Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 36

Sponsored Links

Arewabooks hafsatrano

Page 36

***Yau ba kamar ranar farko ba, ta karbi sakon da yake son isar mata cikin dakiya duk da tasha bakar wahala kamar ranar amma bata so yayi fushi, ko ta katse shi dan yadda ya zamar mata kamar karamin yaro a gaban mahaifiyar sa. Ya jaddada mata irin kaunar da yake mata har ta ba zai kirgu ba, mamakin ta yadda akayi yake mata irin soyayyar da yake furta mata wadda take ganin ta a zahiri da kuma aikace. Duk da tayi kuka yau din ma kamar ranar amma ta daure sosai, albarka ya dinga saka mata yana shafa gashin kanta da ya barbazu a saman gadon yana jin su da danshin hawayen ta. Tare suka tashi ya taimaka mata ta gyara kanta shi kuma ya wuce dakin sa achan yayi wanka hade da alwala yazo ya fuskanci al’kibla. Yana da kyau duk sanda Allah yayi maka wani abu na farin ciki da jin dadi ka gode maSa, ba sai kana bukata zaka fuskance shi ba. Raka’a biyu yayi, yayi addua sosai ga mahaifiyar sa da duk wanda suka riga mu gidan gaskiya sannan ya roki Allah ya hana Mummy samun tasiri a akan Asim dan ba zai iya jure rashin sa kusa dashi ba, Asim mutum ne na gari me dadin zama da kaunar duk wanda ya rabe shi, ya sani sarai akwai ciwo abinda ya faru amma zai jira shi,har ya huce yazo ya sameshi su daidai ta kansu, duk abinda ya faru dama mukaddari ne, Allah ya riga ya kaddara musu hakan a rayuwar su dole sai suyi hakuri su karbi komai su cigaba da rayuwa.
A nannade ya same ta cikin duvet tana baccin ta peacefully, kyakkyawar cute face dinta ya dinga kala yana jin wani shaukin soyayyar ta na fuzgar sa. Kissing forehead dinta yayi a hankali sannan ya haye gadon ya shige jikinta bayan ya rage rigar da ke jikinsa.
Ita ta fara tashi bakin ta dauke da adduar tashi daga bacci, lokacin anyi kiran farko, zamewa tayi a hankali ta wuce toilet tayi alwala tazo ta tada sallah raka’atanil fajr tana idarwa shima ya tashi. Mika yayi yana salati kafin ya waiga gefen sa yaga wayaam, da sauri ya tashi zaune sai ya hange ta akan abun sallah tana addua a hankali gudun kada ta tada shi. Sakkowa yayi ya isko ta ya rankwafa ya manna mata kiss a cheeks dinta sannan ya wuce toilet ya dauro alwala, tashi tayi ta bashi wajen yayi nafilar shima sannan ya wuce masjid bayan yaje dakin sa ya saka wankakkiyar jallabiya ya fesa turare.
Tana zaune saman abun sallar ya dawo, zuwa yayi ya zauna ya tankwashe kafar sa yana fuskantar ta.

Related Articles

“Ina kwana?” Ta gaishe shi a kunyace ganin yana mata wani kallon kasa kasa.

“Lafiya lou, kin tashi lafiya?”

“Lafiya lou.”

“Ya gajiya kuma?”

Ya kanne mata ido daya, turo baki tayi tana kauda kanta gefe ta gane sarai àbinda yake nufi sai ya sa dariya yana mikewa

“Yau 8 zan fita office, zo mu dan kwanta zuwa 7;30am.”

Noke kafadarta tayi alamar um um sannan tace

“Akwai abinda zanyi a falo.”

“Me? Ba dai shara ba ko? Yau zasu dawo masu aikin akwai dakunan su a bq kuma, anjima ki dudduba gidan akwai love garden idan kinji boredom ya dame ki.”

“Ok tam.”

“Oya zamu kwanta, inaso naji ki kusa dani.”

“Um um ni ba bacci zan ba.” Ta fice da sauri. Murmushi yayi ya rufe idonsa nan da nan bacci ya dauke shi dan daren ranar ba wani bacci ya samu ba.

Falon ta fara gyarawa sannan ta wuce kitchen lokacin rana ta soma hudowa. Breakfast ta shirya masa me rai da lafiya kamar yadda ta saba a gidan su da tana aiki, ta jera komai a saman dinning sannan ta wuce dakin sa, ta gyara abinda zata gyara ta yi wanka lokacin bakwai da rabi, daure da towel ta nufi dakin ta tunda duk kayan ta a chan suke ta bude kofar a hankula sannan ta shiga sad’af sad’af dan kar ta tada shi. Tunda ta shigo ya farka yana kallon ta har ta isa closet dinta ta bude zata dauki kayan da zata saka. Yaye duvet din yayi ya sakko shima a sand’a din kamar yadda ta shigo bata ji tafiyar sa ba sai ji tayi an rungume ta, ta baya gaba daya. Da farko tsoro taji ta dan yi kara kadan kafin ta hau sauke ajiyar zuciya tana kokarin juyowa. Hanata yayi ya kara kankame ta yana shinshinar jikinta yana shakar kamshin jikinta.

