Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 37

Sponsored Links

MIJIN MALAMA* It’s a paid book pay before you read don Allah…….. For more information via WhatsApp number 08119237616Baya tayi da ɗan sauri ganin yadda idanunsa rufe a gaban ɗarurun jama’a yake ƙoƙarin rungumeta. Abraham ya tsaya cak, zuciyarta ba harbawa na fargabar kar da Mamainsa ta manta da shi a duniya, bayan duk tsayin shekarun daya ɗauka basa tare ya rayuwa ne da tunaninta, duk yake tunanin zai ganta ya duba bata nan. Malama Majeederh a kallon ƙwayar idanun Abraham na farko ta fahimci Little ɗinta ne, Yaronta he came back. Kallonsa ta dinga yi without blinking, shi ma itan yake kallon yana kwaɓe mata fuska, saboda ya fahimci kallon na mene tuhumarsa take, da kuma son gasgata shi ne ɗin ne ko yaya? Wani irin rawa jikinta ya fara duk yadda take so ta riƙe kanta, ta hana shocked shigarta tana mamakin ganin Little ɗinta Yaronta wanda take masa wani irin mugun so…. Rufe idanu ta yi a hankali ta buɗe lokacin da shagwaɓiyyar muryarsa wacce ya saba yi mata magana da ita idan yana son abu ta ji ya ce “It’s me Mamina” Ita dai bata ce komai ba domin tana cikin wani irin farin cikin da zata iya losing control ɗinta a wajan. Fahimtar kamar akwai sanayya tsakanin Abraham da Malama Majeederh ya sanya securities ɗin tsaya daga nufar inda Abraham yake, mai gabatar da Shadol na taron ya kalli Majeederh yana ɗan rusinawa domin bata girma ya ce “Malama Majeederh ke muke sauraro babu lokaci” A kame cikin riƙe kanta ta jinjina masa kanta, tana haɗe fuska tamau kamar wacce ake ganinta ta ƙarasa gaban loud speaker ɗin cikin nutsuwa da wani irin golden voice ta ce “Please bear with us for wasting your time, and we will go directly to what has brought us together here…!” Da ɗan yi shiru tana mai da numfashi, Abraham ji ya yi hankalinsu ya kasa kwanciya saboda daddaɗar muryar Mamainsa daya cika wajan haka kurum ransa ya ɓaci, ya turɓuɗe fuska idanunsa sukai jajur naman jikinsa har rawa yake, ya kasa motsawa sai kafe da gajiyayyun idanunsa da ya yi abubuwa ne fal a ransa. Malama Majeederh a jikinta ta ji yana kallonta maybe yana kare mata kallo saboda tsayin shekarun daya ɗauka bai ganta bane. Ta kalli hall ɗin ta ɗora da faɗin
” رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي* وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي وَاحْلُلْ عُقْدَةً مِّن لِّسَانِي يَفْقَهُوا قَوْلِي…..“
Caraf ta ji an riƙe mata ƙaramin bakinta dake motsawa ta cikin liƙab ɗin fuskarta, wani Irin zaro idanu ta yi waje hankali tashe ta ware idanunta akan wanda ya yi mata wannan ɗan yan aikin da son kunyatata a gaban jama’a. Abraham ta gani tsaye dab da ita ya riƙe mata bakinta sosai sai zare idanu yake yana haɗe girar sama data ƙasa kamar wani ɗan shekaru 30 nan kowa ko 20 bai ba. Kunya kamar Majeederh ta nutse a wajan, idanunta ta ware ta kallesa sai taga yama ɗauke kansa can saboda kar idanunta ya yi masa kaifi ta kuma san taurin kansa sarai! Wani ya ce “Kai wanne hauka ne wannan sbd rashin kunya da rashin addini dake damunka kamar Malama Majeederh zaka riƙewa baki, C’mon saketa ta ƙarasa mana addu’ar” Abraham ya