Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 35-36

Sponsored Links

35-36*_

 

Daukota yayi kamar wata bby ya fito da ita ya bude jakkar daya dauki mata ya bata doguwar riga ta zura ya zubanta ido kamar mai karantar wani abu sai kuma ya share ya juya ya nuhi waje ya jima ya dawo da magungunan ya dubeta ya debe kayan itadai ko kallon inda yake batayi tanaji ya sake fita da kayan ya dawo yace “zamu iya tafiya gda Allurai ne guda 12 zaayi miki daya kullum har zuwa lkcn da zaki warke”
Zaro ido tayi cikin firgici zatayi mgn ya fice yana cewa “ki fito ina jiranki” dole haka taja jiki ta fito ya budenta motar ta shiga yaja suka tafi, suna tafe yana sauraron wata waqa zahirinsa hankalinsa ba akan waqar yake ba abubuwa ne da yawa cunkushe a ransa yama rasa ta inane zai fara, wani guri ya biya ya tsaya ya fita ya siyo musu gasasshen nama ya dawo yaja motar suka tafi lkcn da suka isa gda 11:30pm yana budewa ta shige dakin.

Related Articles

Dakinta ta barshi tsaye yana binta da kallo jin da yayi ta mayar da qofar ta danna mata key yasashi jan fasali ya nufi kitchen ya bude freegde ya sanya mata kayan daya siyo a ciki ya nufi saman ya bude dakinsa da tsayin watanni bakwai din da tayi matsayin matarsa bai taba shigansa ba, mamaki ya cikashi ganin komai dake dakin tsaf kamar dama ana amfani dashi ya bude bayin shima ya ganshi tsaf dashi yaja numfashi yace “kowa da irin baiwarsa” komawa yayi ya zauna hakanan yaji yana sha’awar kwana a part din ya jima a zaune sannan ya tashi ya shigo bathroom din ya watso ruwa ya fito ya bude wardrobe din ya dauki sabon towel ya  budeshi a leda ya goge jikinsa.

 

Ya koma ya kwanta yanata tunanin ta inda zai farawa Asmah tabbas lkc yayi daya kamata ya fara neman haqqinsa na aure a gurinta itama kamar ko wacce mace zuwa yanzun idan yaci gaba da kawar mata dakai to cutuwa zai farayi, miqewa yayi kamar wanda aka tsikara ya bude qofar dakin nasa ya fito parlor harya kama handle din qofar zai murda sai kuma zuciyarsa ta fara ayyana masa yanzu kamar shi yaje yace zai nemi wani abu gurin wannan yarinyar yar rainin sense ai kawai gara ya bari ya samawa kansa wata hanyar.
Aminta yayi da shawarar zuciyarsa ya koma dakin nasa ya kwanta yanata matse matsen cinya feelings na damunsa amma girman kansa na bala’i ya hanashi samawa kansa maslaha, washegari tun asuba daya fita bai dawo part dinba to itama dake ba daidai takeba bata fitoba balle tasan meye yake faruwa a daddafe tayi sallah ta sake narkewa a gado tanajin yanayin zazzabin yana sake sauko mata.

 

Wajen 8:30am ya shigo cikin shirinsa na tafiya office ya bude dakin ya shiga ya isketa kwance kamar ruwa ya qarasa ya janye mata blanket din ya  zubanta ido gabadaya hankalinsa yana kan qirjinta baiyi tunanin idanunta biyu ba saida yaga ta bude idonta ya sosa qeya da yanayi na borin kunya yace “kinsha magungunan?” Lumshe idonta tayi ya juya ya fita ya hado mata tea ya dauko mata tarkacen daya siyo mata jiya duka babu wanda ta taba ya dawo ya taimaka mata ta tashi zanne ya rinqa bata a baki tanaci a hankali tana hawaye gabadaya sai yaji tausayinta ya qara mamaye zucciyarsa magunginan ya ballo ya bata tasha ya gyaranta kwanciya yace “zan sake sanya miki drip idan ya qare ki cire sannan kada ki zauna da yunwa kinji” dagowa tayi idanunta ya shiga cikin nasa yayi ajiyar zuciya shi kansa yanayin da yayi mata mgn dashi ya sanyashi jin wani yanayi na daban.
Juyawa yayi ya fita ya dauko drip din ya dawo ya sanya mata yanata zuba mata sannu ya fice tananan kwance bacci har ya fara daukarta taji an shigo part din nata saida gabanta ya fadi tayi tunanin Hajja ce aka bude qofar aka shigo ta sauke ajiyar zucciya ganin Jiddarh ce zama tayi kusa da ita tace “na shiga school najiki shiru inata kiran wayarki baa dauka ba qarshe wannan miskilin mijin naki ya daga yacemin bakida lfy shine hankalina yaqi kwanciya nace bari nazo naga jikin naki” lumshe idonta tayi batasan sanda hawaye ya zubonta ba tace “ina Innata kwana biyu idan na kira wayarta bata shiga” kallonta Jiddarh tayi tace “wai kina nufin baki sani ba ai bama ta qasar tana Saudia zaayi mata aikin ido” zaro ido asmah tayi ta yunqura zata miqe Jidda ta taimaka mata ta zauna tace “waye ya biya mata?” Harararta tayi tace “kinji ki toda wa kike tunani bayan mijinki”