“Zaka makara, 7:30 ta wuce.”

“Ai baki zo kin tashe ni ba, da kika shigo ma tip toeing kike dan kar na tashi.”

“Kaya zan saka fa.”

“Shine bakya so na ganki.”

Daga masa kai tayi alamar eh, sai yayi murmushi irin na mugunta din nan sannan ya cije lips dinsa yana kama towel din ya sauke shi kasa gaba daya.
Ihun shagwaba ta saka masa tana yin saurin makale jikinsa ta chusa fuskarta a cikin kirjinsa tana kai masa dukan wasa. Take towel din yayi da kafar sa, sai da ya more kallon sa sannan ya dauka ya zagaya mata shi a jikinta yana kallon kwayar idon ta da lumsassun idanun sa da suka shige ciki, ba dan AJI ba yasan da wuri zai fita ba, da ba abinda zai hanashi karbar hot tea dinsa amma ba komai akwai next time. Fita yayi ya barta tana kukan shagwaba ya wuce dakin sa yaje yayi wanka ya fito a shirye cikin wani farin voile me tsada dinkin doguwar riga da wando. Yana karya hular da zai saka ta turo kofar ta shigo rik’e da wayar sa dake ta faman ringing, mika masa tayi maimakon ya karbi wayar ita kadai sai ya hada da hannun ta ya rike sannan ya zame wayar ya rike ta da dayan hannun yana kallon me kiran nasa

“Sun karaso kenan.” Yace ba tare da ya daga ba, suka fito a tare zuwa falon. Dinning suka wuce ya zauna ta zuba masa breakfast din yana ta faman kallon ta yana mamakin yadda ta sauya lokaci daya. A tsanake yayi breakfast din yana more kallonta dan duk sai yaji ma baya son fita amma dole ce ba yadda zai yi, jan ta yayi har kofar sannan ya bude mata hannunsa, ya kunyace ta taho ta shige tana sunne kai, yan sakanni suka dauka a haka kafin ya cikata ya juya ya fita, ita kuma ta juya zuwa falon tana jin gidan na yi mata wani irin girma.
Sai da taji tashin motocin sannan ta tashi taje tayi breakfast ta dawo ta zauna ta kunna TV ta kamo arewa 24 tana dan kalla har ta gaji. Wayarta ta dauka tayi downloading whatsapp ta duba yan contact din nata da basu da yawa ta gano wata class mate dinta sai tayi mata magana tayi sa’a kuwa tana online suka gaisa sannan tace mata idan tana da novels masu dadi ta tura mata dan sanda suna school ita ce me turawa mutane tana jinsu bata dai taba cewa a tura mata ba dan lokacin wayar tata akwala ce bata kuma ma damu da ita ba.
Kamar wasa ta kashe datar ta zauna ta hau karatun sai gashi ta zarme da ta gama page daya sai tace dashi shi ta hakura amma ta kasa, wasa wasa sai gashi tana neman gama book din wanda tayi masifar karuwa musamman ta fannin kula da miji da yadda zata tafiyar da rayuwar gidan auren ta, idan ta cire kunya tayi abinda ya dace. Samun kanta tayi da hasaso kanta a matsayin yarinyar littafin har tana kwatanta yadda zata yi wasu abubuwan kama daga tsaftar gida da ta muhalli, kamshi da ado ya zama cikin priority dinta sannan uwa uba ladafi. Wajen sha biyu taji ana ringing bell ta tashi ba dan taso ba, ta maida wayar chargy taje ta bude. Wasu mata ne su biyu masu matsakai cin shekaru, suka durkusa har kasa suka gaishe ta, duk kunyar su ta kamata haka dai ta daure sukayi mata bayanin kansu sannan suka ce idan tana bukatar su, suna bq kiran su kawai zatayi. Godiya sukayi mata sannan suka wuce bq din sai duk taji tausayin su na kamata, irin rayuwar ta da tayi wadda ke cike da rashin yanci da gata. Jiki a sanyaye ta dawo falon ta dauki wayar sai ta lura ashe garin kashe data dazu a flight mood ta saka wayar. Cirewa tayi ta mayar charging tana mikewa zata tashi daga wajen kira ya shigo.
Capital letter R da read heart yayi mata saving number tashi, murmushi tayi ta zare charging ta koma ta haye saman sofa tana daga wayar

“Huhh!” Yaja doguwar ajiyar zuciya ya sauke

“Ina kika shiga? Wayarki switch off gaba daya na kasa nutsuwa a office, kina so AJI ya koroni gida ko?”

