Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 31

Sponsored Links

Arewabooks;hafsatrano

Page 31

****Kofar ya tura ya shiga dakin da babu haske ko kadan yana mamakin rashin hasken. switch din ya kama ya kunna sannan ya hange ta a chan gaban gadon, saurin karasawa ya dago ta gaba daya yana cewa

Related Articles

“Subhanallahi.”

“Baki da lafiya? Me yake damun ki?”

Da hannu ta nuna masa kanta, dagata yayi gaba dayanta ya dora ta a saman gadon yana jin yadda jikinta yayi zafi zau.

“What have I done?”

Yace yana kokarin zare mata hannun rigar ta dan yadda jikin yayi zafi yana bukatar rage mata kayan.

“I’m so sorry da na tafi na barki.” Ya sake fada yana fita da sauri. Wankakken mini towel ya dauko ya zubo ruwa a wata yar roba ya dawo dakin ya zauna yana jawo ta jikinsa gaba daya. Ruwan ya shiga danna mata yana jera mata sannu har ya samu zazAbin ya ragu sai ya tashi yana gyara mata kwanciya sosai ya sake fita.
Saddam ya kira yana fita yace ya turo masa Dr Mas’ud yazo gida ya same shi yanzu please. Sannan ya je kitchen ya dauko mata yogurt mara sanyi da cup ya kawo mata yana tunanin kila hadda yunwa a abinda yake damun ta.
Tana kallon sa har ya ajiye sannan ya dago ta, ya zuba mata a cup din ya shiga bata a hankali yana kallon yadda ta rame lokaci daya ga wani fari da ta kara daga jiya zuwa yau kamar babu jini a jikinta. Sosai tasha yoghurt din sannan ya balla mata paracetamol tasha ta koma ta kwanta ya dan rufa mata duvet ganin kamar sanyi take ji. Zama ya gyara a gefenta ya kama hannun ta ya rike gam a cikin nasa yana dan matsa mata shi a hankali duk ya damu wani irin tausayin ta na shigar sa. Haushin kansa da kansa yake ji akan biye ma shirmen ta da yayi duk da yasan dama hakan ne amma ya kasa controlling din kansa, yasan da ya zauna da ita a gidan babu abinda zai faru.
Kusan awa daya yana zaune yana kallon ta har bacci ya fara daukar ta, ta soma zufa alamun zazzabin ya sauka. Gyara mata kwanciyar yayi sosai yadda zataji dadi ya janye mata cover din. Kiran Dr Mas’ud ne ya shigo wayar sa, ya kalleta yaga ta soma bacci amma kuma tana bukatar ganin Dr din dan yasan maganin da zai bata. Ba dan yaso ba, ya tada ta ya taimaka mata ta mayar da rigar ta sannan ya saka mata Hijab ya riko hannun ta suka fito falon. Sai da ya zaunar da ita sannan yaje ya budewa Dr Mas’ud din kofar ya shigo suka gaisa sannan ya nuna masa wajen zama.

“Ina wuni?” Ta gaishe shi muryar ta na dan rawa ya amsa a sake sannan ya tambaye ta jikin nata.

“Da sauki.” Tace tana sake narkewa.

“Me yake damun ta Oga?”

“Fever ne da headache.”

“Taci abinci?”

“Bata ci ba, ta sha dai yogurt yanzu amma bashi da yawwa.”

“Akwai wani abu apart from headache din da fever?”

“Nan dina yana min ciwo, cikina kuma yana zafi sosai.”

“Kina da ulcer ne?”

“Umm.”

“Hadda ulcer oga.”

“Ok, ayi abinda ya dace.”

“Zan dauki sample na jinin ta, mu duba muga ko akwai malaria duk da nasan dai anan babu sauro, sai kuma treatment din ulcer din.”

“Ok.”

“Madam sai kinyi hakuri, zan dan dauki jinin ki kadan.”

“Kina jin tsoro?”

Yace mata yana kallon idonta, girgiza masa kai tayi tana nannade hannun rigar ta shi kuma ya taso bayan ya dauko tourniquet da syringe din ya dauka Rafeeq din na tallafe da bayan hannun ta yana mata sannu.

“Bari muje da Saddam sai ya kawo magungunan, Allah ya kara sauki madam.”

“Amin.”

Tace a hankali. Godiya Rafeeq din yayi masa ya rakashi kofa sannan ya dawo in da take.

“Me zaki ci? Ko Saddam ya taho miki da liver peopersoup da kidney? Ko me kike so?”

“Ba komai, kwanciya kawai zan yi.”

“Ok. Let me help you.”