yi shiru mutumin ya ce “Baka ji na ne, ko sai an kira securities?” Gently Abraham ya ɗago kansa ya kalli mutumin ya ce “Ohk” Yana faɗin hakan ya kalli Majeederh dake tsaye kunya ta gama daskarar da ita, gashi bata son taɓa hannun Abraham sbd idanun jama’a, he’s her little son nothing else amma wasu na iya juya hakan. Ya narke mata fuska ya ce “Mami let’s go!” “Ji wani ɗan rainin hankali, ku tafi ku je ina” A haukace Abraham ya saki bakin Majeederh ya juya kan mutumin kamar zai dakesa, cikin turanci ya ce “Stop interfere ko na ci uwarka” Mutumin ya ce “Ni kake zagi? Kai waye, waye ubanka a garin nan” Ya faɗa yana ƙoƙarin kaiwa Abraham duka, Nan da nan Gang team suka shiga tattare hannun riƙe suna zuwa wajan da sauri umarnin Bad boy kawai suke jira, yatsu biyu ya kaɗa musu suka ɗan tsaya ya kalli mutumin sai kuma ya yi wani killer smile ya ce “Ni ba kowa ba ne, bani da uba amma ina da uwa Maluma is my mother, ka taɓa ta kasan waye ni” Yana faɗin hakan ya nufi tsakiyar hall ɗin tare da ɗaukar speaker cikin gadara yana feeling kansa ya ce “Babu uban wanda zai ji muryarta, ku nemi wani ya yi muku” Ya faɗi cikin turanci domin few words ya sani in Hausa language kuma a gurɓace yake magana, kuma yana bala’in son magana da Hausa kawai bai iya bane. Gabaɗaya mutanen wajan suka shiga mamakin wannan al’amarin, yaushe Majeederh ta samu ɗa? Kuma mene haɗin ta da wanda ba Musulmi ba, ma biyin addinin Yesu, ganin faɗa na ƙoƙarin sarƙewa tsakanin Gang team da securities ya sanya Majeederh daurewa ta nufi wajan wani mai muƙami a makarantar magana kaɗan ta yi masa ya ce “Oh! Na fahimta that’s not a problem” Ta jinjina kai alamar godiya ya ce “Sure think” Juyawa tayi ta nufi hanyar fita daga hall idanun jama’a a kanta, a hankali shi ma ya juya tare da bin bayanta yadda yake tafiya fuska ɗaure zaka ɗauka wani babban mutum ne kowa sai ya yi shakkar fuskarsa, lokacin daya fita harabar makaranta tuni ta yi nisa saboda rawar da ƙafarta ke mata, a haka ta isa office ɗinta tare da neman kujerar ta zauna tana kifa kanta saman table ɗin gabanta. Nutsuwa ta ji tana saukar mata a hankali babu shakka Addu’arta ce ta karɓo wacce take yi dare da rana akan Ubangiji ya bayyana mata shi cikin ko wanne hali ne, addu’a ta amsu amma bata taɓa tunani zai dawo mata a halin da yake ciki ba, hankalin ta ya yi masifar tashi ganinsa a wani addini wanda ba nata ba, waye ya sauya mata Yaronta! Waye ya ruguza mata tarbiyyar shekara biyun da tayi cike da kulawa da soyayya? Wane ya dawo mata da hannun agogo baya? Tana tsaka da wannan tunanin ne ta ji an buɗe Ƙofar office ɗin nata tare da shigowa, ta ɗan matse kana ta ɗago kanta a hankali zuba masa idanu tayi kamar yadda yake kallonta a hankali ta harɗe hannunta a ƙirjinta kana kallonta kaga uwa mai nagarta ga yaranta, ganin kallon da take masa ya sanya shi yin ƙasa da kansa ya rasa sukinsa bakiɗaya a hankali ya ce “Am sorry Mami” Bata ce masa komai ta miƙe a hankali tare da nufar fridge ɗin office ta ɗauki gorar ruwa mara sanyi sosai da Glasses cup ta tsiyaya ruwan a ciki sabis gabaɗaya ta rasa tunaninta saboda ganin Little ɗinta cikin wannan halin, jin ta yi masa banza ya sanya ya ƙarasa gabanta tare da zubewa akan ƙafafuwansa ko Grandpa bai taba yiwa haka ba cikin wata damulalliyyar Hausa ya ce “Na ce ka yi haƙuri” Na ce ɗin ya kusa bawa Majeederh dariya ta dake ya marairaice ya ce “Am sorry Jee”
