayi ba dan ita android ma a cikin yan kananan tayi bata taba wata babbar android ba kaman su Samsung ko techno sai yan kananan wanda zaka ga sunayen su wani iri.
Tana zaune a dakin kamar marainiya tana jin marar ta na dan murda mata kadan ga wata yunwa da take taso mata dan ko da ta tashi ji tayi kamar an yashe mata cikin ta. Tana zaune har sha daya da rabi ko ruwa bata sawa cikin ta ba zuwa lokacin har ta soma galabaita gashi ko lekowa be yi ba bare yaga halin da take ciki, shi ya ma fice daga gidan duk da beyi niyyar fita ba ranar gaba daya amma ji yayi zaman ba zai yiwu ba dole ya fita idan ya cigaba da zama ciwo zai kwantar dashi.

Karar zuge gate din gidan ya fargar da ita, ta tashi da kyar ta leka ta window din gidan sai taga wasu shegun motoci guda biyu da bata san na Rafeeq din bane ko na waye sun shigo sun samu waje sunyi parking. Fuskar ta, ta kalla da tayi jeme jeme a mudubi idon ta ya kode kana gani zaka san ta yi kuka ta gode Allah. Doorbell aka taba tayi dan jim tana tunanin abun yi dan bata san ko wajen sa aka zo ba ko kuma yana falon ba. Jin shiru shiru be bude ba yasa ta fito da tunanin idan ma baki ne ita ya zata iya bude kofar tunda dai daga gani rufe ta yayi shiyasa ta kasa.

“Waye?”

Tace tana matsawa jikin kofar ta dan leka ta jikin dan opening din. Dafe kirjinta tayi gabanta na tsinkewa ganin Mummy da wata hamshakiyar mata sai Hajiya Lubabatu da suka kawo ta ranar tare

“Na shiga uku.”

“Ko ba zaki bude mana yar talakawa.”

“Ban iya budewa bane ba.”

Dariya suka kwashe da ita, mummy ta dan bugi kofar tana jin kamar ta faso kofar ta shigo tayi ta jibgar yarinyar dake neman zame mata alakakai musamman da Asim zai dawo gobe duk da ta shirya zuwan sa amma kuma dole tazo ta sake yin wani plan din anan din ma.

“Ki ja lock din sosai sannan ki cika malama, ba wata wahala bace ba.”

Yin yadda Mummy din tace tayi sai ga kofar ta bude Wanda daxu har hakan tayi amma kofar taki budewa sam.

“Tsiyar talaka kenan, wannan shegiya kofa abun banza ba zaki iya budewa ba.”

“Sannun ku da zuwa.” Tace jiki na rawa tayi gaba da sauri zata gudu daki ganin jibga jibgan matan da Mummyn tazo dazu.

“Ina zaki gudu? Al’mura dawo ki zauna.”

Dawowa tayi sum sum tazo ta zauna a kasan rug tana matse jikinta waje daya

“Ina Rafeeq din?”

“Nima bansani ba. Dazu dai yana falo.”

“Ke kina ina kuma?”

“Ina daki.”

“Kinji ko Hajiya? Ni nasan Rafeeq pretending ne kawai amma ba zai taba iya zama da yarinyar nan ba, nasan shi sarai nasan class dinsa, kawai dan kar naga gazawar sa yace yaji ya gani har yana manna jikin sa da nata a gabana.”

“Na yarda dake kam, namijin duniya ne ai ba zai taba bari kiga gazawar sa ba.”

“Aiko daga gobe zamu gani idan zai iya cigaba da pretending din, ke kuma.. ”

“Ki cire Asim daga ranki gaba daya dan ba sa’an auren ki bane ba. Sannan wannan auren naku nice nan na hada shi saboda cikar burina na raba soyayyar dake tsakanin Rafeeq da yarona Asim. Duk yadda naso na nunawa Asim ya tsani Rafeeq ya tashi tsaye ya kwaci dukiyar sa daga hannun sa ko su dinga juyata tare yaki, amma yanxu tunda gaki a tsakiya nasan zan samu cikar burina. Ki kwantar da kai kici arziki kafin yayi waje road dake dan nasan dole zai gaji da nuna ba komai din musamman idan kika chusa masa wani abun bacin ran dan nasan sai kin bashi haushi a yadda kike dinnan ba wayo ba aji sam.”

“Tashi ki bamu waje.” Tace tana jan tsaki. Mikewa tayi Hajiya Lubabatu ta bi tafiyar ta da kallo amma bata ce komai ba,dan bata tunanin abinda take tunani zai faru din.

Bata san sanda suka gama suka tafi ba, ta daina dai juyo hayaniyar su. Gaba daya bata da kuzarin yin komai saboda yadda kanta ke mata masifaffan ciwo wanda ya saka mata amai da zazzabi me zafi. Kusan azahar ta kasa jurewa, ta rarrafa da kyar ta fito falon ta samu abinci ta zuba kadan ta zauna ci, tana gama ci ta dawo dashi gaba daya. Tana kuka ta sake dawowa gaban gadon ta kwanta ciwon kan na sake matsa mata.
La’asar likis ya dawo gidan shima dan ba shi da wajen zuwa ne kuma, ya gama abinda zai yi ranar. Tunda ya fita ake cuku cukun samarwa baba sabon gida da zai zauna wanda baya so AJI yaji labari shiyasa be dauka a cikin gidajen sa da yake dasu ba, ya gwammace ya fitar da kudi a samu wani a siya masa.
Har ya wuce dakin sa yana danna zuciyar sa kar ta sashi zuwa wajenta amma sai ya kasa jin rashin motsin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button