Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 4

Sponsored Links

*YANCI DA RAYUWA*

©️®️HAFSAT RANO

Page 4

Related Articles

 

****Tana tsaye a kitchen din tana jiran a kira ta jikin ta sai tsuma yake sai ga Ben ya shigo.

“Let’s go.”

Yace yana yin gaba tabi bayan sa da sauri. Karo na biyu kenan da ta taka hamshakin falon gidan, ranar zuwan da na farko da Hajiya Maryam ta kawo ta, sai kuma yau da ta nemi izinin ganin matar gidan. Falon farko suka wuce zuwa na biyu, sannan ya tura wata kofa suka shiga wani dogon hallway zuwa wani part din me dauke da madaidaici living room. Kamshi da sanyi ne suka buge ta, ta lumshe idon ta a hankali sannan ta bude su jin alamun magana kasa kasa. A chan kujerar karshe ta hangi Hajiyar hakimce tana amsa waya sai yan aiki biyu daya tana matsa mata kafafunta dayar kuma tana tsaye alamun jira take ta gama wayar.

Durkusawa tayi kasa da sauri, kanta a matukar kasa sosai tana jin faduwar gabanta na karuwa.

“Menene ma sunan ki?”

Da sauri tace

“Noor.”

“Me kike so kike nema na?”

“Am dama, dama dan Allah so nake naje na duba jikin babana gone.”

“Aikin ki fa? Kinsan dai yadda tsarin gidan yake.”

“Zanyi na gama komai da wuri, sai naje tsakanin azahar zuwa la’asar kafin lokacin shiga aikin.”

“Kinsan muhimmancin aikin da kike yi kuwa? Kinsan wanne kalar gida kike aiki kuwa ko har yanzu baki fahimta ba? Kinsan mutane nawa na sallama akan sakaci da aikin su? Ba haka muke anan ba, aikin ki aiki ne me hatsarin gaske, I can’t risk my family life saboda wani personal issue naki.”

“Mumm… please ki barta taje.” Yace yana karasowa ciki tun da suka fara maganar yana tsaye yana jin su

“Why? Kasan me zataje tayi.”

“Babu komai, zaki iya sakawa a rakata idan ma kina doubting ne.”

“Asim… Baka san rayuwar nan ba, you can trust just anyone.”

“Na sani Mum, but itama tana da YANCIN ganin family dinta. Please don’t deny her the right to see her family.”

“YANCI? Har akwai wani yanci a rayuwar talaka ne?” Sai tasa dariya

“Babu wani YANCI da take dashi, rayuwar talaka gaba dayan ta har nawa ce da za’a din ga kira mata YANCI.”

Shiru yayi ransa na soma baci, wannan shine akidar iyayen su, wannan bakar akidar ce tasa Rafeeq baya shiri da mahaifin su sam, basu dauki mutum talaka a bakin komai ba. Baya tare dasu akan wannan akidar tasu, kuma zai yi iya yinsa wajen ganin ya chanja musu ita.

“Tashi ki bamu waje.”

Tace tana jan tsaki. Mikewa tayi da sauri bayan tayi godiya tana rike hawayen dake kokarin sakko mata, ta fice da sauri. Da kallo ya bi ta ransa babu dadi. An kuntace ta an hana ta ko wanne motsi, tun daga kan shigar da take yi a gidan zaka san tabbas akwai tauye hakkin dan Adam, taya za’a ce dole dole sai ta saka nikaf a cikin gida hadda safa? Bayan dole akwai takura akwai zafi. Tashi yayi ya fice kawai ta bishi da kallo sannan tayi kwafa tana jin haushi da tsanar yarinyar na gaske. Ba dan dai tana musu abinda suke so ba da babu abinda zai hana bata koreta ba, kyawunta da ta fara gani yayi matukar firgitata, tana tsoron a samu matsalar har ta zame mata matsala shiyasa ta kafa mata wannan dokar ta kuma hanata muamula da kowa a gidan ta kaita chan baya ta rufe ta yadda babu wata alaka da zata taba hadata da kowa tayi aikin ta kawai shikenan.