A hankali ta ajjiye cup ɗin bayan ta gama shan ruwan ta ɗan yi ƙyakƙyawan murmushi tana ɗaga liƙab ɗinta sama, domin ita bata taɓa haɗa Little da wasu maza ba, kawai kallon ɗan cikinta take masa dole ta buɗe fuskarta ta ƙyakƙyawan Yaronta ta kuma gyara masa rayuwa! “Stand up”
“Jee, Mami” Ya faɗa lokacin daya miƙe ya zubawa fuskarta sexy eyes ɗinsa masu launin cikin sauri kuma ya ƙarasa wajanta yana zuwa ya rungumeta sosai yana sauke wata mahaukaciyar ajjiyar zuciya ya ce “I miss Mom, bana da kowa” Tausayinsa ya kamata tayi hugging nasa bag tana shafa ƙyakƙyawar sumar kansa murmushi kwance a fuskarta, sun jima a haka sai sauke ajjiyar zuciya yake yana ƙara ƙanƙameta idanunsa, tasan ɗumin jikin uwa ɗaya daɗe bai ji bane yake ɗawainiyya da shi. A hankali ta cire shi a jininta tare da kama hannunsa zuwa duguwar kujerar office ɗin ta nemi waje ta zauna, ta nuna masa kusa da ita amma yaƙi ya zame a hankali wajan ƙafafuwanta ya zauna tare da ɗora kansa a cinyarta. Shiru shiru can ta ce “Your name?”
“Bad boy” Ya bata amsa. Ta haɗe fuska a takaice ta ce “Kai ne Bad boy ɗin?” Bai kalleta ba, bata san kuma dalilin daya sanya baya son kallon nata ba Ya ce “Yes, Jee”
“Call me Mami” Ya jinjina kai ta ce “Real name”
Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ɗago kansa gabaɗaya ya zuba mata idanu yana kwaɓe mata fuska ta harare shi tana janye idanunta ya ce “Wai Abraham, Maa i don’t like it ka sauya mi” Ta ce “Ki not ka, ki sauya mini” Ya jinjina kai ta zame hannunta daga sumar shi jin y daina sauke numfashi ta ce “But it’s beautiful name, Ibrahim or Khalil in Musulmi name” Ya ce “Uhm”
Irin sunan bai wani gamshe shi ba, In a serious talking Majeederh ta ce “Khalil”
“Maa!!” Irin baya son sunan ganin wani irin kallon da take masa yasa ya ce “Am sorry, Bad boy is my name” “Who gave you that name?” Ya ce “Gang team, ni ne leader na team ɗin, Ni nakewa mutane duka na karya kowa Jee” Ta dinga kallonsa kawai tana girgiza ƙafa nan da nan fuskarta ta yi jajur daman ta san ba zai taɓa yin ƙarya ba. Ya ce “Ni nake tare hanya sbd kawai naga ko zan ganki, ni nake shigarwa mutane faɗa, police su kama ni su kaini station amma Grandpa na karɓo ni, Ance ni criminal ne, ina da record wajan ko wanne station na kano har state C.i.d na je, saboda faɗa maka n gudu daga Rushia zuwa Naija” Jin shiru yasa Abraham ɗago kansa ya kalli Majeederh ganinta ya yi ta tura kanta tsakanin cinyoyinta ya dinga kallonta ya ce “Jee” Ta jima kana ta ɗago kanta a rikice ya durƙoshe gabanta ganin fuskarta ta rine ta yi jajur ya ce “Am sorry Maa, Na tuba” Sosai take Mamakin yadda Little bai manta komai nata ba, wato ya fahimci ranta a ɓace a hankali ta ce “Wajan wa ka ke nan?” “My Grandpa, shi ne Pasto na church” Gabanta ya faɗi ƙirjinta dinga ɗagawa da gaske Little ɗinta Christa ne? Wani ya sauya masa addini ko daman can shi ne ba musulmi bane? Ta ce “Full name?”
