Yanci da Rayuwa 8
*YANCI DA RAYUWA*
Arewabook; Hafsatrano
Page 8
****Sanda ya isa office din duk sun iso, suna zazzaune kowa yana duba abubuwan da za’a tattauna a meeting din, yana shiga duk suka mike suka hau gaisawa kafin ya zauna a kujerar da aka ware masa. Yana zama Asim ya shigo, suka kalli juna sukayi ma juna murmushi kafin Asim ya zauna a kujerar dake daura dashi. Cikin matukar kwarewa da sanin kasuwanci ya shiga yi musu bayani cikin tsadadden turancin sa me matukar kayatarwa. Ba yau ya fara zama a irin wannan meeting din ba, ya hadu da mutane manyan gaske mabanbanta a rayuwar sa da yayi a Greece na wata uku haka ma UAE da kuma zaman Scotland da yayi. Sai da ya gama bayanin sa tas sannan Asim ya karba shima ya gabatar da nasa part din kafin a bawa sauran suma kowa ya kawo idea dinsa akan zaman nasu. Wajen sha biyu da yan mintuna suka fito daga meeting din a jere da juna Asim na mayar masa da bayanin wasu abubuwan da suka faru da bayanan yana ji yana sauraron sa har suka dangana da sabon office din Rafeeq din da akayi matukar kawata shi, daga saman kofar dauke da tambarin chairman. Asim ne ya bude masa kofar sannan ya matsa baya ya shiga sannan yabi bayan sa. Murmushi ne kwance a fuskar sa, tabbas Asim ya gama sanin waye shi, da taste dinsa a abubuwa, komai an yi shi ne standard sannan komai na office din brand ne masu tsadar gaske kuma.
“Kayi kokari sosai.” Yace yana zama a kujerar sa dake dauke da table da kujeru biyu a gefe.
“Really? Hope komai yayi maka.”
“Perfect, komai yayi daidai. Kasan ina son condusive environment and komai yayi sosai.”
“I’m glad.”
“Yanzu menene zamu fara dashi?”
Hannu yasa ya zaro flash ya mika masa sannan yace
“Check this out!”
Sai ya juya ya fice gami da jawo masa kofar yana jin dadin dawowar sa. Tura kujerar yayi baya, ya mike ya shiga takawa a cikin office din yana jin duk babu dadi. Tunanin abinda ya faru dazu ne ya shiga dawo masa, tausayi da wani irin zazzafar kaunar ta na huda shi. A yanzu idan yana da bukatar shigar da kansa wajenta zai iya, sai dai yana tunanin akwai right time din yin hakan, musamman idan ya tuna babban kalubalen dake gabansa sai yaji duk ya sare, baya so tarihi ya maimaita kansa dan haka ne ma zai bi komai a sannu har ya samu abinda yake so din ba tare da ya batawa kowa ba.
Dawowa yayi ya zauna a kujerar da ya tashin, ya makala flash drive din jikin system din sannan yayi baya kadan yana kallon screen din har komai ya bayyana. Briefing din abinda ya faru a meeting din ne sai kuma wasu papers na abubuwan da company yake bukata da bayanan komai a tsare daki -daki. Ya dan dau lokaci yana duba ayyukan da Asim din ya jagoranta kuma ya yaba sosai da kokari da kwazon sa wajen yin aiki me kyau, hakan ya kara masa karfin guiwar tunkarar aikin dake gabansa din.
Ringing wayar dake kusa dashi tayi, sai a lokacin ya lura da ita a ajiye a gefe, hannu yasa ya dauka ya kara a kunnen sa a nutse yace
“Hello…”
“Sir, it’s your manager. Kana da visitors.”
“Let them in.”
Yace ya ajiye wayar cikin tunanin su waye visitors din. Turo kofar akayi ya bi kofar da kallo kafin ta bayyana a gaban sa cikin matukar addua da kawa. Dauke kansa yayi daga kallon kofar ya maida hankalin sa bisa system din kamar be ga wadda ta shigo din ba. Takun dogon takalmin ta da yaji ya matso shi ya gane ta karaso ciki sosai, sake daga kansa yayi ya kalleta yana gimtse fuska.
“Me ya kawo ki?”
“Haka ake karbar baki feeqq?”
Be amsa ba, sai ya mike ya dauki wayar sa ya nufi hanyar fita daga office din.
“I can wait.”
Tace tana murmushi sannan ta zauna a kujerar dake kusa da ita tana karewa office din kallo tana murmushi kamar bata ji komai ba.
Yana fitowa da sauri Manager ta mike tsaye cikin girmamawa tace
“Kana bukatar wani abu ne sir?”
“Ki fito da matar nan daga office dina and lock it up.”
“Ok Sir.”
“Karki sake barin ta ko tazo daga yau.”
“An gama Sir.”
Tace ya wuce kansa tsaye ya fice daga building din gaba daya. Ba zai iya zaman minti daya inuwa daya da ita ba, ta sani kuma sarai dan ta bata masa rai ne wanda tayi nasarar hakan. Yasan Aneesa ce ta fada mata maganar dawowar sa, shiyasa ta dauko kafa tazo ta bata masa rai.