 

Hawaye ne ya zubonta tace “shiyasa kullum yake qara samun damar cimin mutunci duk mgnr da tazo bakinsa ya fadamin uwarsa ma ta fadamin Jiddarh meye yasa Innah itama takeson zama irin Mal ne basa tunanin mutunci na da qimata a gdan aure kawai biyan buqatarsu suke dabbaqawa nikam wannan rayuwar bansonta zanso ace sun hqr da talaucinsu don mutumcinsu da qimata Jiddarh yaushe ne don Allah rana zatazo? Yaushe ne nima zanyi farin ciki a gdan mijina Jiddarh yaushe zan zama cikakkiyar mace me yancin zama da mijinta tayi hira tayi dariya suyi nishadi su bawa juna farin cikine, wlh a baya bana damuwa duk da cewar nasan cewa abin zai dameni wataran amma banyi tunanin zuwanshi a wannan lkcn ba Jiddarh babu irin kirsar da banayi domin na samu kan mijina amma na kasa samu harma takai na hqr na qyaleshi amma duk da haka bana tsira daga rashin albarkarsa na gaji Jiddarh na gaji gara na kauce na samu salama shima ya samu……..”

 

Shigowar da sukaji anyi dakin ne yasasu dagowa suka kai dubansu inda ake shigowar Hajja ce take shigowa ita da wata mata gaban Asmah ya fadi taja hijjab da sauri tana shirin sanyawa tajita a baje a qasa bata gama tantance meye yake faruwa ba taji an rufeta da duka kamar saqon Allah aikuwa tuni ta fice daga hayyacinta Jiddarh ce tayi kukan kura ta angaje Hajja tace “kutmar Ubancan wannan wanne irin rashin mutunci ne ubanme tayi miki…?” Daidai lkcn Aseem ya shigo da mugun gudu ya hawo saman dan ko motarsa bai kashe ba saboda yanda Aunty Aseemah ta kirashi ta sanar dashi cewa Hajja zata kashe yar mutane Mimee ta shirya mata qarya da gaskiya”
Lkcn daya shiga ya tarar da Hajja tana zabura zata qara dukan Asmah Aunty Aseema da Jiddarh sun kakkare asmah dake kwance a qasa kamar gawa da gudu ya qarasa ya turesu ya dago Asmah da bakinta kanta da hancinta ke fitar da jini ya fara jijjigata fadi yake “Asma’uh! Asma’uh!! Ke Asma’uh Innanillahi wa inna ilaihirraji’un Hajjah kin kasheta meye wai Asma’uh ta tare muku ne kukeson ganin bayanta…..” Miqewa yayi ya dorata a gado ya haura gadon da sauri da ruwa a hannunsa ya balle bottle din ya rinqa kwara mata yana kiran sunanta yana danna qirjinta a hargitse yana cewa “don Allah ki rufamin asiri kada ki mutu wlh bansan hakan zata faru ba da bazan fita ba” sake miqewa yayi ya fara zagaya dakin Aunty Aseema da Nasmah qanwarsa suna tsaye suna kallonsa itakam Hajjah murmushi tayi ta dubesa tace “badai ni zakaciwa mutumci ba na dauki yar aminiyata na baka kai kasan Maryam ba tsarar aurenka bace amma kayi mata wannan sakayyar da danyen jikinta kai kazama dan zaki ayu sarkin jaraba bazaka zauna kayi jinyarta ba ka taho gurin wannan shegiyar yarinya to wlh tallahi yau indai ni Zainab na haifeka saika saki wannan tsinannar yarinyar kafin ta qarasa shanyemin kai ka fara dukana akanta……”

 

Dago jajayen idanunsa yayi da suka qanqance maqwallatonsa sai motsi yakeyi abinka da farin mutum gabadaya jijiyoyinsa sun wani mimmiqe yayi mata wani mugun kallo da yasanya gabanta faduwa ya juya zai sunkuci matarsa tasha gabansa ya sake matsawa ta sake shan gabansa tace “bakaji abinda na fada maka bane Aseem ko sai naci ubanka……
Haurawa gadon yayi ya sunkuci asmah ya nufi qofa ta riqe rigarsa ya juyo yana qara rungume Asmah a qirjinsa yace “Ina sauke miki duk wani haqqinki na uwa dake kaina babu wanda na gaza so kema ki daina shiga lamarin gdana idan ba hakaba zan bawa duniya mamaki akan wannan yarinyar wlh zan iya batawa da kowa babu abinda ya shafeni domin banga abinda ta tare muku ba iyakar rigimar Asma’uh danine ko Maryam qarya take tace Asma’uh tayi mata wani abu Hajja kina yawan furtamin saina saki asmah na rantse da girman Allah idan kika matsamin zanyi miki biyayya zanyi abinda kikeso amma kisani bazata tafi ita kadai ba dole saida yar rakiya itama Maryam din zan yanka mata ticket inyaaso saiki bata guri a gdanki………..”

 

_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_

_*Oum Hairan*_

[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

*ELEGANT ONLINE WTITERS*

_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button