“Abraham Denial David” Ta runtse Idanunta tare da yin jikin kujera ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Ta dinga maimaitawa hankali tashe. “I hate my father”
Bata kula da maganar Father ɗin ba ta ce “Your mother where’s?” Ya kwaɓe fuska yana ɗan ɗage mata gira bai ce komai ba. “Ka yarda kai Bad boy ne?” Ya jinjina kai ya ce “Yhhhh” “Kai Mahaukaci ne?” Nan ma ya ce “Eh” Ta dinga kallonsa cike da tausayawa kana ta miƙe tsaye shi ma ya miƙe Ta ce “Jeka gida” Ya marairaice mata ya ce “Jee zan bika, I will sleep with you today, Mami, I miss you so much” Ta kalle shi bata ce komai ba har ta nufi wajan motar ta, yana ta mamaki Maminsa tayi kuɗi ko me? Ganin zata shiga mota ya ce “Kawo key ɗin, I’ll drop you” Frm head to toe ta kalle shi tana harɗe hannu a ƙirji ta ce “Wani ɗan kwanini da kai ina ka iya driving?” Kasancewar da Hausa tayi maganar sai bai fahimta ya kalleta da kasalallun idanunsa yana riƙe da murfin motar ya ce “Me?” Da Turanci ta ce “Idan zaka iya Hausa ka iya Little ban iya surutu da turanci dama dai larabci ne” ba tare daya fahimta ya ce “Ohk” A hankali ya zuba hannunsa a aljihu yana kame fuska ya ce “Let me drive you and drop you off at home” Ta ce “Wai kai yaushe kaga ɗan ƙaramin yaro yana driving? Kawai ka zubar dani lallai yaron nan” Ta faɗa cikin turanci sbd bata son wani surutun kuma. Wani irin Expression Abraham ke kallon Mamin tasa, a ransa yana ƙara maimaita kalmar yaro Ta ce “Kabari ka ƙara girma da wayo ka san halin kanka zuwa matakin aure” Calmly ya ce “Ohk” Yana tsaye harta fice daga cikin makamatar yamma lis, ya dinga kallon ƙofar kana ya cire hannunsa ɗaya daga aljihu ya dinga hargitse sumar shi. Gang team ɗin suka dinga dariya Taj yadda riƙe ciki ya ce “Gaskiya Mamin nan taka ta rainka da yawa, wai kai ne yaro?” John ya ce “Da kana kula babies wata rana ta ganka da wata a kwance manne kamar chewing gum ai ba zata ce maka yaro ba” Joshua ya ce “Wai kabari ka ƙara wayo sai ka yi driving nata, Goodness!” Abraham kallon su kawai yake. Taj ya ce “Amma seriously i like ur mother classes one Educated women, amma mene wannan a fuskarta? Naso ganinta” John ya ce “Amma dai ƴar rainin hankali ce wai kai ne yaro?” Gadan-gadan Abraham ya yi kan John tare da shaƙe masa wuya kamar wanda ke ƙoƙarin kashe shi “Am sorry Bad boy, sorry” Sai dai Numfashin John ya fara sama kana ya sake shi yana pointing nasa da hannu ya ce “Ko Grandpa ba zan ƙyalle ba akan Malumana Mamina, Jeena balle kai” Yana faɗin hakan ya shige motarsa ya mance kalmar yaro ya nufi gida wajan Grandpa cike da farin ciki yaga Mamainsa….. Wani irin kwara amai Aliyu yake kamar kayan cikinsa zai fita lokaci ɗaya ya fita hayyacinsa, Latifa ta dinga masa sannu ko kulata bai ba, da ƙyar ya wanke bakinsa a sink yana mai da numfashi ya fita parlourn daya zage ya gyara shi, zubewa ya yi saman kujera yana ƙaro gudun A.c Latifa ta ce “Wai lafiya? Mene ya saka amai?” Ya yi mata banza daga ƙarshe ya miƙe zai bar parlourn ta ce “Please