Tana zaune tana duba wata paper da ya tashi ya bari tana murmushi kamshin ta ya cika office din gaba daya Mary ta shigo. Tana ganin ta shigo tasan abinda tazo yi, murmushin ta sake yi tana mikewa tsaye sannan tace
“Yace kizo ki fito dani ko?”
“Yes ma.”
“Kuma yace karki sake bari na na shigo masa office ko?”
“Yes..” murmushi ta sakeyi yanzu da dan sauti sannan tace
“Na sani, nasan abinda zai yi kenan. He just can’t face me shine kawai. Anyways ba sai kin sha wahala ba, I’m leaving.”
Ta wuce ta cikin takun ta, ta fice tana dariya kasa kasa. Sam Rafeeq be san abinda zata iya ba, amma tunda ya dawo zasu zuba, kuma zatayi nasara.
Motocin sa da ta gani a harabar wajen ta gane be fita ba, yana cikin building din. Mota ta fada kawai driver ta yaja suka bar wajen dan ta riga tayi abinda ya kawo ta.
Har la’asar suna office din, sai da sukayi sallah sannan suka tafi gida tare shi da Asim. Suna tafe suna hirar abinda ya faru a office din ranar da abubuwan da suke ganin zasuyi achieving idan har suka hada kai sukayi aikin tare. Dukkan bayanin Asim ne yakeyi Rafeeq na jinsa ya tafi wata duniya ta daban, tunani daya ne yake nukurkusar zuciyar ya hana masa sukuni. Kyakkyawr fuskar ta da ya gani a dazun cikin wani yanayi da yake iya hanga kwance akan fuskarta ya sake sakashi cikin matukar damuwa.
“Kana ji kuwa?” Asim yace ganin kamar attention dinsa na wani wajen ba abinda yake fada masa din ba. Shafa gaban kansa yayi yana dagawa Asim din kai kafin yace
“Na gaji ne Asim, ma karasa mahanar anjima.”
“Ok.” Yace sai yayi shiru kawai shima yana juya wayar sa yana tunanin dalilin da yasa wayar take a kashe tun sanda ya kira. Ya damu ainun kawai yana dannewa ne baya son abun yayi tasiri a kansa amma tabbas yana so ya ganta ya tambaye ta dalilin ta na kin amsa wayar sa bayan ita tayi masa alkawari. Rashin sanin in da zai sameta ne ya katse masa dukkan wani hanzari, ji yake kamar yabi Street din nasu gaba daya house by house yana yambayar ta ko zai dace ya samu saukin tunanin dake addabar sa. Ganin yayi shiru yasa Rafeeq jin ko be kyauta ba da yace su bar maganar da suke yi, yasan Asim in dai har suna tare baya rabo da bashi labarai da duk abubuwa da suka faru baya nan. Shirun nasa yanzu sai yake jin kamar ba kalou ba, kamar yana da damuwa dan yanayin fuskar sa ta nuna gaba daya.
“Ya labarin new girlfriend dinka daka ce min kayi?” Ya sako masa tambayar dan yayi gingering nasa aikuwa kamar me jiran kiris yace
“I’m just thinking about her wallahi, ta bani number ta na kira no answer karshe kuma naji switch off, shikenan har yau switch off bata shiga, na damu sosai.”
“Oh wow!”
“Serious fa, ban taba jin na damu sosai haka ba.”
“Ko dai aljana ce?” Ya tsokane shi yana dariya kasa kasa.
“It’s obvious fa, dan ban taba ganin irin ta a garin nan ba.”
“I’m just kidding, kila jan aji zata maka taga ka damu.”
“Ta taimaka min, wallahi da gaske nake.”
“iKon Allah.”
Rafeeq yace yana dariya. Shi dariya ma abun yake bashi yadda ya hakikance.
“Laila tazo office dazu.”
Da sauri Asim ya kalle shi, ya tabbatar da gaske yake sai yace
“Waya fada mata ka dawo?”
“Ba zai wuce Aneesa ba.”
“Ohh Neesa, sai fa da nayi mata fada fa last, har ta ke ganin na takura mata. Bari muje gidan.”
“A ah kyale ta kawai, ko bata fada mata ba ma nasan dole zata sani.”
“Toh me ya faru?”
“Fita nayi na bar mata office din, kasan ba zan iya zama waje daya da ita ba.”
“Lallai, bata da kunya ma wallahi, next time ta dawo let me know dan Allah, tana taking advantage na shirun da kake mata ne, I will teach her a lesson.”
“Ka fiya rigima.”
“Abun nasu ne, gwara a taka masa burki itama munafuka Aneesa zan hadu da ita ne.”
“Noo please, kyale ta.”
“Shikenan.”