Dariya tayi me dan sauti sannan tace

“Bansan na sakata a flight mood ba.”

“Tsabar baki damu dani ba, shikenan shikenan.”

“Allah ba haka bane ba.”

“Toh menene?”

“Ba komai.”

“Me kike yi yanzu?”

“Lunch zan hada mana.”

“Ok, kiyi mana kadan wajen 3 zanzo mu fita, ki shirya kafin na dawo.”

“Ok, sai ka dawo.”

“I love you.”

Yace sai tayi shiru tana jin nauyin kalmar a bakin ta, dan jim yayi yana jiran yaji ko zata fada masa amma ta kasa, sai yayi murmushi kawai ya katse wayar. Akwai sauran time yasan, zai bi komai tunda ba rushing ake ba, nan da lokaci kadan zai gama cikata da zazzafar kaunar sa, yadda zata kasa jurewa kamar yadda yake kasawa.

***Da safen wuri Mummy ta koma dakin Asim ta bubbuga, yana kwance zazzabi ya rufe shi ruf ko sallar asubah be tashi yayi ba, dakin a bude yake ya bude shi cikin dare da yaji yana neman tafiya barzahu, ya rasa dalilin da yasa kasan zuciyar sa har yanzu baya jin zafin Rafeeq kwata kwata, idan ya zurfafa tunani sai yaji yana so ya ji ta bakin sa, kila zai fi gamsuwa idan yaji komai daga bakin sa. Da gudu tayi kan gadon tana kiran sunan sa, ta yaye abinda ya rufa tana kwala kiran sunan sa. Idanun sa da suka kada sukayi jajur ya zuba mata, a tsorace ta kalle shi tana fashewa da kuka

“Tashi dan Allah, menene haka Asim? Kana da hankali kuwa? Tashi ba zan iya jiran Dr yazo ba, asibiti zamu.”

Bashi da karfin musa mata dan yayi weak sosai, tun da ya dawo yaci wannan abincin be sake cin komai a cikin sa ba sai ruwa kawai, shiyasa yayi masifar galabaita karshe yayi collapsing ko tsaiwa kwakwara ba zai iya ba. Fita tayi ta samo masu taimaka mata suka zo suka sakashi a mota, bata gayawa AJI ba kawai tace su wuce asibiti. Duk abinda suke yi AJIn na kallon su, yana tsaye jikin curtains din sashen sa har suka fice daga gidan. Sai da ya shirya da gama komai sannan ya kira Rafeeq yace ya biyo ta gida yazo tare zasu fita, ba’a dau lokaci ba yazo suka fita, ya kira driver da ya tafi kaisu asibitin ya fada masa in a suke, sa a sannan ya gayawa Rafeeq din abinda yake faruwa. Sosai hankalin sa ya tashi, ya damu sosai har suka isa asibitin baya cikin nutsuwar sa, suna zuwa suka tarar da mummy a VIP parlour taci kuka ta koshi dadin ta, ita kadai ce babu kowa dama wajen na ire iren su ne. Tana ganin Rafeeq ta taso da sauri ta tare shi tana riko hannun sa

“Dan girman Allah ka ceci rayuwar dan uwanka, wallahi yana cikin matsanancin hali dan Allah ka bar masa yarinyar nan ya aura, dan Allah.”

Wata irin tsawa da Daddy ya buga sai da duk suka tsorata, ya nuna ta da hannu yace

“Ashe mahaukaciya ce ke Saratu ban sani ba? A wanne garin mahaukatan kika taba jin anyi haka?”

“Sai a fara yanzu, Asim shi yake son yarinyar nan na Rafeeq ba.”

“Auw Allah ko? Sai yanzu kika san haka?”

“Muje wajen likitan, kazo ka wuce office ka dawo. Ke kuma zamu hadu a gida ne.”

Suka wuce suka barta a tsaye. Wajen Dr din suka je, yayi musu bayanin ulcer ce ta kama shi lokaci daya saboda rashin cin abincin da be yi ba kwana da yawa, shi yasa ya galabaita amma da zarar ya gama shan drip din da suka saka masa zai dawo daidai. Godiya sukayi masa suka fito AJI yace wa Rafeeq ya wuce office ya dawo anjima ba musu ya juya ya tafi shi kuma AJIn ya koma ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button