Aliyu what’s going on? Muje hospital” Ya kalleta kawai ta ce “Please Sweetheart” Ya girgiza kai ya ce “Kyankyaso cikin abincina Latifa? Kyankyaso dai na cikin toilet ki haɗe kika dafa abinci da shi, Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Ya dafe kansa yama rasa me zai ce Ta ce “Kayi haƙuri ban san yaushe ya shiga ba” Da ƙarfi ya ce “Haƙuri haƙuri, I’m tired of your behavior, I feel sorry for you” Yana faɗin hakan ya fice daga gidan bakiɗaya he need to see a doctor ji yake kamar komai na cikinsa zai zube. Cikin dare Latifa na bacci ta ji an jawota ta yi saurin buɗe idanu tare da kunna switch haske ya bayyana, Suka haɗa idanu da Aliyu ta ce “Lafiya?” Da mamaki ya ce “Are you exlty questioning me?” Ta yi shiru ya ce “Ke ba matata ba ce?” Ta haɗe fuska ta ce “Yanzu mene?” Ya miƙe tare da jingina da frame ɗin gadon ya ce “Why are you answering my questions with a question?” Ta ce “Naga ai dare lokacin da ko wanne mai rai yake hutawa yana bacci gajiya, 1/24 idanun Mutum biyu” Ya jinjina kai ya ce “Ko?” Ta ce “Wallahi fa, mu kwanta mu yi bacci” A hankali ya ce “To” Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye yana jin mararsa kamar zata cire saboda azabar ciwo haka ya raya dare ido biyu tar sai asuba ya yi wanka tare da nufar masallaci a hankali suka haɗu da Abbu suka gaisa… Misalin 9:00 na safe Majeederh na bacci sbd jiya ba tayi baccin kirki ba tunanin yadda zata sauya Little kawai take ya dawo musulmi kamar ita da sauran jama’a, gefe guda kuma maganganun Uncle Bello da ya zo har gida ya yi mata ta tas akan taƙi tana yawo ta gaggauta fito da miji suka taro sukai mata tsaye a zuciya wanda ya hanata bacci sai asuba. tashin da Aaliyah ke mata a gigice ne ya sanya ta buɗe idanu Aaliyah ta ce “Anti Jeederh ki tashi” Ta kalli Aaliyah alamar “Lafiya?” A ruɗe hankali tashe ta ce “Wallahi Wani ne ya zo yana ta kwalla kira wai Mami, Malumana, hadda Jee” Majeederh tar ta buɗe idanu ta ce “Tun yaushe?” Ta ce “Tun Ɗazo fa, am sure Abbu bai ji ba da tuni ya fito” Jikin Majeederh duk rawa yake gashi kayan bacci ne jikinta ta ɗako hijabi ta saka ta ce “Shi da waye?” Ta ce “Shi kaɗai” Ta yi gaba bata saka Liƙab ba, gabaɗaya shap ɗin jikinta juyawa yake sbd ɗan saurin da take, Aaliyah ta rufa mata baya, tana zuwa compound idanunta ya sauka akan shi daga shi sai armless white colour sa gajeren wando gargasa duk kwance a fatar jikinsa gashin kansa a hargitse sai surar jikinsa da ƙarfafan maza ta bayyana, daga nan idanunta ya sauka akan wasu dalla dallan mahaukan matoci a ƙofar gate ɗin su daga waje, kafin ta yi magana taga ya kama katanga ya diro cikin gidan nasu tana ƙoƙarin juyawa tana girgiza masa kai amma ina tuni yayo kanta idanunsa cikin nata yanzu zuwa ya rungumeta sai gabaɗaya ta shige jikinsa duk girmanta hadda empty space daidai nan Abbu da Mami suka fito compound ɗin…

Allah ya nuna mana Monday Lafiya….. Wanda ba zai jira ba mu haɗu Arewabooks

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button