Maganar da sukayi yasa Asim din sake sakewa suka cigaaba da hirar har suka iso gida. Tare suka fito suka nufi cikin gidan wanda saboda Asim din ne yasa Rafeeq farawa ta cikin gidan amma da part dinsu kawai zai wuce daga baya ya shigo idan ya huta. Mum na zaune ita da Aneesa da Ummita ita tana waya su kuma suna hirar Instagram yan mazan suka shigo. Kamar wanda aka aiko ma da sakon mutuwa haka annurin fuskar Asim ta dauke ganin Ummita a zaune a falon. Katse wayar Mum tayi tana kallon su har suka shigo ciki. Gaisheta sukayi ta amsa tana tambayar office Asim be jira ba ya wuce ciki yana sake bata fuskar sa dan kar ma Mum ta tsaida shi gaban mara kunyar yarinyar nan.
“Shi kuma wannan me ya same shi?” Tace tana bin sa da kallo har ya fice daga part din
“Kansa ke masa ciwo ne kadan.”
“Ummita tashi kiji clinic ki samo masa maganin, ki hada masa da lunch dinsa ki kai masa part dinsu.”
“No yasha magani ai, hutu kawai yake bukata so a kyale shi idan ya huta zai dawo daidai.”
Kallon sa Mummy tayi cikin rashin gamsuwa tace
“Oh ok.”
Da sassafa ya wuce ciki shima dan baya son ya cigaaba da zama a wajen. Yana kallon Aneesa na boye fuskarta da ta ganshi ya san itace ta fadawa Laila ya dawo murmushi kawai yayi kadan dan ba abinda zai ce mata akan maganar.
A saman sofa ya samu Asim ya cire rigar sa daga shi sai dogon wando yayi daidai yana ta kumbure kumbure.
“Kaga mum ko?”
“Shine sai ka tafi ka barni nayi maka cover, nace kanka ke ciwo ga Ummitan nan zata zo ta kula da kai. Da sauri ya mike zaune yana ware idon sa waje
“Are you serious?”
Yace yana lalubar rigar sa da ya wurgar da nufin yasa ya bar musu gidan gaba daya.
“Wasa nake.”
Ajiye rigar yayi yana murmushi ya sake komawa ya kwanta ya sa hannu ya jawo wayar sa ya sake gwada kiran ta.
Gama wayar su kenan da babanta sai ta manta bata kashe ba kawai sai ga kiran ya shigo. Kallon number tayi gabanta na faduwa, da ta san zai kira da bata bar wayar a kunne ba.
Zaune ya tashi da sauri jin wayar na ringing, ya bada dukkan attention dinsa a hankali yace
“Please please please.”
Juyawa Rafeeq yayi ya kalle shi da alamun tambaya, nuna masa wayar yayi a hankali yace
“Tana ringing.”
Girgiza kai kawai Rafeeq yayi ya cigaba da abinda yake yi. Kamar ba zata dauka ba, tana ta tunani da wasi wasi tsoro fal zuciyar ta, sai kawai ta daga ta dan karata a gefen kunnen ta kamar wadda take tsoron shocking tace
“Hello…”
Tana Jin sanda ya sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan yace
“Sai na ci tarar ki na azabtar da zuciya ta da kika yi.”
“Kayi hakuri.”
“Nayi, dole na ne ai,wannan daga wayar da kikayi kin wanke kanki, but karki sake please, i can’t take it.”
“Ba zan sake ba.”
“Good, can I see you now? Please karki ce a ah, dawowa na daga office kenan but inaso na ganki. Dan Allah ki bani address din nazo yanzu. Ba zan dau time dinki ba just 5min ya wadatar, please please karki ce a ah. ”
Rasa abinda zatace tayi, gashi ya daure ta gaba daya bata da bakin cewa a ah, gashi ba zata iya bashi house number din ba ko da giyar wake tasha bare, rasa yadda zatayi tayi, sai kawai tace
“Mu hadu a wajen nan.”
“On my way.” Yace yana mikewa tsaye, ya wuce closet dinsa yana jin dadi ya zaro wata shirt ya saka sannan ya chanja wandon sa zuwa sassauka ya fesa turare Rafeeq na zaune yana kallon sa.
“Sai ina?”
“5min zanje na ganta yanzu zan dawo.”
“Ok, nima fita zan, sai kusan magrib zan shigo zamu hadu da AJI.”
“Ok.”
Ya fice da sauri. Yana fita Rafeeq ma ya tashi ya fito dan dama zaman Asim din yake yi. Kofar bayan ya nufa dan yanzu yafi jin dadin fita ta nan ya kira driver sa yace ya dauke shi ta gate din baya. A daidai lokacin Noor ta gama duk adduar da zatayi ta yi deciding taking risk din fita kawai tunda 5min yace hopefully ta dawo ba wanda yayi noticing. Doguwar riga ce a jikinta sai ta dauki Hijab ta dora akai yadda zata fi zama comfortable dan duk yawancin kayan nata zaman daki take dasu sun kama ta sosai musamman yadda jikin ta ya murje sosai tunda ta samu sauyin abinci sai ya zama duk kayan suna kokarin yi mata kadan.
#Thelovetriangle💖
#RafeeqNoor
#AsimNoor
🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥
*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!
Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,
Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶
YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano
AMATULMALEEK
Mamuhgee
Guda biyun 1k
Guda Daya 500
Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
07040727902