***Duk yadda taso ta hana kanta kuka sai da tayi, kuka sosai irin wanda bata taba yi ba a tsawon rayuwar ta. Tabbas talauci masifa ne, idan suna da kudi babu abinda zai sakata aiki, aiki ma irin wannan na kaskanci. Da kyar ta lallashi kanta ta wanko fuskarta sannan ta fito ta nufi kitchen din.
Sukuku tayi komai jikin ta duk babu kwari ta gama sannan ta jira Ben ya zo tayi tasting sannan ta dauki nata ta fito, sai ga yarinyar da ta gani tana ma Hajiya massage a tsaye tana jiran ta. Hannun ta, taja suka yi baya zuwa wajen da babu CCTV a wajen sannan ta kalle ta cikin tausayawa tace

“Yanzu Hajiya ta fita unguwa kuma zata kai dare kafin ta dawo dan taro ne dasu da matar shuganan kasa kiyi sauri kije ki dawo.”

“Nagode nagode sosai. Bari na je na sauya kayan jikina sai naje, wallahi so nake kawai na ganshi bashi da lafiya.”

“Kiyi sauri, karbi wannan ki hau mota idan zaki dawo yadda zaki fi saurin dawowa kinsan 7 ake rufe kofar bayan nan.”

“Nagode sosai.” Ta karba ta juya da sauri zuwa dakin ta, ta chanja kayan jikin ta a gurguje ta fito, tabi gate din bayan ta fice bayan ta gaisa da me gadin wajen.
Sai da ta fara trecking sosai kafin ta samu taxi ta dauke ta sai gida. Tsoro ne fal zuciyar ta da dokin ganin mahaifin nata har suka karasa ta sauka ta gangara tana ta sauri.
Baban na zaune a tsakar gidan nasu me dauke da dakuna hudu na mabanbantan mutane da suke haya a gidan nasu suke biyan kudin da yake rike su da kafin kaddara tasa kowa ya gudu har ya zama an rasa wanda zai kama dakunan bare su samu su rage wanda yayi musababin fara aikin ta a gidan kenan.
Sallama tayi ya amsa cike da farin cikin ganin tilon yar tasa da yake tunani a lokacin.

“Noorun Baba.” Yace fara’ar sa na fadada sosai.

“Baba na.” Sai ta rungume shi tana fashewa da kuka

“Kinji ki ko? Kuka kika zo yi min kenan?”

“A ah baba, nayi kewar ka ne.” Tace tana share hawayen da bayan hannun ta.

“Nima haka yar albarka, yanzu ma tunanin ki nake sai gaki, Allah dai yasa kalou.”

“So nake kawai na ganka Baba.”

“Babu wata matsala ko? Basa takura miki ko tsangwamar ki dai ko?”

“Basa yi baba, suna da kirki.”

“Um um ki fadan gaskia, idan dai suna miki a hakura kawai, da aikin Allah zai kawo mana mafita.”

“Lafiya kalou Baba, yanzu ma ba dadewa zan ba, ganin ka kawai nazo nayi na koma. Saura paper daya na gama jarrabawa ta.”

“Masha Allah, Masha Allah. Allah ya bada saa yasa ki fito da sakamako me kyau.”

“In sha Allahu Baba, sai na cika buri na, yadda zan dawo na cigaba da kula da kai.”

“Karki damu kinji diyata, shiga daki ki dauko abinci kizo kici kafin ki tafi, dazu ne aka Aiko min shi daga gidan hamza, kinsan inason abincin kanawa shinkafa da wake, nasan kuma kema kinaso.”

“Inaso kuwa, Allah yasa da salad da cucumber.”

“Hadda kifi ma. Maza dauko kizo.”

