Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 37-38

Sponsored Links

37-38*_

Yana gama fadin haka bai jira cewar Hajjah ba ya fice da sauri ya nufi motarsa da Asmah yasata yana shirin shiga Jiddarh ta fito ita da Aunty Aseemah suka shiga yaja a guje suka fice Hajjah da Hajiya Kubura sai kallon kallo Nasmah ta tabe baki tace “ai dama tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka natsani mace me yawan kai qarar miji wlh yanzu me gari ya waya Allah da nice Bro Saina tarwatsa nutsuwar duk wanda ya tarwatsa tawa haba Hajja duba fa yanda kika illata yar mutane yanzu baki tsoron ta mutu?”
Tabe baki Hajjah tayi tace “shine me idan ta mutun aidai an rage mugun iri a bayan qasa irin jaraba irin maita sun qalace sun nace sun lashemin kuryar yarona kuma kuma sun dawo kanku dama kece nake gani me sauqi ashe kema kinbi sahu banzaye lusarai ke kinaga wannan rawar jelar ds yakeyi na banza ne ina ai dole na miqe na shiga sabara don qwato dana daga bakin kura”

Murmushi Nasmah tayi tace “kidai bada himma idan baki shiga ba ke ashigar dake karmami ni nayi nan aure ne dai Allah ya riga ya qullah abinsa kuma shi yaji ya gani ya dauko abarsa don yanaso so kawai ki koma gefe ki zama yar kallo zaihi maki sauqi”  tabe baki Hajja tayi ta cokalo kallabi gaba tace “zaiyi bayani ne shegen yaro saina hanashi sakewa da yarinyar nan ni bazan iya masifa ba” da wannan suka koma part din Mimee suka rinqa yimata famfo abin takaici wai uwa da suruka ne memakon su nema mata zaman lafiya sai tsiyar yanda zata hana abokiyar zamanta da mijinta kwanciyar hankali suke koya mata.
Sukam su Aseem daga gda bai zame ko inaba sai asibiti yayi mata dressing gurin da Hajja ta hadanta kai da wardrobe ya sake sanyanta drip ya nemi guri ya zube yana mayar da numfashi yace OMG Hajjah tana bani ciwon kai akan yarinyar nan wlh” dafashi Aseemah tayi tace “kayi qoqarin daidaita tsakaninka da matarka kaba wofi da tafi banza ajiyarsu idan har kuka samu fahimtar juna da Asmee zaka samu sauqin abubuwa” sosai yasan shawarinta gaske ne so amma tambayar da yake yiwa kansa ta ina zai fara daidaita kansa da asmah bayan tanayi masa kallon wani qaton Azzalumi wanda take addu’ar samun sanadin rabuwa dashi koda ta hanyar katsewar rayuwa ne?” Wata gajiyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace “hakane” kawai ya miqe binsa Jiddarh tayi tace “idan fita zakayi ka saukeni a bakin titi na koma makaranta yau zamu cike takardar practical” tsayawa yayi da mamaki lallai Asmah da gaske gaba takeyi dashi wato da yace idan lkcn practical dinsu yayi ta sanar dashi zai sama mata gurbi a hospital dinsa shine ta watsa zancensa a kwadon shara,

Related Articles

Jinjina kai yayi ya shiga motar Jiddarh ta shiga suka nufi makarantar dake private medicine school ce baisha wahala ba wajen yin duk abinda yayi niyyah aka bashi Asmah da Jiddarh zuwa asibitinsa yaji dadin hakan ya koma gidansa lkcn daya shiga mimee na daki taji shigowarsa amma jin barusar da mahaifiyarsa tayi yasa tayi qus har yayi wankansa ya sake fita bata fito ba
Tun tana jiran dawowarsa harta gaji ta fidda rai ta kwanta tana tunanin inda zatayi da Asmah itafah a tsarinta da yanda take kallon kanta ji takeyi wannan ai qasqanci ne ace mijinta bashi da lkcn ta saina wata banza a gefe to waima yaushe ne tayi saken da har mutane suka rigata gane mijinta yaudararta yayi da dadin baki yakece mata babu abinda zaiyi da wannan yarinyar ashe tuni ma yarinya ta gama da zucciyarsa koda yake sauqin da takeji da akace mayya ce lashe masa kurwar tayi yanzu burinta kawai ta warke ta bazama neman yanda zatayi ta batadda Asmah a cikin rayuwar mijinta.
Tana wannan tunanin wayarta tayi ring ta daga ganin number sace yasa gabanta faduwa ta koma ta zauna gabanta na faduwa har saida wayar ta katse sannan ta daga .yaja iska ya furzar  yace “ya jikin naki?” Ajiyar zuciya ta sauke meqarfi tace “uhm! Da sauqi ina ka shigane tun dazun nakeson ganinka” murmushi yayi yace “wai dayake jiya na kwana da Asmah so batada lfy ne shiyasa nakaita asibiti gashi mahaifiyarta bata qasar balle ta tayani jinyarta dole ni nake zaune da ita”

 