Ya kama ta, ya kaita dakin sa ya kwantar da ita yana rage mata sanyin dakin sannan ya fito ya jawo mata kofar. Saddam ya kira ya fada masa abinda zai taho musu dashi sannan ya kashe.
Gaba daya daren jinyar ta, yayi dan amai ta dinga yi sosai har ya dinga tunanin ko asibiti zai kaita. Wajen asubah ya samu tayi bacci yaje ya watsa ruwa ya sauya kayan jikinsa a karo na uku daga farkon daren zuwa yanzu dan ta bata shi sau biyu sannan ya wuce masallaci. Yana idarwa ya dawo ya zare rigar ya kwanta a bayanta yana so ya dan samu baccin shima kafin ta tashi yaga yanayin jikin nata.

***Tun da rana Asim ya tattara koman sa ya hada su waje daya, saboda tafiyar dare zasuyi. Karfe sha biyu da rabi na dare jirgin su ya tashi direct sai Abuja dan AJI ya tsani connecting flight yace gajiya yake gashi jikin girma yawa yawan ma ya soma isar sa yana so ya dawo waje daya ya zauna ya nutsu ya bar musu ragamar komai.
Sanda suka iso Nigeria safiya ce saboda banbancin yanayi da lokaci. Mummy tuni ta shiryawa dawowar tasa tunda tasan zuwa sanda zasu sauka watakila Rafeeq din be tashi ba. Motocin AJIn na fake suna sauka suka shiga sai gida.
Da dan gudu gudun sa ya shigo falon yana kwala kiran Mummy din kamar wanda ya shekara baya nan haka yake ji. Duk nisan dadewar da zaiyi da gida baya wuce saudiya idan sunje Umrah ko Ethiopia sanda AJIn yana rik’e ambassador na Nigeria a kasar sai kuma sanda yayi karatun degree dinsa a University of California shima tattarawa Mummy tayi ta zauna dashi a chan din a lokacin tana wani course itama akan international relation sai ya zama wannan karon ne na farko da ya tafi irin haka babu Mummy din ba Rafeeq ko Aneesa daga shi sai Boss AJI duk a tattakure yayi rayuwar dan gaskia zama da AJI sai ka shirya aiki kawai shiyasa tasu ta zo daya da Rafeeq dan shi jurai ne a wannan fannin kuma dama bashi da hayaniya ko shiga cikin mutane shiyasa baya damuwa.

“Oyoyo my son.” Suka rungume juna tana cike da murnar dawowar sa

“Ya naga kayi kashin wuya ne?”

“Mummy aiki, ba dare ba rana fa, ni gaskia ba zan sake ba.”

“A haka zaka saba,dolen ka ne.”

“A ah mum, ga Feeqq dina nan shi zai cigaba da jan ragamar komai.”

Shiru tayi masa takaici na makure ta

“Ban sanar dashi mun dawo ba fa, so nake na huta sai dai ya ganni a kofar falon su, naje naga wace lucky girl din ce ta samu hot guy irin Feeqq, tayi babbar sa’a.”

“Go and freshen up, ka dawo kaci delicious din da na saka aka shirya maka, daga nan sai muyi magana kuma.”

“Ok favourite, bari na watsa dan na gaji sosai. Duk gajiyar nan amma a haka AJI ya wuce meeting wai, tab suna kokari wallahi.”

“Jeka dai.”

Tace tana tura shi. Part dinsu ya wuce yana cike da karsashi da jin dadin dawowar da yayi. Na farko zai ga family nasa ya kwanta a bed dinsa wanda yasan shi kansa yayi missing nasa, sai kuma yaje yaga queen of heart dinsa duk da sun hadu da wata hot babe a jirgi har sunyi exchanging contact amma shi dai Noor din kawai dan ya hangi wasu qualities da take dasu.
One hour ya dauka kafin ya fito yazo ya tarar da Mummyn tana jiran sa, da kanta tayi serving dinsa ta tabbatar yaci ya koshi kafin ta ce suje bedroom dinta.
Saman bedside ya haye ya zauna ita kuma ta zauna a gefen sa tana kamo hannun sa cikin nata.

“Me ya faru?” Yace ganin yadda fuskar ta, ta nuna damuwa gaba daya

“Abu zan fada maka amma dan Allah karka ce zaka tada hankalin ka, duk da nasan zai yi maka ciwo amma ya zama dole na sanar da kai.”

“Wani abu ne ya faru? Menene?”

“Maganar yarinyar nan Noor ce.”

“Please karki ce kin fasa amincewa, zuciya ta ba zata iya dauka ba, duk abinda nake a chan tunani na, yana nan ina Allah Allah nadawo a je a samu iyayen ta.”