Da sauri ta shiga dakin, ta fara daukar wasu kayanta sannan ta dauko flask din tazo ta zauna a kusa dashi taci sosai dan dama bata ci abincin ta dazu ba ta baro shi a daki. Tana gamawa ta share gidan da dakin baban tas sannan ta cika masa ruwa a buckets dinsa da buta sannan tayi masa sallama. Ba damar ya rakata saboda kafar sa ya bita da addua ta fito tana share hawaye. Sai a sannan ta tuna da satar hanyar da tayi ta hau sauri ta karasa titi ta samu taxi ta hau tana ta addua duk da har lokacin baa kira magriba ba amma dai tana tsoron kar bakwan tayi mata bata koma ba.
Cikin ikon Allah har ta koma ta shiga dakin ta, bata hadu da kowa ba, ajiyar zuciya ta sauke ta cire kayan ta saka na zaman daki, ta dauko books dinta ta bude tana dubawa a hankali.

***Monday ta tashi da wuri duk da exams din tata sai 11 ta shirya tayi dukkan ayyukan ta zuwa 8 ta kammala sai kawai ta dauki jakarta dan tafi so taje school din da wuri ta kara duba books din nata kafin time din shiga exams din.
Yau ma ya fito yana tsakanin hanyoyin biyu da in da ya ganta last yana danna wayar sa a hankali yana kallon hanyar time to time. Kamar an ce ya daga kansa sai gata ta taho kanta a kasa tana kallon gabanta, yanayin tafiyar ta yau kamar ba sauri take ba, iska ya ja ya furzar yana jin wani irin farin ciki na mamaye shi. Sai da tazo daf dashi sannan ta lura dashi. Da sauri ta russuna ta gaishe shi hakan ya bashi mamaki matuka, danne mamakin sa yayi ganin har lokacin tana durkushe tana jiran ya amsa gaisuwar.

“Tashi please.” Yace da sauri yana kai hannun sa kamar zai daga ta. Da sauri ta mike ta kalle shi kadan sai kuma tayi kasa da kanta tana jiran ya bata izinin tafiya.

“School zaki?”

“Eh.”

“Ok muje na rakaki.”

Wani kululu cikin ta yayi saboda tsabar yadda maganar tasa tazo mata.

_”Muje na rakaki, Ina? Ya gane ta ma kuwa?”_

“Na’am?” Tace

“Yes, ko bakya so?”

“Amm….dama… Amm ka barshi kawai.”

Sai tayi gaba zata wuce shi, tare gabanta yayi yana kokarin saka idon shi cikin nata, tayi saurin janyewa tana sauke kanta kasa kirjinta na bugawa sosai.

“Please ki bari na rakaki.” Shiru tayi dan bata kuma san me zata ce ba, gaba daya nutsuwar ta, ta bar jikinta har wani rawa kafarta take yi kamar mazari.

Jerawa sukayi suna tafiya yana satar kallon ta. Tafiya sosai suka mika gashi dogon polo wando ne jikinsa da armless shirt dan ya zata ba nisa zatayi ba.

“Ina ne school din?” Ya tambaya ganin sun karaso main road din.

“Da nisa.”

“A kafa kike zuwa?”

“A ah zan hau taxi idan nayi gaba.”

 

“Nooo… Wait, bani address din.”

Fada masa tayi, ya dauki wayarsa ya shiga Uber yayi searching nearby driver, in less than two minute ya karaso wajen, da kansa ya bude mata kofar ta shiga sannan shima ya shiga suka soma tafiya. Gefen window kawai take kallo tunda suka shiga wani yanayi da ta kasa gane irin sa yana shigarta. Tsoro da firgice da rashin gane komai yasa taji kamar bata da lafiya, kamar zazzabi na neman rufe ta. Gajiya yayi da shirun sake wanzuwa a tsakanin su, ya katse shi ta hanyar jefo mata tambaya

“A wanne gidan kike? Bani house number din.”

“Na’am?”

“Yes, inaso nazo..ko kar nazo?”

Kallon sa tayi ya daga mata kai alamar eh, mamaki ya kamata ta, tabbas be gane ta ba. Toh amma dama ta yaya zai gane ta, tunda kullum fuskarta a rufe take kuma ba wani mugun sani yayi mata ba, lallai akwai babbar matsala idan ta bari ya gano in da take, ba zata taba bari hakan ta faru ba, dan ta tabbatar daga ranar zaman ta a gidan ya kare, hakan kuma yana nufin karshen mahaifin ta da itama kanta.

#Thelovetriangle💓🥰

 

🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
08030811300

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button