Mimee ji tayi kamar zuciyarta zata hantsilo tsabar tuquqin da mgnr tayi mata a zuciya kawai sai tace “Uhmm!” Ta kashe wayarta, murmushi yayi yakai dubansa ga Asmah wadda taketa baccin wahala yaja fasali ya miqe ya sanya hannu ya duba goshinta ya jinjina kai ya fice daga dakin abun kamar wasa saida asmah ta kwana ta yini a asibiti sannan ta farfado lkcn data farka Aseem yana sallar la’asar ta zubansa ido tana kallonsa har ya idar shima din ita yake kallo kusan 10 minutes kana ya tashi ya nufota ya zare mata ledar ruwan dake hannunta ya cire mata abinda anka maqala mata saboda shigar ruwan itadai kallonsa kawai takeyi.
Sassauta muryarsa yayi cikin sanyi yace mata “sannu yanzun inakeyi miki ciwo?” Sai lkcn ta lumshe idonta daga barin kallonsa taja ajiyar zuciya ta yunqura zata miqe ya riqota da sauri daidaita tsaiwarta tayi ta sanya hannunta ta ture hannun daya riqeta ta nufi hanyar ficewa daga dakin tana layi ya kamota ta sake tureshi ya sake riqeta yace “ ke dallah ki nutsu bakiga bakida qarfi a jikinki ba….” Wani kallo da tayi masa ya sanyashi sunkuyar da kansa ya sake riqe hannunta gam ya janyota suka fito a shiga motar ma taso gardame masa kawai ya sunkuceta yasata ya shiga yaja suka fita a asibitin ya nufi gdansa da ita hakanan taji gabanta na faduwa zywa yanzu ta tsani zaman wannan gida fiye da tunanin kowa to amma yanzun idan tace zatabar gdan ina zata? Innah batanan kuma dama ita daya ce me saurarenta ta kawo mata mafita da rahama da jinqai.

Suna zuwa gdan ta bude motar zata fita ya riqo hannunta da sauri ya sanya hannunsa ya janye  mayafin da taja ta rufe fuskarta dashi ga mamakinsa sai yaga ashe kuka takeyi yaja ajiyar zuciya yace “kiyi hqr da dukkan abinda Hajiya tayi miki insha Allahu zai zama na qarshe” ba buqatarta jin wannan surutun ba  don haka ta bude motar ta fice daga ciki yabita da kallo cikin kwana biyun duk ta rame yaja numfashi ya fito ya budenta qofar ta shiga ta haye saman bata damu da qurar da parloun yayi ba saboda jirin da takeji ta fada bathroom ta sakarma kanta ruwa ta fito daure da towel tana goge sumarta data zubawa ruwa ya shigo ya tsaya jikin qofar cikin wata muguwar faduwar gaba da mutuwar jiki ya zubawa bayanta ido itanma tagansa amma ko a jikinta bata nuna taganshi ba taci gaba da gyaran gashinta ta hada ta daure ta bude wardrobe dinta ta zaro doguwar riga ta sanya ta koma ta dauki turare ta fesa ta shimfida sallaya ta tayar da sallah
Gabadaya bayajin dadin yaren shiru din da takoma yi masa mu’amala dashi rabon da kalma ta shiga tsakaninsu tun ranar da ya kawo mata magunguna ya fice” ajiyar numfashi yayi ya juya ya fice qa’idar yau ba kwanakinta bane hakanan ransa naso amma ya daure ya tafi part din Mimie ya kwanta zuciyarsa a cunkushe da tunani barkatai marasa mafita.
Kashegari Asmah da taji jikinta da qwari ta shirya domin tafiya makaranta tana goge takalmi ya shigo ta dago suka dubi juna shikam yanayinta tsoro yake bashi fuskarta babu alamun rahma ta kawar dakai tace masa “ina kwana!” Fasali yaja cikin kwana uku kalma daya shima bai amsa ba yace “kinajin qarfin da zaki iya shiga makaranta ne?” Dagansa kai tayi shima ya jinjina kai yace “ok ki fito saina saukeki”

 

Batace masa komai ba ta miqe tabi bayansa suka fita ya sauketa a makarantar ta nufi lecture hall dinsu ta zauna Jiddarh ta shigo ta nufota tana mata murmishi ta zauna kusa da ita tace “ni bantaba ganin luv irin naku ba mijin nan naki kwai qwallon shege wlh na taho banma kula dashi ba ya tsaya ya miqomin wannan tarkacan wai na kawo miki na tabbatar kinci sannan na kula dake karna barki ki shiga rana har yanzun ba lau kike da ba”
Tabe baki tayi taci gaba da duba book dinta saida takai inda takeso takai ta dago tace “bani posting letter na naje karba ance tana gurinki” buda jakka tayi ta dauko mata ta duba tare da dagowa da sauri tace “garin yaya? Ba Sir Sunusi na cike ba ko Gen Murtala Muhammad?” Numfashin Jiddarh ta sauke tace “to yazanyi da abinda ya gagari tahuna niqawa mijinki yazo yayi uwa yayi makarbiya ya canza mana burget yasa aka kaimu asibitinsa” daga haka Asmah bata kuma cewa komai ba taci gaba da lamarin karatunta hudu da rabi ya kirata a waya tagani kamar bazata dagaba har tayi ring dinta ta gama ya sake kiranta Jiddarh ta dubeta tace “ki daina haka ki daga mana” dagawa tayi ta kara a kunnenta yace “ina jiranki” kashe wayar yayi ta miqe ta dubi Jiddarh tace “tafiya zamuyi” fatan Alkhairi tayi mata ta nufi inda yayi parking tunda ta taho ya zubanta ido har ta iso ya bude mata ta shiga ya dago ya kalleta kawai yaja motar yayi gaba, maimakon taga ya nufi gdansa sai taga ya nufi unguwarsu ta dago suka hada ido babu alamun wasan da zata tambayeshi dole ta gimtse yayi parking a qofar gdan nasu tuni ta saki fuskarta wani farin ciki ya mamaye ruhinta karon farko cikin watanni bakwai na aurenta da tazo gdan iyayenta.

_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_

_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

_*Fauziyyah Tasiu Umar*_

*ELEGANT ONLINE WTITERS*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button