“Na sani, kuma na amince maka tun ranar ka sani ai.”

“Eh.” Ya daga kai jikin sa nayin wani irin sanyi kalou

“Ita Rafeeq ya aura!”

A zabure ya mike tsaye yana sakin hannun ta ,idon sa a bude yace

“Rafeeq??”

“Eh, kuma duk da yasan kana son ta, dan ranar da mukayi maganar nan yana tsaye yaji komai,

“How comes? Ban gane komai ba wallahi, dan Allah Mummy ki ganar dani ko kice wasa kike min.”

“Da gaske nake, yayi threatening dina akan idan ban amince an je an nema masa auren ba toh abinda zai maka sai yafi haka, kasan ni kuma ina son ka, ina tsoron ya cutar min da kai, shiyasa na amince a babu yadda zan yi.”

“Innalillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun, Allahumma Ajirni Fi Musibati.”

Zama yayi dabas a kasa yana dafe kansa, cigaba da zuga maganar tayi

“Nasha fada maka Rafeeq ba son ka yake ba, baya kaunar ganin ka kana farin ciki. Kai kadai kake haukan ka akansa amma shi baya sonka, baya kaunar ka ko kadan. Amma baka gane ba, gani kake nice bana son shi.”

“Please Mummy, kice min ba da wasa kike ba, dan Allah Mummy.”

Zamowa tayi ta zauna tana dafa bayansa a hankali tana shafawa

“Calm down kaji, ka kwantar da hankalin ka. Karka bari wannan abun ya saka samun matsala. Go and confront him, ya fada maka dalilin da zai maka haka.”

Mikewa yayi kawai ya fice daga dakin cikin tsananin bacin rai. Murmushi Mummy tayi, tana fatan idan yaje din Rafeeq ya bashi amsar da zatayi daidai da abinda take fata.
Compound din ya fito yana kwala kiran driver, ya taso da gudu daga bakin gate yazo ya durkusa ya gaishe shi

“Bani key.”

“Ina zamu yallabai, Alhaji yace na daina bari kana fita da kanka.”

“Dallah ka bani nace ba dogon turanci ba.” Da sauri ya mika masa key din dake hannun sa, ya wuce ya shiga ya fita a guje daga gidan.
Cikin mintuna kadan ya isa unguwar saboda yadda ya dinga sharara gudu a titin gashi yaci sa’a babu holdup kwata kwata duk traffic din da ya wuce yana zuwa yake tafiya. Wani irin horn ya danna da karfin gaske gate man din dake dan gyangadawa ya tashi da sauri ya diro daga gadon sa ya fito sannan ya leka yaga waye. Sake danne horn din yayi yana jin kamar yabi ta kan gate din ya shige kawai amma sai yaga an shiga janye gate din, a guje ya kutsa kansa ciki ya yi wani irin parking yana fitowa ya nufi balcony din da zai sadaka da main house din.
Daidai lokacin Rafeeq ya tashi jin motsin Noor din sanda ta shiga toilet, murza idon sa yayi yana karanto addua yayi mika yana jin baccin be isheshi ba amma dole ya tashi ganin sha daya saura kadan.
Tashi yayi zaune yana mikar da kafar sa ya jingina da jikin gadon yana facing din hanyar toilet din. Knocking yaji kamar anayi hade da karar door bell duk a lokaci daya, mamakin wanda zai zo a lokacin yayi amma sai ya tuna sakon Mummy na jiya da ta aiko musu da breakfast kila gateman din ne yau ma ya karba ya kawo. Diro kafarsa yayi kasa yana zura bedside slippers dinsa daidai lokacin ta fito fuskar ta da jikinta jik’e da ruwa alamun wanka tayi. Kallon sa tayi kadan sai ta wuce wajen kayan tana jin nauyin sa sosai tana kuma jinjina kulawar sa gareta.

“Come here.”

Yace mata yana daga tsaye gaban gadon. Takowa tayi a nutse tana jin ta sakayau kamar iska zata dauke ta. Hugging dinta yayi tana karasowa yana lumshe ido kafin yace

“Ya jikin naki?”

“Naji sauki.” Tace da soft voice dinta dake nuna rashin lafiyar ta

“Sannu, Allah ya kara sauki.”

“Amin.”

“Ki shirya bari naje naga wanda ke mana wannan bugun.” Ya saketa yana yin gaba, har ya kai kofar ya kama handle din yaji tace

“Thank you.”

Dan waigowa yayi kadan ya sakar mata murmushi kawai kafin ya karasa ficewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button